Showing 18001 words to 21000 words out of 52652 words

Chapter 7 - YAR RAWA COMPLETE DOCUMENT By HAERMEEBRAERH.txt

07 Jul 2024

12058

ta bashi , tare sa shafa bayan shi, a hankali ya samu nutsuwa, " ka yi hakuri Haerbeebee, ka kwantar da hankalin ka, ka ma Abiin ka addu'a shi da Ammiin ka, ita suke buqata a wajen ka ba kuka da damuwa ba, ba za su so ganin ka a haka ba, sannan ina son ka sa 'yar uwar ka a addu'ae itama Allah ya bayyana mana ita," kuka yake sosai kamar qaramin yaro, yana qara mannewa a jikin Momman shi, a hankali tana shafa bayan shi da kan shi yai bacci, gyara mai kwanciya tai cikin tausaya wa dan nata, dan ta san shaquwar dake tsakanij su, haka ta fita tana share kwalla..........










*celebrate with me Roumie na and Aisha Bixxisiou, kuna raina always, ku din daban ne, love u da yawa*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA 💅🏼








BY HAERMEEBRAERH








*WOW ! i must say thanks to this wonderful and amazing people, u guys ar awsome, and i love u so so so very much u made my day so beautiful*




*My family i love u all❤ My friends ku daban ne na zama ku kun zama ni, Widad Ummu Hafeeza❤ My family freind, and so many others sunayen ku ba zai fadu a dan wannan page ba, amma ina mai tabbatar maku da naji dadin addu'oin ku jiya, Allah ya bar mu tare ya saka maku da alkairi mara yankewa❤*


*Mamu Novella*
*Bani nayi kaina ba G*
*Matsalolin Mata A yau G*
*Safaa & Marwaa Fans*
*Tabital fulaku G*
*Zahrah Surbajo G*
*Ummyn Yusrah G*
*Al'ummata G*
*Sophy And Vc novels*
*Sawwama Novel G*
*Matan Gidan Daraja G*
*Qasaitattun Mata G*




*Na gode da addu'oin kukuma, sosai naji dadi, Allah ya saka maku da alkairi mara yankewa❤*






Page 12:








Sai da Baabaa Mus'ab da Momma Aisha suka sha fama sosai, kafin Ameenullah ya daidaita, ya koma normal, amma ya rage yawan fara'a sosai, sannan ya rage magana, komai akai sai dai yai murmushi, ko ya bada amsa da kai, qasan zuciyar shi cike yake da soj ganin qanwar shi, da yanzu ta tabbatar wa kan shi son ta yake matuqa, so irin na aure ba soyayyar wa da qanwa ba, zuciyar shi na azabtuwa in ya tina har wannaj lokacin ba zai ce ga kamannin ta ba, muryar ta sai ta waya yake ji, abun na matuqar damun shi ba kadan ba, sannan ya zatai ta kula da Mubarak, iya wannan tswon shekarun, yakan yi kuka sosai, ya gode Allah, domin ya san tabbas suma suna cikin kadaicin rashin kowa nasu, cigiya kam a gidan redio da TV tare da jaridu duk sun.bayar, amma shiru kk ji. Yau ne Baaba ya samu Ameenullah, ya ke mai maganar komawar shi Nigeria aiki, don zaman ya isa haka, yana da kyau a ci gaba da kulawa da dukiyar da El-mustapha ya bari ko dan yaran shi, da ci gaba da yin sadaka da kyautukan da ya saba, ba dan Ameenullah yaso ba ya gyada mai kai, bayan ya fita ne ya kwanta yana kallon sama, sai tinani yale kala2, har aka kira sallar magrib, tashi yai yaje yai alwala ya tafi masjid, bayan ya dawo ne, ya fara shirya kayan shi kamar yanda ya saba, kiran abokin shi yai, Faisal,
" Yah Man ya akayi ne? Ina fatan dai gobe zaka zauna gida ba zaka wajen shegiyar rawar nan ta ku da kuka dorawa kan ku ba?" " yessss gobe zaka zo? Alhamdu lilLAAH, dama ina son ka zo akwai wata haja dana aje maka, wannan karon ko min qin kusantar mace da kk akan dalilin wata da ba ta san kana ma son ta ba, wannan karon sai ka dana, wannan kalar kuce, ta hadu iya haduwa, bata da makusa ko ta ina, matsala daya da za a samu shine, bata kula kowa, sannan bata cika magana ba, dan ina jin tin da muke bai fi sau uku na taba jin maganar ta ba, ita dai kawai ta zo tai rawa ta tafi kuma......." "Ya Allah, Faisal, me yasa kk min wannan dogon sharhi haka ne? Ni fa ban ce maka ina son kowa ba,hasalima kai kasan bana son hulda da mata, dan Allah ka aje surutun ka a wata ma'adana wataqila zai ma amfani, wanni karon" kit ya kashe wayar ta dayan bangaren Faisal ko da yake shirin shiga hotel din yai dariya kawai dan yasan halin abokin nashi.












Washegari da sassafe ya nufi Nigeria, bayan nasiha da Baaba ya saba mai wannan karon sai da ya qara akan na da, Momma ma haka tai ta mai nasiha tare da kwantar mai da hankali, cikin so da qaunar dan nata tare da kewar shi da ta fara tin kan ya tafi ta kai bakin ta goshin shi ta manna mai kiss, bayan ya tafi ne Baaba mus'ab yace " To sauran ni, dan na kula gaba daya hankalin ki ya tattara akan dan ki, tin da ya zo kk manta dani" ya qarasa cikin shagwaba kamar wani yaro, kwallar dake idon ta ta mayar nan da nan ta maye gurbin damuwar ta da farin ciki," Habaa Baaban Lamyah, da girman ka kk shagwaba, to matso ka gani," matsawa yai ya miqa mata fuskar shi, lips din shi ta kaiwa soft kiss, nan take ya lumshe ido, kan ya bude ta shige bedroom tana dariya, dariya yai shima ya bita yana," ai sai ki saya ki karbi tukuicin ki kema ko," " A'a ni kam na yafe Allah," dariya sukai cikin nishadi da nunawa junan su so.










Da magrib Lamyah na gani da guntun wando iya cinyar ta, kalar bby pink, sai riga da ta daga hannun ha ana ganin cikin ta, da cibiyar ta, ta daure gashin ta, hannun ta ya sha lalle da qafarta, an mata baqi da ja, sai naga ta dakko tirarukan ta tananta barin su sannan ta shafa powder, tana gamawa ta dora baqar abaya, kusan shigar da Farha tai kenan, Mubarak kuwa manyan kaya suka saka mai, dan shi wataran har kuka yake in an saka mai qananan kaya, sam.basa burge shi,in ba bacci zai ba ya saka na bacci, Farha kan kira shi saurayin qauye kawai, shi kuma ya murguda baki kamar budurwa harda fari da ido, in ta biyo shi ya gudu wajen Mummyn shi, yana mata gwalo," Lamyah yau gaskiya sai mun fi ruda duk wanda Allah ya sa yai tozali da mu, ni har na fara jin kunya, anya bamui shigar tsiraici da yawa ba?" " ke malama in zaki gama ki zo mu tafi ki taso, ai dai naga ba sai da jikin namu zamu ba ko, zamu ne dan nishadin mu kawai mu komo," " haka ne, to ni dai yanzu gaskiya jibi sai naje kasuwa, dan siyo pant da Bra na acuci maza, qawata Cutie kullum shi take sawa, kan na gano ta ba mai cewa ba nata ba, ni nqi ta tafiya zalau2 ba nama ke kuwa ko ina sai san barka," maganar ta ba qaramin ba Lamyah dariya tai ba, har tana kama ciki, "kin ga matakar ki dariyar tsiya dilla ni tashi mu tafi, nimq zan qibar ne ai, sai na baki mamaki, har sai kin nema min abun rage ta, kai kuma da kk guntse dariya ka sake kayi ta sai na zaune ka, ta shi kaje kace ma Bala mun gama," ta fada tana kunburi ita an mata dariyar bata da qiba, aiko sai da mubarak ya kai qofa ya juyo yace " Farha ni dai kk zaune ni sai na mutu, qashi zaki soka min," da gudu ya fita yana dariya zata bishi Lamyah ta riqe ta," haba princess din Bala, ina zaki da gudu haka ai sai Bala yace baki da aji," " to laifij waye in an ganni ban da ajin ? Ba ke kk fadan haka a gaban shi ba gashi nan yai hadda, ko batan wasali baya yi? Ni dai gaskiya asan ya za ai dani, ko kuma kema ki fara slimming cinyoyin da qirjin ki su dawo kamar nawa," ta qarashe maganar cike da shagwaba, Lamyah ce ta shanye dariyar ta ta kamo ta tana buga bayan ta," kar ki damu yanda kk so haka za ai, tashi mu tafi," miqewa tai cikin yanga, kamar zata balle, Lamyah ce ta saki tari, mqi hade da.dariya, aiko cikin fushi fuuuuu tai waje, zama tai gefen kujera tana ta tiqar dariyar ta, sai da tai ta qoshi ta gyara fuskar ta suka fita, lokacin tara ta kusa, a hanya ba mai kula kowa, Bala yayi iya qoqarin shi darling din shi tai magana taqi sam,Lamyah ya zabgawa harara ta madubi, daidai sun hada ido," Whatttt???? Me nai kk hararata," " nasan laifin ki ne koma me yasa Farha fushi, ga shi nan kin ja min," dariya take son yi amma bata son ta bata ma farha rai again,dan yanzu kam tasan tana gab da kuka, kuma tana son ba Bala amsa, haka ta shanye dariyar ta kawai ta koma gefe tana kallon titi, hannu ya sa ya riqo hannun Farha wadda ta zame da sauri, ta na kallon shi, da ma'anoni masu yawa, tsayawar motar a filin da suke parking ne ya janye hankalin ta daga kan shi, da sauri ta kama murfin ta fice, Faisal da Ameenullah su kuma sun fito, suna hira, kawai sai Lamyah ta tsinci kanta da faduwar gaba, like wise Ameenullah, shi ko harda dafe qirjin shi yai, "Man lfy?" " ba komai haka nan naji qirjina na bugawa da sauri, kuma zuciyata ta tsinke sosai Allah ka jiyar da mu alkairi," amsawa faisal yai yana kallon gefen su, inda suke takowa cikin yanga da qasaita irin na hadaddun mata........
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 ' YAR RAWA. 💅🏼











BY HAERMEEBRAERH




















page 13:












Tunda suka qaraso da Ameenullah ya hada ido da Lamyah, gaban shi yai wani irin bugawa, wani irin abu yake ji daha qafar shi zuwa kan shi, itan ma hakan take a wajen ta, kallon kallo sukai, kafin su dauke kai ga barin kallon juna, Farha ce tai fari tace," Hey handsome, ya kk?," banza yai da ita bayan ya mata kallon tara saura kwata, wayar shi ya zaro yana daddanawa, yana kallon tsohuwar Numbern Lamyah, dan guntun tsaki Farha tai wanda ya sa Ameenullah ya kalle ta da wani irin kallon da yasa ta ja hannun Lamyah tai gaba, tace ma Faisal," ka same mu a ciki in wannan dan rainin ya barka, ni kwata, bana son yana dawowa gaba daya baida sabo, dan ma ya samu mace kamar ni tana kula shi yake wani basar wa, dadin abun ina da saurayi, ba a kasuwa nake ba ehe," ta fada lokacin da take kada yan qananun duwais din ta, Lamyah kam yau tana cikin dariya ne sosai, amma wannan karon duk da dariyar da take ji, gaba daya ta kasa yi, saboda yanda take jin mutuwar jiki, bayan sun shiga ne Farha ta kamo hannin ta ta fara cire mata Abayar ta, ," Gurl me ke damun ki ne? Gaba daya naga jikin ki yai sanyi, ko dai wani abi na miki?" " A'a ni kam baki man komai ba haka nan naji jikina ya mutu, amma ba komai da naji taken mu zan ware na san," ta qarasa cikin murmushi, Farha ce ta qarasa mata make up, zata ce Lamyah kenan Faisal ya leqo, sai ta sauya da sunan da tai register da shi wato, Laila, ," lokaci yayi me kuke yi ne har yanzu?" " gamu nan zuwa" miqewa sukai a tare suka fito, kida aka baza masu nan da nan Lamyah ta ware, rawa take kamar ba qashi a jikin ta, juyi take kamar wata tarwada, guqun nan kamar zai karye saboda girgiza shi da take, haka ma qirjin ta, ga gashin ta da ta baza in tana rawa yana gaba yana baya, ko ta maoda kai gefe, abun sai wanda ya gani, Ameenullah da ya leqo fadama Faisal zai kwanta ko ya dawo kar ya neme shi ya tsaya kallon ikon Allah, baki ya bude bai ma san yayi ba, kallon ta yake kamar idon shi zasu fado, wani iri zuciyar shi take kamar ya ruga da gudu ya dauke ta ya boye haka yaji, dukan kafadar shi yaji anyi, " Man ya dai, ko ka gano abinda na hango maka ne?" Faisal ya fada cike da tsokana, daure fuska Ameenullah yai," malam dama na zo fada maka ne ka wuce dakin ka kar ka damen in ka dawo, bacci nake ji," kawai ya sa kai ya wuce " Sunan ta Lailah," iya abinda Faisal ya fada kenan yai gaba, maimaita sunan Ameenullah yai tayi har ya isa dakin shi, kwantawa yai ringingine yana ayyana abubuwa da yawa a ran shi, " Lailah, Lailah kin bata sunan ki, na tabbata wannan ba zata wuce sa'ar Lamyah ta ba, Allah sarki Lamyah, duk in da kk Allah yare man ke, ya kiyaye ki daga fadawa halaka," hawaye ne ya gangaro mai, amma sai me rufe idon da yai hoton Lailah yake kallo, miqewa yai da sauri ya leqa window , aiko yana budewa tana daga kanta, hada ido sukai daidai zata shiga mota, saurin shigewa tai, dan bata zaci zata gan shi ba,saboda gaba daya da tinanin shi ta gama rawar ta, wurga ido take dama taga ina zata sake ganin wannan kyakkyawar fuska? Aiko yana sakewa ya dafe qirji yana murmushi, itama murmushi tai data zauna, Farha ce ta fara zuba kamar kanya, Bala na amsa ta cikin jin dadi, dan dazu ta tsume bai sami damar magana da ita ba, har suka isa gida Lamyah na tina handsome din da ta gani dazu.






A qa'ida kwana biyu suke a tsakani kan su koma rawa, Allah Allah Lamyah take lokacin komawar su yayi tai tozali da wannan kyakkyawa, haka ta bangaren Ameenullah, roqon shi Allah ya bashi ikon daurewa kar ya tambayi wannan sarkin surutun inda zai ga Lailah yake. Bayan ta idar da sallah ne ta yi karatun qur'ani, Farha da Mubarak ne suka zo da nasu qur'anan suka zauna suka tankwashe qafafun su, qari tai masu kamar kullum bayan sun kammala sukai ma iyayen su addu'a, bayan sun idar ne kowa ya miqe yai dakin shi, kwantawa sukai dan su koma bacci, amma kamar daren jiya,haka bacci ya kasa daukar ta, Farha ce ta juyo tace," Lamyah wai me ke damun ki ne? Gaba daya tin jiya na kula baki da walwala, ko wani abun na miki ne ki sanar dani dan Allah," ta qarasa idon ta ya cika da kwalla, Lamyah kamo hannun ta tai da sauri tana girgiza mata kai,idon ta cike da hawaye, nan da nan suka fara kwarara," Farha ban san meke damuna ba, amma ni dai nasan ina missing Abii na da Ammii ga Yah Amee shiru, ba mai nemana, in ma sun neme ni ba zasu ganni ba, zuciyata ta fara raya min na je neman dangin mahaifiyata , dan na samu wasu a kusa da ni da zasu zama majingina a garen ,"kuka take sosai, zuciyar ta na quna sosai, ga shi ba zata iya sanar da Farha me ke damun ta game da wannan Ajnabin da ta gani dazu ba, tabbas zuciyar ta ba wanda take so illa Yah Amee din ta, amma wannan baqon lamarin da take ji game da wannan bawan Allah yana bata tsoro, kukan ta ne ya tsanan ta, Farha sarkin surutu ba baki itama kukan take, haka Tani ta isko su," me zan gani haka yarannan ku sa juna gaba kuna kuka, ko mai yai zafi maganin shi Allah, ku sauqaqa wa zuqatan ku ko kun samu sauqin ko me ke damun ku," a tare suka fada jikin ta suna kuka, bubbuga bayan su tai har suka samu sukai shiru, " to yammatan Tani, ku zo muje a hada abin karyawa," miqewa sukai, suka bi bayan ta suna goge fuskokin su.


Tanj ta kasance tana koyar da su wasu abubuwan da ya zamana basu iya ba, dan kar au tashi ba su san komai ba, a da Lamyah tana ganin hakan a matsayin aikin wahala, tin da bata saba ba, amma da Farha parrot ta zauna ta mata bayani, a cikin bayanin nata ne, take fada mata a nan in ba ta iya komai ba, wata zata karbe mata miji, ko da Yah Amee din ta ne kuwa, habaaa tana jin haka hankalin ta ya tashi, kishin su na Larabawa ya motsa mata, a ranar ta wahala wajen koyon girki, ta yanke ta qone,amma duk bata ji, burin ta bai wuce ta ga ta iya komai da zai ja mata hankalin Yah Amee din ta, a yanzu tana matakin tsakiya, na koyon abubuwa, Tani kuma ta zage damtse tana koya mata abincin kala2 na qasashe daban daban.










*sai nace Lamyah girki adon mace wadda ta iya ta huta, wadda batabiya ba ta sha haushi, mata a dage a iya girki, da sauran abubuwan da suke saka mace ta zama qasaitacciyar mace a wajen miji da ko ina*
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: 💅🏼 'YAR RAWA. 💅🏼










BY HAERMEEBRAERH














page 14:










Yau tin safe Lamyah take cike da farin ciki, zuciyar ta fes, " Mummy why ar u so excited ? " " yeh what's new?" " kunji min mutane kawai ku sani gaba da tambaya akan mutum ba zai farin ciki ba kenan?, to nothing new, kawai yau ina jin nishadi ne saboda RAWA, kema kin san ita ke sani nishadi ko?" Farha tabe baki tai tace " Imm bari kiga na tafi wajen Bala mu sha hirar mu saboda jiya ya wuni school, bamu zanta ba, ina son fada mai how much i love him, ina son na ga kyakkyawar fuskar shi ko hankalina ya kwanta, qawaye na suna ganin a yanda nake bai dace da ni ba, ba zasu gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login