Showing 33001 words to 36000 words out of 52652 words
Chapter 12 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt
aje mai acikin abin take away din ko ta dan mayar wani wajen duk da yasan ba ita tai ba, dan bata iya din ba.
Tana shiga daki wayar ta ta ratumo ta hai kiran Farha,Farha ana can ana zubawa Bala shagwaba , taji waya na ringing, miqa hannu yai ya dakko mata ya amsa ya kara mata,da kyar ta amsa da " Hello" " ke dalla tashi zaune Lamyah ce," ai da hanzari ta miqe har tana kusa kifawa dan murna, tsalle ta daka ta dale Bala, suna fuskantar juna, saka wayar tai a Handsfree, aiko Lamyah ta fashe da kuka, nan da nan jikin Farha ya hau tsuma kamar mazari," wane dan kan uban ne ya taba ki a gidan, kaf din su ki min bayani, bana tsoron ko wanne gauta a cikin su, ni rana ce dafa su zan, maza ki min bayani," Lamyah na jin haka ta tsagaita da kukan," Dalla uwae mafadata ni ba abin da kowa ya min," " to me kk wa kuka?" " Baaba ne ya... ya.... auran Yah Amee, "wata shewa Farha tai tana ta murza Bala, gaba daya Allah 2 yake ta aje wayar ," to in banda ke meye na kukan,bayan mafarki ne ya zama gaskiya," "a da ba? Yanzu yanda nake ji a zuciyata ba zan iya zama da shi ba" " baki da hankali ne, me yasa ba zaki iya zama da shi ba?" " yana da wata matar fa," kuka ta fashe da shi, ta hadiyi wani abu mai daci a wuyan ta, Farha ce ta sake wani ashar, " aure fa" daga Bala tai ta koma gefen shi,"wane qaton ne ya mai aure bayan an san ko ba jima ko ba dade zaki bayyaa agare su, to bari kiji kar ki yarda ki zaina da kishiya, ko ya sake ta ko a raba maku gida, ko kuma ya san abin yi, yo ni mutum ya min kishiya ma ba sai na babballa shi ba," ta qarasa tana huci sosai, wayar Bala ya amshe yana gimste dariya, gaisawa sukai da Lamyah sannan ya fara mata nasiha mai ratsa jiki da jijiya, nan take Farha da ta cika tai fam ta sauka," but still is not fair, yaushe ma Lamyahn tai girman zama da kishiya," daga qarshe suka mata addu'a suka mata fatan alkairi, da alqawarin zuwa bikin nata, kashewa tai ta zame ta kwanta, hankalin ta gaba daya a tashe yake, sai dai kawai a kaso dari t samu sauqin ashirin.
Gyara ta sosai Momma ta fara,ba qaqqautawa, sai dai komai zata bata tana amfani ne da abubuwan mu na gida, kama da ga kayan lambu zuwa kayan marmari, sai kuma dangin aya, dabino, kwakwa, cukui, da zuma, ko gyaran jiki da natural abubuwa Momma ke wa Lamyah amfani, nan da nan ko kyaun ta ya qara fitowa, jikin ta tsabar kyau wani sheqi yake kamar macijiya, gaba daya Momma kanta ta san dan ta ya gama dacen mace anan.
Tin saura kwana uku Farha ta dira a Nijer, sun sha murna sosai ita da Lamyah da Mubarak, sai kace zasu tsaga gidan da murna, dangin Momma sun fara zuwa suma, kowa sai son barka yake da amarya Lamyah, a gefe kuwa amarya zuciyar ta cunkushe take, duk yanda farha ta so mantar da ita baqin cikin ta abun ya faskara, tayi iya yin ta har saida itama ta koma yin shiru, Mubarak ne ya shiga tsakiyar su ya zagayo da hannun shi ta wuyan su" kaiiii shirun nan naku ya burge ni, for the first time Kumburin buredi, da Qashi da rai sun nustu ba fada, ba hira ba hayaniya," ido suka hada a tare sukai kwafa, ai ko kan ya ankara sunyi ram da shi, ihu yake yana neman taimako, dakin rufe yake, sai da suka gama yamutse gadoj kamar wasu yara, sannan suka kwanta suna ta dariya suna maida nunfashi," God i am gonna miss all this," hawaye ne ya gangaro ma Lamyah, Munarak ne yace," My goodnee really, Lamyah? To ba dani ba ni na gudu wajen Mommana, ta hadan abinci duk kun yashen ciki," fita yai a guje , su kuma suka saka dariya, Farha ce tace," yaron nan in yana abu kamar wani babba, he is just 5 to 6 yanzu fa, amma maganganun shi da wayon shi kamar dan 8 ko 9, Allah ya raya shi, tabbas ta bakin nashi ne tin da da yakan ce zai zama yayan ki,in Bala na kitsa mai hakan nakan musa kullum," murmushi sukai suka miqe zuwa sallah.
An ci an sha, an kuma yi biki lfy, in da Farha taso tai rawa amma aka hana ta, taji haushi sosai, tai qunqunin ta ta gama tace aiko yau ko a gidan amarya ne sai ta dance, ile ko bayan an kai amarya, mutane an tattafi, daga Lamyah dake ta kuka, sai ita Farha, sai wata yar uwar su Momma, da ta kan zo, mai suna Rahama, kida Farha ta kunna, tin Lamyah na daurewa ai sai ga amarya ta cire mayafi tana takawa, suna yu suna ihun jin dadi, a haka Ameenullah ya dawo, shi daya ya shigo, dan a nan su Farha zasu kwan, ita gobe zata wuce, shiyasa Lamyah ta dinga kuka sai abar mata ita, da kyar Momma ta yarda, dan gaba dayan su kuka suka sata gaba suna yi, Ramla ma gobe zata koma gidan Momma, leqowa yai ta yar hanyar da basu rufe ba,yana ta qarewa Lamyah kallo, gaba daya hankalin shi ya ma tashi, burin shi kawai ya gan shi kusa da amaryar shi.....
*Sauran qiris wayar nan ta ja na aje rubuta 'yan rawa sai bayan kwana biyu ko uku, inna huce daga faduwar gaban da ta ja min, nai rubutu mai yawa na fice hankalina ya tashi dana tina ban saving ba, ina komawa naga ashe bai gogu ba, da wallah sai na warke na dawo*😭😂😂😂
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*I dedicated this sweet page to all MAMU NOVELLA members, especially the active 1s, Yan labe layi daya ne naku*😙 *I heart u da yawa, mun zama sisters from another mother, Allah ya qara mana hadin kai da so da qaunar juna, My qawalliya rabin duwais ( Mamu Autar Hajiya) Maryam Alqali,ina roqon Allah daya baki ladan hada zumunci da kikai mai qarfi*
Page 21:
Wani juyi Lamyah tai hade da banqara qirjin ta, sannan at the same time qugun ta ta maida shi gefe, ta saka hannu ta tattaro gashin ta gefe, tana kada qugun ta a hakan, wata ajiyar zuciya mai qarfi ya aje, bai san da zuwan Naufaliyyah ba sai ji yai ta daki kafadar shi da dan qarfi, a firgice ya juyo, wani mugun kallo ta ke bin shi da shi, gaba daya idon ta yai jawur, fuskar nan tai jawur, haka ma hancin ta, sunkuyar da kai Ameenullah yai yace," shigowa ta kenan zan miqa masu wannan naga suna shashanci, ni kuma bana son shiga," harar shi tai dan a tsaye take tin shigowar shi, har matse qafafun shi da yake da komai a idon ta, qwace ledar hannun shi tai ta dauki hanyar dakin, zata kai masu, tinawa da yai ba Lamyah kadai bace a dakin, da qawar ta masifaffiyar nan, sannan ga Rahma kar ta fadawa Momma , bayan nan ba zai so wulaqanta Lamyah har haka ba ace a first nyt din ka kishiya ce zata kawo ma kazar amarci ba kuma da arziqi zata ba da fada zata je, shan gaban ta yai ya jawo ta jikin shi, sannan ya hade ta da gini, nan da nan jikin ta ya hau rawa, miqa mai jikin ta take gaba daya tana aje nunfashi, yana ganin haka a ranshi yace," yau na shiga uku," kiss daya ya mata a goshi, ya shafi gefen fuskar ta, sannan ya kauce, idon ta arufe yake amma jin da tai kamar baya nan ya sa ta bude ido, aiko nan take wasu hawaye masu dumi suka fara bin fuskar ta, ta durqusa a wajen tana kuka, mai cin rai, yau Ameenullah din ta ya zama na wata, yau da wata zai kwana ba da ita ba, a qa'ida ko bai kwana da wata ba lokacin waccan ne ba zai kwan da ita ba, aiko yau za a yi ta, dan maganin matan da ta dirkawa kan ta, ba qaramun damun ta yake ba, miqewa tai tai dakin ta, wasu arnan kayan bacci ta saka, ta feshe jikin ta da mayun turarikan ta,wanda a ciki harda hadin na asirin su na mallake Ameenullah, murmushi tai na gefen baki, sannan ta tura qofar dakin Ameenullah dan ta kai mai ziyarar ba zata, me zata gani.....
..
Wucewar Ameenullah, dakin Lamyah ya fada da sauri ya rufe qofar, kamar wanda aka kora ciki, ajiyat zuciya ya sauke kan ya daidaita kan shi, Lamyah da farha masu rawa tare da Rahma yar kallo ba qaramin firgita sukai ba dan ganin yanda ya fado kamar an biyo shi," wayoo Allah kai da waye?" Farha ce ta watsa mai wannan tambayar ta maqale a qarshen gado tana wulla idanu, Lamyah kam har ta fara kuka, sai Ramla data kasa magana jiki na karkarwa, bata rai yai ya harari Farha da take jiran amsa yace," Nida aljani ne," aiko a tare suka zunduma ihu, kowa ta qara qanqame yar uwar ta, dan tabbas da gaske yanda ya fadi akwai abinda ya biyo shi, dariya ce ta kwace mai bai shirya ba, " dalla malamai ku nutsu, wannan uwar Rawar da kuka me ai ta isa kira maku aljanun ba sai na zo da su ba, ke gaki jiki ba nama, a bushe amma kin dage wai ke rawa kk, to gwanda ma ita, tana da abun girgizawar, ba ma wannan ba Lamyah ki zo dakina ina son magana dake," idon Farha ne ya qanqance da masifa, ta miqe kenan tana tattaro kalamai da maganganun wassafa mai ta ga ya kama hannun Lamyah sun fice," Bashi, sai kuma ka biya," shine abinda Farha ta fada kenan ta sakko daga gadon tana ta mitat tsoron daya basu.
...........suna shiga dakin, auran ledojin ya aje a qasa dan dama uku ne ya aje ma su Farha daya ya zo da sauran nan, daya ta Naufaliyyah, daya ta Lamyah da shi, yana ajewa kuwa ya juya kan Lamyah data takure, a gefe tana watsa ido a dakin, kallon ta yai kamar ace fir ta gudu, ," sai kace wata ta Allah, dalla malama ki qaraso , ni magana nake son muyi dake," qarasa wa tai kanta a qasa, tana wasa da yatsan ta,duqar da kan da tai ne ya bata damar ganin kayan jikin ta, aiko wata kunyar shi ce ta kamata, dan laffaya aka nadota da shi, kayan qasan wasu fitinannun kaya ne irin yadin nan me mannewa a jiki, sannan doguwar riga ce iya cinya amma an tsaga ta ta gefe, sannan an matse ta daga sama, bata taba jin kunyar zama da irin kayan nan ba sai yau, Ameenullah kuwa duk inda hankalin shi ya ke ya kai qololuwae tashi, amma daurewa yake kar ya ja musu masifar Naufaliyyah, zama tai a darare, ya daka mata tsawa," ni dalla ki matso ko magana kk son nai ta daga mury ne?" Kada kai tai alamar A'a, matsawa tai sosai, shi ma qara matsawa yai jikin ta sosai, ledar hannun shi ya dakko, ya bude, kaji ne manya, masu laushi, guda biyu, sai drinks, da snaks, janyo dan qaramin table din gefe yai,ya dora su, umartar ta yai da su ci ta tashi ta bace mai a daki, ci ta farayi, dan ko tana jin yunwa, after all Yah Amee din ta ne, bata ga abin jin kunya ba, zagewa tai ta ci sosai ta sha abin sh, suna gamawa tai qoqarin miqewa, juyawar da tai, yai ido biyu da shape dinta nan take ya kware ya hau tari, ba qaqqautawa, da sauri ta juya nan ma ji yai kamar an qara kware shi, dan yanda ta sunkuyo qirjin ta ya bayyana mai jiyai kamar nunfahin shi zai dauke, jus ta zuba a cup ta zauna daf da shi,jikin ta na gogar nashi,ta kai mai baki, tana ta faman zuba mai sannu, idon ta fal hawaye, kurba yai, a hankali nutsuwar shi ta dawo, jan ta yai ya aje cup din hannun ta ya hau kissing din ta ba ji ba gani, suna a hakan ne Naufaliyyah ta shigo, kusan suma tai dan tsabar kishi, ai ko yaja jin qamshin ta bai san sanda ya ture Lamyah ba ta koma gefe, wani kallon mamaki ta bishi da shi, sannan ta bi inda yake kallo itama ta ga meke faruwa? Naufaliyya ce ta cika tai fammm, idon ta har qanqancewa yake dan masifa, " Lamyah sai da safe, ki addu'a kan ki kwanta," wani kallo ta bishi da shi na lallai ka rainan wayo, duk da ba tsoron first nyt da take ji tabbas she really want to experience it at her own first day, in her matrimonial home, amma da dikkan alamu wannaj matar tashi bazata taba bari su sake ba,duk da soj da suke wa junan su, tabb ashe akwai yaqi gaban ta," bakiji ance ki fitsari ki addu'a ba kan ki kwanta,yara qanana sai jarabar tsiya," inji uwar gida amanar Ameenullah, wani mugun kallo Lamyah ta bita da shi,tana son bata amsa taji an kama hannun ta ana leading din ta waje, juyawa tai taga Yah Amee din ta ne, suna kaiwa qofa yace mata a hankali,"My Lamyah sai da safe sleep well, and i love u so much," daskarewa tai a tsaye, yau me take ji, itace fa amrya, sannan kuma ita bata taba tsammanin zai hakura da kasancewar ta YAR RAWA ya aminta da ita da wuri haka ba, amma gashi har kalmar love ya furta mata, wani murmushi ne ya kwace mata,haushin da ta qunsa gaba daya sai taji nafila ne, tin da an bata farilla ai shikenan, ita kuma waccan jarababbiyar taje ta cinye shi, dama ita bata san komai ba ai, hanyar dakin ta tai ta isko mutanen ta na ta hira,Ramla na jin bacci amma iya surutu ta hana ta sai zuba take, kashe fitila tai ta qarasa gadoj ta haye, a hankali ta furta masu," sai da safe, a hakura da hirar nan haka Farha," haushi ne ya kama Farha sannan kuma taji wani iri game da yanayin Lamyahn," me ya miki? Ki sanar dani in wani abu mara dadi ya miki tin kan na tafi na mai tass dan ba wai mun baki shi bane dan ya na bata ranki," " cikin dan murmushi mai sauti Lamyah tace," Ammiii kwantar da hankalin ki, ba abinda ya min, kin hane?" Farha ce ta kada ido sama tace," au nice ma Ammii din yau," " to u ar being over protective,ba fa abinda ya min, da yamin wani abu kin san halina da kuka zaki ganni," ta qarasa cike da dariya, Farha ce tace " kuma fa haka ne," gyara kwanciyar ta tai,ta dan dago kai zata fara zubar ta ta, taji sun hai munsharin qarya,dan ta san Lamyah bama ta munshari ko baccin gaske balle tasan wannan shirun dan tai tsit akayi shi," Fine kui baccin , ai dai gobe zan ma tafi," Lamyah najin haka idon ta ya ciko da kwalla, tai canjen waje da Rahama ta koma kusa da Farha ta kwanta, kamar jaririya,a hankali kuwa Farha ke shafa kan ta har tai bacci, bayan addu'a da suka hada baki sukai a tare, kamar yanda suka saba a gida, cikin sha'awar yanda sike gudanar da rayuwar su kamar 'yan uwan juna ne Ramla itama tai bacci.
Ameenullah, ranar ya ga ta kanshi, ba qaramn wahala Naufaliyyah ta bashi ba, dan ya sanar da ita ba ranar ta bace amma ta qi sam, sai da ta san yanda tai ta daha mai hankali ya kusance ta, qarin abinda ya bashi qarfin guiwa kuwa ganin Lamyah da yai duk dama hankalin shi tashe yake, sai dai dama yasan kawai zai rage zafi da wannan ne , amma qishirwar shi kam mai kashe ta sai Lamyah, da kyar ta hakura ta kyale shi, dan sai da taji gaba daya ya sake baya iya komai again ta barshi,amma still ta manne da jikin shi kamar wadda take tsoron kar ya fita cikin dare, murmushi kawai yai ya kada kai, halin Naufalliyyan shi sai ita.
Kukan rabuwa da Farha Lamyah take kamar ba zasu qara haduwa ba ki kuma ba waya, tin Ameenullah na lallashi, yanda ya ji jikin ta ya dau zafi da alamar zazzab zai kamata,ya sa ya daka mata tsawa, tai tsit, amma idon ta sai hawaye yake,Farha ma kukan take sosai," Malami ka daina firgitan ita,haka xan tafu na bar ma ita baka san meye lallashi ba?" Ta fyace majina tana kare mai kallo, dariya yake son yi dan shi yarinyar dariya take bashi, kamar wata uwar ta, dan dai da gani ba wani girman Lamyah tai sosai ba, amma yanda take mata kamar ita ta haife ta, harara ya watsa mata yace "in zaki wuce ki wuce ni dalla kn sa yarinya zazzabi na neman kama ta," cikin kidima ta taho zata taba jikin Lamyah taji, dan ya bata haushi ya ja Lamyah suka shige gidan suka bar ta nan, dariya kamar ta shaqe shi, suna shiga Lamyah ko ta fashe da kuka, a idon shi da yanda yake jiyo muryar farha kuwa yasan tana can tana masifa, kawai sai ya kwashe da dariya, jan yo Lamyah yai jikin shi yana lallashi,da kyar tai shiru, sai ajiyar zuciya ta ke, waya ya dauka yaji waccan aunty masifar sun isa gidan Momman ne? An sanar da shi sun isa, fadawa Momma yai da a bata dubu dari, dan bai samu sikai rabuwar arziqi ba, sannan a mata godiya sosai, dan tana burge shi, amma yana son kwasar ta yaga tana masifar nan kamar wata uwar mata,