Showing 24001 words to 27000 words out of 45425 words

Chapter 9 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt

zai karbe shi matsayin surukin sa. Zai yaba da zabi na. My dear Abba is not that harsh anymore (Abba na bashi da wannan tsananin), na fara zargin wannan ba Abba na bane wani ne dai mai tsananin kama da shi.
Shi kam Ya Omar ina masa addu'a da fatan zai samu mata wadda ta fini son sa, wadda ta fi ni komai tun daga asali, nasaba, arziki da kyawun halitta. These are my wishes for him. Bai yi min komai ba sai alkhairi wanda yawun baki yayi kadan ya bayyana shi, zan saka masa alkhairin sa gare ni ta hanyoyi da dama musamman addu'a, amma ba ta hanyar aure ba, zai kasance cikin kowacce addu'ar sallahr farillah ta, har sai ranar da na daina numfashi.
Domin hakika Ya Umar ya kaunace ni da kauna ta musamman wadda karfin ta da tasirin ta ya zarta ta ‘yan uwantakar da ke tsakanin mu. Wanda hakan ne yasa bazan iya rayuwar aure da shi ba. Ba zan aure shi in zo in kware shi ba, in na yi hakan ni kaina ba zan taba yafewa kaina ba. Ya Omar dina, bai cancanci irin wannan auren na rashin so ba.


A cikin wannan yanayin na rashin nutsuwa na zana paper ta ta farko ta waec wadda ta kasance darasin Geography.
An ce Juma'ar da zata yi kyau tun daga Laraba a ke gane ta, wannan jarrabawa da na ke zanawa kam tun daga Talata na gane sai wani ikon Allah zai sa in samu abin kirki. Tamkar an yi wiping duk wani ilmi da experience din dana ke tunanin na samu a Regent tsayin shekaru hudu an maye gurbin su da tunanin sa, babu komai a cikin kaina sai zallar tunanin (how would he look like a zahiri? Yadda yake a mafarki haka yake a fili? Ta yaya zan gane shi ranar da ya bayyana? Ko chimpanzee ne shi sabida muni haka nake son kaya na. A kullum da tunanin hanyar da zan bi wajen kaiwa gare shinake kwana nake tashi. Amma kullum bana samun wata idea in ba ta in dauko Radio in kunna ba in soma lalube daga wannan tasha zuwa waccan, sai ko in duniya zan shiga neman sa ba.
Daga ranar dana bar gida kuma zuwa neman mutumin da ban taba gani a zahiri ba, kuma bani da tabbacin inda zan same shi (neman gaibu) nima kaina bana bukatar a kaini psychiatry zan mika kaina Dawanau ta jihar Kano dana ke jin labari, in basu damar kada su bar ni in fita ko'ina daga nan har illa masha Allahu. Zan tabbatar wa kaina hankali na ya gushe.


*****
BAKON CALABAR
M
ota kirar Luxurious irin masu tasowa daga Kudu dinnan ta sauke Ya Omar a daya daga cikin tasoshin motar da suke tsayawa cikin Abuja wato tashar Jabi. Daga nan yayi Bolt zuwa gida. Ya fito sanye cikin kayan NYSC yayi kyau matuka don kudun ta karbe shi sosai, dauke da jakar kayan sa wadda bata cika girma ba.
Mai Bolt din da ya sauke shi ko fita bai yi ba daga harabar gidan mu motar Abba ta shigo, suka yi ido hudu da dan sa Umar.
Abba ya fito da azama ya rungume Umar suka karasa cikin gida yana yi masa barka da zuwa. Daga baya Anti ta fito daga kicin tare da su Maryam-Jamila da Nadia a hannun ta, itama bakin ta ya ki rufo da ganin bakon Calabar, yau watan sa shida rabon sa da gida sai da ya kammala gabadaya tun bayan sunan Nadiya ya tafi.
Faruq Ya karbi Nadiya a hannun Anti yana fadin "yarinya kamar Boddo tana Baby". Anti tace ai Siyama da kai take kama, Nadiya ko da Abban ku take kama, don dai Siyamar ce a ranka shiyasa ka ga sun yi maka kama". Dariya yayi, wadda ta fiddo fararen jerarrun hakoransa kamar kankara dasu don haske, yace cikin jin nauyi. "Anti ni tana ina ne? Ban ji motsin ta ba" Anti ta ce " ka san sun fara WAEC tana can tana zanawa. Yanzu zaka gan ta".


Bata rufe bakin ta ba nayi sallama a falon, rungume da takardu, sanye cikin uniform din Regent. Na rame sosai na kuma yi duhu. Ya Omar ya bi ni da kallo affectionately yana tambayar Anti dalilin wannan ramar tawa da duhun da ya ga na yi, ina ganin Abba ya harare ni cikin takaici. Anti ta ce cikin son kawar da zancen,
"ka san jarrabawa take kuma kwana biyu dai bata ji dadi ba".
Da haka ya bar zancen ba don ya gamsu ba sai don Abba na wurin, bay a son ya zurfafa nuna damuwar sa a kaina a kan idon Abba. A sanyaye na dube shi nace "ban san yau zaka dawo ba Ya Omar ban share dakin ka ba, amma bari in ajiye takardun nan in canza uniform ina zuwa yanzu zan gyara maka" da kulawa yace "na yafe Boddo, jikin ki babu kwari sam, zan share da kaina, da gajiyar jarrabawa zaki ji ko da gyaran daki?"
A yadda yake min magana loving and romantic tamkar ba Ya Omar din ba yau,kamar ya maida ni cikin sa don so da kulawa, idanun sa na ta karakaina a kaina da duk wani motsi na, sai da yasa Abba da Anti jin kunya sosai suka soma kokarin barin wurin. Na wuce ban ce komai ba, don nima yau na ga sauyuka masu yawa a tare da Omar da suka sanyaya jiki na, shikuma Abba yace da shi da safe yana son ganin sa kafin ya fita ko'ina.
Washegari ni da Anti muka shirya breakfast na musamman sabida dawowar Omar, yana gefen Abba ni ina gefen Anti da Maryam-Jamilah akan cinya ta ina bata dankali Anti kuma tana baiwa Nadiya abincin ta, Abba da Omar suka riga mu kammalawa sai Abba ya dauko mukullin mota 'Ranault' sabo dal ya ajiye ma Omar a tafin hannun sa.
"Na cika alkawari kamar yadda ka cika alkawari ka fiddomin ‘first class degree’ Omar, Allah ya sanya albarka.
Ka kammala hidimar kasa lafiya, gashi tuni na bada sunan ka a ECOWAS sabida na kusa yin retiring".
Abba ya dakata yana duban mu dukkan mu, ganin duk mun nutsu muna sauraron sa sai ya samu karfin guiwar cigaba. Kafin ya ce da Umar.
"Me ya saura maka yanzu? Ginin gidan ka na Katampe ya kammala, zaka bar gidan nan daga yau, don BQ ya maka kadan, ka koma gidan ka, ka riga ka zama babban mutum yanzu Umar, kafin ta karasa jarrabawar a daura muku aure ta tare.
Na baku daga nan zuwa ta kammala jarrabawa ku fahimci juna ba irin waccan fahimtar ba, fahimta ta zama miji da mata.
"Siyama!"
Abba ya kira sunana da kakkausar murya kafin in dago in dube shi tuni na fara kakkarwa sabida ban zaci a gaban Ya Omar zai yi zancen nan ba, "har yanzu kina kan bakan ki na iskokai cewa wani kike so ba dan uwan ki ba, ko kuwa kin dawo cikin tunanin ki?"
Ya ilahal alameen ka kawo min agaji, ko daren jiya na sake mafarki da shi ya kara yagalgala zuciyata da nau'ikan soyayyar sa. Bana ji bana kallon kowanne namiji da idanun soyayya sai shi. Kan Omar yana kasa bai iya yayi ko kwakkwaran motsi ba, Abba yace "na kashe wancan maganar taki ko bayan raina kada ki kara tada ita.
Wannan shine mijin da addini yayi min umarni in zaba miki, shi na yarda ya zama uban 'ya'yan ki. Ina so daga yau in ga irin matsayi na a idanun ki Siyama, in ga kuma shin na isa da ke ko kuwa hoto nake a gare ki ba Uba ba?"
Ya maida duban sa ga Omar yace "Faruqu I trust you beyond words, pls don't let me down. Su mata ka sani daga karkataccen kashin hakarkari aka halicce su kullum a karkace suke. Kwakwalwar su a baibai take. Sai ana yi ana mikar dasu, sai an yi hakuri ake cin gajiyar su, balle Siyama da har gobe yarinya ce shiyasa ma nake mata uzuri a wasu lokutan irin wanda nake so kaima ka koyi yi mata har komai ya daidaita a tsakanin ku.
Allah yayi muku albarka zan fita, ina so yau ta zamo ranar da zaka fara zuwa zance gun kanwar ka officially".
Abba yana gama fadin haka shi da Anti suka tashi suka hau sama. Ya zama daga ni sai Ya Omar don Maryam Jamila ma ta sauka daga jiki na ta bi bayan Anti, daga ni har shi kan mu na sunkuye don ji nayi kamar Abba ya dora min dutsen Uhudu a kai na, ya daddaure ni da kalaman sa.
Umar kuwa tunanin sa daban ne da nawa wanda daga shi sai Ubangijin sa suka sani. Ba yau ya fara jin na ce ina son wani daban ba shi ba, karewa ma ya riga kowa ji tun ina fifteen years a Mambila ranar da muka je tebirin Garba mai shayi kuma tun a ranar yake jin ciwon abun a ran sa amma yau da Abba ya sake fade har yana rokon shi yayi hakuri da ni zamu daidaita a hankali kuma kaman by force zai aura masa ni sai ya ji kansa a mara sa'a, kuma mara abinda mace zata so.
Dacin hakan da ya ji a ran sa ne ya sanya shi saurin dago kai ya dube ni da idanun da suka kada, ya ce "Boddo feel free with me, it's your Ya Omar, iknow you don't love me but please..... don't hate me because of him, I beg you.
Ni na san I'm a loser, na sani amma ki kwantar da hankalin ki da yardar Allah in har ina raye ba zan bari Abba yayi miki auren dole ba".
Ya karasa maganar cikin shakewar sauti, in ya tuna shi Boddo ta ke kiran auren sa na dole, kamar tana masa kallon matsala a rayuwar ta.
Na wani irin dago cikin slow motion na dubi Ya Omar, jijiyoyin kan sa sun fito rada-rada abinki da farin mutum idanun sa sun kada, ban taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan yanayin ba.
Sai na ji duk wani guilty conscience na duniya ya rufto a kaina ya danne ni, anya abinda nake shirin yiwa Abba da Omar a kan wani da ban sani ba, bani ma da tabbas a kan sa daidai ne? Anya ba zan yi SAKACIN da zan zo na kasa gyarawa ba?"
"Ya Umar ban taba kin ka ba wallahi ka yarda da ni, ban taba alaqanta aure a tsakanin mu bane, ban taba baka matsayin ka mijin aure ba sabida na fi so kacigaba da zame min bango abin jingina, wanda in mijin ya bata min wajen ka zan zo. I only love you as a brother not as a husband, I'm sorry Ya Umar, i'm very sorry.
I know it will hurt but you don't know how much it deeply hurts the culprit (na san abin da ciwo amma kada ka so tona yadda yafi zama ciwo ga wanda ta aikata), na sani Ya Omar ko da aure ko babu you will stand by me, ka taimaka min in nemo shi bani da idea.
I may sound selfish but that is the bitter truth, my own fate, da iyakacin gaskiya ta nake magana. Babu gurbin kowa na soyayya a zuciya ta sai nasa.
Ba lokaci daya na soma son sa ba, na so shi ne tun ban san son sa na ke ba. Dare da rana yana huntingdreams dina da duk wani sako na zuciya ta cikin shekaru bakwai, alhalin kuma ban san shi ba, ban san inda zan gan shi ba......
Yet i'm craving for him!".
Na kifa kaina a kan teburin cin abincin na shiga rera kuka mai sauti. Jikin Umar har bari yake yi ya matso gabana ya dago ni, bansan ya aka yi ya aka yi ba, na samu kaina da fadawa jikin sa na rungume shi tsam-tsam, ina kuka ina kuma bashi hakuri.
Omar suman zaune yayi don wannan ne karo na farko da hakan ta faru tsakanin sa da Boddo tun balagar su. Irin reaction din da jikin sa ya dauka ya tabbatar masa yana son Boddo, so na hakika pure and real, ba irin wanda ita take masa ba, yana kuma kaunar zamowar ta mata agare shi uwar 'ya'yan sa amma kash!
Ga abinda ke fita daga bakin ta a kan wanin sa, Boddon da tun haihuwar ta ya ke son ta.
Mun jima a haka kafin Ya Omar yayi ta maza ya raba ni da jikin sa, yasa hankicin sa yana share min fuska ya ce "Alright Boddo, na fahimta ki daina kuka ki kuma kwantar da hankalin ki bazan biyewa Abba in aure ki dole ba, zan sama mana solution wanda bazai yi fushi da ke ba.
Amma lamarin naki is too complicated Boddo, ko ina son in taimaka miki din ban san ta ina zan fara ba, yau da ace kin san mutumin nan ne kuma kinsan inda yake, sannan kuma shima yana son ki it will be fine, but na kasa gane maganganun ki na baki san shi ba baki taba ganin shi ba sai a mafarki this is unblievable!.
Ina so in taimaka miki amma ban san ta ina zan taimaka miki ba tunda bazan iya shiga cikin mafarkin ki in gan shi in yi magana da shi ba? I wish he's real (na yi fatan ace akwai shi a gaske) da sai inda karfi na ya kare wajen lallashin Abba.....".
"Wallahi a raye ya ke Ya Omar, kuma mutum ne kamar kowa, ka bani lokaci zan nemo shi, in dai zaka cika alkawarin ka na rarrashin Abba, da kunnuwa na naji muryar sa a radio bayan na mafarki"
"Radio?"
Omar ya tambaya cikin kakabi na mamaki da tunanin Boddo soyayyar gaibu ta sa ta zare. "Kuma sai aka ce miki shine na cikin mafarkin ki? Wahayi aka yi miki ko me?"
A wannan gejin na fara tunzura da tambayoyin da yake min masu son tabbatar da cikakken hankali na. Amma na san Omar yana nufin taimaka min da gaske, don haka na sassauta zuciyata na labarta masa abinda ya faru ranar, da Rukiyyar Aljanu da Anti tasa Abba yasa aka yi min".
Duk halin da Ya Omar ke ciki saida yayi dariya yace "Boddo yanzu ta ina zamu fara neman Mr Radio?"
Na harare shi don ganin shikuma hauka zai lankaya min, nace "in da gaske kake zaka taimake ni ne Ya Omar to mu fara zaga gidajen Radiyon Abuja, kuma ka tambayi Abba wace tasha yake saurare ranar da na fadi musu? Na rantse maka idan na ganshi daga ganin farko zan gane shi, da jin muryar sa zan shaida ta". Omar ya rufe fuska da tafukan sa yana murmushi mai ciwo, yace "a sa cewa mun same shi a gidajen rediyon da zamu je din, a sa cewa kin gane shi, sai mu ce masa me Boddo?
Mr. Radio ka zo ka auri Boddo tana mafarkin ka tana son ka? Kin wuce nan Boddo, a matsayin ki na bafullatanar Mambillah.
Ba kya tunanin hakan zubar da kimar ki ne ta diya mace mai darajar fulanin Mambilla, jikar Malam Dalhatu Gembu da Saudatu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login