Showing 51001 words to 52652 words out of 52652 words
Chapter 18 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt
alamar jira yake a saka mai ita ya goye, sukai sallama, leqowa Inna tai, taga su waye, ganin Lamyah ne ya sa ta zaro ido tana leqa bayan Lamyah taga ita da waye? Dan tabbas ba ta son qara haduwa da Farha ko a hanya, ganin ba farha ne yasa ta dan pito waje,fuskar ta ba yabo ba fallasa, dan yanzu ta gama gane komai game da Lamyah, tsananin kishi ne ya sa Delu ke kushe su ai ga shi nan ta ga ishara itama,sannu da zuwa tai mata ta shiga da ita daki, ta saka mata tabarma, su Yah Amee da Bala tare da Baaba da Mubarak na fadar mai unguwa, Momma ce ta fara zama, tana kallon gidan, a nan ne wai akai wa Lamyah wulaqanci? Sai kace wata uwar ke gare su, gaishe gaishe sukai, dai dai lokacin da Musaddiq da Saddiqa suka fito, dan suga su waye, kwata2 qin yarda yai Saddiqa taje gida inda dan ta'addan dan Delu yake balle aiwa iyalin shi irin na Delun, " Lamyah sarkin rikici, nikam Baban Lamyah anya 'yar uwata ba tai rikici ba tana qarama? Ka duba kaga yanda yarinyar nan ke hana mu bacci? Badan inna na taimaka mana ba," " ba wani riki......." maganar shi ta maqale sakamakon arba da Lamyah babba da yai zaune tana ta maka mai murmushin ta mai kyau, da sauri ya daga labulen ya shiga," Lamyah? Os that you?" " ni ce Yah Musaddiq," ta fada tana miqewa, kallon kallo sukai ita da Saddiqa wadda ta isa da hanzari ta rungume Lamyah, gam kamar za a kwace ta, idon ta cike da hawayen dadin ganin 'yar uwar ta,murna sukai sosai da ganin juna, gaisawa sukai sannan Lamyah ta tsokani Musaddiq," Yah musaddiq a ban takwarar tawa mana, duk da dai naji ana man sharrin rikici," ta maida kallon ta kan Saddiqa," Aaa yanzu ai dana gan ki na janye, sai dai gado tai wajennnnnn," tana kallon Musaddiq daya jefe ta da hararar masoyan da suka shaqu da juna su, hamdala Lamyah tai cikin ranta,dan da dikkan alamu burin ta ya cika, " Yah Musaddiq tare nake da Baaba da Yah Amee suna fada," inna ce da ta fitk daga gurya dauke da jug da ruwan randar sanyi ta ce," kash amma dai ke ma akwai wauta, da baki magana ba wannan yaron ya kai masu koda ruwa ne? Maza tashi ka je ka kai masu wannan bari na kawo maku wani, " yana qoqarin miqewa ne yaji shigowar su ciki da Mai Garin, dake babban parlor ne wajen dan haka zai ishe su dika, shimfida akai ma mai garin ya zauna, bayan gaishe2 ne, da ban hakuri, Baaba ya debo kudi masu yawa ya bawa Musaddiq yace a saiwa Baby kwalli godiya sukai sosai,inda Yah Amee yace ya dau nauyin karatun ta itama har University nan take ya rubuta cheque ya basu, dan yace yana son amaryar shi tai karatu sosai, nan akai wasa akai dariya,inda Yah Amee ya buqaci ganin gidan da aka haifi Ammiin shi, nan take mai gari da Inna sika kalli juna suka sadda kai qasa," ranka ya dade na sha fada maku, in kana jin tsoron wancan shashashan a matsayin ka mutanen ka su ji me? Ka dinga daurewa kana nuna isa da izzar ka a matsayin ka na mai shugabantar wannan unguwa," " Bawai tsoro nake kar naje ba Musaddiq, baqin mu ne bana son su fuskanci matsala daga wajen shi musamman in muka je bai bugu yai bacci ba,dan har ni za a je," " me kefaruwa ne?" " ba komai ku tashi mu je," miqewa sukai, Lamyah duk tsoro ya cika ta, da tsoron sake ganin Delu.
Shigar su gidan ke da wuya suka ji wani wari sosai,toshe nacin su sukai, suka qarasa tsakar gidan duk datti qasu qananan yara ne, a zazzaune a rakube, sai wani mutum a qasa kayan shi sunyi baqiqqirin, shi kanshi kamar mahaukaci, a hakan wai bacci yake, wata mata ce qemasassa ta bushe bazata wuce 34 ba amma kamar ta fi haka dan wuya, Hamza ne ya fito shima daga wani daki da sanda a hannun shi, ," Kulu su waye nan?" " me gida ban san su ba nima amma dai da mai gari da dan shi babba sai Innar mai gari," " To to to ya yi ku shigo bismillah, Lamyah ce ta tiqe Ameenullah dan tsoro da kuma aman da ke taso mata, da sauri kuwa yace,"A'a nan ma yayi dan va dadewa za mui ba," Inna ce ta je wani qofar daki ta daga labulen Delu ce kwance kamar matacciya, ga qafar ta day ta rube, sai fuskar ta ta gefe da ta dauje wajen ya kumbra shima yana ruwa, aman da Lamyah ke riqewa ne ya balle, aiko ta dinga kwara shi kamar ta amayar da hanjin ta, da kyar Delu tai magana," su waye anan?" AMEENULLAH NE MIJIN LAMYAH DIYAR AMEENAATOU ji tai kamar an kwada mata guduma aka, qoqarin juyar da kan ta tai cikin azaba, da kyar ta kalle su,sai ta saka kuka," yar nan ki yafe min ko na ga daidai kan mutuwa ta, ko Allah ya yafen kadan daga laifukana," shima Hamza rusunawa yai yana kuka yana neman yafiya, Lamyah da kyar take magana itan ma kukan take," in dai haqqi na ne ya kama ku haka na yafe maku,zan so ace mahaifiyata na nan ta yafe maku itama ko kun samu sauqin wannan azabar," Hamza ne ya fara basu labari akan lalurar su.
Wata uku da suka wuce ne muna zaune ni da gyatumar mu muka ji kawai an shigo ba sallama,daga kan da zamui sai muka ga dan uwana da ya bar gida sakamakon shaye2 da dabanci,cikin doki Delu ta miqe ta isa gare shi shima ya gaida ta kamar abun arziqi, nan muka bashi abinci da ruwa yai wanka, kwatsam rannan na tafi gona na dawo, sai na tadda dan uwana a dakin iyalina, ta taushe mata baki ba damar tai ihu, Delu naje na kirawo, aiko bai daga ta ba sai da ya ida nufin shi, ya fito yana gyara wando, yana maganar ashe haka nake kwasar gara, daga yau sai dai a raba ta da shi, nai k kukan kura na kwada mai mari, fusatar da yai ta sa ya shaqe ni ya sa gannuwan shi cikin idona ya danne, nai ihun neman ceto , ganin haka Delu ta dakko muciya ta kwada mai, yana juyawa ya kalle ta ta tsorata ta kwasa da gudu, a nata kallon waccan katangar zata iya tsallake ta ne, tana dira qafa daya ta karye, ta fadi kan marmara, bai kula ta ba, ni kuma nan take naji bana gani, munyi kukan azaba ranar ba mataimaki, matata dan qunci da tsamin jiki, dan saida ta sha duka sosai a wajen shi ya samu nasara akan ta, ba zata iya tasowa ba, haka muka wuni zubur, sai da yaran mu sika dawo daga gidan yayar su suka taimaka mana, wannan shine abinda ya same mu bamu da yanda zamui da shi ga shinan kuma bamu da kudin magani.
Lamyah sarkin tausayi,kuka take riris,ran Ameenullah kuwa ba qaramin baci yai ba, dan irin kukan da suka sata,miqewa yai ya zaro waya yai waya sannan ya miqa masu kudi masu yawa sosai,yace kar su damu nan da wasu mintuna za a zo a dauke masu shi a kaishi inda ya dace da shi, sannan ga kudi nan su nemi lfyr su, sun tainaka masu ne kawai dan Saddiqa da ko kallo basu ishe su ba, godiya kam sun sha ta, ba iyaka.
Bayan sun koma gida ne Lamyah jiki ya tsanan ta, asibiti kawai Ameenullah ya wuce da ita, gaba daya Mubarak da Naufaliyyah sai kuka suke, ganin yanda jikin ta yai, suna isa likita ya duba ta, gwajin farki suka gano ciki dan wata hudu a jikin ta,tsananin mamaki kam Ameenullah da Lamyah sun sha shi, ciki har wata hudu ba su sani ba? Ta yaya? Ikon Allah, shine abinda Lamyah ke ta fada kenan, nan take ko ya hau waya yana sanar wa, kafin kace me su Farha an iso, dan da Bala yace su zauna kuka tasa, sai da aka zo da ita.
*Bayan shekara hudu*
"Uncle Mubarak zan sha nima" wata kyakkyawar yarinya ce take fadan haka, ta sha gayun ta da irin kayan mutanen Nijer,gashin ta har bayan ta, an raba biyu an daure kowanne gefe, da band kala2, sai rigar ta data sha saqi fara, da zanin ta blue dark, sai dark blue din takalmi, da sarqa da dan kunne farare, na bits, Ameenaa kenan, diyar Lamyah da Ameenullah, Lamyah na gefe, tana karatun ta a Laptop, Ameenullah na zaune yana kallon Mubarak da Ameenaa.
Mubarak ne ya miqa mata chocolate din Diary milk tai ta tsalle tana murna kuwa," Mubarak dama baka bata va yarinyar nan so take tafi maman ta shan chocolate fa wasa2," tura bak tai ta tafu wajen Lamyah da gudu ta haye cinyar ta tana shagwaba, " yi shiru Ammii na ki sha abin ki in ma basu baki ba zan siyo maki da kaina," " ai ku kam sai Allah abu daya ne kk qi koya mata har yau a halin ki," matsawa kusa da su yai ya rungume su dika bayan ya bisu da kiss, " meye shi?" " RAWA" harar wasa ta mai, sikai dariya,gani nai Ameena ta miqe da gudu tai wajen Naufaliyya da ta riqo hannun wanj qaramin yaro suna kiran shi Sultan, yaci sunan Baaba Mus'ab, wasa ta ja shi inda ita kuma Naufaliyya ta ke tahowa wajen su, tin daga nesa suke sakarwa juna murmushi.
*ALHAMDU LILLAAH NA GODEWA ALLAH DAYA BAN IKON KAMMALA WANNAN NOVEL MAI SUNA 'YAR RAWA, UBANGIJI YA SA MU AMFANA DA ABINDA KE CIKI NA ALKAIRI. WADDA NA BATA WA RAI DAGA FARKON NOVEL DINA ZUWA QARSHEN SHI INA NEMAN TA YAFEN, LAIFIN DA NAI A CIKI ALLAH KA YAFEN.*
*HAERMEEN HAERMMAERH NA GODIYA. LOVE U XOXO❤*