Showing 18001 words to 21000 words out of 35410 words
Chapter 7 - AKAN AIKINA Complete BY UMMU MAHER.txt
harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 32&31*
Sosai Mumtaz ta yi murna da zuwan k'awarta Gidan su Wato Hanan sunyi hira sosai sannan ta ke fad'a mata bikin Sweet brother d'in ta sannan ta bata gate pass d'in wajen.
Har bakin motar ta Mumtaz ta raka ta sannan ta dawo gida,har sai da Mumtaz ta shiga gida sannan Hanan ta ja motarta ta tafi,har zuciyarta tana jin k'aunar Mumtaz tana ji da ma Mumtaz ta zama y'ar uwarsu tana kwad'ai tawa a zuciyarta da ma matar Yayan ta ce da wannan tunanin ta fara driving zuwa gida.
*MUTA'Z*
"Yanzu don Allah Abinda ka ke yi Mu'taz ya da ce kenan ace tunda aka saka rana har yau da za'ayi dinner ba kaje kun dai dai ta da yarinyar nan ba."
"Fulani ki yi hak'uri duk yadda ki ke so haka za'ayi insha Allah idan na fita zan shiga wajen Hajjo insha Allah".
Da d'i ne ya kama Fulani don dama tasan d'an na ta mutun ne shi mai girmama iyayensa shiyyasa ma a kullum ta ke k'ara son d'an na ta.
*MUMTAZ*
" Kai Masha Allah Mumtaz kin ga kuwa yadda ki ka yi kyau kuwa?".
Dariya Mumtaz ta yi sannan ta kalli Ummanta ta ce "sai na fara zuwa Aiki don yau ni ce da duty zan d'auko wani Aiki sannan sai na biya wajen Dinner d'in".
" to Mumtaz ki kula da hanya Allah ya ki ya ye".
"Amin Umma".
*****
Sosai Mimee ta sha kwalliya ta alfarma sannan ta fito don su gana da Muta'z don kiranta kawai ya yi ya ce tazo ta same shi yana son yin magana da i'ta, haka kuwa a kayi yana zaune wajen shak'atawar Hajjo sai ga Mimee tazo.
Tun daga nesa ya hango ta yana sanye cikin shadda blue ya sanya hularsa zanna bukar ya yi kyau sosai shaddar sai walk'iya ta k'eyi da shek'i alamun shaddar mai tsada ce sai wane da wane zasu saka ta.
SLM
Kawai ta ce sannan ta samu waje ta zauna idonta k'uri akansa tana yi mishi kallon tsaf,ta da d'e tana son yayan nata sai yau ne Allah ya kawo mata ranar da za ta malleke sa a matsayin Mijinta don an Riga da an d'aura Aure tare wa kawai za tayi.
Shafa sajensa ya yi Wanda yasha gyara ya kwanta luf abin sha'awa da k'er ya fara juya lulu eyes d'insa zuwa fuskar Mimee.
Babu laifi Mimee kyakkyawa ce fara ce irin fau d'in nan k'irar jikinta kamar na silindium don tana da siranta sosai jikinta dai kamar irin ma asalin turawa.
" Yaya Muta'z gani an ce kana kira na,so ana yimun Make_up ne shiyyasa banzo ba"...
D'aga mata hannu ya yi alamun ta tsaya da maganarta sannan ya ce",daman nazo ne don in gaya miki bazan samu damar zuwa wajen dinner ba,idan ke za kije to ga hanya nan Amman ni bazan je ba,kuma kada ki kuskura ki fad'a wa rigimammiyar tsohuwar nan idan kika gaya mata in kika shigo hannu na ba zakiji da d'i ba,tunda ba tsohuwar ce za yi miki zaman Auren ba."
D'aukar glass d'insa ya yi irin me Skye d'innan yasa ka sannan ya yi wucewarsa yabarta da shak'ar dadda d'an k'amshin turarensa.
Bin bayan shi Mimee ta yi da kallo yana k'ara shiga ranta ji ta ke yi kamar ta janyo dare don ta ganta ga ta ga Yayan ta abin sonta.
Shi kuwa gogan bayan ya fito Gidan hutawarsa ya tafi don yaje ya huta kuma akwai wasu abubuwan da ya keso ya yi saboda haka ne yasa yazo Gidan don baya son hayaniya.
Saida ya yi sadaka sosai da kud'i,tsoffi sai addu'ah suke masa yana amsawa har ya shiga gidan.
Bai samu mai gadi a bakin gate d'in ba don haka da kanshi ya fito ya bud'e gate d'in sannan ya shiga,don yana tunanin ko yana ban d'aki ne.
Koda ya shiga gidan numfarfashi ya dinga ji acikin gidan yana bin lungu da sak'o na gidan yana dubawa.
Abinda ya gani ne yasa shi k'amewa awajen saboda abinda ya gane wa idanunshi.
*MURAT*
"Murat Aiki ya kan kama an gama komai yanzu burinka ya kusa cika ko kuma in ce ya cika ma."
Juyowa ta yi rik'e da wayarta a hannu tana dariya kamar mahaukaciya,sannan ta ce"babu abinda bana ganin bayanshi idan ya ce zai shiga rayuwata don haka mutane suke tsoro na.
Mima ce ta ke fad'in haka ya yin da ta kewayo da hannu ta kan sajen Murat cikin kissa da kisisina."
Janyo hannunta ya yi da k'arfi sannan ya ce"My Mima kin gama min komai dole ne ki zama ta hannun da ma na,dariya ta yi sannan ta d'auki glass cup tana shan lemo,tana jin zak'in lemon har can cikin zuciyarta sai da ta yi kurb'a biyu sannan ta ajje cup d'in ta d'auki wayar ta tana Neman wata number.
*__MUMTAZ___*
"Mohd yaushe zamu tashi ne saboda inason zuwa wata dinner ne?".
Ya bud'e bakinsa zaiyi magana wayar sa ta kama ruri,da sauri ya d'auki wayar yana cewa" hello waye.
Murmushi Mima ta yi sannan ta saita muryarta ta ce"Assalamu Alaikum. "
"Don Allah kutaimaka kuje gidan Muta'z Abubakar yarima Wanda ya ke titin gidan Radio d'inku,mun ganshi ya d'auki wata yarinya da gudu aka yasaka ta acikin motarsa Amman yanzu don Allah kuje kada ya cutar da i'ta."
"Hhh hhh hhh"
Dariya Mima ta yi sannan ta cire sim d'in ta saka shi a kwandon shara,Murat shima dariyar ya ke yi Sannan afili Ya ce".
*_MUTA'Z THE LIFE IS🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥_*
*Real Ummu Maher ce✍🏻*
Vote
Share
&
Comments✍🏻
*Typing*🖌️
💚🤍💚
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
*AKAN AIKI NA 2021*
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
💚🤍💚
Which Means👆🏻
ABOUT MY WORK🤵🏻♀✍🏻
Na
🌹Rabi'atu B/ Abdullahi🌹Ummu Maher
(Miss green)💚☘️
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 33&34*
Dariya Murat ya yi sosai irin dariyar basawa d'innan,sannan ya janyo Mima jikinsa i'ta kuwa ta kanne mishi ido d'aya alamun nasarar da ta samu na shiga tsakanin aminan juna Murat da kuma Muta'z.
*Muta'z*
Kuka ya ke yi kamar k'ara min yaro yana mai kallon yarinyar da aka b'atawa rayuwarta yarinyar da bata wuce shekara takwas zuwa Tara.
Da sauri Mumtaz ta fad'a d'akin tana d'aukar rahoto da sauri Muta'z ya juyo don ganin mai d'aukarsa hoto domin ya hango hasken camera.
Ido hud'u sukayi da Mumtaz a dai dai lokacin da Mohd ya shigo gidan,shak'a Muta'z ya kaiwa Mumtaz Wanda sai da taji ajikinta sannan ya fara magana da kakkausar murya Ya ce".
"wallahi kika sake kika yad'a wannan abin to na lahira sai ya fiki jin da d'i,muguwa masharanciya kawai dai dai lokacin shi kuma Mohd yana k'ara d'aukar rahoto.
Alokacin kuma y'an sanda sukayi wa gidan k'awayenya,har lokacin Muta'z bai saki Mumtaz ba ya shak'eta sosai don Muta'z ya fita daga hayyacinsa gaba ki d'aya.
Mohd kuwa yana ta k'ok'arin kwatar Mumtaz yayinda Muta'z ya saki Mumtaz ya wancakalar sa i'ta gefe ya koma kan Mohd.
Tunda Mumtaz ta ke ba'ah tab'a yi mata makamanciyar wannan shak'ar ba.
Saboda yadda iyayenta suke sonta da k'aunarta kuma ga ta yarinya mai biyayya basu tab'a dukanta ba,sai yau gashi wani abanza ya shak'eta AKAN AIKINTA.
Da k'er aka b'an_b'are Mohd daga jikin Muta'z don Muta'z k'arfi ne dashi kamar na doki.
Ankwa y'an sandan suka mak'alawa Muta'z yana ji yana gani suka tafi dashi Office i'ta kuma yarinyar su Mumtaz suka kaita asibiti don duba lafiyar yarinyar don ba k'aramar wahala Tasha ba don har yanzu a sume ta ke.
*****
Labarai Fulani da mai Martaba suke yayinda gidan ma acike ya ke da y'an uwa saboda bikin d'an gata Muta'z.
Da sauri Fulani da Mai Martaba suka tashi hannun su dafe da k'irjinsu suna kallon Muta'z yadda y'an sanda suka yiwa d'ansu jina jina da duka,don har ga Allah basu San Muta'z d'an sarki bane saboda shi bai fiya shiga Media bama ballanta na har a ganeshi.
Salati suke suna sallallami ya yinda kowannensu ya rasa sukuni nan da nan Suka fita a mota don zuwa ganin d'an nasu Hanan ma kuka ta ke yi kamar ranta zai fita don ganin yadda a kayi wa d'an uwanta tilo rauni.
Sara masa y'an sanda suka shiga yi har sai da ya shiga babbar headquarters d'in,ranshi a b'ace ya zauna gaban babban Inspector y'an sanda.
Ran Mai Martaba ta gama b'aci kuma har lokacin ya kasa bayani,sai Fulani ce ta fara bayanin tana kuka"Akan wani daliline zaku kama mana d'an mu kuyi mishi wannan babbar illar"?
Sai asannan ne inspetor ya gane wa take nufi domin ya hango kamar da Yaron da suka kama d'azun Akan hukuncin fyed'e.
Sunkuyar da kai Inspector ya yi domin har ga Allah kunya ce ta kamasa,saboda bai San d'ansa bane Amman koma menene a dokar k'asa hakan shine dai_dai.
Nan fa Inspector ya fara yi musu bayani Akan abinda ya faru.
Alokacin kuma Inspector ya saka aka fito da Muta'z kuma alokacin Iyayen Fiddausi suka zo wato yarinyar da aka yi wa fyed'e.
Kuka suke sosai kamar ransu a game da lalatawa y'arsu rayuwa da a kayi suna tsinewa Muta'z tare da aibata shi,don tun jiya da'aka turata talla ba'ah sake ganin ta ba.
Kan Muta'z a sunkuye yana zubar da kwallar bak'in ciki a game da wannan jarabtar da ta same sa,ko kuma ya ce sharrin da aka yi mai.
Iyayen Muta'z sun san halin d'an su tun daga girmansa har yarintarshi don haka basu yadda d'an su ne ya Aikata haka ba.
Cikin Kakkausar Murya Mai Martaba ya kirawo sunan d'an nashi Ya ce"Muta'z ka fad'a min gaskiya duk da nasan kai mai gaskiya ne"Waye ya yiwa yarinyar nan fyed'e"?.
Kallon iyayen yarinyar Muta'z ya yi sannan ya fashe da kuka cikin kuka Ya ce Ka gafarceni Mai Martaba Wallahi Ni ne".
*Real Ummu Maher ce✍🏻*
💚🤍💚
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
*AKAN AIKI NA 2021*
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
💚🤍💚
Which means👇🏻👇🏻
*ABOUT MY WORK✍🏻*
Na
*🌹Rabi'atu B/Abdullahi*
(Ummu Maher)Miss green💚☘️
*_💫📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION💪🏻_*
*MURAT FANS*
Yana godiya bisa bashi hadin kai da kuka yi Fans😩🥲
*MUMTAZ FANS*
Tana godiya bisa yadda kuka bata hadin kai wajen d'aukar hoto da kuma rahoto📸📲📲.
*MUTA'Z FANS*
Yana bak'in cikin yadda kuka bawa Murat da Mumtaz goyon baya.😭😭
__,,,,,
Shafi na 38&39
Wani wawan Mari Mai Martaba ya kaiwa d'ansa Yarima,hannunsa yana kakkarwa ya nuna sa da yatsansa sannan ya ce"Muta'z sakayyar da zaka nuna min kenan?"na tarbiyyar da na yi maka,to daga yau na cireka daga cikin y'ay'ana kuma daga kar ka k'ara kirana a matsayin ubanka".
Inspector ga shinan duk wani hukunci da ya kamata a yi mishi a yi mai,tunda duk tsun_tsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka.
Fulani kuwa kuka kawai ta ke yi tana Ce wa"Muta'z kada ka d'orawa kanka abinda kasan ba Kaine ka yi shi ba,don Allah ka fad'i gaskiya."?
"Fulani idan ki ka k'ara yi wa wannan yaron magana to sai dai a kulle Ku tare babu ruwana".
Da k'er Fulani ta fita tana kuka tana me Amman tana ji tana gani aka Tisa k'eyar Muta'z zuwa d'akin ajje masu laifi.
Koda suka i'sa gida kowa da abin da ya ke sak'awa acikin zuciyarsa Mai Martaba kuwa k'arfin hali kawai ya ke yi don babu yadda zaiyi ne shiyyasa ya d'orawa d'ansa laifi son gudun zagin talakawa,don yasan Muta'z bazai tab'a aikata hakan ba.
To wanene ya yi wa Yarima Muta'z sharri haka"? Koma wanene nan ba da dad'ewa ba Allah zai tuna asirinsa don Allah baya basin zalunci a doron k'asa.
*******
Mumtaz
" wai me ye yake damunki tunda kika dawo kin k'i cin abincin na ki gashi kuma yau kun dad'e."?
Shiru Mumtaz ta yi don sarai ta San dole sai ummanta ta yi mata wannan tambayar don tunda ta shiga d'aki bata fito ba sai yanzu don ta tsorata sa ganin abinda ya faru.
Sai ta samu damar ce wa umman nata"Wallahi babu komai kawai sai na gaji ne Aiki ya yi yawa,kuma kinga ban samu Damar zuwa bikin gidansu Hanan ba saboda Aiki."
Umman ta ce
"Ayya Allah sarki Allah ya bada abinda ake nema".
" Amin Umma"waini har yanzu banga Malam ya dawo ba".?
Dariya Umma ta yi sannan ta ce"Ai d'azu ya dawo ba kyanan Malam ya je k'auye saboda an yi musu rasuwa."
Allah yajik'an rai na ce sannan na koma d'aki na kwanta ina tunanin irin wannan rayuwa, har yaushe ne za'ah daina yi wa y'an mata da yara fyed'e a k'asar Hausa.?ki dubi yadda aka lalatawa wannan yarinyar rayuwa,Amman koma menene iyayenta sune da laifi.
Don rashin kulawa sa yaranmu yana saka irin wannan abin ya faru dasu.
******
Babu yadda Fulani bata yi ba akan mai Martaba yasaka baki akan asaki d'ansu Amman ya k'i dolen doliyarta ta hakuri,kuma gashi tana gadon asibiti saboda tunanin d'anta,shima Mai Martaban kawai dauriya ya ke yi shi kad'ai yasan yadda ya ke ji.
Mimee da Hajjo sunsha kuka har sun hak'ura gashi yanzu an d'aura Auren su.
A b'angaren Murat kuwa yaje sau biyu ya duba aminin nashi,agaban Muta'z ya nuna ya damu dashi yana fitowa kuma ya fara dariyar mugunta saboda ya hango nasara k'arara a game da abinda yasa a gaba.
An yan kewa Muta'z hukuncin zama na shekara sha hud'u14 tare da yanke mishi tara mai yawa.
Fulani da Mimee da Hajjo suna zuwa duba Mutaz akai akai Duk sanda sukazo sai sun tasa Mutaz suyi ta kuka,abin tausayi Mimee kuwa akwai sanda ta suma bayan sunje,Mutaz yana tausayawa Mimee yadda zata dad'e da Aurensa akanta don Hajjo ta ce babu wanda ya isa ya raba Auren matukar tana raye.
*******
"Kai Gaye gaskiya nifa zanje in Tina abinda ya faru saboda ko yanzu idan muka mutu sai Allah ya tambaye mu don mun cuci bawan Allah".
By
*Real Ummu Maher ce*
💚🤍💚
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
*AKAN AIKI NA 2021*
🤵🏻♀🤵♀🤵🏻♀
💚🤍💚
Which means👇🏻👇🏻
ABOUT MY WORK✍🏻
NA
*🌹Râbî'âtû ß/ Âbdûllahî*
(Úmmú Máhèr)Míss gréén💚☘️.
💫💫
*_🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION_📚🖊️*
https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Shafi na 40&41*
Gaye ya ce"kai Morris ba ka da hankali ne zaka je ka tona mana asiri to karka soma wallahi don ni fyed'ewa yara yanzu na fara,kai kanka kasan idan Aure muka ce za muyi ina Mike da kud'in Auren?"Aure ya zama tamkar wani ciniki ka ga ai gwara mu more sosai kafin mu samu kud'in Auren tunda ga yaran nan ana sakinsu kamar wasu dabbobi.
"Kai Morris wallahi jiya Dana je wata unguwa naga yara mata suna ta wasansu a unguwa wasu da wando basu kuma babu wallahi baka ji yadda naji tausayin yaranba shin iyayensu kuwa suna sonsu kuwa?" Gaskiya ni dai bazan bar y'ay'ana a titi ba Wallahi,kuma indai iyaye basu daina barin y'ay'ansu saka_saka ba ba za'ah daina yi musu fyed'e ba"ya fad'i hakan yana kunna sugari yana zuk'arta kamar ya samu wata alewa.
Dai dai nan ya gama d'aukar video din su sannan ya yi gidan yayansa don kai mai rahoton wad'anda suka yi wa y'ar yayan nasa fyed'e.
"Innalillahi wa inna Ilaihi Raji'un"
"Yanzu daman ba yaron nan ne ya aikata wannan fyed'en ba?kai Amman mun cuce shi kuma sai Allah ya saka mishi."
Mahaifin Fiddausi ne ya ke fad'ar hakan yarinyar da aka yiwa fyed'e.
Shamsu wato k'anin Mahaifin Fiddausi ya ce"wallahi Yaya Allah ne ya toni asirinsu na taho zan tafi Aiki na hangosu a kusa da wani kango,daman kuma da ta mu dasu saboda mu y'an cumity da y'an Daba bama shiri so shiyyasa na taho don ganin abinda ke faruwa don ansha kawo mana k'ararsu i'sa ta ke da wuya na ji suna irin wannan maganar babu b'ata alokaci na fara yi musu video."
"kai Masha Allah yanzu saimu d'unguma muje police station don mu gudanar da wannan hujjar shima a sakesa a kama wad'annan azzaluman muna fukai masu
"Kai masha Allah" Allah ya k'ara tsare mana yaranmu".
Amin.
★<><><>★
"Haba Fulani wannan wani irin kuka ne da ya zama na kullum kada ki k'ara jawa kanki wata matsalar fa"?.
Shiru Fulani ta yi tana kallon mai Martaba ba tare da ta ce komai ba ta tashi ta koma d'akinta sannan ta cigaba da kuka yanzu sai d'anta ya yi shekara sha hud'u a gidan yari bai mori k'uruciyarsa ba?kai ko wanene ya yi wa d'anta sharri Allah ya Toni asirinsa da gaggawa.
Mai Martaba kuwa kallon Fulani ya yi sanda ta tashi ta koma d'akinta,Hawaye ne ya fito a idanun Mai Martaba ya goge idanunshi harga Allah shi yasan abinda ya ke damunsa akan wannan abin Ya Allah ya bayyana duk Wanda ya yi wa d'ansa Sharri har saukar Ak'urni mai girma yasa a ke yi wa Yarima akan Allah ya toni asirin ko su wanene suka yi wa d'ansa sharri,tunda aka kulle Yarima Mai Martaba baya bacci saboda tunanin d'ansa.
Ya kalli gefensa ya tuno sanda gidansu yana cike Ga Hanan ga Muta'z sun saka Mai Martaba a tsakiya ga kuma Fulani da Mahaifiyarsa Hajjo kullum farlon cike ya ke da Iyalai, amman yau babu kowa,yana cikin wannan tunanin yaga kiran wayarsa yasa hannu da k'er ya d'auka.
"Iye..iye..iye to gani nan yanzu zanzo Allah na gode maka ganinan zuwa yanzu kuwa".
Da k'er Mai Martaba ya gama wayar yana had'a kalamai da k'er,kirawo Fulani ya yi awaya ya shaida mata abinda ya faru da gudu Fulani ta fito har tana had'a hanya da karun gidan suna ta kallon ta suna tunanin me yasa Fulani gudu haka Amman koma menene abin babba ne.
<><>,>,
Muta'z ya rasa farin ciki ya ke ko bak'in ciki Allah ya wanke shi cikin ruwan sanyi,da gudu ya rungume Fulani da Mai Martaba yana kuka,Fulani ta kalli d'an nata yau wata d'aya kenan da faruwar lamarin Amman gaba ki d'aya d'an nata ya canza gashin kansa duk ya cukur_kud'e abin