Showing 6001 words to 9000 words out of 52652 words

Chapter 3 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt

07 Jul 2024

12060

yai shima yai kwalamar kar a varshi a baya, wajen mai gadi ya nufa suka bude suka hau cin gara suma, Ameenullah yai bacci a hannun ta tini, karbar shi yai, dan gani yai kamar ya mata nauyi, dan irin yaran nan ne masu jiki bulbul barakallah,ga hasken shi mai matuqar kyau da daukan ido, in ta qura mai ido gani take anya jinin Niger ne yaronnan???






Washe gari da kanta ta shirya shi ta hada mai abun karyawa da taimakon Iya, tinda ta iya girki na zamani ne dai bata iya ba, shima ta daura damban iyawa.







A hankali kulawar Ameenullah ta dawo hannun ta, ita ta take mai komai, tare suke kwana in tafiya ta kama El-mustapha, a hankali ya maida mata sunan ta Ammii, yana kiran El-mustapha Abee, iyayen shi suna matuqar jin dadin hakan ba kadan ba, kusan a duk bayan kwana biyu uku sai sun je, zasu yini ma Aishaa sosai, sai dare su koma, yana kiran Aishaa da Momma, Mus'ab kuma Baaba, ba qaramin gata Ameenullah ke samu daga iyayen nashi hudu ba, sai ga shi a shekara daya da yai da Ameenee ya kusa yin Hizif 30, wanda tana kyautata zaton yana shekara 8 zai sauke alqur'ani, mahaifan uku sunji dadin hakan, kuma sun jinjina ma Ameenee.




A kwana a tashi, yau shekarar Ameenullah uku a hannun su, Ameenee na hango kwance jikin mijin ta,Ameenullah na wajen qafar ta yana matsa mata, yana ta zubo haddar shi, Abee din shi na ta saurara yana lumshe ido, Ameenee na cin yalon da ta sa aka nemo da kyar, sakamakon tulelen cikin dake gaban ta, haihuwa ko wanne lokaci zata iya sallama, tana daga kwance ta miqe da sauri kamar an mintsineta, har tana buge Ameenullah, duk da bakin shi daya dan fashe bai damu ba, hankalin shi ya tashi ganin yanayin da Ammin shi ta shiga lokaci kadan, abu kamar wasa, sai ga Ammin shi na kuka, dan wata irin shagwaba take bugawa El-mustapha, riqe mai wuya tai ta qanqame shi, fuskar ta a girjin shi tana murza kanta dan azaba, " Haerbeebee je ka kirawo Iya da sauri," yana kuka ya fita tare da waigen ta, haka yaje ya kira Iyan, da hanzarin su suka shigo inda ta umarci El-mustapha da fuskar shi ta jiqe da gumi da hawaye da ya kai ta dakin da suka tanadi komai na haihuwa, zuwa yai ya aje ta agaban kujera ta durqusa tadan buda qafa kadan, Ameenullah ya je ya ba hakuri " Haerbeebee ka zauna anan kaji, kai tai ma Ammin ka addu'a Allah ya sa ta haifa maka qanwa ko qani lafiya kaji, kar kai kuka, ka zama namiji, " haka ya dan bubbuga fuskar shi, " To Abii kaima ka daina kukan, inshaa Allah zata haihu lafiya," rungume shi yai, ya dan yi kukan kadan, sannan yai kissing goshim shi ya shige dakin, Iya ta saka komai a qasan ta na tarba jariri, ta dafe kujera yaje ta gefen damar ta ya tsugunna, ya riqe hannun ta daya, dayan ta dafe kujera da shi, yana shafa bayan ta da daya, addu'a kawai take, tana yi ma iyayen ta da suka rasu addu'a, ko tai da qarfi ko tai a zuci, ganin wahalar da take sha ba kadan ba yace "ko asibiti zamu kaita Iya" " karka damu da ikon Allah zata haihu lfy, ni na karbi haihuwar Ameenullah, duk jikokina ni nake karbar haihuwar su," gyada mata kai yai, zai magana kenan yaji Ameenee tayi wani nishi mai qarfi, ta damqe shi kamar zata karya, sai da yai wata 'yar qara, Iya na qara mata gwarin guiwa, akan ta ci gaba da nishin, qoqarin zama take, ta ware qafa iya ta hana, a haka take son ta haihu( in mace ta haihu ta haka ba ta da matsalar samun qari wajen haihuwa, inshaa Allah) wani kyakkyawan nishi da tai sai ga Baby ta fado, ta saka kuka, cikin farin ciki iya ta duqa ta janye yarinyar, sannan ta umarci El-mustapha daya girgiza ta mahaifa ta fado, haka yayi ko, ta nuna mai yanda zai ya kwaso jini daya kwanta mata, cikin nutsuwa da tausayawa,yai hakan, nan da nan ya daga ta ya shiga da ita toilet, ya fara wanke ta da gasa ta, tin a ciki ta fara gyangyadi, suna fitowa waje yai qal, Iya ta gyara har Baby, ta mata wanka,ga qamshi da ke tashi a wajen, bayan ya shirya tane, suka bude wa Ameenullah qofa, fuskar shi tayi jawur, ga hawaye ga dariya, ya rasa wanne zai yi, yana shiga ya fada jikin Abiin shi ya fashe da kukan murna, da sauri ya qarasa jikin Ammin shi ya kwanta a jikin ta yana mata sannu, shafa kan shi tai tana murmushi, ta daga kan shi ta kada mai nata, alamar ya bar kuka,
Iya ce ta miqa mai qanwar shi a hannu, kasa tsaida hawayen shi yai, wata irin soyayyar ta ce ta dira a zuciyar shi lokaci daya, ya qara qanqame ta, yana kissing din ta, " Ammii ina son bbyn nan, tana da kyau, Ammii Allah ya sa tai halin ki, itama ta zama bata duka ko fada" dariya suka saka sosai, " Inshaa Allah ba zata zama me fada ba Yaya Ameenullah, dan kai zaka na koya mata komai" murna ce fal cikin shi har ya zama Yaya ," Abii yau she zata fara ce min Yayan?" Cikin murya ta dariya Iya ta amsa da" In dai ba ta da yanga gobe ma sai ta fara, amma in zata maka yanga sai ta kai shekara biyu zuwa uku" kallon yarin yar dake ta bacci a hannun shi tana tsotsar yatsa yai yace," dan Allah kar ki min yanga kinji qanwata?" Dariya suke tayi dika," zo nan haerbeebee, ba zata maka yanga ba, dan ko Ammii ba zan bari ta fara kira ba Yaya zamu koya mata, kaji yaro na" dadi ne ya kama shi sosai, ya kwantar da kanshi jikin Ammin nashi.






Ameenee ta yi kukan rashin dangi, ita daya a daki, dan ba zata so ya ga ni ba, gudun shigar shi damuwa shima, tinanin ta yanzu haka zata fara tara zuri'a da qanan shekaru, sannan ba ta da kowa, sai mijin ta, murmushi tai dan tina waye mijin nata, ya kasance namiji daya tamkar da ba iyaka, tasan yana maye mata gurbin yan uwa da ta rasa, amma gaba wa zata nuna ma yaran ta a matsayin dangin ta, Ameenullah ne ya shigo, ganin ta na kuka kan ya qaraso wajen ta idon shi ya cika da hawaye, zauna wa yai a kusan rabin jikin ta, yana tambayar ta meya same ta, cikin qarasa gangarowar hawayen shi," Haerbeebee, ka kula da qanwar ka, har girman ku kaji, kar ka bar qanwar ka ta shiga halin maraici, ko da yaushe ka zama kana tare da ita, ina nufin ka maida ta rabin jikin ka, ta zama ba inda zaka iya shiga ba da ita ba, har qarshen nunfashin ku, ka min al'qawari Ameenuna, duk da na san kana da qarancin shekaru amma na san kana da kaifin hankali, da kuma riqe abu,na san ka fahimce ni, kuma ka riqe abinda nake fada maka," gyada mata kai yai yana kuka, yace" Ammii na na miki alqawari zan kula da ita, har qarshen nunfahin mu, ki daina kuka," share hawayen ta tai ta dakko mai ita ta miqa mai, dai dai nan Abii n shi ya qaraso" ashe nan ka gudo ka barni da ball a hannu, " dariya ya mai yana mai gwalo,....
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼








BY HAERMEEBRAERH








Hey guys, ina roqon duk wanda suka tambayen novel dinnan ta pc da su min hakuri sakamakon rashin tura shi ta pc da bana samun damar yi, i am truelly sorry, ku dinga adanawa a wani wajen saboda daga baya in kunji ya maku ku karanta, na gode. ME LOVE U XX❤






Page 5:










Ran suna an sama yarinya Aishaa domin yi wa matar mus'ab takwara, amma shi Ameenullah na kiran ta da Lamyah, ( macen da take baqa kuma siririya) dan gaba daya Aishaa kamar ta daban ba baqa ba kuma ba fara ba kuma bata da wani girma, abu kamar wasa suna ya bita da wuya wani yace mata Aishaa in ba Ameenee ba.


A kwana a tashi har ta kai shekara hudu sai kuma kamanannin ta suka canja, ta fara qiba da haske, kyaun ta ba qaramin ban mamaki yake ba mutane ba, hakane yasa Ameenee bata wasa da mata azkar din safe da yamma, ba qaramin son juna suke ba ita da Yah Amee din ta, haka take kiran shi, duk da baya so amma baya nuna wa sai bata kusa yake ma Ammiin shi magana, " ni Ammii bana son wani Yah Amee, yarinyar nan da akama ramawa tai, dan na bata sunan yar baqa sai ta rama, ai naga tayi haske ta tashi daga baqa yanzu" dariya Ammiin shi da Abii suke mai suce " to ai sau ka canja mata da sunan masu haske maybe ta canja maka kaima," " A'a wannan zai fi mata dadi in ta girma, kuma ma naga ba kowa ne yake da wannan sunan ba ai, zata zama daban a cikin mata kamar yanda take daban itama," sukan kalle shi da so da qauna a cikin ran su su rungume shi.






Wayar shi ce take ringing a gefen shi, suna parlo suna kallo, miqa hannu yai yace " wake kira da darennan?" Yana dubawa sai yaga no qasar su ce, ea mammaki yake nunawa Ameenee har ta katse, aka sake bugowa, nuna mai tai ya daga yaji waye? Daga wa yai ya amsa, yayan shi ne, da suke uba daya, yake wanar da shi cewar Bappan su ba lafiya kamar zai mutu, yana ta tambayar shi, akwai abinda yake son ya bashi, nan take zuciyar shi tai rauni, dan Allah ya saka mai son yan uwan shi, ba kadan ba, hankalin shi ya tashi matuqa, miqewa yai ya shiga daki ya zauna bakin gado, zuciyar shi ta kasu kashi biyu, wani bangaren ana fada mai ya qi zuwa, dan suma sun yada shi, wani bangaren na ce mai yaje ba komai, yaje domin zumunci kuma domin Allah, beside baida kowa nan , can ne tushen shi, yaje ko yar shi ma ta san iyayen ta da suka guje ta, wata qila ma su daidaita, su so Ameenee, kodan hai fa masu kyakkawar diya da tai, a haka ta isko shi, bata tambaye shi ba, saboda ta kula, gaba daya hankalin shi a tashe yake, zama tai dab da shi ta kwantar da jikin ta a bayan shi, ta jingina da jikin gado, ta kwantar da jikin shi a nata, tana ta shafa qirjin shi da hannun ta daya, dayan kuma tana shafa sumar kanshi, a hankali take kissing din wuyan shi, tana hura ma kunnen shi iska, runtse idon shi yai, tin yana jin zafi a zuciyar shi har yaji ba komai, a hankali ta rada mai kalmar" I love u" da murmushi ya janyo ta ta koma saman shi ya ce " iiyeee ashe dai da gaske ake koyon turancin nan" dariya tai tace" ai dole na koyi duk yaren duniyar nan just to tell u how much i lobe u" daga ta yai sama kamar bbyn roba yana dubawa anya da gaske ita ce, na farko ta samu wani courage, hqr tana iya fadan tana son shi, wanda kullum sai dai shi ya fada, in ya matsa ta fada mai sai dai tace itama haka, sannan ga mamakin yanda har wani slanks take a turancin, " tsaya a ina kk koyi wannan turancin ne" dariya tai kan tai fari tace mai " a wajen Haerbeebee" gyada kai yai yana murmushi, can ya tuno da maganar da akai mai a waya, sai yace mata, " Habibty, ina son in kin aminve zamu tafi Dubai nan da kwana biyar, Bappana ba lafiya, da ni da ke bamu da kowa a Nigeria, domin kowan ki ya kuje ki, ni kuma ina son mu je ko shekara mu samu, saboda yarinyar mu ta san yan uwana duk da rashin son da suke mata, ba a san gawar fari ba, a qalla dai ta je" " Zaujee kar ka damu kan ka da neman yarda ta, ni mallakin ka ce, a qarqashin ikon ka nake, ko me kk so, ni zan kasance mai biyayya da mana fatan alkairi" kissing din ta ya shiga yi dan bai zaci zata yarda ba.






A gidan Mus'ab kuwa duk jikin Aishaa da mus'ab din kanshi yayi sanyi, Ameenullah kam har zazzabi yai saboda jin wannan mummunan labarin, sosai labarin ya rikita shi, hakuri suka bashi, da alkawarin in ya gama secondary zai koma can in har basu dawo ba ya qarasa karatun shi, da kyar suka samu ya daina kuka,ranar da zasu tafi kam, kamar Ameenullah ba zai kai ba, sun so matuqa su tafi da shi, amma suna ganin ba zasui ma Aishaa daidai ba, tinda shi kadai gare ta, haka suka tafi kowa na cike da qunar rabuwa da dan uwan shi.






Sun isa dubai lafiya inda suka nufi gidan shi na asali da yake can, an gyara shi kamar wani babban mai muqami na zuwa, haka Ameenee tai ta mamaki dama mijin da take tare da shi kenan? Yaran shi na dane ta kalla ko wanne fuakar shi cike da annuri, cikin harahen larabci daya daga cikin su yace, bai zaci zasu sake ganin shi ba, ba dan aiken da yake masu ba akai akai sai suce ko ya manta da qasae gaba daya, murmushi kawai yai yace, komai lokaci ne ai, gashi da lokaci yai na dawo, maraba suka qara mai suka bat shi da iyalan shi, kowa kallon Lamyah yake cike da so da qauna, dan ganin kyakkyawar yarinya, mai cike da kuzari.


Bayan sun huta ne sun ci abinci sunyi wanka, sika shirya sai asibitin da aka mashi kwatancen a can aka kwantar da Uncle din nashi, isar su ke da wuya, ya hango yan uwan shi uku maza, kowannen su fuskar nan ba alamar walwala, iya abinda ya zata shine jikin uncle din su ne yai tsanani, abinda bai sani ba shine, baqar fatar matar shi ce basu so gani ba, ga tsarabar yarinya da suka gani, isa yai ya miqa masu hannu dan ya kula ko dan rungumar larabawan nan ma ba samu zai ba a wajen su, da kyar suka bashi hannu, da yatsa dayan su ya nuna mai dakin kama Ameenee yai ta qugu sannan ya karbi Lamyah suka shiga, a kwance suka tadda Uncle din nashi, kamar baya nunfashi,yana jin muryar shi ya bude ido a hankali, miqa mai hannu yai da nufin ya isa gare shi, kama hannun na shi yai, yai kissing, a hankali, a hankali ya mai nunu da qasan pillo din da yake kai, daga shi yai a hankali, ya ya dakko wasu takardu, yana ganin ya karba yai murmushi ya koma ya kwanta, shikenan rai yayi halin shi, cikin kidima ya leqa ya kira Doctor da yan uwan shi kowa ya shiga damuwa da tashin hankalin. Bayan an kai shi komai ya lafa ne yana zaune a daki shi kadai, Ameenee tana can dakin Lamyah tana mata wanka, ita kuma sai rashin ji take, tana tsalle2, dan Lamya ba dai son RAWA ba , gata qarama, amma yanda take son rawa abun na ba iyayen ta mamaki, dan dai in ba a TV ba ba ganin Ameenee tai tana rawa ba, dubawa yai yaga wasu takardu ne na dukiya mai tarin yawa, da wasiqa a ciki,wadda Uncle din shi ke neman gafarar shi akan tauye mai hakkin sa da yai, tin mutuwar iyayen shi, yayi kuka sosai shi daya inda nan take ya tina wata magana da daya daga cikin yan uwan shi ya fada mai, kan cewar, ko yaqi ko yaso sai dukiyar nan ta dawo wajen su, mamakin su yake sosai, amma ya yanke shawarar miqa masu dika, dan a yanzu ma yana da ninkin ta, dan haka ba komai dan ya mallaka masu, da gudu suka shigo Ameenee da Lamyah, in da ta biyo ta da rigar ta a hannu suna ta dariya, sai tayi nesa da ita sai ta tsaya tana rawa tana karya qugu, tana daga hannu sama, in taga Ammiin nata ta kusa amata sai ta diba da gudu, wajen Abiin ta taje ta kwanta tana daria, wurga masu rigar tai ita kuma ta kwanta tana haki, " ga shi nan ku qarata, wannan yarinyar sai an mata addu'a ita kenan rawa, na rasa in da ta ke gani, ina jin zamu daina kallon tashoshin rawa a gidannan," dariya tai tace " A'a. Ammii ina so plsssss" Abiin ta ce yace " Baza a canja maki, tasha ba, duk san da kk kallo kinji, abun da nake son da ke shine, ki zama mai yawan karatu da neman ilimi, kinji, in kina qoqari kika zama yarinyar kirki, to har wajen koyon rawa zan kai ki" Ameenee ce ta kama baki tana girgiza nai kai, dan gaba daya ba ta son wannan bangaren na shi na ba wa yarinyar su duk wani abu da take so mai kyau ko mara kyau, amma tai shiru dan ganin bai dace ta mai magana a gaban yar ta su ba.






Bayan shekara 11 a Dubai da sukai, kullum suna waya da ita da Yah Amee din ta da Momma Aishaa, sai Baaba Mus'ab din ta, cikin da Ameenee ke dauke da shi ya girma sosai, in da yanzu Lamyah mai shekara 16, kowa ya ganta sau daya sai yai saurin sake juyawa dan kallon ta a karo na ba iyaka, tsabar kyau, da shape din da take dauke da shi, ga gashin ta mai tsaho da cika, santsi da baqi, Lamyah ta zama yarinya mai matuqar kyau son kowa qaunar wanda ya rasa, ga ilimi dan tinj ta sauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login