Showing 15001 words to 18000 words out of 45425 words
Chapter 6 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt
a waje. Ya Umar in ya tafi Gwagwalada tun safe sai yamma yake dawowa, motar haya yake hawa don Abba motar shi daya ce tal Anti ma haka, ina ji rannan yana masa alkawarin idan ya fito da (first class) mota sai wadda ya zaba zai saya masa. Amma a yanzu ya fi so ya koyi rayuwar gwagwarmaya irin ta kowanne dalibin public university a Najeriya.
Ta hakan ne zai san muhimmancin wahalar neman ilmi. Ya iya tattalin abinda yake da shi. Sai a ka yi sa'a kusan duka halayen Abba irin na Umar ne, abin nufi anan Abba da Umar-Faruq ko kadan basu dauki rayuwar duniya da zafi ba, suna tafiyar da ita a saukake, a duk yadda ta riske su. Sun yarda jin dadi da daukaka basa zuwar ma mutum ta sauki a lokaci guda sai bayan ya sha gwagwarmaya a rayuwa.
A tsayin watanni uku kacal na zama wata kasaitattar ‘yar hutu, budurwa ‘yar kwalisa mai aji da hankali na kwatance, mai nutsuwa mai kuma kyawun surar da yake samun gyara da attention din uwa, sannan da gani babu tambaya ka ga ‘yar gatan uwar riko da Abban ta.
Rayuwa ta ta canza min baki daya positively, jiki na ma ya samu canji, ya nuna samun hutu da tsabta. Abu daya ne kawai har gobe bai canza a tare da ni ba wato (strong fulfulde accent) din Mambila bai bar baki na ya iya furta kalaman turanci dana hausa sosai ba.
Ni kaina na san ina daga cikin ‘ya’ya masu sa’ar mahaifi a rayuwar su, wadanda basu taba neman wani abu daga mahaifi sun rasa ba. Wadanda maraicin uwa bai taba affecting walwalar su da jin dadin su ba, ko kuma don ban taba sanin ta bane?
Farkon zuwa na sabida yadda Anti ke faman takuramin da aiyuka bana samun lokacin kaina balle har in samu lokacin tuna mijin mafarki na ko yin mafarkin sa. Kusan kullum sai na kira Ummati a wayar Anti mun sha hira, don ni Abba ya ce ba zai mallaka min waya ba sai na gama sakandire amma ya baiwa Faruq bayan dawowar mu nan, kullum na kira Ummati sai na bata labarin duk abinda nake ciki kamar kawata aminiya, rannan Anti bata nan ta bar wayar a hannu na nake ce da Ummati.
“Oh! Ummati ban taba sanin haka tsafta yake da dadi ba, ashe da ba karamin cutar kaina na ke ba da nake zama cikin kazanta, ko'ina na tsami, yanzu fa Ummati da zan wuce ta gaban ki bazaki gane ni ba, gashi ke wayar ki Raka-ni-kashi ce (nokia) balle in yi hoto in turo miki ki ganni, ki ga yadda na koma, in kin ji irin kamshin dana ke yi kamar a kasar da ake sarrafa turare (Paris) din Faransa aka ahaife ni. Kai Allah dai ya yiwa Aunty Wasila albarka, ashe da can ni tantagaryar kazama ce ban sani ba Ummati?
Ummati dai sai dariya take tana jin dadi a ranta. Na cigaba da fada mata.
"Ashe Anti Wasila ba takura min take yi ba so na take yi da alkhairi kamar yadda Ya Umar ke yawan cewa? Ummati don Allah kullum kika yi sallah ki ke yi mata addu’a kin ji? Kice Allah ya bar ta da Abba na, Allah yasa ta haifa min kanne masu yawa”.
Kafin Ummati ta samu zarafin amsa min na ji tafi raf-raf a kaina. Daga kan nan da zan yi sai nayi ido hudu da Anti da Abba a bakin kofar shigowa suna kallo na suna tafa hannayen su, da alama sun gama jin duk abinda na gama fadawa Ummati na. Kunya ta kama ni, nayi saurin rufe fuska da tafuka na. Nace.
"Abba da Anti, Allah ya hana labe".
Dariya suka yi su duka. Abba yace “mu bamu labe ba shigewa zamu yi muka ji ana ambatar mu.
Sai in ce "Aamin to all your beautiful Du’as Siyama. Get ready for school tomorrow. Anti Waseelah zata sauke ki a Regent, kafin ta wuce nata aikin”.
Na rasa murna zan yi yau ko bakin ciki, don dai na san a da can na ki jinin karatu kamar yadda na ki jinin mutuwa ta, amma wallahi yanzu ji nayi ina shawagi tsakanin farin ciki da doki, wadanda duka suka taru suka mamaye ni duka a lokaci guda. Na soma jerowa Anti tambayoyi.
"Amma dai makarantar basa duka ko Anti?"
Cikin rashin damuwa tace “in kin yi laifi me zai hana a duke ki?” Nace “ai ni matsala ta da makaranta Anti guda daya ce kin sani. Assignment/Homework da classwork, idan babu su to komai zai tafi lafiya kalau.
Idan kuma kin yarda kullum na dawo gida zaki dinga yi mini da kan ki shike nan”. Anti ta dubi Abba tana fadin "saidai Abba yayi miki ya fi ni iyawa". Abba ya girgiza kai ya wuce sama yana fadin “Siyama har yanzu da sauran ki, bansan yaushe zaki girma ba”.
Washegari Anti ce ta taimakamin na shirya tsaf cikin sabon uniform dina na daliban Regent, nayi matukar kyau kamar ba ni ba, na kawo mini hijab kalar uniform din na dora a kai, kai bazaka taba cewa nice wadda ta zo daga Mambilan nan firgai-firgai dani watanni ukku da suka wuce ba.
Anti ta kai ni har makaranta ta karasa cike - ciken takardun da ya saura ba'ayi min ba, tukunna ta tafi ta bar ni cikin dalibai 'yan uwa na, wadanda duka 'ya'yan manyan ma'aikatan Abuja ne.
Na lura daliban makarantar kabilu sun fi hausawa yawa, hausawan kuma wadanda sune (minority group) duk ‘yan girman kai ne, don babu wacce ta kula ni, basu san ni nafi son hakan ba, don dukkan su da lafiyayyen turanci suke magana, wanda ko come din su bana ganewa sabida yadda suke furtawa a gwanance, nikuwa ko sentence guda daya kwakkwara mai kyau bazan iya hada miki a wannan lokacin ba. A hakan kuma wai na gama juniorclass a garin Gembu, nan kuwa a aji biyu na sakandire aka barni wato an maida ni baya.
Ana gab da tashi wata yarinya ta zo kaina ta tsaya tana min magana, da muryar ta mai sanyi, in zan girmeta to bazai fi da shekara daya ba.
“Ke ya ba kya note?”
Ta tambaye ni da Hausa, jin ta yi min husa sai naji dadi, na bata amsa da tawa hausar da ba fita take sosai ba,
“shai gobe jan yi?”
“Shaboda me? (Itama ta kwaikwayi baki na). Bata jira amsata ba ta cigaba da cewa "Idan Mr Kehinde yazo karbar Assignment gobe baki yi ba zai baki punishment”, “me ye kuma punishment?” Na tambaye ta, babu girman kai babu raini ta amsa min tace "horo, zai saki shara ko wankin toilet din sa, ba ruwan sa da ko ke 'yar waye a garin nan”.
Ban san sanda nace “ai gara min punishment din da wannan uban rubutun, hannu na ciwo zai yi, baya na ma qagewa zai yi, na dade ban yi rubutu ba gaskiya” na bata dariya sosai ganin yadda nake magana da iyakar gaskiya ta, ta ce, “da alama ke 'yar auta ce” nace “ba wata auta fa, don kuwa Anti na tana da ciki yanzu haka. Kuma ta yi min alkawarin samun kanne duk shekara” na kara bata dariya tace “ya sunan ki don Allah? I like you” “sunana Aishatu Mamman Dalhatu Gembu” “ni kuma suna na “Azima Salim Ko’oje. Mu 'yan Sokoto ne. Kina iya kira na Ko'oje. Aisha can we be friends?” Ta fada tana miko min hannun ta, na mika mata nawa muka yi musabaha irin ta muslunci, ta samu wuri gefe na ta zauna tace.
“Kawata dole ki cire kiwar rubutu da assignment if you really want to stay in Regent (idan da gaske kina so ki cigaba da zama a Regent) bazasu doke ki ba amma zasu sallame ki in kika ce haka zaki zauna ba kya rubutun class notes da yin assignment” cikin damuwa nace “to Azima kiyi min na yau don Allah, nayi miki alkawarin gobe zan fara da kai na, yanzu kam hutawa zan yi”. Tace to shikenan, kawo in miki”.
Nan gefena ta zauna ta kwafar min aikin da aka yi duka tace in naje gida in tabbata na yi assignment din, wanda na darasin English ne akan darasin letterwriting (rubutun wasika)”.
Tun daga ranar muka wani irin kulle ni da Ko’oje, tunda ta fahimci inada rauni take karfafani, idan na nemi sarewa ta ciccibe ni, tare da taimaka min kullum da rubutu har na fara sabawa da rubutun aji da kai na komin yawan sa da yin assignment.
Idan na koma gida kuma Ya Umar shi yake zama malami na, duk abinda aka koya min a aji sai ya zauna ya tusa min shi da koyarwa mai nagarta ta juriya da repetition wato ayi ta maimaita karatu kamar ana koyar da karamin yaro mai lalurar LearningDisability, ba zai gaji ba har sai na gane. Ya bani aikin gwaji na yi a gaban sa. Idan ya ga na yi daidai sai ya tafa min sosai har wani lokacin ya bani kit-kat as a gift, shiyasa abin ya shiga raina farat daya na daina tsanar karatun makaranta sam a dalilin Yaya Faruq da Ko'oje. Ina cikin yaran da ke bukatar (special consideration) a yayin koyarwa don ban samu soundbackground wato tushen ilmin boko mai nagarta ba.
Anan falon kasa muke zama a gefen su Abba kullum bayan salllahr isha'i, gefe daya zaka ga Anti bisa kujera da laptop din ta a cinya tana aikin office din ta. Anti ma'aikaciya ce karkashin Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development, Abba kuma yana sauraron labaran harshen Hausa a rediyon sa, ko ka same shi yana kallon labaran Aljazeera ko na CNN, amma ya fi karkata ga sauraron (VOA-Hausa) ban san meyasa ba, sai in ba su da labari wanda ya dauki hankalin sa ne yake murdo wata tashar daga cikin wadancan. Idan goma ta buga duk zamu tashi muyi sallama da juna kowa ya nufi makwancin sa.
Wannan sabuwar rayuwar mai tsari da tarin abubuwan alfanu da abubuwan yi masu muhimmmanci ita ta kara kai ni FarAway daga mafarkan Dream Husband dina. Anti ta yi mana time - table ta kafe a kitchenkullum akwai abinda zamu dafa, bama taba maimaita abinci a sati sai satin ya zagayo. Aunty na son varities Abba na ganin tana masa almubazzaranci. Dole ta rage don Abba malamin tsimi da tanadi ne har gobe duk da ya bar jami'a.
Sau biyu Ko’oje na zuwa gidan mu, har mun hada kawance tsakanin Maman ta da Anti, nice dai ban taba zuwa gidan su ba don Abba ba zai bar ni ba amma Anti ta san ta sosai yanzu, kuma ta yaba da ita har ma dai ranar da Maman ta ta kawo ta, su a Guzape suke zaune.
Sabida Ko’oje yanzu bana shayin homework ko classwork duk wahalar sa, don sai ta tabbatar na gane na kuma gama nawa kafin ta yi nata, a gida kuma ga babban malami na can na bayan almuru yana jirana wato Professor Omar Faruq Gidado Gembu.
Da ana bada ‘Professorial Chair’ daga matakin karatun dalibai a Jami'a tabbas da na dade da baiwa nawa mallamin; Mallam Omar Faruq Gidado Gembu, sabida koyarwar sa is in style da ko kai kafi kowa daqiqanci dole ka gane karatun da ya ke koya maka, ka kuma rungume shi da hannu bibbiyu sabida saukin koyarwar sa.
******
Y
au Asabar a gidan iyayen Anti muka wuni, dake a unguwar Apo, Hajiyar su Anti mace karimiya mai son mutane, nan na tabbatar wa kaina Anti ba a kasa ta dauka ba, ita din 'yar na gada ce ba ‘yar na koya ba a karrama ‘yan adam kuma 'yar babban gida na tarbiyya da arziki sosai. Yau har Daddyn su Anti na gani, na kuma yi hira da shi inda ya tambaye ni abubuwa game da makaranta, don yana gida a yinin ranar bakidaya.
Yadda kullum nake dada canzawa haka ma Omar ke girma yana dada murjewa, wani abin mamaki kwanannan na dade ban kara mafarkin 'Dream Husband' dina ba, sakamakon yadda na zama busy da karatu da ayyukan gida bani da lokacin kaina sam, balle in samu nutsuwar da zan yi mafarki ya zauna a cikin kai na.
Koda muka samu hutu Abba yace ba zani Mambila ba sabida Tahfiz dana ke zuwa a nan kasan Estate dinmu kullum karfe hudu zuwa shidda, ba’a yi nasu hutun ba. Ya ce mu bari sai ya dauki annual leave (hutunkarshen shekara)Anti ma ta dauki nata in yasodukkan mu sai mu tattara mu tafi Gembun. Ummati dai kullum muna waya ko tuntube na yi a rana sai Ummati dake Mambila ta ji labarin sa. Shiyasa ban damu sosai da rashin zuwa na hutun ba kamar yadda aka riga aka yimin alkawari cewa duk hutun makaranta a Mambila zanyi.
Nutsuwa ta shige ni sosai, ilmin addini dana zamani ya soma ratsa ni, ta ko’ina na zama cikakkar AISHATU-SIYAMA MAMMAN GEMBU na tashi daga (Boddon nan ta Mambila). Bani da abunda zan ce da Aunty Wasila sai Allah ya ja girman ta, ya kara hasken tauraruwar ta a zuciyar Dr. Mamman Dalhatu Gembu. Ya kuma sauke ta lafiya da abinda ke cikin ta, yasa ayi wa abinda zata haifa duk irin abinda ta yi min a bayan ran ta.
Da ace duka matan uba irin Wasila ne tabbas da ‘ya’yan da wani dalili yasa suka rasa iyayen su bazasu taba koka maraicin uwa ba. She is really a MODEL!
*****
H
aka kwanaki suka yi ta shudewa a hankali suna mirginawa suna komawa watanni, har muka gangara wata na tara da komawa FCT, dukkan mu sai muka samu hutun kirsimeti Anti da Abba kuma suka dauki (Annual Leave) a lokaci daya don haka muka tattaro zuwa Mambila don yin hutun mu, dauke da tsarabar Ummati niki-niki iri-iri.
Irin sukuwar dokin da na yi a jikin Ummati da shigar mu gidan sai da Abba ya daka min tsawa, "karasa min uwar zaki yi? Wannan wane irin rashin hankali ne? Ummatin kwari gareta har haka?"
A can ne muka tarar dasu Young Abba (Adamu) da matarsa Anti Nasara suma sun zo hutun kirsimeti daga Lagos, familyn Ummati ya hadu ya batse waje daya abin sai masha Allah. A washegari aka yi (Get-together Party) na family, aka yi hotuna da vedio don tarihi aka yiwa mamatan mu Addua; Kakan mu Malam Dalhatu, Baba Gidado, iyayen mu Hassu da Asshe. Abba na yi wa Young Abba korafin bai taba zuwa gidan mu ba, in shi ba zai je ba ya dinga kai mana Nasara, Young Abba ya ce aikin shi sam bashi da lokacin tafiye tafiye amma ita Nasaran zai iya sako ta a jirgi ta zo insha Allahu idan sun koma sun samu dama.
Young Abba dai dama rayuwar shi duka ta bakaken turawa ce, sai kuma ya zo ya samu aiki da US Diplomatic Mission tunanin sa ya kara sauyawa ya karkata kacokam kan rayuwar malam bature, bai wani damu da dangi ba, rayuwar sa ta 'yanci kawai yake yi da matar sa, yana dadewa bai zo gida ba. Kuma in ya zo ba ya jimawa. Hana rantsuwa ya san shi cikakken musulmi ne.
Wato kowa ya bar gida gida ya bar shi kuma gaskiyar bature da ya ce “no place like home”. Mun ji dadin hutun mu a Mambila domin daga can mun je Gashaka ni da Ya Umar wajen dangin mahaifan mu na Uwa, Kakanmu Malam Muhammadu Jauro ya jima da rasuwa Amma akwai kanwar sa Goggo Halima da sauran dangin mu duk suna raye ba inda Goggo Halima bata sa a n kaimu ba, aka kuma rako mu da tsaraba rankatakaf ta fruits (Piya) kwan Zabbi da kwaryar Zuma, muka baro Gashaka cike da kaunar ‘yan uwa.
Satin mu hudu cur a Mambila muka koma FCT don fara shirin komawa makaranta.
*******
SHEKARU UKU A GABA
A
wannan lokacin ‘ya’yan Anti Wasila biyu; Maryam-Jamila yar shekara biyu da goyon Shukra-Nadiya 'yar watanni shidda. Anti haifar 'ya'yan kawai take amma ni ce komai din su, ma'ana ni nake musu komai amma dole dagabaya ta dauki Nanny sabida bana wuni a gida kullum ina makaranta har a Asabar da Lahadi muna yin Tahfiz. Ita kuma ga zuwa aikin ta.Ni da kaina “Azumi-Siyama” idan na dubi kaina a mudubi a wannan shekarar dana ke cika shekaru goma sha tara da haihuwa, ajin karshe na sakandire, bana saurin yarda cewa nice. Sabida girman da na kara da samun cigaban rayuwa ta kowannne fanni.
Nafi yarda in aka ce wata bakuwar