Showing 30001 words to 33000 words out of 35410 words

Chapter 11 - AKAN AIKINA Complete BY UMMU MAHER.txt

Kallon Mumtaz ai takanas ta taso ta zauna kusa da Muta'z Amman bai san Meema tana wani Abu wai shi kishi ba.










Ummu Maher ce














*Vote*
*share*
Comments👌🏻
*_AKAN AIKI NA_*





By
_Ummu Maher(Miss green🍀)_




Littafaina


Uwar gidana
Auren dole
Ruhi d'aya
Inayatullah
Farouk
Kaddarar rayuwa ce
Asanadin Abayar Sallah
Akan Aikina
Jameeler
Doctor Nawwara




_gaskiya ina jin dad'in yadda kuke nuna min k'auna mussam duk masu yimin post.


*Kaltum Khanna*
*Dr Amira*
*Nabiha Aminu*
*Rukayya gawata*
*Hjr L Sadiq*
*mmn teddy*
*Momin Shukura*
*Nana M sha'aban*
*Fauziyya d s*
*Autar Mama*
*Ummu najma*
*koise baby*
*Bilkisu*


Da duk masoya na wad'anda ban samu damar ambato sunansu ba.


Please nayi mistake tun a baya na page maimakon in saka 70 na saka 65har sau biyu yanzu zan tashi a 70.






70
Da sauri Hajjo ta taso ta rungumeni tana cewa"Allah Sarki jikata gakinan kamar Ku d'aya da Muta'z."


Gaba d'aya ban gane inda zancen nasu ya dosa ba sai da Mlm yayi mata bayanin komai sannan na tashi da Sauri na rungume Hajjo harda Mai Marta ba ina kuka Ashe Mahaifiyata tana da gatanta haka ta zauna cikin talauci da k'uncin rayuwa sannan ta zauna ba tare da tasan danginta ba ko kuma ta nemesu ba, sai yanzu da Allah ya kawo k'arshen komai.








Ai aranar Hajjo a gidan ta kwana ana ta hira ni kuwa kaina na kan cinyar Hajjo a haka har bacci ya d'aukeni Umma kuwa suna ta bada labarin yadda aka yi aka yarda Umma na a bola.






Ban San ya akayi Hajjo tasan abinda ke tsakanina da Muta'z ba,ai kuwa Hajjo cewa ta yi a satinnan za'ayi Auren don hankalin Muta'z ya kwanta shikkenan ya had'a Auren y'an uwan juna.




Ranar kamar in Zane tsohuwar nayi don na lura fitinanniyar tsohuwa CE,Mai Martaba kuwa ya ce Ummana ta dawo Gidan sarauta kusa dashi yana ganinta hankalinsa zai fi kwanciya,Umma ta CE yayi hak'uri soon zata dawo.




Yau kusan sati 1 kenan Muta'z baya gari,don ya kwana biyu baizo gidanmu ba,nima ban damu ba don kwata kwata baya gabana har yau idan naganshi wani irin mugun haushinshi na keji sai dai kwata kwata bana iya had'a idanu dashi don tsoron I'danunsa na keji.




Fulani kuwa sai Jana a jiki ta ke yi,na rasa me yasa nake son matar don tana burgeni sosai.








***
Duniya fa ta juyawa Murar sosai don Meema ta rikita lissafinsa don ta ce matuk'ar tana numfashi dole ne ya Aureta,a yanzu kuwa har ya kai kud'i harda sarana babu Wanda ya Sani,saboda tsabar zubar da aji Meema da kanta ta amshi kud'inta harda na sadaki kuma an saka sati2masu zuwa asha biki,bak'in ciki kuwa Murat yasha sa wannan wani Irin Aure zaiyi babu albarka manya ko kad'an a ciki,gashi don tsabar abin kunya wai amarya CE ta ke amsar kud'in Aurenta da kanta.




A yanzu kuwa wasan b'uya suke yi da Muta'z don besan abinda zai CE masa idan sun had'u ba,ayanzu yayi nadamar duk abinda ya yiwa Amininsa kuma d'an uwansa Muta'z yasan Allah bazai tab'a barin hakkin Muta'z akansa ba,ya zama dole ya nemi yafiyarsa ko Allah zai dubesa,don yasan Auren Meema k'addararsa ce don Bai tab'a tunanin zai Auri mace Y'ar duniya kuma fasik'a ba.




A duk duniyar nan babu yarinyar da ya ke so, kuma yake k'auna kamar Hanan ita kad'ai ya ke so ya mallaka a matsayin matarsa uwar y'ay'an sa sai dai yasan Hanan ta yi mishi nisa Nisan da bazai iya kamota ba,don fasik'i baya Auren wadda ba fasik'a ba,yafi kowa sanin halin Hanan yarinya ce mai ilimi,tarbiyya,da kuma biyayya,uwa uba addini,ada kafin Hanan tasan halinshi tana matuk'ar yi mai biyayya a matsayinta na k'anwarsa har Allah yasa suka fara soyayya sai gashi ya b'ata rawarsa da tsalle akaran banza,don babu wata mace mai mutunci da zata so ta Auri mazinaci ,dumu² Hanan ta kamashi shida Meemi suna aikata masha'a da Allah ya Toni asirinsa ranar Aikenta Muta'z yayi wajensa Allah yasa tayi mummunan gamo tun daga ranar Hanan ta tsani Murat kamar ta caka mai wuk'a ta kashe shi.








***
Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,yau CE ranar da aka kawo kud'i na baiko da kud'in saka ranar Muta'z da Mumtaz,ranar Mumtaz tasha kuka kamar ranta zai fita,don ma sauk'inta har yanzu bata ganin Muta'z har yanzu bai dawo ba da sai ta tona mishi asiri kowa yasan halinsa,ita kanta bata San yadda za ayi ta yi rayuwar Aure da Muta'z ba,mutumin da ya b'ata mata rayuwarta ya yi mata fyed'e harda kullin cikin shege,idan ta tuno da wannan abin yana matuk'ar b'ata mata rai sosai, kuma tana tunanin tona mai asiri zumuncin da ke tsakanin iyayensu ya lalaci ga Hajjo da ta shige gaba akan komai,matuk'ar ta Sani to wallahi sai ta tsani Muta'z tsana mai tsanani.




Wata biyu aka saka alokacin Meemi ta haihu,kuma har yanzu bata San halin da ake ciki ba na maganar k'arin Auren mijinta,Hajjo ta CE a k'eleta da kanta zata fad'a mata har sai ta haihu sannan za'a fad'a mata.




Ni kuwa kallonsu kawai na ke yi don abinda Muta'z ya min sai na rama Wanda yafi nashi ma,Amman ni kad'ai na barwa zuciyata don sai ya gane nima macece.








*Ummu Maher CE*
*_AKAN AIKI NA_*






By
_Ummu Maher(Miss green)🍀_




Ina gaishe Ku y'an GRP dafatan duk kuna lfy👏🏼daga Ummu Maher dinku.








Pg 71&72




....yau aka kawo lefena akwatina set12 mak'ota da y'an uwa sai tururuwar shigowa suke yi ganin lefena,kowa kuma da abinda ya ke fad'a wasu da basu San alk'armu da su Muta'z ba cewa suke munbi son zuciya munbi kud'i sauran aje a siyar damu.




Ni kuwa basu San da za'a janye Aure na da Muta'z to da tabbas da nafi kowa jin dad'i don ban San me yasa ba ?koda shigowa gidanmu yayi b'oyewa na keyi don bana son in kalli kwayar idonsa don abubuwa da yawa nake gani acikinsu.





****
Cikin dare Mimee ta fara nak'uda dak'er taje d'akin Muta'z ta tashe shi alokacin ta fara fita daga hayyacinta,suna isa emergency aka karb'esu da gaggawa aka shiga da ita.


Da sauri Muta'z ya zaro wayarsa ya kira Fulani harma da Me Martaba don ya sanar musu halin da ake ciki,Har Mumtaz ya kira sai da tayi ringing 5 sannan ta d'aga yaji muryar Mumtaz kamar sarewa don dad'i,don haka yayi gaggawar sanar mata halin da suke ciki.


Duk da k'iyayyar da ta kewa Muta'z Amman tayi matuk'ar tausaya mishi don tasan halinda maza suke shiga idan matansu suna labour.


Da sauri na sakko k'asa na sanarwa Hajjo da Umma halin da ake ciki,cikin rud'ewa Hajjo ta d'auko hijabinta mu ma muka shirya sai Hospital.


Har mukaje bata haihu ba hankalin kowa ya tashi har ana tunanin ko ayi Mata operation, sai Allah ya sauke ta lfy ta haifi Y'arta mace Ku Kakkyawa me kama da Mahaifinta,nan da nan asibitin ya kaure da murna,Amman duk da halin da Mimee ta ke ciki kallon banza ta dinga bina dashi,ina ganin haka nayi tahowa ta gida,INA fitowa daga asibitin naji an janyo hijabina ina juyawa naga Muta'z a tsaye yana murmushi,had'e raina nayi na juya amman bai bani dama ba kawai sai ya rungumeni a k'irjinsa,ban San me yasa ba na kasa hanashi saima wani irin dad'in k'amshin jikinsa da na keji abin sha'awa don tunda na ke ban tab'a jin dad'in turare haka ba.


Muna cikin wannan halin ne naji muryar shi dai dai kunne na ya ce.




"I love u"
Har cikin b'argon jiki na naji wannan dad'in Amman da nayi wani tunani da sauri na wuce parking space,da sauri ya wuce ta gaba na ya janyo hannuna ya ajjeni a kusa dashi ya figi motar sai gida.


Kallona kawai ya ke yi yana tuk'i ya kasa cemin komai saboda miskilanci don na lura Muta'z miskili ne,nima ban ce mai komai ba na juya ina kallon window sai naji yana cewa.


"Mumtaz na Sani ni me babban lefe ne awajenki to ina Neman alfarma a wajenki ki bani dama in gyara lefina don Allah", ya fad'i hakan cikin rarrashi.


Ko kallon shi banyi ba har muka iso wani tafkeken gida me rantsattsan kyau,mamaki ne ya kamani na juya zanyi magana kawai sai naga ya bud'e min murfin k'ofar motar alamar in fito.


Ko kallon sa banyi ba na fito na tsaye a waje,kawai sai naga ya tsugunna a gabana yana cewa" don Allah Mumtaz ki yi hak'uri ki yafe min nayi alk'awarin insha Allah zan gyara lefina please ya had'a hannayensa alamun ban hak'uri.


Ban sanda na had'a hannaye na da nasa ba inq cewa na hak'ura ka tashi mu tafi gida Allah ya yafe mana baki 1.




To tun daga wannan ranar ne Muta'z ya k'ara shigemin kuma ko agaban waye sai ya nuna min soyayyarsa a fili,Amal ta kan CE min na yi dacen miji me sona,kawai kallon ta na ke yi don ni kad'ai nasan me Ya yi min Amman Allah da kansa muna yi mishi lefi ya yafe mana don haka na yafewa Muta'z lefinsa Amman dole sai na gumq masa idan mukayi Aure wannan sirri na barwa zuciyata.








Ummu Maher ce
*_AKAN AIKI NA_*






Rubuta wa✍🏻
_(Ummu Maher)Miss Green_






Pg 74&75


.....ko da naje barkan Meemi ko kallona ba ta yi ba k'arshe ma ta tashi ta barmin wajen,Allah yasa Fulani tana Gidan ta amshi kayan barkan da na kawo sannan ta ringa yiwa Meemi fad'a akan wulak'an ta d'an Adam ko don ina a matsayin y'ar uwarta mafi kusanci.


Ni kuwa daman nasan hakan zai faru don ba kowacce mace ba ce ta ke da b'oye Kishin ta don haka kuwa dole ne ta yi,Amman ni dai har zuciyata bana jin haushin ta ko kad'an don ni shi kanshi mijin ba sonshi na ke yi ba ballan tana inyi kishinsa don haka tuni daga shi har ita na tattarasu na watsar.




Umma ce kad'ai ta je ranar suna Amman babu yadda ba ta yi dani inje ba Amman na k'i k'arshe ma na lafe a gado na ce ba ni da lfy.




Ina kwance a kan gadona daga ni sai wata rigar bacci Red color gashin kaina duk ya barbazu akan gadon kamar wata ba India,k'arar shigowar mota naji Amman sai ban tashi ba don nasan Mlm ne ya dawo kuma watak'il wani abin zai d'auka don haka naci gaba da bacci na.




A cikin bacci na naji wani irin k'amshin turare Wanda k'amshinsa ba ya gushewa a cikin hancina da gangar jiki na baki 1,saurin ta shi na yi don tsabar tsoro gabana ne ya yi wani irin mugun tashi ganin Muta'z a kaina yana yimin wani irin mayen kallo kamar zai cinye ni.




Da Sauri na fara Neman blanket d'ina Amman baya kan gadon,kunya ta bi ta isheni kawai sai naga ya k'araso har inda nake ya lullub'amin a jiki na sannan ya yi min wata signal ya bi hanyar fita,tsayawa naga ya yi a bakin k'ofar sannan ya ce min"ki fito Hanan ta zo ganin ki don jiya ta dawo daga mkrnt......




Ai ban Bari ya k'ara sa ba na d'auko hijab d'ina na saka na wuce ta gabansa da Sauri don zumud'in ganin Hanan,shi kuwa tsayawa yayi a bakin k'ofar yana shak'ar daddad'an k'amshin da Mumtaz ta barmai,har zuciyarsa ya ke jin wani irin tsagwaran son Mumtaz har cikin zuciyar sa so na tsakani da Allah.




A farlo ya samesu sun rungume juna suna ta zuba surutu,ya watsowa Hanan wani kallo sannan ya ce"ke Hanan ki iya bakin ki don Da amarya ta ki ke magana ehee".


Dariya Hanan ta yi sannan ta ce"Kai gaskiya Yaya ka iya zab'e fa gata k'anwarka ga ta matarka kaga shikkenan ka had'a k'annenka a matsayin Matanka".


Nan dai Hanan ta ringa bani labari,shi kuwa Muta'z sai kallo na ya ke yi kamar zai cinye ni da naga ya matsamin sai na rik'e hannun Hanan na ce muje kitchen mu d'ora girki,sannan na juyo Amman na kasa kallon kwayar idonsa na ce"ka koma gida kaga yau suna zamuyi girki."




Zama naga ya k'ara yi sannan ya CE"Wow shikkenan kinga sai inci girkin amaryata".ya fad'i hakan ya na mannemin ido alamar yaji dad'in hakan.




Hanan sai dariya ta ke tana cewa Romio da Juliet kawai,ni kuwa naja hannunta muka shiga kitchen muka fara aikin mu gadan gadan,tunda suka fara girkin Muta'z yake kallon farlon kamar ya bisu ga wani k'amshi da ya faraji Wanda ya gama cika farlon.


Naman kai muka dafa Wanda ya gaji da k'amshi ,sai jallop d'in taliya Wanda Tasha green beans, da hanta,da kayan k'amshi sai coconut&pine apple jus.




Hanan ce ta fara jerawa a dining ni kuma ina gyara wajen da muka b'ata sai da na gama gyarawa tsab sannan nafito,na d'auka gaba d'aya ya tafi baya farlon Ashe yana nan ya hard'e k'afa 1 kan 1,kallo na ya ringa yi har na fara hawa kan step a hankali kamar me tausayin tsep d'in, Muta'z kuwa kamar wani soko sai kallo na ya ke yi Hanan ta kula da hakan sai dariya ta ke yi shi kuwa gogan besan ma meke faruwa.




Yana ganin Mumtaz ta hau sama ya fara cika cikinsa da d'a amun yana santi kamar wani yaro sai da yaci ya more sannan ya tashi yana masha Allah kace na more da amarya me iya girki.




A hankali na fara sakkowa akan step d'in ina sanye da wata doguwar Riga Arabian gown blue black kasan cewa ta fara sai ta haska ni sosai na nad'a belt d'in a kaina na saka plat show me kyau, ina danna wayata har na k'ara so Amman Muta'z besan na k'ara so ba don wani mugun kallo da ya ke bina dashi kamar zai cinye ni,ni kuwa na basar dashi na zauna ina cewa Hanan idan ta gama cin abincin zamuje gidansu Amal don su gaisa.




Saurin tashi Muta'z ya yi wai zai kaimu,Amman na ce mishi ya barshi ga gidansu nan kusa da namu Amman fafur ya CE wallahi sai ya rakani.




Haka kuwa akayi har gidansu Amal ya rakamu sai da yaga mun shiga sannan ya tsaya acikin motar ya ce mu shiga zai jiramu,ina matuk'ar mamakin kishin Muta'z kamar Wanda za'a saceni.




Amal ta yi matuk'ar jin dad'in zuwanmu,Mamansu ma sai nannan ta ke damu don yanzu sona ta ke kamar za ta goyani,ni kuwa a zuciyata oh Ashe dubiyarnan sai kana dashi a ke damawa da kai.










.....Fulani da kanta ta d'auko me yimin dilka da gyaran jiki ciki da waje,ai kuwa matar tasan abinda ta ke yi don irin matan sudawan nanne don haka ta zage awajen gyarani ciki da waje,gabana kuwa ko d'an yatsa bazai shiga ba tsabar gyara kuma an hana Muta'z zuwa gidanmu don har sai an kaini Gidan shi sannan zai ganni don haka Bak'aramun kwaruwa Muta'z ya yi ba don har ciwo sai da yayi,don Ni da kaina na tsara wannan don yadda na ke ada ma Muta'z yana k'ok'arin tab'a jikina ballan tana yanzu da komai nawa ya canza Wanda ya sanni ada yanzu ba zai gane ni ba.






Please kuyi hak'uri abubuwa ne suke yimin yawa shiyyasa bana tyiping da wuri✍🏻.








Ummu Maher CE
Vote
Share
And
Comments.
*_AKAN AIKI NA_*






Rubuta wa✍🏻
_(Ummu Maher)Miss green🍀_














_*Please don Allah kuyi hak'uri fans bana samun kawo muku labarin Jamila abubuwa ne suka yi yawa*_






_(The Wedding)_


💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
To fa ranar muke jira yau gata tazooo,ranar bikin Muta'z da Mumtaz.






Page 76&77


Wani irin kyau me had'e da sirrika kala² Mumtaz ta yi kamar ka d'auke ta gaba d'aya,tun jiya na ke kuka don idan na tuna ayanzu haka na zama Matar Mumtaz ba k'ara min tashi hankali na ya ke yi ba,don gaba d'aya yanzu tsoron Mumtaz na ke yi don na dad'e da sanin ba k'ara min mugu bane.




Tun k'arfe 4 y'an d'aukar amarya suka zo muna ta kuka nida Amal,don tun safe muke kukan rabuwa ni da aminiyata Hajjo kuwa sai masifa ta ke Wai min isheta da kuka kamar wad'anda za'a yanka kukan ya yi yawa.




Hajjo CE ta shiryani da kanta da wata had'addiyar tamfa super me Golding ta yi kyau sosai sannan aka d'oramin wata lafiyayyiyar Lifaya fara Sol sai ratsin gold ajikinta aka fesheni da turare exsense ne k'amshin gaske.




Har aka gama shirin kuka na ke yi aka shigar dani babban farlon Mlm ya yi min nasiha sosai me ratsa jiki nan fa kuka na ya k'ara k'aruwa da k'er Mlm ya rarrasheni don shima kukan zuci ya ke yi.






Wata sabuwar mota muka shiga wadda Muta'z ya yimin kyautarta yau bayan d'aurin Aure motar sai k'elli ta ke yi.





Muna shiga Gidan Sarauta ya d'auka a ko ina bakajin komai sai tashin kid'a da tambura ta ko ina,Muta'z kuwa yana d'akinshi shida abokansa suna ta yimai tsiya Mijin Meemi da Mumtaz abin shi kanshi burgesa ya ke yi sosai.




Meemi kuwa tana sashenta lokacin da aka shigo da Mumtaz ji ta ke kamar ta kashe kanta tsabar kishi,Baby kuwa sai kuka ta ke yi baiwar Allah Amman tak'i kulata da ta dame ta ma har dungure mata kai ta yi ai kuwa ta ringa tsala kuka.


"Don ubanki ba ubanki bane ya janyomin wannan fitanar ba ina zaman zamana yarinya ta lik'ewa mijina ai kuwa duk sai sun gane kurensu don wallahi bazan yarda wacce mace ta had'a shimfid'a da mijina ba.




B'angaren Fulani aka fara kaini ta karb'eni hannu bibbiyu sannan ta kaimu b'angaren mai martaba shima ya yimin nasiha sosai ta zaman hak'uri agidan miji,sannan ya mik'omin wasu mukulli na kyautar wani Gidan shak'atawarsa Har kuka saida Hajjo ta yi na ganin irin kyautar da Mai Martaba ya yiwa jikarta ta dinga saka mai albarka.




Sashen Meemi aka nufa dani Amman muna zuwa Masu yi mata hidama wato bayinta suka CE mana ta fita,Hajjo kuwa cewa ta yi "Uban ta fita ba bata fita ba🥴wallahi sai tadawo munanan muna jiranta ko in shigo d'akin tafito ja'ira,da k'er aka bata hak'uri ta hak'ura ammanfa tana ta sababi.




Sashena aka kaini aka ce in shiga da bismillah,ai kuwa na shiga da addu'oi a bakina gwanin sha'awa,sai da na CE alhmdh don wani dad'i da nishad'i na dinga ji sosai.




Akan faffad'an gadona aka ajjeni Amal ta rungumeni tana ta kuka y'an kai Amarya suka fara watsewa daga ni sai Amal sai Hanan ita kuwa sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login