Showing 30001 words to 33000 words out of 45425 words

Chapter 11 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt

yace "but an fi son barci natural, yin allura don kawai ayi barci?""Likitan da yayi mata ya san abinda yake yi, wajen specialist (psychiatrist) na kaita, ko ba komai yanzu hankali na ya kwanta tunda na tabbatar Siyama bata da tabin hankali kuma bata da aljanin dare as well. Imagination ne data dade da sakawa a ranta yake zamar mata mafarki.”.
"Sai tsabagen iya shege kuma ba!"
Inji Abba cikin takaici. "Ni kuma nafi kowa iya shegantaka dani take zancen. Ko lefe bazan mata ba.
Wai Umar ne Siyama bata so? Humm, duniya mai abin mamaki. Zuciya mugun nama mai kawace - kawacen banza.
Allah ka shirya min Siyama, ka fidda rabon shaidan daga zuciyar ta". Anti ta amsa da "Amin, amma Abba don Allah likita ya roki a daga auren kada ayi a yanzu, a kara bata lokaci zai yi counselling din ta ta manta da wancan din"
"Aikin banza aikin wofi, kada Allah yasa ta manta shi koma waye. Ta dauke shi su tafi gidan mijin ta tare. Bani da burin Siyama tayi zurfin ilmi a hannu na, gidan miji zan kaita a wannan watan da zamu shiga.
Duk wani nauyi da Allah ya dora min nata na sauke, a yanzu aure kawai ya rage, kuma zan tabbatar a hannu nagari na damkata, ba ruwa na da shirmen ta.
In ya so tayi tayi gunduwa-gunduwa da Umar din ta kawo mini, karewar rashin so kenan dai ko?"
Anti kasa magana ta yi, don tsakanin uban da 'yar bata san wa ya fi wani taurin kai ba. Ba mamaki in ya kasance gadowa Siyaman tayi.
Kwana uku ina bacci sai dai Anti ta tada ni ta bani ‘fresh milk’ in sha in koma, dama kuma cikin al'ada nake, wani zubin sai tazo da kanta ta kaini toilet ta taimakamin na canza Pad sabida nauyin barcin da ke kaina. Ranar da barcin ya sake ni na koma na karasa jarrabawoyi na. Wanda babu laifi na dan amsa wasu yanzu domin na samu nutsuwa sosai.
*****




FAREWELL FROM REGENT COLLEGE
A
yau mun kammala Regent College Abuja, kowa ka gani cikin farin ciki marar misaltuwa yake sai hotuna ake dauka da 'yan uwa da iyaye da kawaye. Anti ce da su Nadia suka zo dauka na bayan mun yi sallama da Azima Ko'oje da sauran wadanda muke mutunci dasu, da alkawarin zan je gidan su Azima idan na huta, kai tsaye muka kama hanyar gida, amma sai Anti tace Dr. Amir yace mu biya ta wajen sa ya kara gani na. Ban ce komai ba, ko babu komai shine wanda ya wanke ni daga hauka a idanun ta.
"Aisha Siyama an gama jarabawa lafiya ko, ina fatan akwai improvement?"
"Alhmdulillah Dr., na dan tabuka ana karshe-karshen"
"To wane course kike so zaki yi yanzu a jami’a?"
"Babana ba zai barni ba"
"Sai aure kenan"
Na hadiyi miyau da kyar. Ji kake mukut.
"Kin kara yin mafarkin sa?"
Girgiza masa kai na yi alamar a'ah,
"I only enjoyed my sleep"
Masha Allahu Aisha, kin karbi maganar Baban ki da muhimmanci yanzu ko? Imean ta auren dan uwan ki?"
Shiru nayi ban ce masa komai ba. Shi da kan sa sai y ace.
"Prefer not to say?"
Na gyada masa kai da sauri, yace “to ya yawan tunanin har yanzu yana nan?"
Na ce a hankali "bana tunanin komai tunda na gama barcin nan, ni ina zargin ba allurar barci kayi min ba gaskiya, damuwar tayi nesa da zuciya ta sosai. Bana jin bacin bacin rai sam ko wata damuwa, sai an tada min maganar auren Ya Omar".
Dr. Ya maida hankalin sa ga Aunty yace "Alhamdulillah, she has responded fully to the treatment made. Shawara ta karshe itace ku hakura da yi mata auren nan, if not, abinda ake gudu shi zai faru da Siyama wato, zata tabu".
Aunty Wasila tayi zugum da ita, tace "Dr. Matsalar ba daga gare ni bane, ba kuma daga Umar bane, wallahi yafi kowa damuwa da farin cikin 'yar uwar sa, Baban su ne matsalar, ba zai taba yarda da wannan shawarar ba, iknowhim kamar tafin hannu na. In yace YES to da gaske yana nufin YES din, babu gudu babu ja da baya, baya waiwayen abinda zai je ya zo".
*******


M
una isowa gida Abba na dawowa, duk muka yi gare shi muna masa oyoyo, ya dube ni sai ya ga na rame ga idanu na sun zurma yace "jinya kika yi ne halan?” Girgiza kai nayi ban ce komai ba. Anti ce ta ce “na gaya maka ai, tayi jinyar baccin kwana uku", "to Allah ya kara lafiya, ya batun jarrabawa kuma sai yaushe za’a gama?""An gama yau". Ta fada da fargabar abinda zai biyo baya.
Daidai sanda muka shiga cikin gidan duk muka zazzauna a leather seats na falon kasa. Abba ya bude ‘brief case’ dinsa ya fiddo (flight tickets) guda biyu ya mikowa Anti. "Ga nan, amshi, flighttickets din ku ne na tafiya Lagos gidan Adamu gobe, zaku hadu ke da matar Adamu ku yi sayayyar duk abinda ya dace na gidan Omar da Siyama, ku kuma hada mata lefe irin wanda duk take so.
Da na ce bazan yi mata lefen ba amma Ummati ta ki. Rana ita yau da an sakko masallaci daurin auren su insha Allahu a Mambilah".
Ya kawodaya daga cikin ‘credit cards’ din sa na bankin GT ya bata "abinda ke cikin nan nan ina ganin zai ishe ku sayayyar komai, ayi komai na hankali da kula bana son almubazzaranci".
Hannu bibbiyu Anti tasa ta karba tana fadin.
"A madadin Siyama Allah ya saka da alkhairi. Ni kuwa sai nayi kasa da kaina.
Da daddare na bi Anti dakin ta na sameta tana canzawa Nadia Diaper, fuskata ba walwala nace "Anti nikam ba sai na biki Lagos dinnan ba, kuje kawai dik abinda kuka zabo zai min dai dai". Hawaye suka balle mini.
Anti tace "sabida bakya farin ciki ko sabida baki godewa kokarin Baban ki ba ko??"
"Anti....!"
"Siyama ki shirya kayan ki zamu tashi Lagos gobe da safe insha Allahu, zamuyi kwanaki uku na san zasu ishe mu mu gama abinda ya kai mu. Kwana daya lefe, kwana daya furniture da kayan kitchen da labulaye. Nasara ta san ko'ina a Lagos da inda za'a samu komai mai kyau, zata raka mu".
Juyawa nayi kawai na fita ba tareda na kara tankawa ba, don na san duk abinda zan fada din tirjiya ce kuma ta nuna min bazata karbi kowanne uzuri na ba.
Na tashi da zazzafan zazzabi a safiyar washegari, zazzabi mai zafi sosai harda jijjiga, da kartar hakora, wanda yasa dole Anti ta barni a gida ta tafi sayayyar kayan aure a Lagos don bata isa keta umarnin Abba ba, ni kuma na shiga jinyar kaina da kaina don Abba ma ba ya gari daga ni sai Maryam Jamila. Ita take taimakamin da miko min duk abinda nake so ina daga kwance, ta bani paracetamol na sha naji dan dama-dam wajen azahar na dafa mana noodles muka ci nida ita.
********


N
asara da Wasila ba inda basu shiga sun fita ba a kasuwannin garin Lagos suka hada lefe mai tsari, sannan kayan sakawa a gidan amarya. Kwanan Anti uku suka dawo. Ashe har da Ya Omar suka dawo gidan.
Bai nemeni ba sai ana daurin aure saura kwana biyar muka hadu a kitchen yana shan ruwa daga firji, ni nasan na rame sosai amma dana dubi Ya Omar sai naga ya fi ni ramewa, ga kasumba ya bari a fuskarsa wadda a baya bashi da ita. Ya kara zama cikakken namji.
A zuwan sa Lagos ma Young Abba ya yi masa tayin aiki da ofishin su, yace shi a'a a ofishin su Abba zai yi aiki sabida Abba ya kusa retire.
Kaina a kasa na shiga kitchen din nayi kamar ban gan shi ba, har zai fita sai ya dakata yace.
"Boddo ko gaisuwa babu?"
Muryar sa kamar ta wanda ke fama da mura, na kasa kallon cikin idon sa don alkawarin da yayi min bai cika shi ba, ya ce zai lallashi Abba kada a yimin auren dole amma yayi hakan? Shirin angwancewa yake yi.
Da ya ga ba zan gaishe shin ba kamar yadda na saba sai yace "kada ki damu fa Boddo ni ba bakon zafi bane, it's a promise bayan auren mu ba zan zo inda kike ba, I mean... I mean ba zamu hada shimfida ba don na fahimci damuwar ki kenan.
Zan yi hakuri zan jure har sai ranar da kika karbe ni as a husband don radin kan ki. Ranar ne zaki banbance da banbancin da ke tsakanin Aya da tsakuwa; soyyayyar Yaya da ta wani bare da kike underestimating dina a kan sa.
Zaki tabbatar soyayyar gaskiya ba a mafarki take gudana ba, a zahiri take; from theory to practice.
Na tabbata Dream Man din naki, bai fi ni komai ba, haka bai fi sauran maza mazantaka ba, watakila ma.....watakila ma.....ya kyabe baki kafin yayi kasa da murya kada wani ya ji abinda zaya ce, kamar cikin rada ya ce,
"watakila Boddo ko kwakkwarar sumba wannan (kissing) bai iya ba sai shegen tsayi kamar falwaya da bakar kalar sa dana fahimci sune abubuwan sa da ke rudar ki!".
Hannaye na biyu na saka na toshe kunnuwa na na fita daga madafin ina mamakin sa. A baya in wani yace min Ya Umar zai iya irin wannan maganar ba zan taba yarda ba. Sabida kallon wani kasurgumin shaihin malami nake masa.
A raina nayi murmushin tausayin sa, sabida ya gama amanna da ya same ni ya gama. Shi yasa bazai damu da abinda nake gudun auren sa a kan shi ba, tunda ya san ko ba dade ko bajima zai zama nasa ne.
"Ya Omar da muguwar rawa gwanda kin tashi. Zamu ga wa za'a kai gidan ka balle har ayi batun hada shimfida ko akasin ta. Bana yin magana don yaudarar kowa amma tunda an zo wannan gejin zan yanke hukuncin da zuciyata ta fi amincewa da shi.
Lokaci ya kure min da zan nemo ka Dream Husband, kamar komai ya kurace min muddin na bari aka daura min auren nan, suna maganar daurin aure nan da kwanaki uku. Omar ba zai taba saki na ba muddin igiyoyi na suka shiga hannun sa. Damuwa ta daya ce a ina zan nemo ka?"
Anti ta gama shiryawa tsaf, shirin tafiya Mambila a washegari, inda za'a fara gudanar da bikin mu yadda Al'adar garin Gembu ta tsara.
Na tabbatar muddin na saka kafa a Gembu, dakin Ummati aka shafa min lalle; aure na da Ya Omar ya gama tabbata, mai iya raba Omar Gidado Gembu da igiyar aure na kuwa sai dai mutuwa balle in yi fatan zan shiga ne in fito a sanda nake so, ko in Dream Husband ya bayyana kan sa, in bar Omar in koma masa, a halin yanzu kuwa bana bukatar auren kowa na fi so in bar duniyar bakidaya in huta da azabar soyayyar dana ke dandana, tunda bani da nasara a kan ta, da zai bayyana da ya bayyana haka kafin lokaci ya kure mana.
Da in ganni a gidan Ya Omar matsayin matar auren sa gara in bi bayan mahaifiya ta, ko na samu cikar buri na a aljannah, ko mayi aure da wanda nake so a wata duniyar ba wannann tamun wadda muke ciki ba, tunda ya ki bayyana a duniya har gashi za'a yimin auren dole a dalilin (SAKACI) NEGLIGENCE irin nasa......


"FIYA-FIYA TANA TSINKA HANJI IDAN TA SHIGA JIKIN DAN ADAM. DON HAKA UMMATI KADA KI KARA AJIYE FIYA FIYA A DAKI SABIDA YARAN MAKWABTA DA NAKI JIKOKIN KANANA DAKE SHIGOWA SUNA DABDALA A TSAKAR DAKIN KI".


Na tuno wata magana data taba gudana tsakanin Anti da Ummati a zuwan da muka yi mata yawon Arba'in din Nadiya, Maryam Jamila ta dauko wata kwalba akan talbijin tana tambayar Ummati ko turaren Dan Duala ne a ciki? Ummatin ta ce "a'ah fiya - fiya ce maganin sauro guba ce, maza ajiye ki je ki wanke hannun ki".


Abbana ya ce wai ko gawata ce a kai gidan Umar, kafin a wuce da ita makabarta, to watakila ya fada da bakin mala'iku ne. Domin furucin iyaye karbabbe ne shi yasa ake so a kowanne lokaci su dinga tauna kalaman su a kan 'ya'yan su. Na zabi in sha fiya-fiya a kan dai na je zaman aure gidan wanda bana yiwa so na soyayya.....!!!


(A wasu lokutan idan baka barwa Allah lamarin ka ba, idan ka zabi ya barka da dabarar ka sai ya barka din. Babban kuskure na ni Siyama, tunda na fara mafarkan nan da shi ban taba neman zabin Allah a kai ba, ban taba cewa idan soyayyar da nake yiwa wannan bawan Allah daidai ce da addini na, tarbiyya ta da lahira ta, kuma alkhairi ce a gare ni da addinin Allah, Allah ya sada ni da shi cikin hikima, buwaya, mulki da iyawar sa da tsarkin mulkin sa.


Ni na san tun farko da ace wannan addu'ar na dukufa ina yi tsahon shekarun nan dana fara mafarkan sa, na tabbata da tuni na rabauta cikin zabin Allah. Amma a yanzu lamari na yana hannu na ne kacokam! Kuma shedan ya yi min kyakkyawar jagora yana gaya min rayuwa ba tare da shi da na kallafawa rai ba aikin banza ce, don ba zan taba jin dadin ta ba.


Na daga kwalbar fiya-fiya na rufe ido sannan na yi kalmar shahada, ban sani ba ko Allah zai karbi shahadar nan tawa? Tunda ni nayi nufin yin ta da hannu na bata Allah da Annabi bace?? Ko kuma shan fiya fiya don gujewa auren dole daidai yake da kashe kai??? Gara in taimakawa Abba ya cika burin sa ya kai gawa ta dakin Ya Umar, sannan a zarce da ita makabarta.


Shi kuwa Dream Husband dina bazan taba yafe masa ba, duk ranar da ya gama yangar sa ya ga damar bayyana kan sa gare ni, ya samu labarin na gaji da jiran sa na kashe kaina a kan sa he will then take it for granted.... I would love to see his reaction a lokacin da ya samu wannan labarin. Reaction din sa na samun labarin mutuwa ta a dalilin sa, shi zai nuna girman matsayi na a zuciyar sa..... shi zai bayyanawa mai karanta labari na cewa shima yana so na ko ni kadai nake koshin wahala a kan sa? Duk da 90% na zuciya ta na tabbatar min our hearts are jointly connected internally by the creator..... Ba ni kadai nake wannan suffering din ba.


Na hango kaina Abba na binne ni yana kuka yana cewa da na sani na taimaka miki kin nemo shi Boddo, ba wanda ba zan iya nemowa a duniya ba idan na saka kaina, da na sani ban yi gaggawa ba wajen yanke hukuncin yi miki auren dole, da na sani ban ki bin shawarar likita ba da ya ce a tsahirta, da na sani Omar ya zabo duk macen da yake so da kan sa, in ya so na aura masa ko wacece koda zan rasa banten daurawa....Da na sani din da Abba zai yi a kan hukuncin da yayi wa rayuwata tana da yawa.....
Amma me? Wani bangare mafi rinjaye na zuciya ta ya ki amincewa da hakan, cewa yake dani cikin amsa-kuwwa....
"Abba ba zai taba yin dana sani ba, don hukuncin sa bai sabawa Allah ba, ke ce zaki yi da kin sani, kece zaki dawwama cikin sa, kuma ki tabbata cikinsa daga nan har karshen rayuwar ki muddin kika aikata abinda zuciyar ki ke umartar ki a yanzu".
Amma hakan bai sa ko kadan na fasa abinda nayi niyya ba, a ganina hanyar tsira daga auren dolen da Abbana zai min kawai kenan wanda zai zamo shinge/katanga ga tabbatuwar mafarkaina da wanda nake so. Da in rasa wadannan mafarkan nawa gara na rasa rayuwar dungurungum bakidayan ta. Love is real, kuma nawa baya karbar uzurin kowa face na samun wannan soyayyar gaibun dana ke so.
Na soma tittila ruwan fiya-fiya a baki na ina hango DREAM HUSBAND dina, yau kam tar-tar nake ganin sa cikin idanu na ba kamar kullum da a fizge kawai nake iya ganin sa ba; those beautiful eyelashes sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login