Showing 45001 words to 45425 words out of 45425 words

Chapter 16 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt


Kullum burin su shine su dora ni akan hanya kuma turba sahihiya idan na karkace, in kasance yarinya ta gari abin koyi, abin alfahari gare su da mahaifina..iyakacin rudani na shige shi a wannan ranar, rudanin daya kusa fiddani a hankalina. Ba musulmi bane a ina ya samo sunan sahabin manzan Allah kuma baffansa sayyidina Hamza (A.S)? Ina ya samo sunan shugaban halitta (Almustapha) a surname din sa???
Duka wannan ma idan an bi salsala ai basu da wani amfani a wuri na, ba kuma zasu amfane Ni da komai ba.Tunda kuwa hamza bai taba sanin da wanzuwata a duniya ba,Hamza bai ce yana son siyama ba, Hamza bai Sanni ba....A takaice Ni kadai nake kida na, nake kuma taka rawa ta iri - iri akan sa, cikin wata duniya ta fantasy and imagination wadda ban taba jin mai irin taba sai ni. Amma kuma ina tababa hadi da waswasi a cikin al'amarina da wannan bawan Allah, tabbas akwai wani BOYAYYEN SIRRI wanda Allah kadai ya san shi, ya kuma ke nufi a kaina dashi hamzan, in ba haka ba ta ina ya kutso ya shigo cikin mafarkaina, na rayu shekara kusan goma ina mafarkinsa, na kuma Ganshi exactly a talabijin yanda nake ganinsa a mafarki da imaginations dina???
"Ya Allah taimakeni kafin na haukace!" Na fada a fili, cikin kama kaina dake neman rabuwa gida biyu saboda sarawar da yake min, ina girgizawa da karfi ina qara girgizawa da karfi ko hakan zai rage nauyin daya yimin. Anty tace mata dayawa sun yi RIDDAH wato sun bar addinin musulunci akan hamza, wanda ke nufin ta san shi farin sani, ta kuma san duk abinda nake ciki Akan sa, domin har zana shi nayi da pencil na kafe a cikin Frame din gefen gado na, sannan cikin wayata da laptop dina duka hotunan Hamza mawonmase ne,wanda nake saukewa daga cikin hotunan sa na shafukan social media, ga kuma kona mata girki da nake tayi akai akai tun daga lokacin da young Abba ya mallaka min waya, sannan a fili nake kunna Muryar tasa sautin na tashi daga Radio na, ko talabijin din gidan dake falo, in kura masa ido kamar tsohuwar mayya data ga Nana ko kuwa kamar mai shirin hadiye shi don so.
A zahiri duk wata uwa indai mai kula ce akan al'amarin 'ya'yanta to tabbas zata yi saurin gano inda na dosa akan HAMZA VOA, ba wai labaran nasu nake kallo ko nake saurare ba, tunda kuwa in bashi yake labarai ba ai bana ko tsayawa in kalla ko in saurara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login