Showing 42001 words to 45000 words out of 45425 words
Chapter 15 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt
ya tafi ya dan rankwafa kadan a saman bakin sa sabida tsayin sa).
Mutumin nan ne mai tarin gargasa a fuska da saman giran idon sa, mai murya irin ta Asians mai sassarfar magana, maimakon Hausar dana san shi da ita yau turanci yake yi zallah.
Bashi da kauri kuma babu annuri a fuskar, a lokacin da yake gabatar da shirin "....... OVERCOMING OBSTACLES...., LIVING WITH CELEBRAL PALSY.... !". Tamkar yana taya client din sa Toobin alhini da juyayin halin lalurar rashin lafiya na har abada da yake ciki.
Yana sanye da farin siririn gilashi na kara karfin gani. Wanda na tabbata yawan duban camera ne ya yi mujazar lalaurar idanun nan.
Sanye a jikin sa 'Black - Grey Japanese Suit' ne, ya matse wuyan sa daga ciki da tsukakken neck-tie fari sol.
Exactly yadda nake ganin sa cikin MAFARKI na, exactly yadda nake ganin sa a IDO BIYU na, wato inimaginations... haka exactly yadda nake picturing din kasancewar sa! Sannan muryar bata canza daga yadda na santa na kuma haddace ta ba.
Wannan shine HAMZAH ALMUSTAPHA ........ da na dade ina baku labari, wanda na rayu shekaru rututu cikin mafarkan sa, wanda na taba tsinkayar muryar sa a kunnuwa na daga gidan rediyon VOA watanni masu yawa a baya.
Yau dai ga Hamzah na gani cikin idanu na, Hamzah a kan screen din talbijin din daki na, a kan allon talbijin dina.... In reality ba'a mafarki ba, ba kuma a sautin murya ba. Yau na ganshi ne ganin idanu na. Ina kallon sa ina kuma jin sa.
Kwarai sunan da ya ambaci kan sa da shi a wancan lokacin ma da na kasa tunawa kenan “HAMZAH ALMUSTAPHA MAWONMASE....!!!” Amma a wancan lokacin kidima da ikon Allah basu bani ikon rikewa ko tunawa ba!!!
Wani abu tamkar zubar kankara ya bi ilahirin jikina ya sankarar da ni a inda nake kwance. Zuciya ta tamkar ta fito ta baki na. Yawun baki na ya kafe rayas. Nayi kokarin hadiyar miyau don jika makoshi na da ya bushe kamas, amma na gagara yin hakan saboda kidima. Sakamakon haka na jin numfashi na na shirin barin gangar jiki na. Ko wanene wannan shine 'dream man' dina, da ya hana rayuwata sukuni, ya rabo ni da gidan mu da iyaye na, ya raba ni da Ya Umar, ya jefa rayuwata cikin kaka-nikayi, shine mutumin da ke zuwa min kullum cikin MAFARKI KO A IDO BIYU! Shine wanda Ubangiji ke nufin al'amura da dama a tsakani na da shi tun ban san kai na ba, wadanda ban san farkon su balle karshen su ba.
Iya abinda na iya tunawa kenan sai na shide cikin emotion, kowacce gaba ta sassan jikina na maimaita kiran sunan "Hamzah Mawonmase!" Don kada in kara mantawa ko ya kara bace min in sake shiga halin ha'u'la'i.
To amma sanin da na yiwa Hamzah a yau bashi da wani amfani tunda dai ba zan dauki kafa a matsayi na na diya mace bafullatana mai daraja in tafi ofishin VOA neman sa ba, in ganshi in ce masa me? Ai sai kima da daraja ta na diya mace su fadi. In nayi haka na siyar da mata, na siyar da fulanin Mambilah wadanda ko a cikin fulani daban suke.
A hakan dai zan cigaba da kwankwadar azabar soyayyata ni kadai, har zuwa ranar da numfashi na zai kare da sunan Hamzah Almustapha a cikin sa.
Ko babu komai yanzu zuciyata ta samu sa'idah, na cewa Hamzah mutum ne bil adama, yana rayuwa ne a gidan radiyo da talbijin na VOA. Kuma muna cikin kasa daya. Kuma Allah ya nufa na gan shi in a silent way. Zuciya ta ta yarda shine mutumin mafarki na dana rayu da shi tsayin shekaru kusan goma a zuciya da kwakwalwata.
Koda wannan kadai na tsira ya ishe ni kwanciyar hankali har karshen rayuwa ta; HAMZAH ALMUSTAPHA is a human, living in America.
*******
EMOTIONS
S
ai ya kasance tun daga ranar dana gan shi a talbijin nake bibiyar sa, nake bibiyar komai nasa da wani irin emotion, yawanci na kan ga hotunan sa tare da sauran VOA TEAM na talbijin ko na radio, na kuma fahimci ba'a bangare daya yake broadcasting ba, yana yi a sashen hausa, yana kuma yi a sashen vedio na turanci.
Wata irin walwala ta same ni a kwanakin nan, ba abinda ke bani nishadi irin kasancewar Hamzah mutum ne a raye ba aljani ba ba jinnul Aashiq ba, na koma bani da abin yi muhimmi irin na dinga bibiyar shirye-shiryen sa. Kullum da sabon shirin da zai kawo mai matukar muhimmanci da kayatarwa.
Daga yadda yake gabatar da muhimman shirye-shirye a gidan radiyon da talbijin na VOA zaka fahimci dan gaban goshin su ne. Kusan duk wani shiri mai muhimmanci shi yake gabatar da shi. Watakila wannan ba zai rasa nasaba da zazzakar muryar da Allah yayi masa baiwar ta ba, mai wata irin sassarfar magana wadda ke karawa shirin sa armashi da jan attention din al'ummah, murya ce mai taushi da sanyawa dan adam nutsuwaka saurare shi koda baka ra'ayi, sassarfar ta kuma bata hana a gane me yake cewa cikin dadin rai. Sai take kara mata wani irin armashi.
Hamzah na tafiya da zukata da dama ba tawa nikadai ba, na gane hakan ne ta hanyar comments da yake samu na miliyoyin mutane a shafin sa na Twitter da na Instagram a duk lokacin da VOA suka saki shirin sa.
Babu cikakken bayani a kan sa a google amma akwai cikakken bayani na aiki da profession din sa a shafin sa na LinkedIN.
Matakin Digiri dai-dai har guda uku reras yake rike dasu akan aikin Jarida daga Jami'ar 'Sussex'. He's a Chevening Scholar wato wanda yayi karatun sa na Masters daga tallafin 'Chevening', yayi Ph.D daga tallafin 'Commowealth Scholarship', cikakken dan Nigeria daga jihar Filato (Jos).
Ya yi aiki na lokaci mai tsaho da British Broadcasting Corporation, yayi da Radiyon Jamani (Deustche Welle) kafin ya bari duka ya dawo uwar su VOA.
Wadannan sune muhiman bayanan dana samu a kan Hamzahn da zuciyata ta ki hutawa a kan sa, daga shafin sa na professionalism wato LinkedIn. Suka zame min ababen taya hira, ababen debe kewa, ababen saka nishadi, hotunan sa kuma suka cika wayata fam. Wadanda nake sauke su daga shafukan sa na yanar gizo. Murmushin sa kadai mai kokarin narka zuciya ta ne, wanda ke tafiyar da numfashi na na wucin gadi.
Na yarda ba abinda ya kai soyayya dadi a zuciya da ruhi. To ina ga inda take samun martani daga wannan masoyin?Gare ni dai, ni kadai nake ninkaya a koramar da zakin ta yafi na zuma, gardin ta yafi na madara.
Koda Aunty Wasila ta aikowa da Young Abba sakamako na na WAEC da NECO babu wani abin a zo a gani a cikin su ban damu ba, a yanzu kam ko diyar Qaruna bana jin ta rufa bayana a kwanciyar hankali da samun contentment na rayuwa. I'm feeling myself on top of the world of happiness and excitedness. Tunda kullum idanuwa na na kallon abinda suke so, kunnuwa na na jin sautin mutumin da suka fi son ji a duniya bakidaya, wani abu wai shi karatu na rantse baya gabana idan ba yadda zan mallaki Hamzah ba.
Uwar dakina Nasara Alkali, ta dade tana lura da sabuwar rayuwar dana fada, kamar bana cikin tamu duniyar, kamar a wata duniyar nake rayuwa nikadai, na zama addicted ga wayata ko bandaki zan shiga da wayar nake shiga, idan kuwa akan masai nake zaka sameta like ga kunnuwana ina sauraron Hamzah - Mawonmase.
Duk abinda nake ciki ashe aunty Nasara na lura dani. Yau da Young Abba ya fita aiki sai ta shigo daki na cikin shiri, a daidai lokacin da Hamzah ya kammala shirin sa na safe wanda yayi akan janyewar yajin aikin jami'o'i na kasar Najeriya.
“Mrs VOA, ko zan samu ki rakiyar ki zuwa Walmart Supermarket?"
Nasara ta tambayeni tana kada mukullan motar hannun ta, tayi shigar ta islamically kamar kullum ta hanyar yin rolling da bakin mayafi akan doguwar riga samfurin kasar Oman ruwan kwaiduwar kwai data ke sanye da ita.
Tunda Hamzah ya gama shirin dana ke saurare, ba matsala zan iya raka ta. Don haka nace Aunty bani mintuna biyu in dan watsa ruwa, nima ina son fita in motsa jiki na, yau kwana goma kenan ban je koina ba".
"Sai sauraren Hamzah Mawonmase!".
Anty ta fada cikin kirjin ta har sautin maganar ta ya dan fito. Na juyo daga kofar toilet bayan na zari towel daga ma'ajiyar sa, nace "na'am Aunty magana kike yi ne?"
Ta girgiza kai tace "Oh! Ban ce komai ba fa. Yi maza ina jiran ki a mota".
A gurguje nayi wankan na fito wani wajen ma kumfa bata fita ba, a haka na saka jacket wadda ta kai min har kasan guiwa da wandon Jeans baki. Na saka hijab wanda iyakacin sa kafaduna, na dauki wayata da 'yar karamar jakata 'Chanel' na bi bayan Anti zuwa mota.
*****
"NASARA ALKALI"
(MY SECOND LIFESTYLE INFLUENCER)
M
una kan hanyar mu ta zuwa ‘Walmart Supermarket' dake kan titin Riggs Road, South Dakota, inda a can Anti Nasara ke yin duk wani provision din kayan abincin mu dana amfanin ta. Anti ta dube ni da wutsiyar idon ta. Kafin ta maida hankalin ta kacokam kan tukin data ke yi cikin gwaninta. Sannan ta kira sunana cikin siga mai nuna muhimmiyar magana take son yi da ni.
"Sai yanzu na gane dalilin da yasa Abban ki ya zabi yayi fushi da ke har ya kore ki Siyama. Nima kuma ina gab da yi; fushi da kora".
Na zaro ido ina kallon Anti cikin tsoro da razanar maganar ta. Me nake shirin ji haka ni Siyama!
Aunty Nasara bata damu da reaction dina ba kan maganar ta, ta cigaba da cewa.
"As long as mace zata bari wani namiji da ba mijin ta na aure ba ya shiga zuciyar ta, ya shiga cikin rayuwar ta yayi kane-kane irin haka ya hana ta cigaba, ya hanata wani tunani bayan nasa, ya shiga tsakanin ta da iyayen ta, ya yi galaba a kan karatun ta, ya dauki ragamar zuciyar ta daga kan turba sahihiya, wannan mace macen sunan ta sorry domin mara hankali ce, kuma wadda bazata iya fighting da emotions din ta ba.
Maimakon hakan, it's the emotions that drives her, not her own humble self, su suke jan ragamar ta tare da wannan namijin. Musamman wanda bata cikin rayuwar sa, ba kuma son ta ya ce yake yi ba".
Anti ta dakata ta yi kwana ta dauki titin Walmart Supermarket, ta bar kalamanta na ragargaza ni, sannan ba tare da ta damu dani ba ko halin da ta jefa ni ta cigaba da cewa,
"Siyama kin dauki hanya ta ruguza rayuwar ki, kin bar emotions suna driving din ki. Kin bar ALLAH Siyama tunda kin bar koyarwar AL'QUR'ANI, bayan cewa sune kadai abinda idan ka rike komi na rayuwa zai zo maka da sauki".
Jiki na bakidaya ya saki, gwuiwoyi na sun yi sanyi kalau. Buri na kawai Aunty Nasara ta dauki hanya dodar kai tsaye ta gayamin me nake yi har haka da har take tunanin na bar ALLAH na dau hanyar rusa rayuwa ta.
"Amsa ga tambayar da kike yiwa zuciyar ki a yanzu Siyama, yaushe rabon ki da karanta littafin Allah, yaushe rabon ki da yin sallahr dare don gayawa Allah bukatun ki da rokon sa a kan ya sassauta zuciyar mahaifin ki?
Siyama kin fadi WAEC kin fadi NECO amma ba abinda ya dame ki sabida kin saka soyayya a zuciyar ki, soyayyar da bata da madafa don kuwa Hamzah Almustapha na gidan Rediyon VOA; BA MUSULMI BANE CHRISTIAN NE (Ahlil Kitabi) dake bin Addinin CHRISTIANITY."
Don haka in zaki shiga hankalin ki ki shiga, in zaki dawo hayyacin ki ki dawo. Ki kama Allah ki kama iyayen ki. Ki maida hankali wajen gyara kuskuren da kika yiwa mahaifin ki, ya fiye miki alfanu duniya da lahira akan bibiyar shirye-shiryen Hamzah dare da rana, ya fiye miki alkhairi ga cigaban rayuwar ki, ya fiye miki maslaha da Ubangijin ki.
Yara mata irin ki sun fi goma dana samu labarin sun yi RIDDAH a kan soyayyar wannan mushrikin a Najeriya.
Don baiwar iya magana da ta halitta Allah yayi masa karshe, amma arne ne Siyama, ba addinin ku daya ba, ko kusa bai cancanci soyayyar ki ba. Siyama Gembu, 'yar musulmai ce rainon musulunci.
Umar Faruq shine mijin da ya dace da rayuwar ki kamar yadda Abban ki ya hango miki, abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutsen dala da gwauron dutse ba zai hango ba. Shiyasa aka ce ta yaro kyau take amma bata taba yin karko.
Don haka Siyama a matsayi na na UWA ba MARIKIYA ba nake baki shawarar ki kama abinda zai amfane ki ki manta da Hamzah, ki manta da Mawonmase, har yanzu ke yarinya ce da take kan gabar gina rayuwar ta. Baki kai ga cimma komi a rayuwar ki ba. You are still a Teen.
Na sama miki islamiyyah school a New York na gama komai zan kai ki gobe, a tsayin watanni shidda kacal ake haddar Al'qurani, ta wasu musulman Canada ce Dr. Ismail Memon da dan sa Dr. Shaykh Ibrahim Memon Madani, su suka bude ta a birnin Buffalo, New York.
Kafin watanni shidda nake son ganin Hafizah Siyama a gabana, in ga sabuwar Siyama mai Qira'ar Madani, wadda iyayen ta zasu yi alfahari da samun ta, kasancewar ta mahaddaciyar Al'qur'ani.
Idan kin kammala wannan makarantar zan maida ke aji shidda na sakandire da sunan transfer daga Regent, ki sake zana jarrabawar kammmala sakandire sannan ki fara karatun Jami'a.
Wannan shine tsarin da na yi miki nake kuma fatan ki bani hadin kai a kan sa, ko in mayar da ke Mambillah!!!".
******
MURFIN LITTAFI NA DAYA
Ban iya tsayawa kallon yanayin da Siyamar mu ta fada ba na ajiye Biron, ba don komai ba sai don nafi Siyama kidimewa. Abinda ban sani ba; Shin SIYAMA zata bi tsarin uwardakin ta Nasara don a zauna lafiya da ita? Ko kuwa a'ah itama zata bi sahun masu yin RIDDAH ne kamar sauran matan da aka yi ittifakin sun yi RIDDAH a kan sa??? Tunda dai mun ga har fiya-fiya ta sha don ta tsira da shi da fantasie din ta a kan sa???
Sanin hakikanin wannan amsar sai ita kadai ‘yar mutanen Mambillah; Aisha-Siyama Mamman Gembu. Don haka mu biyo Boddon mu-Siyamar mu a littafi na biyu don jin yadda zata wakana tsakanin ta da ‘Dream Man' din ta.
Shin da gaske Hamzah kafirin ne ko kuwa shaci-fadi ne irin na Nasara don ta samu hanyar raba Siyama da emotions din ta???
SAKACIN WAYE? 2 TARE SUKE DA LITTAFI NA DAYA. TAKU HAR ABADA SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI).
In kinji tashin hankali, razani da kidimewar da suka sameni a wannan dan tsakanin da nasara ta dauka tana magana to guda daya kenan. Na shiga abinda ake kira bewilderment8 na zuciya da ƙwaƙwalwa.
Na shiga coma ba dan na kwanta a kwance ba, sai don kasancewar ilahirin gaban jikina sun daina aiki na kame a kujerar da nake zaune.wani bangare na zuciya kuma yana Mai gasgata kowacce kalma da kowanne harafi dake fita daga bakin anti na. Na yarda iyakar gaskiyar da kowacce uwa zata fadamin kenan, iyakar mataki da kowacce uwa ta gari zata dauka kenan don tseratar da 'yarta daga fadawa halaka, shi nasara ta dauka take Kuma aiwatarwa a halin ynz.
Ban tashi tare da mahaifiyarta ba amma
Sai Allah ya hada Ni da wasu irin matan uba na gari wadanda irin su sun yi ƙaranci a wannan zamanin da muke ciki, wadanda