Showing 21001 words to 24000 words out of 35410 words

Chapter 8 - AKAN AIKINA Complete BY UMMU MAHER.txt

tausayi.






An kamo su Gaye da Morris tambayar duniya suka cw ba wani ne ya saka suba sune suka aikata hakan da Kansu,Ai kuwa aka k'ulle su Suna Nadamar abinda suka Aikata.




Ban hak'uri Iyayen Fiddausi suka rink'a yiwa Mai Martaba duk da Basusan Muta'z d'an sarki bane sai yanzu,nan fa suka ringa yabawa Mai Martaba k'ok'arin shi na sakawa a kulle d'an shi duk da kud'in da ya ke dashi.








Nan fa y'an jarida suka cika wajen kafin ka ce me harda su Mumtaz a wajen suna mamakin yadda abin ya faru,Mumtaz ta yi k'asak'e tana kallon Muta'z duk daman kowa ya fad'i irin halin shi Mai kyau.






Ko wanni d'an Jarida ya saka lasi fik'arsa wajen bakin Muta'z don jin abinda zaice,Kawai sai kallonshi Ya kai kan Mumtaz wacce ta fara yad'a labarin Fyed'en da aka ce ya yi wa wata yarinya.






Kallon Banza Muta'z ya aikawa Mumtaz sannan ya zari lasifik'ar hannunta da k'arfin gaske Wanda har ciwo sai da ya jiwa Mumtaz, abinka da farar fata sai ga wajen ya yi jajir harda jini.




Sai da ya k'ara yi mata kallon banza kallon alamar zamu had'u sannan ya fara magana kamar haka..........."


















Kash! naso inji abinda zai faru Amman idan na ga ruwan sharhi gobe zan k'ara Rubuta.












Daga
Ak'alamin


Ummu Maher




Vote
Share &Comments
*🪦✨AKAN AIKI NA✨🪦*


Book 2 sabon salo📖✍🏻




Na
_*Rêãl🌹 Oum Maher*_
(Mîss gréén💚)


*MATAR BASH💎*




📲MINAL MULTIMEDIA
https://youtu.be/NCrdsZmuh6E


Dan Allah kushiga ku danna Mana subscribe






_*📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*✍🏻_






42/43


Jikin Mumtaz ne ya yi wani irin sanyi ganin kallon da Muta'z ya ke yi mata.


Harya gama jawabinsa bata k'ara sanin me ake tattaunawa ita dai taji tashin motoci,sai da kowa ya watse sannan taja k'afafunta da k'er ta bar wajen.






Har taje gida bata daina tunanin irin kallon da Muta'z ya ke yi mata shin d'aukar jawabin da ta ke yi ya zama laifi? Ko kuwa d'aukar jawabin da ta yi ne alokacin da a ka kirawo su zuwa gidanshi shine laifi?






"Ke Mumtaz lafiyarki kuwa ki ka zauna kina tunani haka?kuma me ya samu hannun ki harda jini?".


" Wallahi Umma bugewa na yi to shine wajen ya ke yi min zafi Amman yanzu zanje chemist d'in Sale ya yi min treatment d'in waje babu komai kada ki damu Umma wajen ya yi sauk'i".


Ta fad'i hakan ne don ganin yadda Umman ta damu sosai don tafi kowa sanin halin da iyayenta suke shiga a duk sanda suka ga wani Abu yana damunta.














★<><>★
Wani sabon biki a ka k'ara yi agidan mai Martaba don dawowar Shalelen d'ansa kuma Magajinsa,Murat kuwa yak'e kawai ya ke yi don yadda ya ke jin zuciyarsa kamar zata fashe duk shirinsa akan Muta'z ya war_ware to waye ya lalata mishi shirinsa yasan dai Morris da gaye Mimaa ce ta had'a su akan ce wa Suyi mishi sharrin da za'ah d'auresa har igiya ta yi rara Mimaa ce ta shirya duk wani shirin da aka yi shidai na shi taimakon kawai nuna b'oyayyen gidan Muta'z Wanda ya ke hutawa a ciki sannan ya sace mukullin gidan ba tare da ya gani ba.






Har aka gama shahararren bikin na Muta'z da Mimee,Murat bai iya ce wa k'ala ba daga baya ma sai ya sulale ya bar wajen tsabar bak'in ciki.






Shi kuwa Muta'z a yanzu nunawa Mimee so ya ke kamar me don ya yi matuk'ar tausaya wa yarinyar alokacin da aka kulleshi don da k'er Hajjo ta ke lallab'asa su ta fi gida don yadda ta ke matuk'ar rike cewa Hajjo wataran ma har suma ta ke yi.






Ita kuwa Mimee koda taga yadda Muta'z ya ke nuna mata sai ta dinga wani karai Raye kamar wata Kifi,shi kuwa har dariya ya ke mata don yadda ta ke siririya kamar wata silindium yadda kasan ba ta cin Abinci.











*Bayan buki*


Ko irin kunyar nan Mimee ba ta ji ba ta zage ta ringa yi wa Muta'z soyayya kamar ba Amarya ba kuma ranar farko,Shi kuwa kallon ta kawai sai ya fara tausayinta don matuk'ar ta shigo hannunsa ba za ta ji da d'i ba.






Hakan ce kuwa ta faru don a ranar Muta'z ya nuna mata ba maza bane kuma ba d'aya suke ba a fannin k'arfi da nuna Iko kiran sunan Hajjo kuwa ta yishi babu adadi shi kuwa ko a jikinsa don ita ce ta kawo kanta.




Duk da yadda tasha wuya bai hana ta k'ara son Yayan nata ba don yadda ya iya da ma ce babu dama zaka rantse da Allah daman ya saba harkar Amman ba haka bane kawai dai hallitarsa ce haka.








Koda safiya ta yi Mimee ba ta ga Yaya Muta'z ba koda ta kira wayarsa ma bata same sa ba,ta tashi daga ita sai rigar bacci ta lek'a ta Window ta hango fitar Motarshi daga gidan, kamar taje ta tsayar da motar Amman ya Riga da ya fita haka ta hak'ura ta nufa fridge don nemawa cikinta abin tab'a wa ba tare da ko Sallah ta yi ba ballanta na wankan Tsarki.











★<><>★
Sai da Muta'z ya zauna a Office d'insa sannan ya d'auki wayarsa rai a b'ace ya fara kiran wata number.


"Atiku wai har yanzu bata fito daga gidan bane don wallahi idan wata matsala ta faru akan harkar nan to Ku kuka sa kanku".


Ya fad'i hakan cikin tsawa" Oga ka d'an k'ara jira yanzu ne lokacin fito warta daga gida don haka kad'an k'ara jira.




Cikin fushi ya kashe wayar domin ya shirya komai a lokacin da ya shirya amman suna son b'ata mishi lokaci,Don ya shirya nuna wa Mumtaz kuskurenta na yad'a abinda bata da masaniya akai.












Mumtaz kuwa baiwar Allah tana cen bata San what going on ba.






"Kai Uwata kinga yadda kuwa Abayarnan ta yi miki Kyau kamar wata Balarabiyar Asali".
Malam ne ya ke fad'in hakan ya yinda ya ke kai k'osai bakinsa Ita kuwa Umma tana k'ara sa sakin K'osan.




Dariya Mumtaz ta yi Wanda ya ke k'ara fito da ita, ya yinda ta ke jin fad'uwar gaba sosai aranta ta ce"Malam Amman yau da wuri zan dawo don Aikin babu yawa."


"To uwata Akula da hanya Allah ya bada sa'ah".




" Amin Malam sai na dawo" ta fad'i hakan tana d'aukar k'osai guda d'aya tana ci,Mumtaz kenan akwai zuciyar kula da iyaye d'aukar Albashinta 4 kenan yanzu,da k'er Mlm ya ke tilasta mata don ta siya sutura saboda sutura itace mutum babu yadda za ta yi dole ta ke siya don itama ta yarda sutura ita ce mutum. kuma tana siya musu kayan abinci sosai harda mai da magi Lipton madara kai harda au kwai.




Ni kuwa Ummu Maher na ce muma Allah ya bamu y'ay'a masu son mu Amin👏🏻👏🏻.








Tana fitowa daga gidan ta kalli hannun dama da hagu sai ta hango wani d'an adaidata da alama tafiya zaiyi,da Sauri ta tsayar dashi ta alama da baki.




Tsayawa ya yi sannan ta shiga ta fad'a mishi inda zata je.




Sunyi nisa sosai a cikin tafiyarsu kawai sai taga ya juyo ya shek'a mata Abu a hancinta tun daga nan bata k'ara sanin inda kanta ya ke ba.














*Oum Maher ce*








_*don Allah ku ta yani da Addu'ah akwai wani Abu da ya ke damuna na keson in samu,Allah ya bamu duk abinda muke nema na Alkhairi Amin.*_
*_✨AKAN AIKI NA_ ✨*


✍🏻Ummu Maher(Miss green)💚
44/45


*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION*






Tunda Mumtaz ta tashi daga dogon baccin da ta yi sai taji gaba ki d'aya an d'aure ta akan kujera,ko iya motsi ba ta yi, gashi d'akin gaba ki d'aya duhu ne,ko hannunka ba zaka iya gani ba hankalin Mumtaz ya kai matuk'a a tashi saboda batasan ko ina aka kawota ba.




Ta dad'e acikin wannan hali sannan taji k'arar bud'e k'ofar d'akin,wani k'amshi ya daki hancinta wanda ta ke tunanin ta tab'a jinshi amman bata san a inda ta sanshi ba.




Tsoronta ne ya k'aru a lokacin da taji mutumin yana takowa har zuwa inda ta ke,amman kafin yazo Wani irin haske mai wuyar gani ya haske d'akin,da d'ewar da na yi acikin duhu sai yasa idanu na suka zama kamar na makauniya,na rintse idanuwa naji gaba ki d'aya so nake in bud'e idona inga a i'na na ke,wata kakkausar Murya na ji,muryar namiji wadda itama na ke tunanin kamar na tab'a jin irin muryar,da k'er na bud'e idona don in ga waye wannan.






"İnna lillahi wa İnna İlaihi Raji'un."


"Na san za ki yi mamakin ganina ko?to ba abin mamaki bane don kinga haka ta faru da ke,kuma ki daina mamaki domin yanzu zaki gane tsakanin aya da tsakuwa."






Wasu hawaye ne masu zafi suka fara ambaliya a kyakkyawar fuskata murya ta na rawa Na ce"Don Allah kada ka cutar dani saboda nasan ahalin yanzu iyaye na suna cen suna nema na,don Allah kada ka lalatamin rayuwata kamar yadda ka lalata rayuwar yarinyar.........


Wani ruwan sanyu me kamar k'ank'ara Muta'z ya watsamin har cikin bakina,abinda ban k'arasa maganar kenan ba,wani numfashi mai wahala na furzar sannan na fasa wanu irin kuka.




"A'i ba ki yi kuka ba har yanzu domin kuwa keda farin ciki har abadan abadan,sabida baki isa ki shiga rayuwata ki gurb'ata min ita ba sannan ki ce zaki zauna lafiya".


" Zan cen iyayenki kuma kada ki damu domin inason in d'an d'ana musu yadda nawa iyayen suka ji alokacin da sukuma na ki iyayen suke cikin farin ciki,kinga kuwa dole kema yanzu na ki iyayen suji a jikinsu."




Ya fad'i hakan yana mai janyo dogon gashina da ya warware ya fad'o a gadon baya na,K'ara jan gashin nawa ya yi da k'arfin gaske yana magana da kakkausar murya.




"Kinyi gangancin shigowa rayuwata har ki ke ganin ce wa ya kamata ki yi min sharri,to wallahi tallahi sai na koya miki hankali ta inda ba zaki yi tunanin k'ara yi min sharri ba nonsence kawai".


Ya saki gashin na wa sannan ya fita daga d'akin ya kashe hasken, da k'arfin gaske ya rufo k'ofar ji ka ke gammmmmm....tsabar rufe k'ofar da a ka yi da k'arfi sai da na kusan sakin fitsari a wando.






Sai da na kwana a zaune babu ci babu sha,har lokacin sallar asuba ya yi ban yi bacci ba,tsanar Muta'z na ji a raina da kuma mummunan halayensa,na shiga tsinemai ina magana da k'arfi don so na ke yi ya ji,don duk muguntar da zaiyi min na saka azuciyata baki na bazai tab'a rufuwa ba.






A b'an garen su Mlm kuwa sunyi neman duniya amman ba suga Mumtaz ba, har wajen Aikinsu sai da Mlm ya je amman babu wata maganar da aka samu akan Mumtaz,hankalin Mlm da Umma ya yi matuk'ar tashi sosai,yadda suka ga dare haka suka ga safiya Mlm na kuka Umma na kuka,haka suka kwana suna Sallah suna kaiwa Allah kukansu Akan b'atan y'arsu Mumtaz.




Har Police station Mlm ya je ya kai report amman shiru ka ke ji abin har mamaki ya ke bawa Su Mlm yadda y'ar tasu ta b'ata kamar b'atan d'an mutum ba.




Tun asuba Umma da Mlm suka k'ara fita yawon neman y'ar tasu Hamma har yamma har dare babu labari,Akan dole suka hak'ura zuciyoyinsu kamar zasu fashe don tsabar bak'in ciki,amman da ya ke masu tawakkali ne sai suka fauwalawa Allah tare da rok'onsa akan ya bayyana musu y'arsu abar sonsu wato Mumtaz.






Sai da yamma ta yi alokacin na fara gajiya har na suma tsabar yunwa,na ji an watsamin ruwa, gaba ki d'aya kayana suka jik'e sharkaf ni kuwa sai haki na ke ina kiran sunan Allah.




Haske ya k'ara kunnawa a d'akim wnda yasa na fara tunanin ko a lahira na ke,saboda abin ya yi min yawa ga ruwa ga idanuna da suka koma kamar na makauniya.


Kallona ya shiga yi yana dariya,acikon zuciyarshi kuwa kawai tausayani ya ke ji na d'auko yarinya har gidansu,ganin irin tuanin da ya fara zuwa zuciyarsa kawai sai ya yi saurin ba sarwa,sannan yazo ya kin ceni daga mugun k'ullin da na sha.


Gaba ki d'aya na fad'o jikinsa yarab,tsabar galabaitar da na yi,wani yamm ya ji ajikinsa tsigar jikinsa ta fara ta shi,da sauri ya saki mumtaz ta fad'i ajikin bango,na fara wani irin nishi mai wahalarwa..










_Kuyi manage saboda jikin nawa da sai a hankali._












*Ummu Maher ce*
*AKAN AIKI NA*


Book 3


Ummu Maher(miss green)




46/47
Yanzu Mlm haka zamu saka idanu muna kalllon Y'ar ta b'ata an rasa gane wad'anda suka d'auke mana y'armu,gaskiya yau har Gidan radionsu saina koma don su naga kamar basu damu ba,Umma CE ke ta sababinta tana yi tana share hawaye da gefen zaninta,Malam kuwa yana gefe ya saka handkacif yana goge hawayenda suka zamar masa sabo.






Iya wahala Mumtaz tana Shanta awajen Muta'z Wanda yake jin har yanzu baiyi ramuwar da yake son yi ba,don haka yau ya shirya muguntar da zaiyi mata Wanda baza ta tab'a manta irin muguntar da ya yi mata ba har ta mutu.


Yau ma kamar kullum da kanshi ya kawo mata abinci,Mumtaz ta d'aga idonta da k'er wad'anda suka yi mata nauyi tsabar wahala ta Kalli abincin sai dai duk da yunwar da ta ke ji ba zata iya cin abincin ba saboda wani mugun yaji da Ake zubawa acikin abincin don sai ka kusa zuba fitsari saboda azabar yaji.


Cikin tsawa ya fara yi mata magana "d'auki abincin kici ko kuwa yanzu na gana miki mummunar azaba Y'ar jaridar k'arya mai d'orawa mutane sharri, yau sai kinyi Dana sanin had'a min sharri domin muguntar yau tafi ta kullum.




Tun kafin ya gama maganarsa Mumtaz ta fara cin abincin tana kwallah don sai taga yajin ma yafi na kullum,kai Muta'z ya karanci tsabar mugunta,har ta gama ci yana kallon fuskarta tare da k'ara tsanarta tunda ta kunya tashi a idon duniya dole ne shima ya kunyata ta.


Bata Ankara ba ya fizge kwanan tare da turo mata ruwa nan ta d'aga ta fara kwankwad'a sai da ta shanye sannan ta ajje jarkar a nan ta fara wani bacci mai wahala,shi kuwa Muta'z wani mummunan kallo ya bita da shi tare da yin wata mik'a kamar zai yi aikin k'arfi.




Mumtaz kuwa baiwar Allah sai baccinta ta ke yi a d'akin baccin wahala,shed'an yafara bugawa Muta'z ganga nan fa ya fara aiwatarwa da Mumtaz mummunan k'udurinsa akanta.




Cikin baccin wahala ta fara jiyo wani bak'on lamari yayinda ta fara jiyo wata irin azaba a k'asanta,wani yunk'uri ta yi don ta tashi taga menene?


Abun da ta gani ne yasa gabanta wani mummunan fad'uwa tana rintsa idanunta jin kamar zata mutu saboda azaba,wani irin kuka ta saki mai ban tausayi tana son tashi Amman ta kasa,Muta'z kuwa baima son aduniyar da yake ba don yayi nisa baya jin kira,don tunda yake bai tab'a zuwa wannan duniya mai matuk'ar dad'i ba.






Kuka Mumtaz ta ke tana tausayin kanta dana iyayenta,tun tana k'arama suke kula da ita tare da bata tarbiyya dai_dai gqargwado Amman yau gashi wani abanza ya lalata mata rayuwarta wajen amfani da kud'in da ya ke dashi wajen yi mata fyed'e.




Sai da ya gama ne ya fara kuka da idanuwansa don tunda yake bai tab'a zina ba,yayi zama cikin turawa Amman bai saka ya watsar da tarbiyyar da iyayensa suka yi masa, yana fita daga d'akin ya kirawo wata number tare da bada umarni,shi kuma gaba Ki d'aya ya fita daga Gidan,da k'er ya kawo kansa gidansa yana had'a hanya kamar Wanda yasha wani Abu.




Taji sanda aka bud'e k'ofa Amman bata san ko waye ba don ko d'aga idonta bata iyayi tsabar kukan da taji gashi ko tafiya ba zata iyayi ba saboda azaba.




Wani Abu suka busa mata kamar ranar da suka d'auko ta har suka kawota k'ofar gidansu bata San anzo ba.




Alokacin kusan k'arfe 8na dare ne,suka ajje ta a hankali a soron gidansu,suka taho a hankali cikin sand'a suka shiga mota,alokacin Malam ya dawo daga Sallah ya hango fitowarsu daga Gidan tun kafin ya iso wajen suka shiga motar suka jata da k'arfi suka fita daga layin baki d'aya.




Salati Malam ya saka bayan ya haska soron ya ce"Mumtaz ke ce me suka yi miki,Innalillahi Wa inna Ilaihi Raji'un."










Ummu Maher ce.
*AKAN AIKI NA*






_Ummu Maher (Miss green)_






48&49


Tsananin tashin hankali ranar Mlm ya yi shi,don ganin y'arsa tilo a k'asa kamar gawa baisan yanada wani k'arfi ba, sai yau don gaba ki d'aya ya d'auki Mumtaz ya yi cikin Gidan da ita yana kwallawa Umma kira,da gudu itama ta fito har tana tuntub'e jin ya ambaci sunan Y'arsu Mumtaz,Tayashi rik'e Mumtaz ta yi tana cike da tsoro don ganin y'ar tasu kamar gawa a d'akinta ta kwantar da ita tana faman yayyafa mata ruwa Mlm kuwa yarasa tudun dafawa ga y'arsu Amman tana cikin wani hali Wanda basai an gaya maka irin wahalar da tasha ba,ta rame ta k'anjame abun tausayi wata kwallah Malam ya share yana k'ara kallon fuskar Mumtaz wadda ta ke cikin wani hali na wahala.






Wata irin ajiyar zuciya Mumtaz ta saki a hankali jin hannun Ummanta ajikinta don koda bata bud'e idonta ba tasan waye don bazata tab'a manta sanyin jikin Mahaifiyar taba,da sauri ta rungume Umman tana k'ara sautin kukanta,Malam ma cike da tausayi ya ke kallonsu.




"Don Allah Umma kada kuga laifina Wallahi d'auke ni a kayi aka kaini wani gida aka yi ta azabtar dani AKAN AIKI NA,wallahi Umma kodon samun kwanciyar hankalinku daga yau nabar Aikin Jarida don samuwar kwanciyar hankulanku keda Mlm,sai ta k'ara rungume Umma d'in tana k'ara sakin wani irin marayan kuka na tausayin kanta dana iyayenta.




Likita Malam ya kirawo ya duba Mumtaz d'in tare da yi mata allurai nan da nan sai kuwa bacci ya d'auke ta awajen,Malam yasan Mumtaz zata iya tashi tana jin yunwa don haka ya siyo mata Shayi da baredi hakan kuwa a ka yi tana tashi daga bacci cikin dare Umma ta bata shayin da buredi ta cinye tas kamar mayunwaciya,Umma kuwa tana zaune tana kallon y'ar ta cike da tausayi,koda ta gama kwanciya ta k'ara ba ita ce ta tashi daga wannan baccin ba sai k'arfe 9na safe,tana tashi Umma ta gama dafa mata ruwan zafi,ai kuwa taji dad'in ruwan zafin don ta gasa jikinta don haryanzu tana jin azaba dauriya kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login