Showing 3001 words to 6000 words out of 45425 words
Chapter 2 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt
bakin tagar ajin su ya ki tafiya yana leke yana sauraron karatun daga bakin taga, dole malamin su yake jin tausayin sa ya kyale shi yake zuwa karatu da ni. Don ya lura kaunar da Ya Omar yake min tana da yawa.
Wannan ya faru ne a sanda na fara wayo. Wani abun jimami da ya biyo bayan murnar haihuwa ta shine tun bayan haihuwar Asshe ke fama da matsalar zubar jini, an yi yawon neman magani iri-iri har babban asibitin jihar Taraba inda likitoci suka tabbatar da cewa magunguna masu karfi data yi ta sha na gargajiya don neman haihuwa su suka lalata mahaifar ta, Allah ne ya rubuta zan shaki iskar duniya shiyasa har ta iya ta haife ni.
Aka saka ranar da za’a yi mata aikin cire mahaifa don a samu zubar jinin ya tsaya ta huta ta samu lafiya gabadaya amma babu batun sake haihuwa.
Da ranar ta zo aka yi komai lafiya aka gama lafiya, ana ta murna wahala ta kare, ashe kuwa da gaske babbar wahala ta kare domin kuwa Inna Asshe, bata farfado daga allurar anaesthesia ba.
******
MAMMAN
“
Kina nufin Hassu da Asshe duka sun shigo rayuwar mu ne ni da Yaya Gidado halan don kawai su haifa mana marayun ‘ya’ya su bar mu da kananan marayu su koma?
Me kike nufi da cewa ta zarce a cikin allura??
Kina nufin, nima ni kadai zan raini ‘dan nan/'yar nan kamar yadda Yaya Gidado yake rainon Omar Faruk shi kadai???
To shin da wanne nonon kike nufin zan raine shi/raine ta?
Ai gara Umar ya sha nonon uwa har na tsayin shekaru biyu ko ba komai ya san dumin jikin uwar sa, ki ji tausayin halittar Allah baiwar Allah ki fada min gaskiya cewa wasa ki ke….. k ice min mata ta Asshe barci take yi a cikin allurar yanzunnan allurar za ta sake ta ta tashi mu tafi gida ta shayar da Dan ta”. Sai hawaye wasu na korar wasu suka biyo bayan maganganun da zaka tabbatar cikin fita hayyacin sa yake yin su.
Abinda Baba na ya fadawa Nos din da ta gaya masa rasuwar mahaifiyata kenan kafin hawaye su cigaba da tsinke masa, ya kuma kasa karbar jaririn da take ta faman bashi kamar ya ce mata "ki musanya min shi da mata ta Asshe. Zata iya kara haifa min wani, amma ita bazan kara samun kamar ta ba!!!"
Nos dai bata gane sambatun wannan mijin mai tsananin son matar sa me yake nufi ba, ta dai san zafin mutuwar matar sa ne ke bugun sa ya kuma fidda shi a hayyacin sa, sai hakuri take bashi. Tana tuna masa ayar Ubangiji da ta ce “Kullu Nafsin Za’ikatul Maut”.
Ta kuma miko masa ni nannade cikin zanin atamfar mahaifiya ta tana fadin,
“Yi hakuri ka karbi kyakkyawar kyautar ‘yar da Allah yayi maka ka ji! ‘Ya mace ce ba namiji ba. Idan ka yi mata kyakkyawan raino watarana zata ji kan ka kamar mahaifiyar ta”.
Haka Abba ya karbe ni cikin yanayi na dimauta da yankewar buri gabadaya ya fito waje neman Ummati, can ya gano ta inda ya bar ta tana tahiyar sallame sallahr walha a inda ya bar ta tun safe kenan tana rokawa Ashe sauki a cikin tahiyar ta, ya karasa gabanta ya ajiye mata jaririyar a saman cinyar ta sannan ya koma gefe ya saka kai cikin kafafuwan sa ya saka kuka.
Kukan da tun kafin ta san dalilin sa Ummati ta tabbatar itama Asshe maraya ta bar mata, marayun sun zame mata biyu, Ya ilahi, sai ta sallame sallahr ta ce masa “ka ce Innalillahiwa’innailaihiraji’oun Muhammadu, shine kawai abinda zaka yi Allah ya yi farin ciki da kai a wannan yanayin. Ka kuma karbi ‘yar ka ka yi mata huduba da sunan mahaifiyar ta.
Ka yi fatan Allah ya baku tsahon rai ku ku raine su, ka je ka daukota mu tafi ka wanketa da hannun ka ka yi mata suttura ka kai ta makwancin ta da kan ka shine babbar soyayyar ka gare ta a yanzu, ka cigaba da nema mata aljannah”.
D
aga Jalingo kai tsaye suka yi shatar mota zuwa Manbila aka yi wa mahaifiyata sutturah. Mutuwar Inna Asshe ta fi taba Ya Omar fiye da kowa a gidan don shi bai san cewa ba ita ta haife shi bama.
Omar bai san maraicin uwa ba sai da Inna Asshe ta rasu, kulawar mu ta koma hannun Ummati, duk da Ummati bata raga mana komai ba na kulawa da tarbiyyah amma Kakar mu ce kuma tsohuwa ce. Kulawar Kaka daban kulawar uwa-mahaifiya daban, idan ka hada duka biyun zaka fi kowa morewa, uwa ta kwabe ka har da bulala Kaka ta lallashe ka da tuwo da koko, tunda dai Kaka da sangarta jika aka san shi.
Mafari kenan da raino na ya koma hannun Ummati, muka shaku wata irin shakuwa da Kakata Ummatin Mambila, kakkarfar dattijiya, doguwa fara mai kyawun surah wadda bata daukar kowanne irin wargi ko raini a kan jikokin ta, zaka yi mata komai ka kwana lafiya amma kada ka taba Aisha da Omar. Da ganin Ummati zaka san an zuba zamani kuma an zuba kyau an juya miji a lokacin kurucciya.
Abu na farko da ya assasa shaquwar mu zuwa shakuwar da ta zarta ainahin wacce ke a tsakanin Kaka da jika ta zama ta mahaifiya da tilon ‘yar ta, ya sanya kuma ta dora min soyayyar duniya shine kasancewar ita bata taba haihuwar diya mace ba, na biyu ita ta shayar da ni daga madarar shanun ta, kuma na ci sunan mahaifiyata wadda tayi mata biyayya sosai.
Baba Gidado yayi aure da jimawa da Jaru, matar wani marigayin abokin sa, bayan tsayin lokacin da ya dauka babu aure, don ya tabbata ba zai sake samun mace tamkar (Ummu-Faruqu) ba kamar yadda ya ke kiran Hassu har gobe, amma ko kadan baya jin dadin ta, haka dai ake zaman da dadi ba dadi.
Ya riga ya saba da matar sa Hassu mai addini, mai hakuri da kuma godiya da duk abinda ya kawo mata, mai yakanah, wadda ko kara ya ajiye ya ce kada ta tsallaka bazata tsallaka ba, wadda in ya ce farin yadin nan baki ne zata ce da shi “bakikkirin kuwa”, amma Jaru? Akasin Hassu ce a komai.
Ya yarda hakika Allah ba ya barin wani, don wani ya ji dadi. Da bai dauke masa Hassu ya hada shi da Jaru ba, da bai raba Mamman da Aishatu ba sabida wadannan matan guda biyu tamakar Hurul ‘eenin duniya suke ga mazajen da Allah ya baiwa su;
Ga kyau ga kuma kyan hali. Ga addini da nasaba mai tsafta. A hakan dai suke zaune shi da Jaru; yau fari gobe tsumma, sabida ya yi alkawarin ba zai taba sakin mace a rayuwar sa ba, sai dai ta bizne shi ko ya bizne ta.
Babbar damuwar sa da Jaru shine ta ki jinin Omar Faruq, ba dama ya zo sassan su goye da ni zata kora mu da tsawa da bulala, daga sanda ta fahimci Omar dan sa ne na cikin sa ba na kanin sa ba tsanar da ta ke ma Omar ta karu, sabida kanin nasa (wanda ta fahimci a Jos yake zaune zuwa yake yi ya koma), kullum ya zo tsarabar sa ta Omar-Faruq ce baya ko ta kan tashi ‘yar da ya haifa a cikin sa sai Omar, Omar dai Omar dai ko’ina ka shiga sunan sa ne a bakin jama’ar gidan alamar ya gama mamaye zukatan su.
Ita kuma Jaru sai wata jarabta ta same ta; nan duniya babu namjin da yake burge ta irin Mamman sabida gayun sa, bokon sa da tsaftar sa, ya fita daban da mutanen garin Mambila domin a lokacin yana aikin koyarwa a jami’ar Jos matsayin Lecturer, a lokaci guda kuma yana hada digirin sa na ukku a can jami’ar Jos din.
Lokaci - lokaci ya ke zuwa Gembu kuma in ya zo din baya jimawa bai fi yayi sati ko kwana uku ba ya koma, kasancewar dukkansu a gidan gadon su suke zaune har zuwa lokacin illa kowa da sassan sa, sassan Ummati da jikokin ta daban wanda yake daga can karshen gidan, nasu ita da Gidado daban a tsakiya sai na Mamman din a farkon shiga gidan wanda kullum yake a rufe sai idan ya zo garin Omar yake budewa ya share masa ya shigar da kayan sa.
A babban zauren gidan kuma dakin Baffan mu Adamu ne wanda a wannan shekarar Abba (Mamman) sunan da na mayar masa kenan tunda na soma baki, shi kuma Baffa Gidado in ce masa Malam, Abba ya samar ma Baffa Adamu tagomashin tallafin karatu daga (federal scholarship board) zuwa kasar Algers inda zai yi karatun degree akan Diplomasiyya.
A wancan lokacin su Abban mu sune manyan ‘yan bokon da kasar Najeriya yankin arewa maso gabas ke ji da su da kuma alfahari da su, yana daga cikin pioneers (sahun farko) na malaman tsangayar tsimi da tanadi ko kuwa tattalin arzikin kasa (department of economics) lokacin da aka fara darasin a jami’ar Jos, suna da damarmaki masu yawa a kan scholarships, ya baiwa samarin Mambila da dama tallafin karatu da scholarship zuwa Algers kasancewar a zamanin ba duka ne suka yarda suka karbi ilmin bokon ba a sanda ya kutso Taraba ya isko Manbila sai daidaiku irin su Abba, don haka su suka fi kowa cin gajiyar shi a zamanin da ake ciki yanzu sanda kai ya fara wayewa samarin Mambila na ta rububin shiga karatun.
A kan Mamman Jaru ta raina Gidado take kuma ganin ta yi rashin dace da auren sa, da ta san da kanin da bazata auri wan ba, har fata take ya mutu don ta samu damar auren kanin sa. Ita kam dama ba ‘yar asalin Mambila bane bakin haure ne daga yankin kasar Kamaru, tsautsayi ya kai shi ga auren ta kasancewar tsohon mijin ta mai rasuwa Malam Jibo aminin sa ne kuma bata taba haihuwa ba, a tunanin sa rashin haihuwa da bata samu ba da Jibo, tsahon shekaru goma sha biyar da suka yi tare da shi zai sanya ta so tilon dan sa Faruku, ta taya Ummati kula da su shi da kanwar sa.
Ba da jimawa ba ya fahimci ba wanda ta tsana a duniya irin Omar din. Abinda ke ran ta a kan kanin sa Mamman ne bai taba sani ba kuma tunanin sa bai taba bashi ba. To ta ina ma zai taba tunanin matar sa kanin sa take so?
Har zuwa wannan lokacin da ya amsa sunan Dr. na ilmi, Mamman Gembu, bai yarda yayi aure ba, fada da nasiha da tsoratarwa babu irin wanda Ummati bata yi masa ba amma ya ki. A karshe Jaru ta ga babu mafita gareta ta samun damar auren Mamman in har Gidado na raye, sai ta soma tunanin hanyar da zata bi ta kawar da Gidado.
Duk abinda ta yi tunanin yi, sai ta ga cewa za’a iya gane ta, a karshe ta nemi guba mai tsinka hanji ta saka mishi a cikin fura. Ta zauna jiran dawowar sa.
Tun tana gadin dawowar sa, ta saka furar da abincin a gaba tana ta kiyasin gobe I yanzu tana cikin Takaba, wata uku masu zuwa sai ta maye gurbin wan da kanin, ko da tsiya ko da arziki (ko da ta asiri ne), tana nan zaune tana wannan saka da warwarar har wani mugun kashi ya zo ya matse ta.
Da fari ta yi kokarin danne shi musamman da yake lokacin dawowar Gidado ya yi amma bayan gidan nan ya ki yarda da hakan, neman fitowa kawai yake yi ko ta halin kaka. Sai ta ga cewa zata iya zuwa tayi kashin ta dawo ba tare da ya dawo ba ko wani ya shigo.
Ta ajiye masa a inda ta saba ajiye abincin sa ta koma sashen ta ta shiga bayan gida kenan Gidado ya shigo tare da wani saurayi.
A nan falon sa suka zauna suna hira ya dauki furar ya baiwa bakon yana fadin.
“Jira ta ta fito Bashari, na san ta zaga ne, ga nan fura ka sha, bari in dibo Asshe cikin gida na ji kukan ta yayi yawa, yanzu haka Faruqu ke cin zalin ta”.
Ya saka takalmin sa ya nufi cikin gida da sauri babbar rigar sa na neman tadiye, shi don in da abinda yafi tsana a duniya to kukan Asshe ne.
Bakon da ya kira da Bashari kuma ya kafa fura a kai yana kwankwada don a yunwace yake ainun a matsayin sa na matafiyi, ko ludayin kan faifai din bai saka ba kada ya bata masa lokaci a yunwar da ya kwaso tun daga kasar Kamaru.
Yana sauke kwaryar daga fuskar sa suna hada ido da Yayar sa Jaru. Jaru ta kwalla kara tana fadin “na shiga uku na lalace Bashari furar Gidado ka sha??? Furar da na sakawa guba ce fa!”
Yayi daidai da dawowar Gidado tsakar gidan tare da Ummati, ya na dauke da Asshe a kafadun sa. Omar na biye da su.
Suna jin abinda Jaru ke fadi cikin yanayi na rashin hayyaci cewa ya ci gubar data sawa Gidado don ya mutu ta auri Mamman, abin nata kamar kaikayi ne ya koma mata, kasancewar Gidado Malami ne ya dade yana yi wa kan sa da ‘ya’yan sa tsari iri iri da ba dai mutum ba sai dai Allah.
Ko kafin su farga Basharin ya fara shure shure kumfa na fita daga bakin sa, sai kuma jikin ya saki bakidaya alamar babu sauran rai a jikin sa.
Wannan bakin al’amari da ya faru a gidan Malam Gidado babu wanda bai ji labarin sa a garin Gembu ba, aka saka Jaru a waka, hukuma tayi mata hukuncin da ya dace, Baba Gidado yayi alkawarin ba zai saki mace ba amma Ummati ta saka shi a gaba ta ce sai ya saki Jaru a take in yaso ya yi kaffara, wannan ba matar zama bace.
Wannan shi ya kawo karshen auren Jaru (Hadiza) da Gidado Dalhatu Gembu.
******
MALLAMGIDADO DALHATU GEMBU
H
akika ya firgita da al’amarin mata wanda ya kai shi ga cewa babu shi babu kara aure har abada, wai a kan kanin sa ta yi niyyar kashe shi, wannan wane irin rikitaccen zamani ne na son zuciya da rashin tsoron Allah Allah ya kawo mu? Da yake Shi fa’aalun lima yuridu ne sai Ya juya abin a kan dan uwan ta.
Shi kan sa Dr. Mamman Gembu da ya zo gari ya samu labarin ya firgita iya firgita, Allah ya tuba ko mata sun kare a duniya ai ba zai auri matar yaya Gidado ba koda mutuwar yayi ta Allah da Annabi. Shi kam! A lokacin ya kara jin tsoron duniya dana kaidin mata. Ya kama Omar - Faruq da Asshe dake zaune bisa cinyoyin sa ya rungume a jikin sa yana nema musu tsarin Ubangiji daga mugun ji da mugun gani da sharrin mutum da aljan. Ya roki Allah ya raya musu su har su aurar da su da hannun su shi da Yayan sa, ya yi alkawari tun a lokaci in har yana raye to Asshe bata da miji sai dan uwanta Omar, Omar baya da mata sai kanwar sa Aisha. Kada su je bare su cutar da su da sunan aure.
Wannan abinda ya faru din ya kara nesanta shi daga kan turbar son sake aure shima, dan sauran hope din da ya fara samu na yin aure bayan kammala digirin sa na uku ya bi ruwa. A lokacin ya cika shekaru talatin da biyar a duniya, sabida kyawun surar sa na ‘yan Gembu da kamewar sa Allah kadai ya san iyakar matan da ke haukar ya aure su a can jami’ar Jos, inda yake aikin koyarwa.
Lamarin Jaru ya taba Malam Gidado sosai ya kasa barin ran sa, tun daga lokacin kuma sai ya fara shiga ittikafi, yana nemawa ‘ya’yan sa tsari daga sharrin mutane.
Ya fara fama da ciwon suga kadan kadan da hawan jini