Showing 15001 words to 18000 words out of 24149 words

Chapter 6 - MUMINA KO AZZALUMA 1 By Sadi-sakhna.txt

18 Oct 2025

468

neman alfarma a wajensa kan ya haɗaku aure kaida Safeenah saboda ƙarin danƙon zumunci. Ka girmi auren dole,amma dai bai yada maganarta ta ba yabani saƙo na faɗamaka shin ya kake gani,saboda yasan tsakaninka da matarka yanda kuke son juna,kada ya amince kai kuma zuciyarka ba haka bane azo a samu wata matsala ta bullo. Shin ya kake gani zaka aureta ko kuma ......."

"A ɗaura auren kawai duk sanda suka shirya itama ta shirya kuma kuka shirya,ni zan wuce office ummi idan muka gaisa da Mama. Ina fatan ita ta kasance alkhairi"

"Tohh uhmm banace komai ba,to yaushe kake ganin zakaje wajenta kaji mai da mai take so saboda tunda ka amince yanzu a matsayin mai shirin zama matarka take ba ƙanwarka ba,dolene koda sau ɗayane ka tashi takanas kaje ka kuyi magana ta fahimtar juna.

Wata ƴar dariyar takaici yayi tareda kallon agogo.

"Hhhh haba ummee inje wajenta kuma,nace da ita me? Ba dama naji labarin ana cewa wannan ne burinta,to tunda ta samu ai murnar dazatayi ma ya isheta,banda bango ya tsage kinsan Ummee da bazan bar ƙadangare ya samu damar shigowa ba. Kawai kuyi komai yanda ya dace,infact ni inada tafiya abroad ma zuwa jibi,kuma zan iya yin Two month a can,kafin nadawo sai kuyi duk abinda ya dace"

Yana gama faɗin hakan ya ɗauki jakarsa tareda gyara rigarsa ya bar bangaren.

Ɗan murmushi Hajiya Ummee tayi tareda jijjiga kai.
"Hmmm namiji dai idan bayason abu ko? Ina tausaya miki Hunaiza daga ke har Safeenah,wanann gurgun burin zuciyar taki babu abinda zai haifar maki sai ɗa marar ido. Ace kai bakada zabin kanka saina ƴaƴanka,kuma in antabasu kaman an soka maka mashi. Duk da ban taba haihuwa ba amma rashin kawaicin Hunaiza yayi yawa"

"Ummee dawa kike,Da maman Safeenah koh,hmmmm bakiga ma rawar kan da Safeenah take a makaranta ba,wai yau mamanta tayiwa Abba magana kan aurensu itada Yah Ahmad,wai tariga ta tabbatar ma dolene zai amince,har ta fara yiwa mutane burgar wai takusa zama Mrs Amjad,bakiga ba har sabin ƙawaye tayi. Kullum ina faɗamata ta amince da saurayinta Ridwan ta ƙyale batun ya Ahmad amma taƙi sam,ya Ahmad bazai taba amincewa ya aureta ba"

"Amincewa kuma na nawa,yariga ya amince ai"

Zaro ido tayi tareda dafe ƙirji kafin tace.

"Ehh ya amince Ummee,kuma Safeenah kaman ta sani tace tanada tabbacin dole zai amince.....mtsss ni Ummee anya kuwa Safeenah na Baaba Hunaiza ba Asiri sukeyiwa Yah Ahmad ba,domin daga yanayin confident ɗinta alamar saida ta shirya kafin ta......"

"Ke Nimrah to kuma surutunnaki yana shirin wuce gona da iri,zato ance zunubi ko ya kasance gaskiya,kuma kada ki manta Safeenah ƴar uwarki ce koma ya take,haka uwarta itama uwa take a gareki tunda cikinsu ɗaya da ubanki. Inma asiri suke Allah ya ganar dasu su daina,inkuma shi suka zaba zai basu nasara ba Allah ba nan ma ga wajennan mai fili da mai doki sau suyita sukuwa. Kedai kiyi shuru da bakinki ki zubawa sarautar Allah ido,na sanki da shegen surutu,da Zainab ce ba ruwanta,amma ke kam hmmmm"

Da haka Hajiya Ummee ta kwa'bi Nimrah daga 'barin zancen da takeyi zancen ya mutu a wajen.



Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 14_⚫


Tunda yaje Office ɗin kaman abin arziƙi ya wuce kansa tsaye ya zauna akan kujerar amma ya zubawa wasu takardu ido ya gagara rubuta komai a cikinsu,gabaɗaya ma tunaninsa baya cikin office ɗin yana wata duniya daban.

Ƙarar wayar security line ne ta firgitoshi ya kalli wajen tareda miƙa hannu ya ɗauka.Gaisheshi akayi daga ɗaya bangaren ya amsa a taƙaice tareda nunawa wanda ya ƙirashin yatafi kai tsaye da bayaninsa kada ya bata masa lokaci.

"Am sir batun bincike dakace muyine gameda hoton daka turo mana,maganar gaskiya abin ya ɗauremana kai,mai wannan sunan mutane dayawa sunce tayi aiki har anan companyn a kaduna,amma kuma sam babu wani record nata a cikin bayananmu,kuma ance bata daɗe ba ta daina,sannan zancen ya jima zaikai shekara shida haka. Toh amma yallabai wannan ba hoton madam bane,mai yakawota yin aiki anan companyn to kafin ku haɗu,dama kasan tayi aiki anan ne kafin ka aureta?"

"Kaga bincike nasa kayimin ba tambaya nace kayimin ba Naseer,kawai na baka nan da wasu lokuta ka ganomin menene dalilin dayasa taje can ɗin aiki,wanne aiki tayi,adadin wanne lokaci ta ɗauka a garin. Babban ma'aikacina mai wannan aikin yanzu haka bashida lafiya amma bari zan haɗaka da wani anan wanda zai tayaka. Zan tafi germany akan wani aiki idan nadawo zan nemeka gameda ƙarin bayani. Kafin sannan please focus and found reasonable things"

Bayan sunyi sallama wayar office ɗin Saleem yaƙira ko yana nan,haka kawai yaji yanaso suyi magana koda kuwa na faɗane da suka saba wani lokacin. Bata gama ringing ba ya katse tareda tashi ya nufi office ɗinnasa da kansa.

Da sauri ta fito daga cikin gidan da makullin mota a hannunta,duk da tana Ƙoƙarin saita kanta amma kallo ɗaya mai hankali zayyi mata ya tabbatar hankalin ta ba'a saiti yake ba.

"Sauri kike ina zuwa haka,ko labarin zan shigo cikin gidan kai kikaji har kin fara birkicewa"

Harta riƙe maruƙar ƙofar zata buɗe sai kuma ta tsaya tareda juyowa ta kalli mai maganar.

Safeenah ce sanye da riga da wando na palazo tayi rolling ɗan ƙaramin gyale a wuyanta,farace amma sam Safeenah batada jiki,haka zalika kyau na fuska ma saidai muce alhamdulillah kawai.

Ƙaremata kallo Surayyah tayi daga sama har ƙasa kafin tace.

"Wanne gidan zaki shigo?"

"Cikin gidanki mana,hala to bakida labari Yah Ahmad ya amince da aurenmu,ki shiryar tarbata a matsayin kishiyarki nan da wasu watanni masu zuwa,bake kina sunkuyar dakai wai ke ga mutuniyar kirki kingama sace zuciyarsa baya ganin kowa saike ba? Tun ba'aje ko ina ba gashi ya dawo daga rakiyarki akalar hankalin sa ya dawo kaina. Ki zuba ido kiga yanda zan shigo gidan kallo ma sai yagagareki samu daga wajensa"

Tana maganar ne tana jujjuya ido tareda rangwaɗa kaman an ciro tarwaɗa daga cikin ruwa.

Wata arniyar dariya da Surayyah ta sheqe da itane yasa Safeenah tsayawa da maganar tayi sororo tana kallonta.

"Dama keɗin kina maganane,ai bansani ba sai yau. To in gidane waya hanaki shiga,yanzu ma gashinan kije ki ɗauko kayanki ki shiga mana.Kinga in bama nan mun samu mai gyaran gidan dayin abinci. Dama yace bayacin abincin ƴan aiki,faɗuwa tazo daidai da zama,naji ance ke ƴar uwarsace maybe zaici naki musamman in kika zama matar tasa."

Buɗe motarta tayi tashiga,har tayi ribas zata fita ta leƙo da kanta inda Safeenah take daskare tace.

"Amm idan mai gadi yazo kice yabaki key guda ɗayane wajena,inkin masa abincin ki ajiyemin,amma kinsan cikine dani bana cin curry dan haka kada kisaka"

Ɗan murmushi tayi bayan ta mayar dakan tareda cewa.

"Nice mutuniyar kirkin ko? Zaki kuwa gane kuranki,zakuna suna faɗa kina ƴar ƙaramar akuya zaki shigo tsakani. Ina tausaya miki sosai,i swear you may suffer girl"

Waƙar davido tasake a motar,sautin yana tashi da ƙarfi tana ni tana karkaɗa kai,kaman ba dambun cakwakiyane a gabanta ba.

Bayan ta bar wajen Safeenah ta daɗe kafin ta rufe bakinta wanda tasakeshi batareda tasani ba,kanta ta ɗauke daga kallon inda motar tabi kafin ta nufi sashensu,a ranta banda saƙe saƙe babu abinda takeyi.

Babu sallama tashiga falon,Hajiya Hunaiza ce zaune itada wata ƙawarta Wai ita Madam Aliya babbar matace amma daga ganinta kasan wayewa tayi wani abu waishi zama a jikinta.

"Tana saida duk wani nau'i na kayan mata,mallaka dakuma na kaucewa hanya. Sannan tana haɗa kayan kitchen kayan ɗaki da dukkan abinda yashafi amare in mutum yanaso. A online suka haɗu,tace zatazo Abuja Hajiya Hunaiza taroqi akan tazo su gaisa"

Baki a kumbure tashigo falon,kai tsaye inda hajiya Hunaiza ke zaune ta nufa tareda kwanciya akan cinyarta.

"Ohh ke kuma daga ina haka,hala kun sake faɗa keda Nimrah,domin nasan haka kuke saikace ƙananun yara"

"Ahah ni banganta bama yau balle muyi faɗa,daga sashen yah Ahmad nake,naje na tabattarwa Surayyah zan zama kishiyarta,amma saikuma naga kaman abun bai dameta na,har cewa tayi idan inaso yauma na dawo sashen bai dameta ba"

"Hhhhhh ke har yanzu yarinya ce,ya dameta kenan tunda har tatsaya ta saurareki kuma ta faɗamiki haka, babu wata mace da zata samu miji kamar Ahmad za'ayi mata kishiya tace kuma bai dameta ba,musamman ma ta yake bata kulawa taga ya sauya ya daina bata,ƙarshe yace zai ƙara aure kuma bataji komai ba? Wannan ai zancene. Shakuruminki ƴar nan ai watan damu damarne ya kama. Zan haɗamiki magunguna masu kyau da tsada,ai tunda ya amince shine farkon babbar nasararmu,wani abun saima kin shiga daga ciki. Inta kama ma waje kawai zamuyi da ita. Kiyi zamanki keda yayanki,gaba in kika tara zuri'a kuma mu fara tunanin malllakar campanoni"

Duk abinda suke madam Aliya tana kallonsu banda murmushi babu abinda takeyi.

"Hmmm ai kisha kuruminki yarinya daminki ne ya tsinke a gindin kaba,indai mallakarsane kuma kuna tareda ni kaman kunyine,ke iyayensa ma saikinga dama yaje inda suke"

Kallonta Safeenah tayi saikuma ta kalli hajiya Hunaiza akan ta gaskata mata zancen matar. Ɗaga mata kai tayi alamar eh,wanda hakan yasakata sakin murmushin daɗi.



Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 15_⚫




Tana shiga ɗakin jefar da gyalen tayi a kan katifar,bata ce komai ba kuma batada niyyar faɗar.

Duk abinda take zeezah tana kallonta wacce ke zaune a mini seater dake ɗakin.

Daga yanayinta tasha ruwan jikinta,dan tasan jira take ta kulata ta sauƙe mata kwandon dayake kanta.
Ganin tunda tashigo bata kulata ba yasa ta kalli inda take cikeda ƙufula.

"Kinga shirmenki abinda ya jawo ko,wai sau nawa zan faɗamiki ki daina sakamin alcohol ingredient a abin sha na,ina tsaka da yin shirye shirye gashi kin ruguzamin su. Ahmad yashigo ɗakina jiya amma bansan mai nace masa ba,ina tunanin nafaɗa masa abinda yafaru. Yanzu shikenan yasan koni wacece ta ainihi,abinda nake boyewa yasani,hatta kayan danayi aiki dasu sun baci da jini a gida na jefarsu kuma yagani ya dauka har yakai asibiti anyi masa bincike akai"

"Asibiti kuma ya akayi suka gane,sannan kuma mai zasuyi dashi a asibiti?"

"Hmmm you see hala kina manta dawa muke buga wasane,Amjad ne fah ko kin manta ne. Mutumin da ta wani wajen yafima shugaban ƙasa iko dakuma access dasamun abinda yakeso saboda yanada kuɗi. Yanzu haka zancen danake miki sunbi diddigin mutumin dasuka saka bibiyata yana asibiti a halin yanzu"

"What to kuma kika barshi idan ya farka ya faɗamusu mai yake faruwa fah?"

"Shikenan mana tawa taƙare,duk gadar zaren dana saƙa ta warware idan har ya tashi,amma yanzu ni bashine damuwata ba,ahmad ɗinne domin bansan iya adadin sirrina da yasani ba. Banida tabbacin ma ko ya faɗamasa mai yagani kafin ya faɗa doguwar suma"

"To inaga in abin yafi ƙarfinmu kawai mu faɗawa big Mommy,ita nasan guarantee zatasan abinyi"

"Mtss anya kuwa,nifa kinsan bason faɗamata shirgina nake ba,saboda haɗarin matar nan na kula ke baki gama sanin zurfinsa ba. Idan har matsalata zata kawo cikass a bayyanar sirrinta to zatayi kashe ahmad,ke har nima inada tabbacin zata iya kasheni ba iya shi ba"

"To kafin abun yakai haka ke ki kasheshi mana kawai shida na kwance a asibitin,kinga kinyi maganin abun,sannan ga babbar dama zaki mallaki manya manyan kadarori na ƴaƴan ma dukka ki maidasu ƙarƙashin sunanki,ko ya kika ce?"

Jijjiga kai Surayyah tayi tareda cewa.
"Kashe ahmad baya cikin jerin tsarina,infact ko kin manta makasudin shirina shine zama dashi?"

"To amma kinsan haka bazaiyiyu wu ba,domin kinriga kin makaro yagane ƙarfin dafinki,ba yanda za'ayi ya sake ya zauna dake kaman komai bai faru ba irin na da matuƙar yana cikin hankalinsa. Surayyah nasan ƙarfin taƙadarancin ki amma wannan yanzu yazama tarihi,a baya bakida wani lago da Za'a karyaki,amma yanxu kinada shi shine ahmad,domin zuciyarki tana danƙare da sonsa,uban ƴaƴanki yayi zurfi a zuciyarki batareda kinsani ba. Kuma shine babban lagonki wanda zai jaki ƙasa warwas.

Cikin takaici zeezah take maganar,kuma ita kanta tasan maganar tata gaskiyace,tabbas tana babban lago a yanxu wanda da batada shi ,saidai abinda zeezah tayi kuskure shine ba ahmad bane logonta,wani abu ne daban wanda ya kasance sirrin ta,ita kanta tasan abinda ta aikata zatayi nadama wanda zayyi tacinta idan bata maganceshi ba,to amma yazatayi,batada ikon magance abin. Hukuncinta ɗaya shine wannan abun yayi ta damun zuciyarta har zuwa ranar dazai kaita ƙasa.

Jakarta ta ɗauka cikin sanyin jiki zata bar ɗakin.
Kallonta zeezah tayi da mamaki tareda cewa.
"Ina kuma zuwa daganan?"

"Akwai abinda zanje nayi wanda nake tunanin shine Backup to my solution"

"Okay to shikenan saikin dawo,nima yanzu haka akwai inda zanje"

"Sannan idan na dawo ki shirya amsa query na abinda kikayimin kinsanni bana yafiya"

Cikin tsuke fuska tayi maganar daganan tafice a ɗakin. Jinin jikinta zeezah tasha tana ƙiƙƙifta ido,inta dawo zasu kwashi ƴan kallo kenan,kokuma tashirya mata wani abun ta bazata ji daɗinsa ba. Duk da Surayyah ƙawarta ce amma tana shakkarta sosai.
Bayan ta tada motarta hanyar barin gari ta nufah,saida tayi tafiya mai ɗan nisa kafin ta karya akalar motarta daga kan titi tashiga cikin jeji. Tafiya takeyi har saida tazo wani waje inda mota bazata shigaba. Tsayawa tayi da motar ta kasheta kana ta fito daga ciki ta rufeta.

Tafiya tafarayi kanta tsaye zuwa cikin dajin. Daga yanda take tafiya saika ɗauka dama tasan inda zata nufa.

Bakin cikin wata duhuwa hanyar data biyo ta kawota,daga nan ma wata hanyar ce tashiga ciki,amma ta yanxu tafi ƙanƙanta da duhuwa fiyeda wanda ta biyo.

Ajiyar zuciya tasake kafin tasaka kanta zuwa cikin duhuwar.

Tafiya take tana kallon inda zata saka ƙafarta,wajen shuru ne dashi,babu komai sai kukan wasu irin tsuntsaye da ba'ajin irin kukansu a cikin jeji haka normal bare kuma cikin gari.

Babu alamar tsoro a fuskar Surayyah hartazo bakin wani ƙaton dutsi da baka iya ganin ta inane wajen shirgasa,domin tako ina a mulmule yake.

Waigawa tayi gefen damanta idonta yakai kan wata ƴar ƙwarya a can gefe da bakin kogon. Wajen ta nufah ta tsugunna a gabanta.

Wata allura a ɗauka a gefen wajen ta dandala a cikin ƙwaryar.Hoton ƙofane ya fito a cikin ƙwaryar,hannunta tasaka ta murɗa tareda turawa ta buɗe.

Tana turawa wata murya ta ƙyalƙyale da dariya kaman ta birirrika. Dutsen dake gefenta kuma ya fara girgiza yana sauyawa. Lokaci guda ƙofa irinta cikin ƙwaryar ta bayyana a jikin dutsin.

Tashi tayi taje bakin ƙofar ta tura ta buɗe,kanta tsaye tashige cikin kogon dutsen.

Maimakon kogon dutse gidane ya bayyana a gabanta ta ciki,matsakaici mai kyau sosai. Kujera tagani a gaban tebur ta zauna tana jiran maigidan ya fito,wanda da alama ba mutum bane,koma mutum ne to ba ƙaramin shu'umi bane kuma mai aiki da manya manyan aljanu.

" yau kuma kece a gidana?"

Wata matace ta bayyana a gabanta wacce bazata wuce shekarunta ba,sanye da doguwar riga fara.

Kallonta Surayyah take batareda tace mata komai ba,saikuma ta numfasa sannan tace.

"Uhmm nice wani abune yake tafe dani nakeso kiyimin Inayah"

Itama zama tayi a ɗaya daga
cikin kujerun dasuke wajen.
"Dama baki manta kwatancen danayi miki ba kenan,a yanda muka rabu kina kiɗime nayi zaton bazaki gane wajen ba. Duk da daman yaƙinin son neman wajen shiyake saka a ganshi. Yanzu dai mai yake tafe dake kike so nayimiki. Kinkuwa sa'ar samuna,dan yanzu haka shiri nake zan tafi wajen mijina a syria yana nemana,kuma zan daɗe ban dawo ba."

Kallon ta Surayyah tayi da nutsuwar ta kafin tafara karanto mata mai ya kawota wajenta.




Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 16_⚫



"Alfarma nakeso kiyimin,wannan matar zaki nemomin,a ina take wanne hali take ciki?

Tana gama maganar ta miƙamata wani hoto,hannu tasaka ta karba tareda yin murmushi.
"Wannan ai......."

"Ehh itace inaya,nayi mata wani abun da bana tunanin zan iya mantawa,bayan mun rabu a bakin makaranta kince idan inada wata alfarma na ƙiraki zakiyimin to ga wanann ki taimaka ki nemomin inda dake dan Allah,kafin ki tafi wajen mijinnaki"

"To shikenan bari zan duba a nahiyar nan da kewaye ki bani nan da kwana biyu,tunda bansan inda take ba saina duba"

Tashi tayi tabi wata hanya a gidan,jimm kaɗan sai gata ta fito da tire a hannunta. Ajiyewa tayi a gaban Surayyah,kayan marmari ne masu kyau sau kuma wani jug da ruwan inibi a cikinsa.

Kallon abubuwan Surayyah tayi kaman mai tantama,duk da a fuska tana nuna jarumta amma kallo ɗaya mutum zai mata ya tabbatar a tsorace take da inda taken.

Ƴar dariya Inaya tayi tasake tura mata tiren gabanta a hankali.

"Habadai Ƙawata da alama har yanzu kin kasa gasgata cewar ni bamai cutarwa bace a gareki,koda wani zaiji tsoron zama kusadani a tunanina bandake ciki,kada ki manta tun aji ɗaya na makarantar boarding muke tare a matsayin aminai har muka gama. Duk da cewar ba jinsinmu ɗaya ba amma kinsan bazan cutar dake ba. Naga kinada cikine shiyasa naje gonarmu na yanko miki kayan marmarin dazasuyi miki amfani. Ni ban tambayeki bama hala kinyi aurene?"

"Uhmmm nayi aure,da bansan ke wacece ba shiyasa,amma danasani kinsan yanayin bazai zama kaman da ba"

"Ƴar hararar wasa inaya tayi mata kafin tace,hmmm kin manta a makaranta kaman bakece mai nuna kece shugaba ba,ba wanda kika raina kamanni,amma yanzu ni kike taoro?"

"Uhmmm rayuwar makaranta ba,inna tuna nakanyi dariya ni kaɗai,saidai nakanji wani iri idan nasake tunawa ashe ƙawata uda ɗaya tall danayi rayuwa da ita na shekara shida ba jinsi na bace,abin yana ɗauremin kai kaman a mafarki. To ma taya kika boyeminne ko kika boyewa kowa a makaranta har malamai?"

"Wannan ba sabon abu bane kuma ba kaina farau ba,domin ɗauke kewa ko kuma samun wata ƙaruwa mukanyi cuɗanya da mutane tsawon shekaru batareda sun sani ba. Ko a makarantar ma bani kaɗai bace akwai wasu,saidai bama cutar da kowa,mukanyi har meeting na abinda yake faruwa damu da daddare idan kunyi bacci."

"Ina fatan dai yanxu kin daina hulɗa da wannan jinsinnamu wanda ba nagari ba dana sha gagargaɗinki ki rabu dasu"

Inaya tayi maganar tana ɗan ɗaure fuska.
Wani juyi da ido Surayyah tayi kafin ta ɗora da cewar.
"Haba no wonder ni sai yanzu ma abin ya dawomin,taya kikasan mai nake aikatawa,duk bankawo haka ba sai yanzu,ashe danke ba mutum bace. Karki damu Inaya wannan duk zai wuce,ke kanki shaidace da inda na fito,idan ba haka ba to da yanzu bana raye"

"Karkice haka Surayyah ita mutuwa ai lokaci ce,idan tazo ko ka kauce hanya domin kare kanka ko baka kauce ba to saita ɗaukeka"

"Uhmm to nagode Inaya ni zan tafi kar Ahmad ya nemeni,sai kuma yaushe zaki dawo?"

"Kiyi haƙuri a yau ne ganawarmu ta ƙarshe,inna tafi ba lallai nadawo yankinnan ba,yanzunnan ya aiko min saƙo kan na taho da komai nawa,saidai idan nazo yawo in Allah yaso zan nemeki. Saƙonki kuma inna bincika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login