Showing 15001 words to 18000 words out of 52652 words

Chapter 6 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt

07 Jul 2024

12069

" Abii hannun wa ka bar mu? Ina zan samu Yah Amee na ? Ya zan na samu Baaba Mus'ab ? Ban da tabbacin dangin Ammii zasu karbe mu, na fi son sai Mubarak ya kai matakin Secondary,a qallah dai da wayon shi, sai mu je, don ko sun koren ba zan ji kadaici ya min yawa na rashin Ammii ba" kuka suke dikan su su ukun, kwankwasa qofar akai, da kyar Farha ta tashi ta miqawa Lamyah Hijab din da ta gani a ninke a gefen kujera, ita kuma ta maida rigar ta, sannan ta je ta bude qofar, Bala ta gani, murmushin qarfin hali tai masa, izini Lamyah ta bashi ya shiga, ya zauna a gefe, " Farha na sha gaya maki ki daina kuka, kowa da kk gani a duniya akwai rayuwar da Allah ya tsara masa, taki jarabawar kenan, dan haka ki ragewa kan ki damuwa, ko kin daina ramar nan da bana so" ya qarasa cikin fara'a, murmushi tai, cike da shagwaba tace" Allah Bala in ka qarasa abunda ke zuciyar ka zamui fada" " Habaaa ni.na isa nace maki qugu kamar an daurawa tabarya zani? Wane ni?" Ya fada yana kama baki, murmushi sukai, in da Farha ta nemi izinin sanar da Bala komai, dan Farha ta dauke shi aboki, shine dai ke baya2 da ita, dan a unguwar sun dauke ta a ' Yar mace, kuma karuwa, Farha batai ilimin boko mai zurfi ba, dan mahaifiyar ta ta rasu tana SS1 so yanz haka shekarar ta 16, wajen karatun islama kuwa, itan A ce ba B ba, dan akwai shi sosai, wannan dalili ne yasa Bala ke koya mata karatun bokon sosai, bayan Bala yaji labarin dika, ya matuqar tausaya ma wadannan bayin Allah, da kan shi..... dan shi ta shi uwar rabuwa sukai da Baba mai gadi wai ba zata iya rayuwa da miji mai gadi ba duk kyaun ta, haka dai ya sallame ta, shi ko Bala yaqi binta dan bata da dalili mai kyau.




A haka Bala, Lamyah, da Farha suka zama abokai, qoqari Lamyah tai ta koma makarantar boko, inda Baba Mai gadi ya shige masu gaba a matsayin uba, ita da Farha, suka koma, suka fara daga SS1 , dan su samu su shiga University, su samu damar yun ilimi, dan sun kula ba zasu samu rayuwa mai kyau ba ba ilimi.














Mubarak kuwa mai aiki Lamyah ta dakko, take kula da shi ta musamman, wata dattijuwa ce sa bazata wuce 45 ba, mai suna Tani, waiiii Tani ba dai magana ba,ita da Farha Lamyah na rasa wa ya fi surutu, in suka fara wataran tashi take ta bar masu wajen.






*Bayan shekara uku da wata biyu*






Result din su Lamyah ya fito,kuma yai matuqar kyau, inda suka samu duk abinda suke da buqata. Mubarak ya iya magana, yai wayo, kamannin shi da Abiii na qara fitowa, sau da damar lokuta, Lamyah kan sashi gaba tai ta kuka, yai ta tambayar ta Mummy mene? Dan sunan da yake kuran ta kenan, a zaton shi ita ce mahaifiyar shi, san da ya fara kiran Lamyah da wannan suna ta sha kuka, dan ba qaramin tausaya ma kansu tai ba, bata hana shi ba, sannan bata bari kowa ya hana shi ba.......






















*to makaranta ga dai lamyah an gama secondary, kun san dai yanzu kyau ba a magana, ko yaushe zata fara rawar? Ni na matsu ta faraπŸ™„*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ ' YAR RAWA πŸ’…πŸΌ








BY HAERMEEBRAERH








Me koko kawas, this page is for u dear, ai sana'a lfy, sana'a goma maganin mai zaman banzaπŸ˜‚ ME LOVE U XX❀












Page 10:
















Lamyah ce zaune tana ta danna waya , tayi sabbin qawaye, ta whatsapp, ta sanadin Farha, wadan da da damar su masoya rawa ne, hirar wata waqa suke da tanda ake stapes din rawar waqar, yanda Lamyah take bayani ba qaramin burge su tai ba, dan ta nuna masu ita fa gwana ce wajen rawa, ji tai an zauna a gefen.ta, " kaiii kaiii waye wannan dan Allah ni duk zaki soke ni da qashiπŸ™„" ai ko Farha ta ji haushi dan ba ta so ana zancen ramar ta, qara zaune Lamyah tau tana dada sossoke ta da guiwar hannun ta, ita kuma Lamyah tana ta dariya dan abun kamar cakulkuli yake mata, Tani ce ta shigo, riqe da hannun Mubarak, yana ganin su haka da gudu shima ya taho ya haye" Mama Tani kina gani sun min taron dangi ko?" Dariya Tani tai tace" Hmmm yanzu na topa nawa ku juya ni kumin taron gari ba, ba ruwana haka na ganku, in kun gama ku taso ku ci abinci," miqewa sukai suna murna, dan dama yunwa suke ji, abinci suka.ci suka zauna suna hira," Lamyah yaushe zamu je wajen Faisal ne, kema a saka ki a wannan harka, ki fara, shiga taro kina bada mamaki? Dan na kula burin ki kenan, ki rawa a kalla a yaba maki, dan na san za sui matuqar son ganin taki salon rawar," kaiiii Farha wannan dogon sharhi haka, ni ko yau da yamma muje Bala ya kaimu," "yippyyyy, ba ri naje na dau wankan sikari, yau sai mun ba ma yara mamaki, dan kaf stapes din ki ba wanda ban dauke ba, yai sai....." " My goodness Farha, do u really need to talk much all the time?" πŸ™„ " yeh right, ya kamata na nutsu kar a raina mu, dan kin san akwai ni da maqiya a wajen nan basu son a ce yau ni zan rawa , dan ba qaramin kudi nake samu ba, sun san bana bin ko wanne qato daki, so kudin dana ke samu na daban ne" " mu ai ba ruwan mu da kowacce qatuwa kawai burina bai wuce nai rawa a min tafi ba na burge kowa sai naji nishadi a zuciya ta," haka sukai ta tattaunawa, har biyar na yamma, Lamyah ce ta fara tashi ta shige dakin su, dan tare suke kwana, yanzu mubarak ya zama yana kwana shi daya, wannan dalilin ne yasa suka ware mai daya dakin shi daya, Tani da sassafe take zuwa sai takwas na dare take tafiya.




Bayan sunyi saallar isha'i ne suka yi ma Bala magana, ya fiddi mota, kowaccen su ta sha baqar abaya, tai rolling kanta, cikin ko kayane qanana, inda Lamyah ta saka skirt tsukakke ta qugu, qasan shi kuma mai fadi sosai, ga wasu yan stones masu gyalli da shegi daga qadan, haka akai wa ta saman ma ado, sai rigar ra dingilalliya, data kama jikin ta, tsam, ta gyara gashin ta , ta daure ta sake shi bayan ta tsaga gefen shi.ta kwantar da shi, avun dai ba a cewa komai sai wanda ya gani, Lamyah ba qaramin kyau tai ba, Farha sake baki tai.tana kallon ta kawai, " Farha kallon yao yawa tun muna shiri kk kallo na har yanzu, sai munje kin ja an raina mu," Farha ce ta gyara zama ta juyo gaba dayan ta ta fuskanci Lamyah zata fara zuba danneman surutun nata, Lamyah ta katse ta da" Farha na roqe ki da Allah ki hakuri, kar ki zuqen energy kan rawar," murguda baki tai ta juya ta ce " Fine"πŸ™„ dariya Lamyah tai qasa2, dan tai imanin ta bar Farha ta bude baki, har su isa ba zatai shiru ba.


Sun isa suka tadda Faisal a gofar shiga wajen rawar yana ta jiran su " Haba dan Allah sai kace wadan da ba zaku zo ba, kun shanya ni malamai," hakuri Farha ta fara bashi tana fari tana son zuba mai zancen nata yace" dakata kanya, dan in kk fara zuba sai an rasa mai kwashe ki yanzu, muje ciki a rubuta sunan ta ai komai a gama ta fara gudanar wa yau mu gani," ran farha ya baci sosai " Eh ai ko yau ko kun qi Allah sai nai surutu, dan kuwa ina cikin farin ciki, ba wanda ya isa ya hana ni magana ehe tin da ba d leben kowa nake zancen ba," ta qarashe cikin hawayen shagwaba, ita a dole yau an qi sauraren ta, Lamyah ce ta kamo ta tana lallashi, sannan ta hakura ta gyara tsaiwa zatai qala'in maganar da. Batai ba dazun aiko suna kula da hakan basui.magana.ba bare tace anqi ji suka sa kai ciki, bata gane ba, bin.su tai tana ta zuba , ko A ba mai gane wa, Bala dake gefe sai dariya yake, kama hannun Mubarak.yai suka tafi shan ice cream, dan da shi suka.taho, Lamyah ta ce suna tahowa da shi.tinda.ba kowa gida, Tani ta tafi. Wani waje suka je aka gama komai na tabbatar da Lamyah a cikin masu rawa, zuwa sukai wani daki dan yin kwalliya, sai Faisal ya dakko wasu kaya ya bata akan ta saka, qanana ne sosai, tace " A'a wannan ma sun yi qanqanta in gaskiya ne, balle ka ban wannan, barni da wadannan, tinda ni.ba wai wani abu ya kawoni ba bayan rawa, and wannan sune perfect kayan da zan yi rawar da nake son yi d su, cire doguwar rigar tai, ta baza gashin ta, sai da faisak ya kusa suma dan ganin kyau tsabar shi, ga wani gashi da tin da take sai dai a TV yake ganin irin shi,magana take mai ta shirya bai ji ba, sai d ta bugi kafadar shi sannan cikin in ina ya amsa ta da su je, yana tafe yana juyowa baya, sai tuntube yake, dariya kawai suke ta mashi, har suka isa, wani irin kishi ne mai tsanani ya kama yammatan wajen da ganin fitowar Lamyah.............
































*nima dai kishi ya kama ni na ganin Lamyah zata danse ba ni a ciki*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ ' YAR RAWA πŸ’…πŸΌ









BY HAERMEEBRAERH










*Alhamdu lilLAAH for another blessed and healthy year, Ya Allah increase me in Eeman, health, wealth, and taqawa, ya Allah make me among the Salihun. HAPPY BIRTH DAY TO MEπŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰πŸŽ‰*
❀
















Page 11:












Tana hawa wajen da zata gudanar da rawar kuwa gaba daya hankulan mazajen wajen ya dawo kanta, wasu daga cikin matan dake wajen kansu sai da suka razana da ganin ta," wannan daga ina?" Waqa ce ta Arabs aka kunna mai matuqar dadi , a hankali ta fara takawa, dan sai taji gaba daya idon mutane ya mata yawa, amma da ta ci gaba da yanayin yanda aka fara tafa mata sai ta ware, daga nesa Farha ta kwada mata kira " Go Lamyah, show them what u got" kaii rawa fa tai rawa, kudi ne kawai on air, sai watsa mata su ake, qugun nan kamar zai karye saboda juya shi da take, amma ko a jikin ta, Farha ce ta zabura ta haye itama, rigar ta ta wurgowa Faisal, dan ko ankarewa bai ba, kan ya miqa hannu ya cafo ta har ta zille, tana " inaaaa wannan casu ba zan taba bari ya wuce ni ba, in na bari ya wuce ni sai kunyi jinya ta" gaba daya stapes din Lamyah kusan ba wanda bata dauke b a zman su, nan fa suka ci gaba da bada mamaki, haba mana, wasu maza ne daga gefe suka taso su biyu, suka iso gaban su suka balle farare bugun ABUJA, zuba su suke kamar ba sa so, tun faisal na kwasa shi daya sai da wasu ma'aikatan cikin wajen suka fara taya su, as promised, suna cikin rawae 10 na dare tayi, Faisal ne ya matsa kusa da Lamyah ya rada mata, ai ko tai wani irin juyi da qugun ta, tai baya da kanta sannan a hankali, cikin kwarewa ta dago, wani ihu.aka saka a cikin wajen, cikin nishadi da jin dadi ta jawo hannun Farha da ba ta san me ke faruwa ba kawai tiqar rawa take, masifa ta juyo tayi sai taga Lamyah," My goodness ni fa ban dade da fara wa ba , haba ki bari nima.na maida kwadayin rawata mana," Lamyah bata kula ta ba, Faisal ya wurga mata rigar ta, Lamyah ta nuna mata agogon jikin wayar ta da ta karba hannun Faisal, kame baki Farha tai, ta bi bayan Lamyah, suka shiga wajen kwalliya, ta dau kayan ta, bayan sun kimtsa ne, Faisal ya shigo, riqe da kudi masu yawa a hannun shi, wanda a qalla zasui dubu 70k hankalin farha ba qaramin tashi yai ba data ga yawan su, ita da sai dai a bata irin 30k 20k dinnan, tana ganin ta sha kwana da yawa, yau ga kudi masu yawa a gabanta, gyara tsaiwa tai tana son magana, sai ta bude baki ta yarfa hannu.sai kuma.tai shiru ta hadiyi yawu, data kasa magana kawai sai ta doka tsalle ta dane Lamyah, Lamyah dariya tai ta karbi kudin sukai godiya suka tafi, a mota suka tarda Bala daga shi har Mubarak sun fara bacci, shiga sukai, suka zauna inda Lamyah ta mannawa Mubarak kiss a goshi, tana shafa kanshi, nan take ta sa hannu a jaka ta zaro kudin rawar da suka samo, dubu goma ta miqawa Bala, sannan sauran gaba daya ta miqawa Lamyah, sannan ta dora mata gannu akan lips din ta alamar bata son godiya ko wani surutu, Farha kasa magana tai, ta qame qam, toshe bakin ta tai tana hawayen farin ciki, Lamyah zamewa tai kadan ta jingina da bayan kujerar ta lumshe ido, tunani kala2 ne cikin zuciyar ta, tinanin Abii, Ammiii, Yah Amee din ta, da kuma rayuwar kadaici ta rashin 'Yan uwa da iyaye da take ciki, kiss taji an mata a kumatu, ta bude ido tace " WTF Farha, do u have to do that? Ni nace maki na yafe komai kin tsorata ni gaba daya hankali na baya nan," rungume ta Farha ta qara yi, tana kukan murna," you have no idea how this mean to me, ba wan da ya taba ban dubu biyar ba tare da ya nemi wani abu daga wajena ba, na shiga qunci da matsin rayuwa, ba mai taimakona, a kullum inna tashi kk ga na samu kudi to naje nai rawa ne, dan ita kadai ce abinda na iya nake mora a rayuwata, mutanen duniya basu da kirki Lamyah, ki gode Allah baki san babu ba, baki san halayyar mutane ba, wanda sai sun ga kina cikin matsi zasu so kassara rayuwar ki" ta qarashe cikin kuka sosai, sakamakon tina baya da tai lokacin tana ita daya, ba mataimaki sai Allah, Lamyah qara rungume ta tai," its k dear, everything s ganna be just fine inshaa Allah, nothing will ever disturbe u i promise,"Lamyah na shafa bayan ta sai ji tai Farha na munshari, to an gaji, ga uwar rawar da ba a sa ta ba ta tiqa, dariya ce ta kwacewa Bala da Lamyah, aiki suka hau darawa, Bala ne yace" shi yasa nake son ta she is so innocent, ba ruwan ta da shirme, amma gaba daya a unguwa sun qi gane hakan, ka dan ne suka fahimce ta, akwai lokacin da aka ce za a kore fa a unguwa kar ta bata tarbiyyan yaran wajen, Farha ta musu hauka, tace nan nan wakilin mai unguwa da ta taba kai mai koken ya taimaka mata kwanan ta biyu ba abincin kirki neman ya keta mata mutunci yai, da ita din yar iska ce yan da take a yunwace ai da ta yarda, ke na taqaice maki a haka dai magana ta mutu, sai ga 'yar da suke cewa tafi kowa hankali a unguwar 'yar wani kamilin mutum Malam Sule, ta yi ciki, kaiiii ranar sun ga tijara wajen Farha" ya qarasa yana dariya sakamakon tina me ya faru ranar da yai, isar su gida ne ya katse shi, su kai ta dariyar rikici irin na Farha, har yanzu da suka girma suke jin suma manya ne tin da sun cika 20 da yan kai Farha bata barin shiririta, sai son girma, in Mubarak yace ma Lamyah mummy, ita kuma Farha yanzu zata kamo shi tace," to mara ta ido, in ka qara ce man Farha ba Aunty ba , ko Adda, ko Yayah zaka ga ya zan da kai sai na balle maka haqori daya," tin Mubarak na kuka har ya koma mata dariya, data sake shi zace Farha ya kwasa da gudu, ba ko zata tsaya bata lokaci wajen bin bayan shi ba.














*NIJER REPOBLIC*










Yau shekara hudu da watanni kenan da Baaba Mus'ab ya san mutuwar Amini kuma aboki sannan dan uwan shi El-mustapha, ran da suka sani dan qaramin hauka ya masu, Ameenullah kuwa, ya suma yafi a qirga, sai da ta kai an mai qarin ruwa tare sa allurar bacci, dan gudun kar wani abu ya same shi, satin shi biyu cif aka sallamo shi, ya rame yai baqi, baya umm baya umm umm, tinanin dake daga mai hankali, da ganin gawar yasan kashe mai Abiii akai, amma an hana su yarda da hakan, domin duk wani shaidar mutuwa yai sakamakon taka bawon Ayaba, da yai an gabatar, in ya mutu ne haka kawai ina Lamyan shi? Ina Mubarak? Sannan ya akai ba a ga komai na dukiyar shi ba? Dakko wayar shi yai ya bude, yana duba messages nan ya ga saqon , da Abiin shi ya turo mai, jiki na rawa yana hawaye ya ke qoqarin bude saqon,
Sallama ce sai gaisuwa, sannan ya fada mai yana cikin hadari, game da 'yan uwan shi, amma kar ya samu koma mene ne Lamyah da mubarak will be safe inshaa Allah, wasu hawaye ne masu zafi sosai suka zubo mai, "to ina take? Ina zan gan su? Me yasami qanwa ta, amana ta? Wace irin rayuwa suke? Ta ina zan fara neman su?" Tari ne ya sarqe shi, ya fara yi ba tsayawa, Mommaa Aisha ce ta shigo cikin hanzari, fridge din cikin parlorn shi ta bude ta dakko ruwa ta kamo shi jikin ta tana hawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login