Showing 12001 words to 15000 words out of 35410 words

Chapter 5 - AKAN AIKINA Complete BY UMMU MAHER.txt

inji kunyar ubanku ko saboda shine ubana to ba ranji kunyar ba y'ar mara kunya,kuma Aure babu fashi indai ina raye Meemi Muta'z zata Aura ko yana so ko baya son hakan.
Cikin fushi Muta'z ya tashi ya fita,Hajja tayi kwafa tace kaji dashi dai Aure babu fashi,d'an nema kawai Hannan ma "tace Nifa Hajja kidaina had'ani da Murat saboda wallahi ni bana sonshi kwata kwata kinfi kowa sanin mugayen halayenshi amman kike cewa wai shi zan Aura to wallahi da in Aureshi gwara in mutu banyi Aure ba,tana fad'in hakan ta tashi ta fita tana maijin haushin kakar tata da take had'a ta da fasik'i mai neman mata tabbas tasan tana son Murat saboda babu macen da zaice Yana sonta tak'i amince mai saboda yana da kyau kud'i ga iya magana ga iya soyayya sai dai ba shida hali ko kad'an.












*MUMTAZ*


Mumtaz"tace wallahi Baba sun ce idan ban kawo da wuri ba zasu rufe Exam din da zamuyi yanzu itace ta k'arshe kuma zuwa jibi duk wanda bai kawo ba bazai zana Jarrabawar ba.
Mahaifina"yace babu komai uwata zan nemo kud'in yau Insha Allah kada ki damu Insha Allah sai burinki ya cika na zama y'ar jarida.
Dariya nayi "nace Allah ya amsa Baba,Mahaifina da Umma suka had'a bakinsu wajen cewa Amin Allah ya amsa,Tunda Babana ya fita tun safe sai yamma ya dawo yana cen yana ne marmin kud'in da zan samu shiga jarrabawa.
Umma ta kalle ni taga nayi ta gumi," tace haba Muta'z babu kyau ta gumi fa,Insha Allah Malam zai samo kud'innan kidaina damun kanki da tunani kinji"Nace to Umma...Ban gama rufe ba kina ba mukaga Malam ya shigo da sallamarsa muka amsa mishi,koda ba'ah gaya maka ba kasan babu nasara afitar da Malam yayi duk farar fatar Malam saida ta nuna alamun yasha wahala.
da sauri na tashi na d'au komai abincinshi da ruwan wanke hannu,ya kalle ni yace sannu Mamana Allah ubangiji yayi miki albarka nace Amin Baba.
Yace Mamana wallahi ban samu kud'innan ba andai samu rabi da k'er shima faskare nayi mai yawan gaske to anan nema na samu rabona,kuka na fashe dashi na tausayin Mahaifina hanna yenshi sunyi jajir abunka da farar fata,Malam yace haba Mumtaz kidaina kuka mana ko idan kika kai musu baza su amshi rabin bane?.
Da sauri na goge hawayena nace zasu amsa Baba amman don Allah kadaina wannan faskaren akaina jibi fa yadda hannayen ka fa sukayi jajir,Malam"yace babu komai ai Y'ay'a amanane a gurin iyayensu hakk'i ne akanmu mu kula dasu shiyyasa kika ina yin duk ai kin da zanyi don in kula daku.












*Washe gari*


tun sassafe na tashi nayi shirina na makaranta naci abinci,na fito na gashe dasu Malam sannan ya mik'omin kud'in yace gashi in kai makarantar ince za'ah ciko sauran kud'in,"Nace to Baba na gode Allah ubangiji ya k'ara bud'i Babana yace Amin ya Mamana Allah ubangiji ya baku sa'ah a jarrabawar nan"Nace Amin Baba na.
Ina zuwa makaranta na had'u da Zainab itama lokacin tazo makarantar,Muka gaisa take cemun in rakata Zata biya kud'i"Nace to muna tafiya muna hira har muka iso wajen muka ga gaida mutumin sai fara'ah yake mana yana kallona, bayan Zainab ta bada nata kud'in aka bata recief sannan nima na bashi nawa.
"Nace ga nawa amman rabi ne zan ciko sauran,Kallona yafara yi kamar yana nazarin wani abu a fuska ta cen yace,Amman yadda kike d'innan abun ya bani mamaki don duk wanda ya ganki zai d'auka wata y'ar gidan mai kud'in ce.
Shiru nayi ina kallonshi don ni gani na keyi rainin wayo ne ma idan bazai amsa ba yaga yamun mana amman sai yayi mun wulak'anci sannan zai amsa.
Kallo na yayi akaro na biyu sannan yace yanzu nawa zaki ciko,nace mishi dubu biyar ne," Yace oky babu komai zan bada kud'in kar kiji komai,Shiru nayi ina kallonshi da mamaki a fuska ta ina mamakin kud'in da yace ya cikamun saina jiyo Muryar Zainab tana"Cewa Mun gode Sir Allah yasaka da Alkhairi.
Ban sanda nima na fara yimai godiya ba,Muka fito daga Office d'in yana mai k'ara kallona Cikin zuciyarshi kuwa shi kad'ai yasan abunda yake shiryawa akan Mumtaz Shiru yayi yana tuno sanda ya tambaye ta sunanta tace Sunana Mumtaz,Ahankali yace Wow Nice Name ya fara juyi akan kujerar sa ta Alfarma.
Muna fitowa"Nace Zainab Wai don Allah me mutumin nan yake nufi dani ne daya ke cewa Ya d'auka ni y'ar Maikud'i ce?Shiru Zainab tayi sannan tace to wai ke Mumtaz baki gane ba ne?,nace kwarai kuwa ban gane me yake nufi ba sam.
Zainab"Tace Hmm wato Mumtaz ked'in ta da bance ke Wallahi saboda komai naki i'rin na y'ay'an sarakai ne ko Y'ay'an masu kud'i, Saboda Allah yayi miki wata irin baiwa.
Allah ya baki baiwar kyau da baiwar Ilimi da baiwar Hankali da nutsuwa kinga kuwa Babu Wanda zai samu wad'annan abubuwan ba tare da anyi sha'awarsa ba,Dariya nayi "Nace Hmm Zainab kenen kedai kawai kice kina wasa k'awarki kawai amman ni banga wani abu dana fi kowa ba,Dariya itama tayi sannan " Tace ni kuwa Wallahi naga abunda kika fi dubbun mutane,Nan dai muka cigaba da hirarmu ta k'awaye cikin Fasaha da fahimtar Juna.









**********
Mumtaz"Tace Malam Wallahi Wani Malamin mune ya biya mun sauran kud'in,Malam yace to Mamana wani Malamin ne? "Nace Wallahi a makarantar mu yake,Malam yace to Allah ya saka da Alkhairi ,Nace Amin Baba "Malam Yace Amman Mama na kuringa kula da Makaranta zaka had'u da Mutane kala kala wala d'alibai wala Malamai don haka ki kiyaye,Nace to Malam Insha Allah.
Mun fara jarrabawa cikin sa'ah har muka gama exam,cikin sa,ah yanzu kuma mun tafi hutun sati biyu.




Ina zaune a tsakar gida ina yanke farce na,Wani yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Mumtaz inji wani a waje,Shiru nayi ina kallon Yaron sai naji Umma tace kaje gatanan zuwa.












*Gaskiya kun rage tyiping Fans"*
Yawan tyiping yawan comments




*Ummu Maher ce*






Vote
Share
And
Comments๐Ÿ“
*Tyiping*๐Ÿ–Œ๏ธ


ABOUT MY WORKโœ๐Ÿป




๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’š


*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
(Ummu Maher)Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ“—


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…
_________________
______
๐Ÿ…™๏ธŽ๐—ฎ๐—ฟ๐˜‚๐—บ๐—ฎ๐—ถ ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐—ฟ๐—ถ๐˜๐—ฒ๐—ฟ๐˜€ ๐Ÿ…๏ธŽ๐˜€๐˜€๐—ผ๐—ฐ๐—ถ๐—ฎ๐˜๐—ฒ๐—ฑ๐Ÿ“š๐Ÿ–Š
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa _


๐Ÿ”๐Ÿ…™๏ธŽ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ๐Ÿ…๐Ÿ”


*BABI NA 21&22*๐Ÿ“


Nayi kamar banji abunda Umma ta fad'a ba don haka nayi shiru nak'i tashi Cikin zuciyata kuma tunani kawai na keyi wannan waye ya turo a kirawo ni?to koma dai waye ba zanje ba Don ni anawa tunanin bazan Fara zance ba har sai na gama makaranta sannan Zan Fara zance ,don ba Zan had'a makaranta da soyayya ba.
"Umma tace Mumtaz dake fa nake magana ki tashi kije waje kinyi bak'o," Nace to Umma Bari in k'ara sa yanke farce na"Umma tace to kiyi sauri dai ki tashi kije babu dad'i wulak'anci.
Wata kyakkyawar Mota na hango a k'ofar gidanmu irin mai bak'in glass d'innan,kuma ba'a hango mutumin da ke cikin motar,don haka a hankali na'isa wajen cikin murya ta mai dad'i"Nace Assalamu Alaikum,Wanda ke cikin motar ya amsa ba tare da ya fito ba.
Don haka nima sai naja na tsaya awajen ba tare Dana sake magana ba, Saboda ni arayuwata babu abunda na tsana aduniya sama da girman Kai,to idan ba girman Kai ba to menene?Nayi sallama ya amsa Amman bai fito ba nufinshi ni Zan bud'e motar in shiga kome?to A'i kuwa in dai haka ne zai dad'e don ni babu abunda na tsana irin zance a mota.
Cikin fushi nayi hanyar gidanmu saboda bazai yiyu yazo har k'ofar gidanmu ba sannan kuma yace zai raina mun wayo ba.
"Mumtaz don Allah ki tsaya kiji da abunda nazo miki da Alkhairi nazo miki,Muryarshi ce naji tazo mun a bazata koda ba'ah fad'amun ba nasan cewa Sir Mukhtar ne na makarantar mu,to meye ya kawoshi gidan mu kuma?.
Juyowa nayi Sannan "nace Sir sannu da zuwa ba tare da na had'a ido dashi ba,Saboda wani irin kwarjini da yayi mun ga wani irin kunyarshi da naji lokaci d'aya.
" Sannunki Mumtaz ya gida yasu Mama da Baba?"Nace duk suna lafiya Sir"Oky to Masha Allah wato Mumtaz nasan zakiyi mamakin zuwa na gidanku, Amman ba abun mamaki bane Saboda sone yaja Hakan.
"Mumtaz tun ranar da na Fara ganinki naji zuciyata ta aminta dake kuma zanso ki zamo Uwa awajen y'ay'a na,Ayanzu inada shekara 35 Amman tun ban Kai haka ba iyaye na suka damu inyi Aure,Saboda ni kad'ai ne d'ansu da suka mallaka arayuwarsu,don haka suke son inyi Aure suga Matata da Y'ay'ana.
Sai dai haryanzu banga matar da ta kwanta araina irinki ba ina sonki Ina k'aunarki Wallahi Mumtaz tun Ranar da na ganki naji Ina matuk'ar sonki so mai wuyar fassaruwa,Amman Ina fatan kema zaki Soni kamar yadda nake sonki?.
Shiru Nayi sa kama kon jin furucin Sir Mukhtar,Tabbas babu macen da zata ga Sir Mukhtar tace bata sonshi,Saboda yana da abubu wanda duk mace zata soshi,Yanada ilimi arabi da boko,yanada kyau,kud'i Da kuma hankali,kusan dai ya had'a dukkanin wani Abu Wanda mace zata soshi,Sai dai A i'nda gizo yake sak'a Shine kwata kwata ban shirya yin Aure yanzu ba Saboda inason inyi karatu in samu A'iki in taima kawa iyaye na,Sannan kuma bana son in had'a Soyayya da kuma karatu,don mafi akasarin y'an matanda suke biyewa Samari suyi ta soyayya k'arshe sai kiga babu abun arzik'in da suke shukawa A'cikin ajinsu.
"Mumtaz kina jina kuwa naji kinyi Shiru? kodai abunda nazo miki dashi ne ba kiyi a munna dashi ba?
DA k'er na bud'e bakina" Nace kayi hak'uri Sir Mukhtar bawai nak'i aminta da abunda kazo mun dashi bane A'ah kawai dai ni banason had'a Makaranta da Soyayya kawai shine matsala ta,kuma inason inyi karatu in samu Aiki don in taimakawa Iyaye na.
Sir Mukhtar "Yace babu komai Mumtaz kada ki damu indai kin amince Dani ni bazan zalin ceki ba,Ba kuma Zan ta kuraki ba Zan jira har lokacin da zaki gama karatunki sannan kuma in samo miki A'iki.
Kunya ce ta kama Mumtaz tayi saurin yin hanyar gidansu tana rufe fuska,tabbas tasan Son Sir Mukhtar ya Fara Kama ta don gashi tun daga yanzu ya Fara yi Mata kwarjini kuma ta Fara jin kunyarshi.
Shi kuwa Sir Mukhtar shafa kanshi ya Fara yi yana kallon Mumtaz cike daso da k'aunarta,ya shiga motar shi ya d'auko wasu kaya,sannan ya fito ya samu yaro yace ya kaiwa Mumtaz yana ganin yaron ya shiga saiya shiga motarshi ya tafi yana mai farinciki.
Mumtaz kuwa tana shigowa gida ta wuce d'akin ta da sauri tana fara'ah don bata kula da Umma dake tsakar gida ba tana yi Mata magana,Umma kuwa Murmushi tayi tabi Mumtaz da kallo Saboda idan kaga Budurwa tana farin ciki irin wannan to ta fad'a cikin soyayya,Umma bata gama rufe bakinta ba taji sallamar yaro,Yaron"Yace wai gashi inji wani a waje a bawa Mumtaz wannan.
Umma ta amsa tana cewa to An gode, Umma ta fara bud'e wani kwali kamar na wayar Hannu,ta bud'e shi me zata gani?wata dan k'areriyar waya ce mai kyau da tsari,Hannun Umma kuwa kakkarwa kawai ya keyi,sannan ta bud'e wata envelop โœ‰ kud'i masu yawa aciki ga wata zungureriyar ta karda aciki,da k'arfi Umma ta Fara kiran Mumtaz cike da tashin hankali.
Da sauri Mumtaz ta fito ta tsugunna"Tace Umma gani,Mumtaz waye wanda yazo gurinki yanzu? "Umma Sunanshi Sir Mukhtar Malamin mune a makaranta Shine wai yace yana sona.
Umma tayi shiru kamar baza tayi magana Cen kuma" Tace shikkenan tashi ki tafi Bari Malam ya dawo zamuyi magana dashi, a hankali Nace to Umma.
















********
Meema ta kalli Farida"tace kinsan Allah Farida bazan fito bariki a banza ba in koma a banza,kina ganin Murat sai binshi na keyi ya Aureni Amman sai wulak'anci ya keyi mun Saboda yaci moriyar ganga yanzu saiya zubar Dani.
Farida"tace A'i ni wallahi mamaki ma kike bani da kika lik'ewa Murat meye amfanin son Wanda bai damu da Kai ba,Saboda haka kawai gwara ma ki hak'uri dashi kawai,ga maza nan y'an bariki sai binki su keyi kina wulak'an tasu ke kince sai Murat kuma har kina maganar ya Aure ki,kada ki manta fa kunyi bariki dashi koda kin Aureshi ba lallai bane kuzauna zaman aminci da kyau na ba.
Haba Farida meyasa kike fad'in haka Kinsan cewa matuk'ar ban Auri Murat ba komai zai iya faruwa dani,Nidai don Allah Farida ki samomin mafita don Allah.
Farida"tace Meema Zan baki wata y'ar shawara da kuma wata dabara irin tamu ta y'an bariki,Meema tayi y'ar fara'Ar da tunda suka Fara magana ba tayi ba,"Tace ina jinki Farida nasan ba zaki bani banzar shawara ba,Farida tayi dariya sannan "Tace A'i dole in baki shawara tunda Ina cin banza, don Meema idan ban baki shawara ba ma sai Allah ya tambayeni don duk kud'in da muke samowa tare muke cinye romon kinga kuwa dole ne in baki shawara don a cigaba da samo mana d'an abun b'atarwa.


Farida" tace Meema yanzu zamu Fara tun tub'ar Murat akan maganar Aurenki i'dan yak'i yarda saimu had'a mishi gadar zare Wanda ba zai i'ya tsallakewa ba.
Meema"tace k'awata wani i'rin gadar zare ne Wanda ban San dashi ba?Farida"tace Meema tambayar da nakeso inyi miki wani mutunne Murat yafi tsana aduniya saboda da haka ne zamu had'a mishi gadar zare.
Meema tayi shiru cen Kuma "tace kwarai akwai hallitar da Murat yafi tsana aduniya don kuwa ko zancen Muta'z kika yiwa Murat sai kunyi fad'a.












*Yawan Comments*
yawan tyipingโœ๐Ÿป








*Ummu Maher ce*










*Vote*
*share*
And
*Comments*
*Tyiping*๐Ÿ–Œ๏ธ


๐Ÿ’š๐Ÿค๐Ÿ’š
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKINA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿค๐Ÿ’š



ABOUT MY WORK๐Ÿ‘ฉ๐Ÿปโ€๐Ÿซ




*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
{{Ummu Maher}Miss green
๐Ÿ’š}
*๐Ÿ’…Shalelen Jarumai writers Ass๐Ÿ’…*.
____________
Y'AR MUTAN NIGERIA๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ๐Ÿ’š๐Ÿค๐Ÿ’š




*BABI NA 23&24๐Ÿ“*




Wata irin soyayya mai k'arfi ce ta shiga tsakanin Mumtaz da Sir Mukhtar,kuma ayanzu Umma ta gaya wa Malam Abinda Mumtaz ta fad'a mishi a ga me da Mukhtar,Babu b'ata lokaci Malam yayi bin cike a ga me da Mukhtar kuma Alhamdilillah ya samu shaida ta gari shi da Mahaifansa,don Asalin Familynsu FAmily ne na da mutunta duk wani d'an Adam,kuma sun samu shaida mai kyau don haka kowa ya ke ganin mutuncinsu,ga su suna da asali mai kyau shiyyasa kowa ya ke sha'awar zama dasu.





*Bayan wasu watanni*


Su Mumtaz na hango suna Celebration wato Murnar gama makaranta,Wanda Sir Mukhtar ya shirya wa Masoyiyarsa Mumtaz Tare da k'awayenta idan har kaga Mumtaz yanzu ba za ka gane taba Saboda yadda ta k'ara kyau ta k'ara wa yewa ta fuskar abun hannu kuma ma'ana kud'i shima Alhamdulillah,saboda a yanzu babu abinda za su cewa Sir Mukhtar don ya gama musu komai ta fannin Rayuwa.








*SIR MUKHTAR*




"Mumtaz kin yanzu Allah ya yadda kin gama makarantar ki KO?Kuma a yanzu babu abinda zamu ce sai dai mu yi wa Allah Godiya,tunda ga shi yanzu kin gama makaranta sai asha biki KO?.




Wata i'rin kunya ce ta ka ma Mumtaz kamar ta nitse a k'asa don tsabar kunya," Ta ce Malam ma ya yi mun wannan maganar da man jiran ta ba kin ka na ke jira sai ga shi kuma ka yi,Allah dai ya kad'e mana duk wata fitina.




"Amin my Mumtaz, ya fad'i hakan yana mai yiwa Mumtaz dariya tare da k'arajin wani son ta har cikin zuciyarsa,ya ji kamar ya janyo ranar Auransa da Mumtaz.




Nan dai suka cigaba da hirarsu tsakanin Mukhtar da Mumtaz.








*MU'TAZ*




" Yanzu don Allah Momi ba zaku bar maganar Auren nan ba yarinyar nan ba tada hankali KO kad'an In banda Hajju da rigima ta k'eleni mana in za b'a da Kai na mana, amman ta da meni da maganar wannan yarinyar da gaba ki d'ayanta goyon ka ka ce.






"Haba d'a na ka daina fad'in haka kaga wannan Alk'awarin Hajjo ne babu yadda zakayi dole sai hak'uri,ka ga Mahaifinka bai tab'a tsallake maganar Mahaifiyarsa ba kada kasa a wannan karan ya ba wa Mahaifiyarsa kunya akan Ta ce zata had'a Auren Zumunci tsakaninka da y'ar k'anwar Mahaifinka,kayi hak'uri don nima za ka janyomun zagi a wajen Hajjo.




" Cikin fushi Muta'z ya ta shi ya fad'a sa shensa ba tare da ya k'ara magana,saboda yadda ya tsani yarinyar nan abun ba'ah magana.










*SIR MUKHTAR*




"Hajiya kin San na dad'e i'na baki labarin Soyayyata da Mumtaz tsahon lokaci,to yanzu Iyayenta sun ce In turo Shine Na ce Bari in gaya miki,Saboda tun jiya na fad'awa Alhaji ya ce zai tura gidansu Mumtaz d'in,Shine Nace Bari in fad'a miki........


"Hajiya ce cikin fushi ta mik'e tsaye Ta ce Kai tsaya da wannan banzar maganar da ka ke yi ni kake fad'awa wai ka fad'awa Alhaji wai ya ce zai tura gidansu Mumtaz Ce wa za'ah tura gidansu, to Bari kaji bazan had'a Zuri'a ta y'ar talakawa ba.......










*Yawan sharhi*
*Yawan Rubutu*


don wallahi bakwa Sharhi.










*Kayi Sharhi*
sannan ka ๐Ÿ‘‰๐Ÿป
*Ka tura*




*Miss green๐Ÿ’š ce*
*๐Ÿ’…๐Ÿ’ƒShalelen Jarumai*
*๐Ÿ–Š๏ธTyiping*


๐Ÿ’š๐Ÿค๐Ÿ’š๐Ÿค
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
*AKAN A'IKI NA 2021*
(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)(แƒฆห˜โŒฃห˜แƒฆ)
๐Ÿ’š๐Ÿค๐Ÿ’š๐Ÿค


Which means๐Ÿ‘‡๐Ÿป


*ABOUT MY WORK*๐Ÿ‘ฉโ€๐ŸŽ“
________โœ๐Ÿป


*NA*
*RABI'ATU.B.ABDULLAHI*
{{Ummu Maher}}Miss green๐Ÿ’š๐Ÿ’š


Y'AR MUTAN KANAWAN NIGERIA๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ






*Nabila dikko anda Nabiha Aminu uwayen d'aki ns gaisuwa ta ban girma gareku*




*Mominal Minal ban girma gare ki Marubucuyar Samiha y'ar mace*


da
*Momin shukura shugabar k'unguyar mu ban girma gareki Allah ya k'ara lfy*






*Na sa daukar da wannan shafin ga Y'an k'ungiya Baki d'aya*
wato
Jarumai Writer's Assโœ๐Ÿป


Da
Fans d'ina a duk inda suke, mussaman.




*KALTUM

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login