Showing 45001 words to 48000 words out of 52652 words

Chapter 16 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt

07 Jul 2024

12062

daki," Hello Sisto, ya abubuwan ke tafiya, na lallaba Bala da kyar ya barni zuwa amma tace sai jibi zan taho, dan haka kan na zo ki fara takalar fadan shegiya yanda dana zo zan qarasa cin uban ta," dariya Lamyah tai sosai tace" sannu iya masifa, kin sa kowa na jiran ya ga zuwan ku Nijer, musamman yan Group din BANI NAI KAINA BA, QASAI TATTUN MATA, RIBAR BIYAYYA, ZO KIJI YAR UWA, INA MATAN SUKE, da dai sauran groups, sai ki sha zaman ki" nan ta kwashe duk abin da ya faru daga farko zuwa qarshe ta fada mata, Farha cizin lebe tai da yatsa," Kashhhhh na si matuqa na zo na dan dirji shegen leben nan nata na qasa daya zazzago, jikin ta yai tsami dan uban ta,ta ji ba wai tsoron ta nake ji ba" dariya Lamyah tai sosai, Ameenullah ne ya shiga bai ce komai ba ya kwanta a kusa da ita, ya janyo ta yana shafa kanta, lumshe ido tai, ya fara mata wasa a kunne, nunfashin ta ne ke sauyawa, maganar farha taji daga sama," ke meke damun ki?" "Ba komai" itace amsar da ta bata da kyar, a daidai lokacin da farha ke son mata wata tambayar ne Aneenullah ya zura hannun shi a rigar ta,kashe wayar tai da sauri ta juya gare shi, yana ta mata dariya," ai na zaci zaki iya jure salo..., kan ya qarasa ta kai bakin ta na shi, ina ganin za sui abun manya na feceπŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€kar su lalata maku ni😭😭😭..........
















*Su Lamyah an shahara yanzu Oh ni Haermeen Haermmaerhna😭 na fece kan ta bata ma Haermmaerh na niπŸƒπŸ»β€β™€*




*I am sorry for any typos coz is unedited*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAR RAWA πŸ’…πŸΌ














BY HAERMEEBRAERH






*This page is for u guys*
*Sis Ramlat*
*Sis Hajjaju*
*Baba Larens*
*Bilkisu zarewa*
*(GOGGOS)*
*Fateema Radda*
*Komai nake kuna raina Me love u XX*❀
















Page 27:










Naufaliyyace na hango a zaune a bakin dan qaramin gadon dakin Maman ta, dake malale da ledar daki, sai akwatin kayan ta da ke gefe alamar tin akwatin ta ne na da datana gida, Mamar ta ce ta shigo dauke da flask din abinci da cup a hannun ta," wai ni ba zaki bar wannan kukan da kk kwana kina yi ba, in sarautar sarkin kuka za a baki ai da tini an nada ki kowa ya huta haba, ko an fada maki kukan zai sa ya maida ki? Ki ci abinci ki sha, sai na fada maki shawarar dana yanke," tana jin haka ta miqe ta koma kusa da maman nata," mama sanar dani me zai sa na koma wajen Ameenullah da wuri, Mama bana son abinda zai sa mu rabu da Ameenullah, rayuwata zata wulaqanta, ki duba ku ga irin halin dana shiga a kwana daya, kin sani ina da.matsananciyar buqata, innai sati a gidannan zan koma ruwa, ga aure a kaina, Mama ki taimaka min," ta qarasa cikin matsanancin kuka, mahaifiyar ta ta tausaya ma gudan jinin nata, " karki damu Naufaa na, kamar bani ce uwar ki ba? Me zai daga hankalin ki? Bayan muna da boka aikatau, yanzu ya aikata mana aikin komawa Ameenu," " haka dai xaku qare, a yawon neman asiri ba, ba xaku zauna kui wa kan ku karatun ta nutsu ba, ki saka 'yar ki akan turbar gaskiya sai bata, akan shegen yawon asirin nan dubi dakin ki yanda ya koma,komai ya qare ya lalace, ina ce Uwar Ameenullah qawar ki ce? Amma gidan ta, dakin ta, surturar ta, wa zai hada dana ki, ke da sauran qawayen ki ma da basu biye2n bokayen, babban jahilcin ki har yau kin kasa gane su waye bokaye da malaman tsubbu da kk bi, na farko dai dan ni kk fara bin su, amma ko kin min asirin Allah ya bada iko ya kama ni, baki ganin yanda Allah ke warware man da qarfin roqon mai dika? A iya shekarunnn da muke dake, baki ganin cewa roqon Allah yafi roqon boka ko malamn tsubbu? Habaa ki bude idon ki da zuciyar ki ki gani cewar Allah na basu aron likaci ne , yana basu dama da iko akan abinda suka buqata ne domin ya musu talala, ranar gobe qiyama ya kama su da laifukan su, ku sani ke 'ya ta da kuma mata ta, Allah mai yawan gafara ne, mai karbar tuban bawa ne duk tsananin zunubin shi,har shirka , amma in lokaci bai qurewa mutum ba, kuna da tabbacin ranar da zaku mutu ne? An baku garantin mutuwa lokaci mai tsaho? Ko gajeren lokaci aka baku? Babu daya, dan haka kuji tsoron mutuwar fuji'a mutuwar kwaf daya, ba kusan a ina zaku mutu ba, me kukeyi za a karbi rayuwar ku, ki na aikata zina, kina aikata shan giya, ko kuna kan hanyar ki ta zuwa wajen boka la'anannen Allah? Ko kuwa kina sallah? Ko tasbihi? Ko karatun qur'ani? Ko yiwa iyaye ko miji hidima? Baki san fa lokaci ba,kin dage ke sai kin dora yar da kk haifa a cikin ki, wadda in kukaje lahira sai Allah ya maku hisabi akan komai, har tarbiyyar da kk bata, so kk ta kai qarar ki wajen Allah akan baki bata tarbiyha mai kyau ba? Kuji tsoron Allah, ku zauna ki kame kan ki, ki shiryu, ta dalilin haka Allah zai duba halin da kk ciki ya sa mijin ki ya dawo da ke,kuma batun sha'awa da kk magana akai ai ke kk jawa kan ki ,na farko wannan dure2n magungunan da kuke ke da uwar ki ku hana mutum sakat ai ta abu daya, ku a wahale mutum a wahale, ga na biyu baku banbance haram ke da girman ki kallon iskance2n turawannan kk a waya ko a talabijin, ga maganganun batsa da ba a rasa ku da ita, ke kuma yanzu zamani ya kawo maku wannan wayar ta jaraba,hirar batsa da qawaye maza da mata kina matar aure, ga karanta littafan batsa zalla wani mara tsoron Allahn zai zauna ya rubuta, kema da ba tsoron Allah ne ya cika ki ba ki zauna ki karanta tsaf, sha'awa ta tashi dole ki nemi mafuta, gashi yanzu baku son karanta wa'azin ma da zai amfane ku, sai iskanci, sai kun gama karantawa ku zo kundamu mutane suna zaman zaman su, to in baku gyara wannaj ba, wallahi Allah nesan ta ki zai da Ameenu na fada maku kenan," Baban Naufaliyyah kenan Alhaj, Rabi'u, tinda ya fara wa'azinnan jikin su ya mutu, zuciyar su ta tsinke sosai kuka suke sosai gaba dayan su, a qasan ran su suna dada tina tabargazar da sukai a rayuwa, kowa na tina rabon data kafa goshin ta a qasa da sunan sallah an dade, ba magana Maman ta ta miqe ta bar dakin, kuka ta kwanta tana yi a zuciyar ta tana istigifari, har dai ta miqe ta fita dan dajra alwala, tana yin alwala tinani ta tsaya yi, to ita ta inama zata fara rama sallolin ta? Kuka ta rushe da shi na tsantsar tsoron Allah, tsoron tinawa da irin azabobin daya tana da domin masu wulaqanta sallah, nan da nan ta fara sallah ba ji ba gani, dan tasan Allah ba dauke mata zai ba, ta bi da istigifari.














" Wash Allah, Mine dan tahon da wannan cup din na gefen gado dana aje," dauke da cup din ya fito ya zauna kusa da ita, cikin tsokana ko ya kai cup din bakin shi, warcewa tai ta fara shura qafa," Tab yau inna yarda na zama danwake yara sui kalace da ni da safe, ina ruwan ka da abinda ke cikin cup dina zaka sha min, Allah ni ka biyani abuna," kukan gaske ta fara mai," Haba My Farha, ni ne fa mijn ki Bala abin son ku," " kai ni kar ka wani min dadin baki,tashi ka hadon wata madarar kuma madara cokali biyu, millo cokali uku, ka gauraya kar ka sa sugar, kar ka sa ruwa," " amma dai kin san asibiti sun hana ko," " kai rabu da su qaryar vanza ce, itama likitar dana je tsohon ciki gare ta,yaji ta dauro a leda tana barbadawa a hannu tana sha, shi shan yajin basu hana mu bane? Amma take tandewa, ni debon kae yawuna ya gama zirarewa, ka tashi mana kana bata lokaci Hubby," ta qarasa cike da shagwaba tana buga qafa,miqewa yai yana " Farha halin ki sai ke, Allah ya sa in kin haihu ki rage wasu," " me kace ? Ni dai ko lashe kar ka lasar min abuna ehe ina hango ka bari ma ka ga na biyo ka,"dariya Bala yake sosai, a ranshi yana ayyana kar su haifi yara masu rowa, tinqis2 ta bishi, dan yanzu ta danyi qiba ba laifi, yana hada mata ta amshe tai godiya ta kona ta zauna, lumshe ido tai kawai tana afawa, ga surutu fal bakin ta amma dadin wannan hadin madarar ya hana ta, sai ta dakko zata fesa dai ta tsaya,haka har ta sha iya shan ta tai bacci a wajen,gyara mata kwanciya yai ya rufeta, zama yai ya qura mata ido yana murmushi, lallai xuwan Farha rayuwar shi alkairi ne,gashi ya samu aiki da babban muqami, ga kudi na zuwa mai ko ta ina, ya sau gida ya sai motar kan shi, sai dai bai ma saka ranar tarewar su ba, dan Lamyah tai uwa tai makarbiya tace bazaau bar gidannan ba, in dai ba wasu nasu zasu saka ciki ba.
















*RIMIN GATA*




" kash subhanallahi,wai sau nawa zan fada maki je Saddiqa ki na maida hankali wajen ibada ne, duba lokacin sallah fa ki gani kina kwance abin ku," "dan Allah Yah musaddiq kai hakuri,gaba daya jikina ne a mace zuciya ta na ta tashi shi yasa, yauwa dama ina son fada maka, dazu Delu ta aiko wannan wai na sha maganin mallaka ne," ran shi ne ya baci ainun, dan wannan karon ya ga alama zuwa zai har gida ya tsefe wannan shegiyar tsohuwar, dan yanzu tsabar son da Saddiqa ke mai yasa gaba daya sai a abin da yace shi zatai, shi kan shi yanzu ya fahimci abin da Lamyah ke fada,dayai sanadin shiriyar ta gashi yana jin dadin zama da ita, sai dai fa konda wasa baya barin ta fita, baya bari taje ganin gida, sun yi mitar,sun kai shi qara wajen mai garin, har sun gaji, ga shi yanzu tana da shigar cikin wata uku, ba qaramin son cikin yake ba, Innar shi ma haka, ga mai gari daya qosa yaga jikan shi, gata take sha ko ta ina, tana matuqar son ganin 'yar uwar ta da yake bata labari kusan ko da yaushe, ta kwadaitu da son ganawa da ita, gashi layin da suka basu na waya baya shiga, ta gefe daya kuma Delu kushe mata Lamyah da zuri'ar su kullum take in ta zo,she is so confused,so take kawai taga wacece Lamyah ta karance ta da kan ta ta nemi ajin saka ta a zuciyar ta, duk da tana jin qaunar ta a ranta, dan a dangin su kaf ba mace kusan kamar ta, sai dai labarin Lamyah kawai da take ji, " da wannan dogon tinanin da kk da miqewa kikai kikai alwala," miqa mata hannu yai cike da shagwaba ta kama tana narke mai," A'a fahh ni ki daina min wannan salon baki sallah ba,dan kin san b hakuri na cika ba ni, kuma inna tsaida ki lokaci wucewa yake, je ki alwalar in kin isa ki dawo ki min haka ki gani," cike da dariya ta kwace hannun ta ta wuce shi," kwalelen ka dan ni ba lfy na cika ba ehe," " haka kk ce ko, to amarya zan miki,"kuka ta saka tana buga qafa," ke baki san wasa ba ,kece fa amarya kuma uwar gida ba wata ta biyun ki balle ta ukun ki, har a samu ta hudun ki, kwantat da hankalin ki, maman Aishaaa Lamyah,"wani dadi ne ya kama ta ta fice tana muemushi, dan sunan da suke son sama diyar su kenan in macece.














Yar guje2 naga suna yi a tsakiyar parlorn su, dikkan su ba wasu kayan azo a gani ne da su ba, as usual shigar ta ce ta qananan kaya, shi ma daga boxer sai vest, yayi 'yar qibar jin dadi da hutu,yai matuqar kyau,kalar shi sai haskawa take, haka itama ba qaramin kyau tai ba, gashin ta ya sha gyara, kamota yai yana mata cakulkuli tana ta dariya, da kyar ya qyale ta suna maida nunfashi, miqewa yaga tayi," ina zaki?" Bata amsa shi ba taje ta kunna kida ta dawo ta zauna," wai yaushe zaki dai na RAWA ne," " sai sanda na girma, tin da kullum ce min kake yarinya," ta qarasa tare da turo baki, dariya yainsosai, itama ta biye masa,kama hanun shi tai ,"yau so nake mui rawa tare taso na koya maka," miqewa yai ya bi bayan ta, rawa ta fara takawa a hankali, tana juya jikin ta a nashi, ji yai lallai da haka rawa take kar Lamyah ta daina ta, tai tayi kullum, suna cikin haka ne suka ji kwankwasa qofa.........








*wa muka samu kuma ya katse mana RAWAR mu☹*




*Unedited really sorry for any typing error fans,Me Love u all*❀
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAR RAWA πŸ’…πŸΌ










BY HAERMEEBRAERH












Page 28:
























Miqewa suke qoqarin yi su shiga domin suturta jikin su ne aka murda knob din qofar aka shigo, Naufaliyyace kan ta a qasa sai Maman ta, dake biye da ita, dago kan ta da zatai tai mummunan gani, dan Ameenullah ne dauke da Lamyah sun dauki hanyar dakin shi, yana ganin su ya hade fuska, sanye take da qaton hijab, har qasa, fuskar ta dauke da annuri, alamar nutsuwa, amma kishinnan na maqale a ranta, addu'a ta fara na Allah ya kawar mata da mummunan kishi, a hankali taji zuciyar ta na sanyi, ba sui masu izinin shiga ba, su kuma basui yunqurin shigewa ba, Lamyah ce ta dira qasa, tai dakin ta a kunyace, dan a qallah akwai babba a wajen, yanayin su kuma yayi girma vabba ya gan su haka, Ameenullah ne yai qoqarin shigewa shima, " Yah Ameenullah mu shiga ne?" " Da ni na kawo ku?" Yai shigewar shi, dakin shi, Lamyah ce ta fito sanye da doguwar riga baqa mai fadin qasa sosai, kanta ba dankwali as usual, gashinnan a baje a gyare, izinin shiga tai masu, ta durqusa har qasa ta gaida maman Naufaliyyah, bayan sun gaisa ta miqe tai kitchen ta debo masu drinks, sannan ta hado da snaks, ajewa tai gaban su, aiko ba kunya ba tsoro suka fara diba, Lamyah baki ta sake daga baya ta hade bakin ta, sakamakon murmushin yaqen d Naufaliyyah ta sake mata, miqewa tai ta basu waje, dakin Yah Amee ta shiga, samun shi tai zaune ya dafe goshi, janye hannun shi tai ta zauna kan cinyar shi, ya zagayo hannun shi yana kallon ta yana lumshe ido, goshin ta ta hada da nashi, a hankali yake dago fukar shi yana qoqarin kissing din ta, kwalele take mai, sai tai qoqarin kai nata amma sai tai brushing lips din ta ta janye, magana ta fara mai," My love, ina neman alfarma a wajen ka, ina roqon ka da kome zasu ce maka ka tsaya ka nutsu ka amshi yafiyar su in sun nema, domin duk abin da suka maka nima ya shafen amma ni tin randa ta bar gidannan na ji ban ji dadin tafiyar ta ba, nai shiru ne gudun bacin ranka, amma ni gaskiya ina buqatar dawowar ta, ba dan bana jin dadin zama na da kai ba sai dan ina tinanin Momma bazata ji dadin barin diyar qawarta da kai ba, kuma kasan rashin jin dadin mahaifiyar ka akan ka ba a bune mai kyau ba a rayuwar ka duniya sa lahira, akwai matan da suke ma mazajen su abinda yafi na Naufaliyya kuma a hakura a zauna, plss my baby kai hakuri kaji," ta qarasa tana wani irin juyi a jikin shi, tare da motsa hips din ta, cikin hanzari ta qarasa riqe lips din shi , kamar jira yake, tana ji ya kama tai qoqari ta zare tana mai dariya, "je ka ka dawo zan maka wani abu" yana lumshe ido ya fita, kifewa tai a wajen tana kuka mara sauti, kishi ne danqare a cikin zuciyar ta, amma sai ta tina da Hadith din Rasulullah da yace" imanin dayan ku baya cika sai ya so ma dan uwan shi abin da ya so ma kan shi," ta haka ne kawai take ganin zata iya daidai ta su, in ba haka ba yanda Yah Amee ya dau fushi bata jin zai saurari kowa akan Naufaliyyah dan tin da ta tafi ko da batan hanya bai taba kiran sunan ta ba.




Bayan gaishe2 da sukai, idon shi ya sauka kan Naifaliyya da ta qura mai ido, tsaf ya gane irin kallon, dan guntsun tsaki yai ya kauda kai, dauke idon ta tai daya ciko da hawayen, ta cije lips din ta, " Ameenullah naji labbarin duk abinda yarinyar nan ta aikata, kuma a gaskiya na zo nan ne domin baka hakuri, domin duk abinda tai akwai sa hannuna ciki, da kuma gurbatacciyar tarbiyyar data samu daga wajena, mahaifin ta ya mana waazin da ya shiga zuqatan mu daga ni har ita, dan son Rasulullah kai hakuri, ka yafe mata, ka kira abokiyar zaman nata domin ta bata hakuri, tabbas mun cutar da ku," ta qarasa cikin tsananin nadama wadda ta kasa boyuwa a fuskar ta, jikin shi ne yai sanyi da yanayin su dika, tabbas akwai tsantsar nadama a tattare da su,miqewa yai ya shige bedroom din shi, kwance ya tadda ta, tayi kuka har ta gaji, fuskar ta tai ja,musamman hancin ta, dago ta yai yana bubbuga bayan ta, saurin miqewa tai tana yaqe, murmushi ta so yi amma tai failing,hawaye ne ya biyo baya, girgiza mata kai yai," in ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login