Showing 21001 words to 24000 words out of 52652 words

Chapter 8 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt

07 Jul 2024

12067

mene ne so ba, so ba ruwan shi da waye kai, wana matsayi ka taka a rayuwa, wace kala ce fatar ka, ya tsahon ka yake, ko ya jikin ka yake, da ya tashi shiga zuciya baya kwankwasa, fadawa yake cikin zuciya, ba notice," tabbas Lamyah ta fada tarkon son baqon da bata sani ba, dan na tabbata in da dane wannan cakwaikwaiwar take wannan zuba zamcen sai ta katse ta, ko ta bar wajen , amma wannan karon lumshe ido take tana jin tabbas in haka ake so to itama ta fada tarkon shi a farkon ganin ta da wannan bawan Allah da ko sunan shi bata sani ba, Farha ce ta katse ta, " Kar dai ki ce man tin da na fita har yanzu haka kk baki motsa ba, naje Bala baya nan Baba ya ake shi," ta qarashe cikin zumbura baki, kwantar da kan ta tai akan cinyar Lamyah ta juya bayan ta, Lamyah ce ta dora hannun ka akan ta tana shafawa," Farha me zai hana wani satin Bala ya kaini Rimin Gata? Na matsu na ga dangin Ammii na yanzu ko na gaggauta wucewa Niger neman Yah Amee, saboda Farha my heart us trying to betray me, tana son kuma ta ci amanar Yah Amee, tabbas in abinda nake ji ya tabbata zan shiga uku, Farha zan shiga matsananciyar damuwa, domin zuciya ta bata kasamce daga cikin masu adalci ba," Farga dake kwance tana lumshe ido jin kalaman Lamyah sai zuciyar ta tai sanyi, gaba daya tausayin ta ya kama Farha, musamman da taji ruwan hawaye a kafadar ta, miqewa tai ta zauna kusa da Lamyah sosai ta jawo ta ta dora kan ta a kafadar ta( duk da dai ba wani tsokar arziqi sai dai ma ta soke wa baiwar Allah kumatu da qashin kafada🙊) lallashin ta ta yi sosai sai da ta gama kukan ta sannan tace mata " Lamyah ki sani Allah baya dorawa rai abinda ba zata iya ba, wannan wa'azin ki ne, ina son kamar yanda kk fadakar da mu kullum ya zamana kema kina saka maganganun ki a cikin aiki inshaa Allahu zaki samu komai da sauqi, don Allah ya hore maki sanin daidai da kuma abinda ba daidai ba, sai ki gode mai ta hanyar amfani da su din, ina roqon Allah daya yaye maki damuwar ki Lamyah na," da Ameen ta amsa, sai taji zuciyar ta wasai, tashi sukai suka shiga daki, Lamyah ta fara fiddo masu da kayan da zasu saka da dare, wasu skirt ne masu hade da dan gajeren wando a ciki, skirt din iyakar shi guiwa, sai rigar da ba ta wuce masu cibiya ba, iri daga multicolor ne kayan, kusan kowacce kala akwai a jiki, amma ya sha adon stones, masu kyalli,n golden a jiki," wai ban gane ba kin kwanta?" " to mi zan, dan Allah barni na dan taba bacci kafin daten yayi, yau na gaji haka kawai nake jin gajiya , kewar Bala ta cikan zuciya, rabona da shi tin shekaran jiya fa," juyi tai ta kwanta abinta, Lamyah ta dakko masu takalman sunda zasu saka nan ma ta aje, sai abayar da zasu dora, tashi tai ta tafi kitchen ta dakko cucumber ta markade bata wani saka ruwa ba amma saida ta yanka qanana sosai, tana fara markaduwa sai ta debo madarar shanu, da zuma sannan ta saka kwai a ciki, sai dan tomeric powder da cinnamon powder da ta zuba, qara markadawa tai saida suka hade tsaf, sannan ta juyo a dan mazubi, dakin su ta koma ta dakko masu zannuwan da suka ware don gyara jikin su, dadawa Farha duka tai a yar cinyar ta da ihu kuwa ta miqe, dariya ta saka , ta miqa mata zanin, harara ta banka mata " dan cin zali kawai ina kwance har bacci ya fara dibata, ki makan duka a cinya sai kin lotsamin ita," dariya abun ya ba Lamyah sosai," me din zan lotsa kamar wata katifa? Ke ai sai dai a karya ba dai lotsawa ba," Farha ce ta biyo ta akan sai ta rama kuwa tun da abun haka ne, aiko suka fara zagaye dakin, da Lamyah ta samu dama sai ta shafawa Farha wannan hadin , sannan ta kwasa da gudu, a haka har suka gaji suka zube a gado, suna maida ninfashi, bayan sun sha dariyar su ne suka tashi kowa ta shafe jikin ta fea da shi," wai ni wannan kuma na meye, kusan kullum sai kin fiddo da sabon abu, duk lokacin gyaran jikin mu yai sai naga sabon abu kk fiddowa ina kk koya?" " a gaskiya a kwa wadan da Ammii na ta koyan, akwai wadan da da kaina na qirqira," " gaskiya na gode dan i want to look beautiful for Bala today, sai ya rasa gane wacece wannan, shin canjo ni akai," sai ta dira wani tsallen murna, Lamyah kada kai kawai tai tana murmushi, dan Farha na bata dariya, ko dake shima Balan ya mato akan ta ba kadan ba,dai dai sun gama ne Mubarak ya shigo, a duniya in yaga su Lamyah sun yi abunnan tsoro ke kama shi, aikk zaro manyan idon shi yai waje ya kama baki, juyawa zai da gudu ya fice aiko abokiyar fadan shi ta cafe shi, shafa mai tai a kuma tu, yana bude ido sika hada ido da fuskar ta da tashi, ya kwalla qara, yana qoqarin sauka, ta hana shi, sai tsorata shi take, Tani ce ta shigo ta karbe shi, " yaro gobe ma ka qara min rowar chocolate din ka, in ba sai na ma wanda ya fi wannan ba, ko kai kadai kk son yin qibar," " to laifi na je da komai kk ci baki qibar," ya fada cikin kuka sannan ga tsoro ar the same time, ai ko cikin fushi ta zabura zata damqo shi ya kwalla qara yace " Tani dauke ni kar ta kama ni," ba Farha ba har Lamyah dake gefe tana sha'anin gaban ta sai da ta sa dariya.












Qarfe takwas da kwata a bakin mota tai masu, wani irin kyau da qamshi ke fita a jikin su, fuskar su tai wani haske mai bam sha'awa, ga shi ba tabon komai tai smooth, Farha na ganin Bala ta fara karairaya har suna hada baki da Mubarak," Bala my baby,"cike da tsokana Mubarak shima ya karye qugu yana yarfa hannu, yanda take yi, ya maqe murya shima sannan ya fada, aikk juyo wa tai zatai magana Lamyah tace," haba ke kamar baki san Mubarak ba, so yake ya bata maki rai, ko hirar ma da Balan ya gagare ki," kwafa tai ta juya tace "zamu hadu ne ai watarana," Bala ne ya qaraso cike da Fara'a ya iso, aiko tin da suka shiga ba abinda ke tashi sai surutun Farha, Bala shi ko dadi yake ji a ranshi, dan muryar abar qaunar shi ba qaramin sanyaya mai take ba, amma Mubarak da Lamyah sun juya idon su ya fi sau a qirga, a haka suka isa, Lamyah ce ta fito cikin faduwar gaba,yau kuma me za ta tarar, haka suka wuce dakin da suke shiryawa, ko ta ina ta wirga ido bata ga Handsome ba, Farha yau cewa tai ba inda zata tana wajen Bala zasui qala'in hirar da ba sui ba tin shekaran jiya, Lamyah ce tai ma Mubarak kiss a goshi ta tafi, tafe take cikin yanga, ta isa dakin da suke kwalliya, Faisal ne ya leqo, "ya kyakkyawar kin shirya ne," daga mai kai kawai tai,kamar yanda ta saba bata magana yauma haka, " ina Farha? Na manta ba ma magana zaki min ba muje kawai," ya sa ta gaba suka isa filin, tafi da ihun mutane ne ya sanyaya zuciyar ta, ji tai wani nishadi ya kama ta, dan ita abinda ke burge ta kenan, hawa tai cikin qasaita da isa, ta fara rawar ta cikin tsantsar kwarewa, da gwanancewa a kowanne stape ta dauka, ta shagaltu da rawa sosai, in da wasu maza su uku suka hada kai, ni kaina saboda qarar kida bana jin me sike fada, tafawa naga sun yi, sannan suka isa gaban ta, kudi masu yawa sosai suka watsa mata, dayan garin watsa maya kudin sai da yai dabara ya taba cinyar ta da ta fito, aiko ji yar kamar ya saka hannin shi cikin buhun flour dan laushi, ji.yai he wants more, qara miqa kudin yai ya shafo gefen qafar ta, nan da nan jikin Lamyah ko ya dau rawa tsoro ya shige ta, a hankali ta fara rage takun ta alamar ta kusa sauka kenan, ta tafi, dan gujewa wadannann mayun da ta kula sun sa mata ido yau, wandon shi har wani dagawa yake dan tsabar jaraba, lashe leben shi yake, yana mata wani irin kallo haka ma abokan shi, nan da nan kuwa ta sauka, tai hanyar tafiya wajen kwalliyar su, binta suka so yi amma suka dakata, tana isa jiki na rawa ta janyo abayar ta ta saka, Faisal ne ya iso da kason ta wanda a yanzu suna karbar wajen dubj dari da ashirin, saboda manyan yaran dake zuwa kallon rawa, nan take ta karba ta saka a jakat, wani guntun murmushi ta sakar mas, ta sa kai ta wuce shi cikin sauri, magana yake mata ma bata kula shi ba, a hanyar ta ta fita ne ta ci karo da wadannan samarin, kan ta daga kai ta ankara da su har sun zo dab da ita, shafo fuskar ta dayn yai," kaiiii yarinyar nan amma ke jinin indiawa ce ko? Ko larabawa, ko turaw? Amma dai ba bahaushiya ba, to wataqila bafullatana?" Dariya suka saka daidai lokacin da dayan su ya janye mayafin ta, gashin ta ya bayyana, ya rufe fuskar ta, kuka ta fara tana qoqarin yin magana ta roqe su ne, sai ga Ameenullah, zai zo leqen rawar ta, sannan ya kira Faisal, yana ganin haka kuwa da gudu ya isa wajen, bai tsaya bata lokaci ba wani bahagon naushi ya sakarma dayan da ya kai hannun shi jikin ta, sannan ya kama hannun ya ja gaba ya mayar baya da qarfi saida yai qara, aikk take wannan saurayu ya kwalla ihu, jin haka yasa sauran saka gudu, wurgashi gefe yai yana bins hi da wani mugun kallo, jan hannun ta yai suka bar wajen, motar shi ya wurga ta, fuskar shi kamar a kai ake tutu dan yanda ya bata ta, kwatancen da Faisal ya mai na gidan su a jiya wajen surutun shi ya ke bi,mamaki ne a ranta amma kukan da take yaqi qarewa haka suka isa gidan su, suna isa ya bude pin din bangaren ta, budewa tai ta sa kai ta fita, kan ta shige gida ta juyo da niyyar mai godiya cikin bacin rai yace," in da kin san baki kware a yawon karuwancin da kk fito ba da zaman ki kikai a gida, dan gaba ba abinda zai sa ni taimakon ki haka ta sake faruwa," da gudu ya ja motar shi ya bar wajen, cikin kidima da kalaman shi, masu qona zuciya ta shiga gida da gudu tana kuka wiwi, ga muryar shi da ta riki ta ta, kamar ta san muryar? To a ina?.....








...










*Haermeen Haermmaerh na son ku da yawa, dan haka take sanar da ku cewar ko wacce mace ta iya creating abubuwan da suka dace tayi ba sai an zaunar da ita an koya mata ba, ke sa kan ki kina zaune zaki iya cewa bari na hada kaza da kaza na saka a miya naga yau ya zai, ko na hada kaza da kaza nai gyaran jiki na ko gidana ko dakina da dainsauran su, be more creative gurls, Allah ya hore mana fasaha da fahimta, Me Love u XX❤*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAN RAWA 💅🏼







BY HAERMEEBRAERH






Page 15:












Haka Lamyah ta kwana cikin tsananin baqin cikin kalaman wannan bawan Allah, da ko sunan shi bata sani ba, ga kuma baqar magana daya gasa mata, ga muryar shi da tai mata kama da ta san ta, to a ina? " kaiii this is so complicating," " meye yake complicating din sis na? Is it the fact that you run back home with out letting us know, or is the fact that i have come to understand cewar Handsome ne ya dawo da ke?" "Gurl pls kui hakuri, wani abu ne mummuna yaso samuna amma Allah ya kare wannan dan rainin ya taimakan," ta fada tare sa gyara kwanciyar ta, ," hmmmm kin san tashin hankalin da kk saka ni? I was so worried, ji nai kamar na sa hannu aka naita ihu, inna rasa ki a rayuwata ban san ya zan ba, na rasa kowa nawa, ina zan saka kaina," Farha ta qarasa tana kuka sosai, " kar ki damu my sis, kinji, qafata qafar ki duk inda zani, yanzu ma si nake ran asabar dinnan mu je dangin Ammiii mu ga ni ko za mu dace su karbi abinda ta haifa, wataqila sun sauqaqa min fayyace wa Mubarak mu su waye, in kin amince ko ina zani ke mai iya zuwa ce in dai ba Bala ne zai hana ki ba sai kui zaman ku anan,ke ko auren ki kina iya wa ki zaman ki nan," rungume ta farha ta yi tana mai zubda kwalla, dan yau surutun ta ya qare, ta samu sister from another mother, tabbas ta yard akwai masu kafa zumunci ba tare da sanayyar komai ba.




Yau farha da asuba bayan sin kammala komai da suka saba, karatu, addu'a, azkar, bata koma bacci ba, wanka tai wa Mubarak, ta hada kayan su,Farha ta so bin ta, amma tace su je ita ta zauna ta kula da gida, bayan nan ma ya kamata ta ci gaba da zuwa rawa, dan so take in auren ta ya tashi, tai ma kan ta komai, zataji dadin hakan,sosai, suna kuka kamar wadan da aka ce ba zasu sake haduwa ba suka rabu, Bala na ta aikin ban hakuri, ya rasa wa zai lallasa cikin su, a haka ya ja mota suka dau hanyar Rimin Gata, suna isa, suka nemi a nuna masu gidan mai gari, nan ko aka kaisu, bayan 'yan gaishe gaishe da kuma tambayar su waye? Lamyah zama tai ta labarta masu komai da ta sani game da mahaifan nata, hawaye taga mai garin na sharewa, duk ya yamushe ya takwarkwashe," oh ni Haladu, ashe ina da rabon ganin zuri'ar Malam Muhammadu ta kwarai kuma a rayuwata? Wadan can yara nashi da suka rage 'yan asara, wahalallu da uwar su ta tsaya masu sui komai da suka ga dama, ko ganin su bana son yi, ina takaicin ace wai zuri'ar Muhammadu ne su, 'yannan Allah ya miki albarka, ya raya mana ku da imani, Allah ya jiqan iyayen ki, sallama akai tare da jinkirtawa, sai da akai mai izinin shiga sannan ya shiga, " Barka da rana Abba, ya kufan jikin?" " barka dai Musaddiq, jiki da sauqi alhamdu lilLAAHi, daga ina haka da uwar ranar nan, ko an kammala bautawa qasar ne yasaka dawowa?" "Eh Abba, nayi ta gwada layin ku jiyan na sanar da ku dawowa ta, sai inna kira yaqi shiga, nace kawai kun ganni," ya qarasa cike da fara'a addu'o'in alkairi mahaifin nashi yai ta mishi, shi kuma yana amsawa, gabatar masa da Lamyah mai gari yai sannan ya mai bayanin ta, dan yana da masaniya akan labarn Ameenee, da El-mustapha, daga kai sukai a tare dan su kalli juna su gaisa, Lamyah a kunyace ta gaida shi, shi kuma kasa amsawa yai saboda ganin tsabar kyau a tattare da ita, sai da mahaifin shi ya maimaita mai me ta ce sannan ya amsa baki sake kamar wawa, umarni mai gari ya mai akan yai leading din su ciki,Bala kuma zai koma a ranar, tare da mata alqawarin dawowa,shi da farha taga wajen, sallama sukai, Mubarak nata kuka, akan zai bi Bala, da kyar aka lallashe shi , Musaddiq ne ya dauke shi yana mai wasa, suka shiga ciki, shigar su ke da wuya, ya nufi dakin uwargida wato mahaifiyar shi da ita, qawa ce a wajen Delu, duk da halayyar su ba ta gama zama daya ba, amma kusan daya suke ta bangaren kishi, banda kishi bata da matsalar komai, bayan gaishe2 da gabatar da su Lamyah ne ya aje Mubarak yai dakin shi, yana shiga ya dafe qirjin shi, at d same time kuma ya daka tsalle ya fada katifar shi, " nayi mata nikam, ya Allah in wannan baiwa taka rabona ce Allah ka bani ita, innba rabona bace Allah ka musanyan da mafi alkairi," lumshe kyawawan idon shi yai, yana tinanin kyakkyawar fuskar ta, murmushi yai, yace " Lamyah" .










Lamyah bata samu matsala ba a kwana hudun da tai a gidan mai gari, sai dai abu biyu kr damun ta, har yanzu ba'a hada ta da dangin mahaifiyar ta ta ba, balle kakar ta, sannan wannan dan mai garin fa na takura mata, da nacin kallo da magana, yauma zaune take tana shan Tea, ita da Mubarak, ya shigo, " A'a qanwata, me kk ci haka, ba gayya , miqa hannu yai ya karbi cup din hannun ta, ya daidaici inda ta saka baki, ya sha, tare da lumahe ido, a ranshi yana ayyana wataran fa bakin ta zan ji a nawa, da sauri ya bude idon shi, dan gudun. Kar ai abin kunya, sai yaji ma kamar ta gane me yace, kauda kai yaga tayi, cike da kunya tace, " Yah Musaddiq, ragowa ta fa ka shanye, kuma ni ai ban qoshi ba," ta qarashe cikin shagwaba, daidai nan Inno ta shigo ta same su, wani kallo tai wa Lamyah ta kauda kai, ta shige daki, kwalawa musaddiq kira tai, ya miqe yana cewa Lamya ta bashi 2mnts, kada kai tai tana mamakin yanda yake rawar qafa akan ta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login