Showing 27001 words to 30000 words out of 45425 words

Chapter 10 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt

Ummatin Mambilla? Idan Ummati taji kin je nemowa kan ki miji a kan titin gidajen radiyo ba kya tunanin bafullatanar zuciyar ta zata iya bugawa da bakin cikin ki, don kuwa Ummati bata daukar abin kunya da zubda kima akan jinin ta.
Idan zan baki shawara ki dauka kada ki taba attempting neman sa a ko'ina. Ki koyi hakuri a kan soyayya ki kuma koyi juriya. Don na fahimci your love for him is extremely hot. (Soyayya mai zafi kike masa). Kisa a ran ki idan mijin ki ne kina zaune Allah zai jefo miki shi daga duk inda yake, idan Allah ya nufa ba mijin ki bane Boddo soyayya bata kisa, why not ni ki aure ni give it a try, nawa son will be enoughfor all of us mu raba ni da ke, bana bukatar martanin soyayyah daga gare ki, ba kuma jikin ki nake so ba. I will only love you Boddo till eternity and actualize my love alone......!!!"
Kuka na saka wiwi, na sa yatsuna hagu da dama na toshe kunnuwa na ina cewa "Ya Omar babu wannan maganar a tsakanin mu. Ba zan iya ba, ba zan iya yaudarar ka ba, in na aure ka na kware ka ba zan taba baka soyayyar da kake bukata daga gare ni ba".
"Shine ni kuma nace miki bana bukatar taki soyayyar, tawa ta ishe ni. Ba zan aure ki don in huta da ke ba, zan aure ki don mu cigaba da rayuwar mu tare yadda Abban mu yake buri, har zuwa lokacin da tunanin ki a kaina zai sauya, ki sammini gurbi komai kankantar sa daga gurbin Mr Radio, i will be glad and grateful".
Umar ya daina bani mamaki ya koma bani tu'ajjibi da tausayi, jin na kasa magana ya kara durkusawa a gabana, ya dora tafin hannun sa saman kafata ta dama yace,
"kin amince ko Boddo?"
Idanun sa na pleading, pink fatar bakin sa na motsawa a hankali kamar ba daga bakin sa maganar ke fita ba.
"Zan yi kokari in sayawa kaina muhalli a zuciyar ki in muna tare, idan shi a mafarki yake nuna tasa soyayyar ni a zahiri zan nuna tawa. Shi matsoraci ne Boddo, raggo ne, tunda ya kasa bayyana kan sa, sai dai ya sadado ta cikin mafarki yana neman haukata ki.
Boddo nine Omar dan Asshe da Hassu, Dan Gidado da Mamman jikan Ummati, shin wannan kakkarfar alaqa bata yi isar da zaki duba ki sadaukar da soyayyar bare a kan ta ba?
Zan bar ki da wannan kiyi tunani a kai daga nan har zuwa ki gama jarrabawa, ba zan kara damun ki da wata magana da ta shafi wannan ba, don na fi so ki tara hankalin ki waje guda yanzu. Watanni uku sun ishe ki yanke mana hukunci, ni kuma duk abinda kika yanke insha Allah zan karba, zan kuma yi kokari Abba ma ya karba, zan yi amfani da karfin soyayyar da yake yi min wajen ganin kin samu duk abinda kike so".


A wannan daren ko na minti goma ban iya na runtsa ba sai juyi a kan gado, ina tuna maganganun Ya Omar, hakika ina cikin rudani amma na kasa gane cewa mafita ta guda daya ce a daidai wannan gabar wato barwa Allah zabi. Na kasa tuna in tashi in gayawa Allah yayi min zabin alkhairi kada ya bar ni da dabarar kaina.
Nafi karkata ga son Ubangiji yayi gaggawar bayyana min shi kawai, idan har ya bayyana komai zai zo da sauki don Umar ba ya magana biyu, tunda ya ce zai lallasar min Abba to kuwa zai yin. Ya Omar zai sa Abba ya aura min shi, Anti zata sa Abba yayi hakuri ya aura ma Ya Omar wata daban ko a cikin dangi, bana son tuno ko daya cikin kalaman Omar domin kuka suke saka ni, a daren ranar ma da kuka mai tsanani muka rabu, ban iya na bashi amsa ba.
Washegari ban gan shi a gidan ba ban ji duriyar shi ba, haka na shirya na tafi makaranta duk jikina sukuku. Jarabawar ma ta yau na dai zana ta ne amma ni kaina nasan sunana loser. Har tsayin kwana uku ban kara ganin Umar ba, daga baya ne na ji Anti na waya da Anti Nasara wai ashe can ya tafi zai yi wata uku kafin ya dawo.
Ko meye hikimar Umar na kauracewa gidan mu? Wata zuciyar ta ce don ya baki dama kiyi karatu. A fili nace Allah sarki Ya Omar, ko kana nan ko baka nan wannan jarabawar ta tashi a banza. Sunanta Fatima Tara (F9×9).
Aka gama WAEC aka shiga NECO, a NECO ne kam Ko'oje ta ankarar da ni wai ina zana Radio akan answersheet dina na darasin lissafi. Da sauri na duba, kwarai Radio nake zanawa da sunayen gidajen Radio a Najeriya dana sani da manyan baki
Bayan mun fita paper din Ko'oje ta kamo ni kamar ta fashe da kuka,
"Aishatu Mamman Gembu me kika zamar da kan ki a kwanakin nan? Maths paper kike zanawa Radio? Meye gamin ki da Radio? Are you in your full senses? (Kina cikin cikakken hankalin ki)"
Kai tsaye na sunkuyar da kai nace "I'm in LOVE Ko'oje, sincerely in love, unimportant love kuma!".
Azima Salim Ko'oje ta kama hannaye na biyu ta rike gam cikin nata, ta ce "how did it become unimportant?""Sabida auren dole Abba na zai yi min da Ya Omar Azima, sun ki yarda mutum nake so dan Adamu da Hawwau, sun fi zaton na samu matsala ta aljanu ko ta kwakwalwa ne".
"ni kuma na yarda da cewa kawata will never lose her sense because of a man, who is he? Who isthatLucky? Ki gayamin ko wanene? Shi din ya san kina son sa?"
"Bai sani ba Ko'oje, nikadai nake kida na nake taka rawa ta karewa ma ban san a inda yake ba""to meye alaqar sa da Radio da kike zanawa a mathematics answersheet?""He's a Radio Presenter I guessed". Ko'oje ta ware manyan idanun ta akai na tana kallo na "kika ce baki san shi ba, yaya akai kika san hakan to?"
"baiwar Allah ke lawyer ce ne?"
Dariya ta yi tace "kwarai shi nake fatan zama,ke kuwa gaki nan a kan yardstick na ruining future din ki gabadaya".
Bude idanu na yi na dube ta sosai, sai tace "ban taba jin wannan almarar ta ki ba, wallahi na dauka saurayin yana tare dake, ko a gida ne ba'a yarda da shi ba. Shiyasa na tsaya ina sauraron ki. Ashe ke you are just on delusions and illusions.
Kafin ya zama worse zan gayawa Anti ta kai ki asibiti a dauki matakin gaggawa, sannan next year ki sake papers din ki".
A fusace na tafi na bar ta tana kiran sunana amma ban ko juyo ba. Na yi tafiya mai dan nisa kafin in zauna akan wani kututturen icce in yi kuka na mai isata. Ko'oje is my last hope, amma kalla....itama yanzu tace delusion nake yi har ina ina hadawa da hallucinations.
Ni na san kaina, kuma a dan ilmin da Allah ya bani na san lafiya ta kalau, kawai kalar tawa jarrabawar kenan, ko kuwa kaddarar rayuwata da ya barranta da na kowacce mace. Ni a mafarki da kuma imaginations nake tawa soyayyar.
Our own love tragedy is unbelievable ga kowanne mai hankali.
Ji nayi ana yimin horn, sai na daga idanuna jage - jage da hawaye na dubi inda motar ke tsaye, Anti ce ta zo dauka na da kanta yau don na gaya mata paper daya kawai zan yi.
Tareda Ko'oje na gan su a tsaye can gefen motar suna magana, suna kuma kallo ni da tausayi a fuskokin su. Mikewa nayi na isa ga motar na shige Anti tayi sallama da Azima ta ja motar bayan ta dora min Nadia a cinya ta. Muka kama hanyar gida daga Mabushi.
A hankali Anti ke jan motar kamar bata so mu isa gida, sai ta dauke kan motar ta yi wata hanyar daban, inda muka isa wani katafaren asibiti, ta dau jakarta tace in biyo ta, na gane asibiti ne na kwakwalwa daga karanta sunan. Wani bakin ciki ya tokare ni na ki fita, daga baya kawai sai na daura hannaye aka na saka mata kuka ina cewa "kema haukan zaki lankaya min?" Anti ta kidime, mutanen da ke wajen kuwa sun saba ganin iri na sai basu wani maida hankali a kan mu ba.
Waya naga Anti ta dauko tana yi daga can gefe sai ga wani likita mai kamala ya fito tare da ma'aikatan jinya biyu karfafa da su. Ma'aikatan suka ce salin alin ki bimu mu shiga ofishin likita, in kika yi gardama mu saka ki a 'guard room' mu kulle". Ai jin haka na hadiye kuka na bakidayan sa ina kuma sakawa a raina gara fa in nutsu, idan gwajin su ya nuna lafiya ta kalau kowa zai shafa min lafiya.
Likita ya bude firjin sa ya dauko ‘fresh milk’ mai sanyi ya bude ya tsiyaya min a tambulan ya miko min da murmushi, bayan ya bani kujerar da ke fuskantar sa na zauna, Anti na tsaye can gefe. Sai na kasa tankwabe wannan kulawar tasa, ko babu komai shi babu kallon mahaukaciya tattare dani cikin idanun sa.
Dama a yunwace nake, na karba na shanye ya kara min na kuma shanyewa. Na lumshe ido nutsuwa ta ziyarce ni. Ya bani kujerar kusa da shi na zauna ina satar kallon Anti. Ya bude file yace
"Yaya sunan kanwar tawa?"
"Sunana Boddo" Na amsa a matukar gajarce. Fuska a gimtse. "Siyama dai ko? Meaning… Ramadan ko? Kyakkyawar yarinya dake haka ki ce sunan ki Boddo?" Sai ya bani dariyar data sa ni murmusawa, Anti ma ta murmusa cikin damuwa, tace masa Boddo yana nufin kyakkyawa, ni kuma nace "Aisha-Siyama sunana". Likita yace "koda na ji.
Siyama Maman ki ta kawo ki a bisa zargin kin samu delusions, haka ne?""To ai ko na ce maka lafiya ta kalau ba lallai ka yarda ba, tunda an ce majority carries the vote". Dr. Amir yayi murmushi yace "wani lokacin majority din suna taruwa su duka su zabi wrong action da zaki ga ya zo ya dame su bakidayan su, wadanda suka zabi kalilan sai kiga sune on the right path.
Don haka Aisha-Siyama saki jikin ki, i'm not among that majority na mutanen da ke miki kallon tabuwa, ina kan katanga ne ina kallon yadda rikicin zaben yake gudana, in an gama a matsayi na na likitan kwakwalwa, sai nayi alkalanci na gaskiya a tsakanin ki da su".
Wani murmushi ya subuce min. Na ji kamar in gamsu da abunda ya ce mun. Wata zuciyar na cewa wayo ne kawai da hikima irin na likitoci in suna son sanin gaskiyar abu. Dr. Amir yace.
"Aisha-Siyama menene damuwar ki har kike zana Radio akan NECO answersheet? Answersheet din ma ta mathematics?"
"Duk abinda kayyi tunani a kaina, daidai ne"
Na baiwa Dr. Amir amsa a gajarce. Don na daina kare kaina a kan haukan da suka riga suka lankaya min, saidai in karbi kowanne magani da za'a bani, amma ba zan sha ya yi min illa ba. Zubarwa zan yi.
Duk dabarar likita naki cewa komai, a karshe ma sai na fashe masa da kuka nace "Dr. Na yarda da duk abinda suke ikirari na cewa na haukace, amma idan aka yi min auren dole zan kashe kaina".
"An zo wurin!".
In ji Anti. Wato irin har na iso critical stage na depression mai sanya wa mara lafiya suicidalthought. A tunanin Anti fa.
Dr. Amir Yasa biro a gefen kunnen sa yana kallo na, "kin ki gaya min me ke damun ki, ni kuma na san lafiyar ki kalau koda kika yi maganan suicide. Amma kullum ki tuna ke din muslma ce wadda ta yarda Allah subhana ke bayarwa kuma shi ke hanawa, sannan shi yayi umarni da mu yi wa iyayen mu biyayya.
Kina cikin soyayya, right?"
Na daga ido na dube shi bance eh, ba ban kuma ce a'ah ba. Na yi alkawarin ba zan kara maganar Dream Husband dina da kowa ba, zan yi abinda zai bani kwanciyar hankali kawai; Nemansa.
Dr. Ya ce "Aisha-Siyama forget him, face your exams, its your future, obey your parents, stop stressing your mental well being, face your reality. You are still young, yanzu ne damar da kike da shi na gina rayuwar ki kada ki bari damar ta wuce a banza cikin mafarkin da ba lallai ya koma gaskiya ba".
Gyada masa kai nayi kawai, fatana ya sallame mu. Ya dubi Anti Wasila yace "yarinyar ki bata tare da delusions, bata tareda kowanne rashin lafiya na kwakwalwa, amma tana bukatar hutu sosai kamar barci mai tsaho don stress ya mata yawa sakamakon infatuations da ta sawa ran ta, in tayi barci sosai zata samu nutsuwar zuciya don haka zan mata allurar barci ne kawai in bata simple drugs that will relax her stress".
Aunty Wasila tayi ajiyar zuciya tace Dr. Kana ji fa tana maganar suicide, kuma kana kira mata lafiya. Dr. Ya ce "then kada kuyi mata auren dole, tunda bata so, abinda yafi suicide ma mata suna yi akan auren dole, wasu su sanya kan su a prostitution ko barin gida. Don haka don Allah ku barta ta nutsu, ku bata dama ta manta da shi a hankali". Anti tace.
"Dr. Tun zuwa na gidan mahaifinta take maganar mutumin nan da take so, ka taba jin an so gaibu?
Ana neman shekaru biyar yanzu, bata taba dainawa ba, don haka bana jin zata daina din ko barcin kwana dubu zata yi". Dr. Amir Yace.
"Siyama where is he? Have you ever meet him in person?" Hawaye suka cika idanuna suka soma digowa, sabida yadda yayi maganar cikin damuwa da damuwata da nuna concern.
"I actually don't know Dr. I don't know." Dr. Ya ce ki bani izni in zama abokin shawarar ki a kan sa, wato komai kika ji ni zaki kira ki gayawa ba kowa ba, sannan kafin ki aiwatar da komai a kan sa ki fara shawara da ni, i'm with you Siyama.
Lafiyar ki kalau, amma kina fama da infatuation wanda kika dade da sanyawa a ranki har ya zama kina mafarkin sa, a zahiri abinda muka saka a ran mu muka kwanta da shi, shi muke gani a cikin barcin mu. Amma babu wani mutum da yake zuwar miki a mafarki face imagination da kika dade da sanyawa a ran ki ya zamar miki (fantasies).
Zaki iya raba kan ki da wannan fantasy da infatuation din ta hanyar treatment din fatar baki kadai da zan dora ki a kai (counselling) don kada ya zamo miki lahani ga kwakwalwa".
"Gashi kuma Dr. Bana bukatar cire MAFARKAN nan nawa a raina sabida ina jin dadin su, na fi so in cigaba da rayuwa cikin mafarkai na, sun fi min komai dadi domin suna debe min kewar jiran sa. Na tabbata ko ba dade ko bajima jiki na na bani zai zo ne, mafarkan da kake son raba ni da su suna taya ni jiran sa, ba ni kadai nake wannan wahalar ba Likita, ka yarda da ni ba koshin wahala nake ba kamar yadda kuke zato. I believe that our hearts are jointly connected internally".
Dr. Amir yayi murmushi ya mike yana hada allura, ya gama fahimtar duk abinda yake son fahimta, (she believed her fantasies and infatuations) na shekaru masu yawa raba ta da su farat daya zai yi wuya, har sai in ta samu actualizing din su.
Ya gama hadawa ya dawo yace "bani hannun ki Siyama zan miki allurar da zata sa ki samu isashshen barci".


Ai kuwa tunda muka shiga mota nake ta barci, Allah ya so ni gobe da jibi duka babu paper. Lallai barci Rahma ne kuma ni'ima ga dan adam, kuma yin sa da ban yi ba kwana biyu ya taimaka wajen birkita ni da ta'azzara infatuation dina.


******


A
bba ya dubi Anti da ke ta kokarin shirya masa abinci "ina 'yar taki ne? Tun jiya ban gan ta ba""likita ya mata allura tana barci" bata da lafiya ne" ya tambaya yana yamutsa fuska. Anti tace "lafiyar ta kalau stress ne na jarrabawa kawai shine nasa aka mata allurar barci don ta huta sosai". Abba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login