Showing 33001 words to 36000 words out of 45425 words

Chapter 12 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt

kwanta sosai a saman lumsassun idanun sa, that cool man's pride da ke dimauta ni, wanda ya tafi ya zagaye habar sa ya kwanta lambam a kan kyakkyawar bakar fuskar sa sai sheki da salki gami da walkiya yake yi. Hakika Ubangijin halitta ya kyautata surar sa a cikin bakaken mutanen Africa, ya qawata min shi a zuciya da ruhi fiye da duk wani da namiji mai numfashi a duniya.
Gani nake kamar ya bude min hannuwa yana min murmushin da ya lotsa gefen kumatunsa guda daya yana jiran isowa ta. Na amince Allah ne ya hada mu ba don komai ba sai don mu rayu tare, rayuwa ta har abada amma a wata duniyar daban, ba wannan tamun wadda muke ciki ba!!!
********














MAI RABON GANIN BADI.......
A
cewar Hausawa ko ana ga uzuru ana ga Shaho sai ya gani. Allah ne ya kawo Wasila a daidai wannan lokacin, wanda yayi dai-dai da zuke kwalbar fiya-fiya da nayi, idan Allah ya ce kwanan dan adam bai kare ba to babu abinda zai kashe shi sai kudura da iradar Ubangiji.
Na yarda da hakan a yau a kaina domin tabbas na san na sha kwalbar fiya-fiya, daga nan sai shigowar Wasila da ihunta da na ji a kaina, bayan wannan ban kara tantance meke faruwa da ni a duniya ba.
Na bude ido ne na ganni akan gadon asibitin Nizamiye, inda anan file din duka 'yan gidan mu yake, sauran abinda ya biyo baya mai ban tausayi ne domin kuwa Abba ba ta jinya ta da Wasila ke yi ya ke ba shi, bata tabbacin da likita ya bashi na nasha guba an samo ni da kyar da taimakon Ubangiji yake ba a'ah, ta shirin daurin aure na yake yi ko in mutu ko in yi rai.
Koda na farfado na yi ido hudu da Abba ban iya kara yi masa kallo na biyu ba, sabida yadda fuskar sa ta koma ta tsantsar bacin rai ban taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan halin ba. A gefe Wasila na share hawaye, Umar na gefenta ya kura min ido harde da hannayen sa a kirji, gabadaya yayi wani zuru-zuru kamar wanda ya mutu ya dawo. Ina jin bai taba gamuwa da tashin hankali da bacin rai a rayuwarvsa irin na wannnan lokacin ba.
Da Abba ya tabbatar na dawo cikin hayyaci na sai ya ja kujerar zaman 'yan dubiya gaba na ya zauna. Ya kura min ido yace "Siyama! Anya Siyamar dana sani na kuma haifa tareda Asshe ce wannan ko kuma dai Nos din data karbi haifuwar ki ta musanya min tawa Siyamar da wani jinin daban? Ina mamaki!
Domin dai nawa sanin. Jinin malam Dalhatu Abdullahi Gembu ba zai taba aikata kisan kai ga kowa ba balle ga karan kan sa a bisa sani kuma, ba zai so ya zo duniya a banza ya koma a hofi ba. Haka ba zai so ya mutu kafiri ba. Akan wata kankanuwar bukata tasa ta duniya.
A matsayi na na uba bazan ce ban so kika kubuta ba, amma na so ki cika burin ki kije lahira ki dandana azabar wuta kona wuni daya ne sannan ki dawo, watakila zaki fi sanin cewa iyaye ba abin wasa bane. Kuma duk wanda ya zabi son zuciya yayi SAKACI dasu yana tareda dawwamammiyar nadama.
A karshe ina sanar dake cewa har yanzu ina nan akan baka na na cewa Omar na zaba miki, kuma jibin dana saka don daura muku aure ba zan fasa ba. Wannan karon sai ki sa wuka ki farke cikin ki don kifi mutuwa da sauri, a mika gawar ki gidan Omar kafin a wuce da ita makwanci.....".
Abba ya fada cikin wani mashahurin bacin rai da ban taba gani a tare da shi ba. Daga bayan sa Ya Omar yayi gyaran murya cikin karaya ya soma rokon Abba "Abba don Allah.... na roke ka ka janye kudirin ka, ka bar Siyama ta nemo wanda take so ka aura mata.
Abba rayuwar Siyama cikin farin ciki ta fiye min auren ta. Abba tunda har Siyama zata iya iya yunkurin kashe kanta a kaina Abba na hakura da Siyama na haramtawa kaina ita. Ina rokon ka kaima kayi hakurin musulunci kada ka yi fushi da ita, ka bata dama ta auri zabinta, don Allah Abba".
Omar ya fada cikin despair da kuma karaya da al'amarina bakidaya.
Anti tace Abba tunda har Umar ya hakura kaima kayi hakuri. Rayuwar Siyama gaba take da komai don Allah Abban Siyama..." Anti ta fada cikin hawaye, don hakika ta shiga tashin hankali irin wanda bata taba shiga a rayuwar ta ba, da tazo ta same ni ina shan fiya-fiya kuma babu jimawa na bi kwalbar muka zube a kasa, kumfa na fita daga baki na.
Allah ne ya so Omar na falo a lokacin, da gudu ta fita tace "Siyama ta kashe kanta Omar, ta sha poison, ban san a ina ta samu ba".
Irin zaburar da Omar yayi kamar ta fitar kibiya ya kuma daukoni a kafadar sa yasa a mota Anti ta shiga gaba basu zame ko’ina ba sai Nizamiye. An karbe ni a emergency likitoci suka rufu akaina don ceto raina. A lokacin ne Anti ta samu sukunin iya kiran Abba wanda bata san ina yayi ba a ranar.
Hakika akwai kwararru ba na wasa ba a Nizamiye, watakila kwarewar su ce ko kuma ince Astagfirullah Allah bai yi kwanaki na sun kare ba kawai shi ya cece ni. Amma an kashe kudi ba na wasa ba. Sannan daga farfadowa ta Abba ya bi ni da wadannan muggan maganganun. Wanda suka nuna ko kadan suicidal attack dina bai sauko da shi daga kan dokin kudirin sa ba.
Anti da Ya Omar suka dukufa roko, rokon Abba suke akan ya janye ya kyale ni in yaso duniya ta koya min hankali don wanda nake so din ma fa babu shi babu dalilin sa cikin duniya, imagination ne kawai nake yi.
"Ai kuwa zata mutu cikin hasashe" inji Abba. Sannan ya juya ga Omar da ke durkushe a gaban sa, ya ce "Omar ba ka son Boddo?"
A firgice Omar ya daga kai ya dubi Abba, Abba ya ce "amsa nake so eh ko a'ah ba wani dogon turanci ba". Omar ya rasa inda zai kansa, ya ce "it does not matter Abba son da nake yi wa Boddo tun tana zanin goyo, tunda ita bata so na na yafe soyayyar dana ke mata, na sadaukar da tawa soyayyar don farin cikin ta da kasancewar ta cikin kwanciyar hankali".
Abba yace "magana ta kare Omar bana son jin karin komai. Ka tashi mu tafi, gobe zamu wuce Mambila ko sun sallameta ko basu sallameta ba a daura muku aure".
Omar zai sake magiya Abba ya daka masa tsawar data gigita shi. Ya kuma sa kai ya fice a dakin asibitin. Dole Umar ya bi bayan sa don mukullin motar Abban na hannun sa. Yana fita yana waiwaye na. Gani yake kamar bazai dawo ya tadda ni a raye ba. A lokacin na lumshe idanuna bansan ya akayi ya akayi ba, kawai naji kwallar tausayin Umar sun wanke min fuska.
Ni da Anty muka kwana duk wani motsi da zan yi a kan idanun ta nake yin sa, don tsoron ta na ko zan sake wani attempt din na salwantar da rayuwa ta. Akwai maganganu fal a bakin Anti amma ta adana su zuwa in samu lafiya. Bakin cikin abinda na aikata ya hana duk wani masoyi na sukuni a zuciyar sa kuma babu wanda na baiwa tausayi banda Ya Umar. Ita Anti da zata samu dama so take ta dan yi min shegen duka ko zata huce tashin hankalin dana jefa ta.
Kwance kawai nake da ledar karin ruwa a jikin hannu na nida ita mun zama tamkar kurame ba mai ce da dan uwan sa uffan. Sai likitoci da ke ta shige da fice a kaina don tabbatar da aikin su na tafiya daidai.
A daren Umar Faruq ya kasa barci, ya tabbata in har ya wayi gari jibi a gidan mu Abba ba zai fasa abinda zai zo yana nadama ba, idan a da yana ganin abin na Boddo wasa ne yanzu ya tabbata Boddo da gaske bata son sa, koda za'a dora mata wuka a makoshi bazata zauna da shi ba, tunda har Boddo zata iya kashe kanta a kansa shi kuwa meye ribar sa a cikin auren ta???
Wane farin ciki ko alheri zai tsinta a cikin auren matar da ke kin sa har haka? Matar data zabi shan guba fiye da hada shimfida da shi. Tausayin Abban mu kadai ya ishe shi amma ya yanke hukuncin da yake ganin yafi masa alkhairi. Ya kuma fi zama maslaha ga Abba sannan ya fi zama kyautatawa a gare ni.
Washegari tunda safe likita ya sallame ni, Anty ta dauko ni muka taho gida jikina duka babu karfi. A falo muka cimma Abba yana saukowa daga matattakalar bene cikin shirin sa tsaf, da gani yayi shirin wucewa Mambila ne daurin aure na a gobe, don sun yi waya da Anti kafin mu taho ta gaya masa an sallame mu yace to yana jiran mu zamu wuce Gembu yanzu.
Don haka muna shigowa Anti ta wuce dakin ta don dauko kayanta, nima na wuce nawa dakin kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ina hawaye, ganin irin kallon tsanar da Abba ya jefa min yau.
Anti ta fito jaye da akwatin ta ta nufo daki na don ta hada min nawa kayan don ta san ba hadawa zan yi ba. Ita ta daukarmin komai ta hada cikin akwati sannan ta kama hannu na muka tadda Abba a falo, yana ta faman gwada layin Ya Omar ya ki shiga don shi zai ja mu a motar.
Bayan tun daren jiya sun gama magana ya kuma gaya masa karfe goma na safe zamu kama hanya ko an sallame ni ko ba'a sallame ni ba, in ya so in karasa mutuwa a hanya. Amma gashi yanzu ana gaya masa layin Omar a rufe yake bakidaya.
"Ban san ina Omar ya yi ba, ki duba min dakin sa ko bayan gida ya shiga" Abba yace da Anti. Anti Wasila tabi bayan Omar amma haka ta dawowa Abba tace bata gan shi ba, kuma bata ji motsi sa a bayan gida ba.
Abba da kan sa ya tafi BQ neman Umar Anti ta rufa masa baya. Babu inda basu duba ba a dakin ba Umar babu mai kama da shi. Sai a lokacin ne ma suka lura babu kayan sa na sanyawa a dakin sai daidaiku. Akan chest-drawer Anti ta hango wata takarda da rubutun Umar ya dora biro a kai alamar bai jima da ajiye ta ba. Kawai sai ta dauka, ganin sunan Abba a jiki baro-baro yasa ta mika masa cikin kidimewa.


-ABBAN MU
Samun mutum irin wanda zumunci ne silar shigar su aljannah tamkar namu Abban na tabbata zai yi wuya a wannan zamanin da muke ciki. Hakika baka nufin komai a kan mu ni da Boddo sai zumuncin da kake so ya dore a zuri'ar Ummati har 'ya'ya da jikoki.
Amma Abba ba kowanne mafarki da buri ne da muke da shi yake iya zama reality ba. Wasu mafarkan a mafarkai suke tabbata musamman idan Ubangiji ya san cewa ba alkhairi bane a gare mu.
Hakika Abba ka yi duk iya kokarin ka na kulla wannan alkhairin a tare da mu, amma kaddara ta riga fata Boddo ta kamu da son wani na wanda take ganin zai hana ta yimin biyayyar aure, maimakon a nemi lahira da auren sai ya zame mata mujazar fadawa halaka. Na fahimci Boddo anan. Ba zan jagoranci ragamar wargajewar rayuwar ta ba sabida nawa farin cikin.
Ni dan ka Omar ina bayan kanwata Boddo, and i will always stand by her, zan taya ta neman wanda take so cikin duniya kuma bazan aure ta bisa tirsasawa ba.
A karshe ina baka hakuri Abban mu hakuri kan hakuri, na san na bata maka nima, akan hukuncin dana yanke. Bani da zabi ne Abba sai hakan don ka ki ka fahimce mu.
Na bar gida Abba zuwa duk inda kaddara zata kai ni sai idan ka janye maganar aure tsakanina da Boddo ne zan dawo bayan shekaru uku masu zuwa in Allah ya kai mu. Idan har lokacin baka janye ba Abba zan ci gaba da zama a duk inda kaddara zata kai ni. Ni na san tunda inada kai to ni ba maraya bane Abba, amma idan na auri Boddo zan koma maraya idan na rasa soyayyar ta.
Ina baka hakuri Abba, Abba Allah ya huci zuciyar ku. Ka yafewa Boddo ka kuma sa mata albarka ba don ni ba don Allah Abba.
Daga Yayan Boddo Umar Gidado.


Gumi, zufa, iri-iri suka ketowa Abba Dr. Mamman Gembu. Omar ya gudu! A dalilin Boddo bata son sa. Kuma yana ikirarin idan har Abba bai janye ba ko bayan shekara ukun da ya ambata ne ba zai dawo ba.
Jikin Abba yayi mugun sanyi, ya saki takardar a kasa kawai sai ya juyo, da ni muka yi ido biyu idanuna a bubbude domin na fuskanci abinda ke faruwa Ya Omar ya zabi ya bar gidan mu akan dai Abba ya tursasa ni ga auren sa, kafin na ankara Abba ya yo kaina, ya soma duka na ta ko'ina da hannaye da kafafun sa iri dukan na huce bacin rai. Anti ta sa kuka ta rufu a kaina ta ce "gara kayi mana dukan tare.
Yadda Omar ya ke Da a gare ka itama 'yar ka ce mai 'yanci. In shi maraya ne itama marainiya ce. Tana da damar ta auri wanda take so, tsaurin ka ne ya janyo komai, ka san Umar son da yakewa Boddo ba zai bari ya zabi nasa farin cikin akan nata ba.
Abba yace "to kuwa bazata zauna min a gida ba, yadda Omar ya bar gidannan itama sai ta bar shi, bazan haifi dan da ban isa in tankwara ba".
Kuka nake ina baiwa Abba hakuri na kuma ce zan nemo masa Ya Omar, zan kuma aure shi koda bana son sa.....
Wannan kalma ita ta kara tunzura ran Abba, yace "kada Allah yasa ki so shi, ki sani daga yau nima na janye maganar aure a tsakanin ku, kije ki auri duk wanda kikeso Boddo, amma ki tabbata kafin na dawo gidannan kin bar min gida na."
"Kada ka yi wa 'yar ka baki Mamman!"
Anti ta tunasar da Abba cikin yanayi na rauni, Abba ya ce "ban yi mata baki ba ai, amma na janye nawa kudurin, na janye nawa burin don in samu Da na ya dawo gare ni. Ya fiye min ita sau dubu, kuma lallai -lallai yanzunnan ta bar min gida na".
Anti zata kara magana Abba ya rufe idanun sa ruf, ya ce da ita. "Idan kika kara kare Boddo a ido na, ko kika kara nema mata alfarma ko afuwa daga gare ni a bakin auren ki".
Wannan magana ba Anti kadai ta firgita ba har da ni. Ina jin sanda fitsari ya kwace min daga tsayen dana ke. Abba ya nuna min kofa da dan alin sa yace "kama hanya ki bar min gida na".
A yanayin dana ga idanun Abba sai naji tsoron sake furta wata kalma, na tabbata in yi masa abinda ya bukata daga gare ni shine kawai mafita ta a wannan lokacin. In yaso daga baya idan ya huce na dawo na bashi hakuri.
Ni kuka Anti kuka Jamila da Nadiya kuka haka na dau jakar kayan da Anti ta hada min na fito, babu ko sisi a jikina kuma bansan ina na nufa ba.
A bakin gate maigadin mu ya biyo ni ganin ina tafe da jaka ina kuka wiwi, ya ce "uwardaki na kada kije ko'ina bada yardar iyayen ki ba, babu wata albarka a cikin sabawa iyaye kuma babu kwanciyar hankali cikin bijirewa umarnin su".
"Abba shi yace in tafi Baba Dattijo, biyayya na yi masa zan tafi".
"To kada kije da nisa, nemi wani waje mara nisa cikin gidajen yan uwa ki fake zuwa gobe idan zuciyar sa tayi sanyi ki dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login