Showing 12001 words to 15000 words out of 45425 words
Chapter 5 - SAKACIN WAYE Document Complete by Takori kabara .txt
annakiyar kazantar taki da gashi fal hammata hadadden mijin zai zo? Lallai fa hadadden miji a mafarki! Ai sai a mafarkin kam! Allah tsinewa uwar mai karya, hatta Umar aka bashi ke a haka an takaice shi, kuma sai na gaya masa ya sayi shavingcream ya ajiye duk sati ya saka ki a toilet ya sullube ki da kan sa….”.
Tashi na yi ina kumburi kamar kububuwa na bar mata dakin don na tsani Anty Wasila yanzu.
Ummati na jin mu banda aika lomar ‘meat ball’ ba abinda take yi, na gama lura Anti ta gama saye Ummati da nau’in kayan dadin ta kala-kala kullum da abin dadin da zata sauya mata na makulashe ashe dama don ta raba mu ne don yanzu haka Ummati ta fi jin maganar Anti a kan tawa.
Da daddare bayan sun gama cin abinci ita da Abba ta kwashe komai ta dawo ta same shi cikin kissa irin tata sai ta ce .
“Baban Siyama amma dai da Siyama zamu koma Abuja ko? Tunda Umar ma komawa zai yi gara suna tare yadda suka taso nima kuma in ke jin motsin mutum a kusa da ni don wallahi bani da ra’ayin ‘yan aiki”.
Abba kamar Anti ta shiga ran sa ta sosa masa inda ke masa kaikayi don ya gama yanke shawarar kai ni makaranta mai kyau don kamar bana koyon komai a makarantar mu ta nan Mambila, cikakken sentence wannan na turanci bazan iya hada maka daidai ba, kawai yana shayin rigimar Ummati ne.
Anty bata fito fili ta gaya masa dalilin ta na son tafiya da ni ba amma shima Abba ya san wasu, musamman rashin kwaba ta da Ummati bata son yi, sannan Umar yana yawan kokan ta masa abubuwa da yawa da suke damun sa akan irin goyon Kaka da Ummati take min.
Sai Abba ya ce “I thought as much. Amma Ummati bazata yarda ba”.
Anti ta ce “ka bar komai a hannu na, I assure you zata yarda idan ni nayi mata magana.
Tsakanina da Allah da kuma kaunar da nake maka Dr. nake son gyara rayuwar Siyama, hakika tana bukatar mentoring na uwa a wannan stage din na puberty da take ciki, ka saka a ranka tamkar Siyama na hannun mahaifiyar ta mai rasuwa a zaman da zamu yi tare ni da ita. Allah ya jikan ta da gafara”.
Abba bai san sanda ya bude ma Wasila hannu ba ta yi azamar shigewa ciki ya rungume ta yana shi mata albarka.
*****
“
Watakila dai matar nan har tsayuwar dare ta yi wa Ummati ta mallake ta!”. Haka na gayawa Ya Omar cikin kuka da ya tabbatar min Ummati ta amince gobe da Anti Wasila ta cika wata guda a Mambila zamu wuce Abuja tare bakidayan mu har da Abba da ita Antin. A kofar gida na dawo daga islamiyya ya tare ni yake gaya min wai maza in je in hada kaya na da sassafe zamu kama hanyar Abuja.
Da kuka na wiwii na shiga gida domin kuwa a karo na biyu Ya Omar ya sake gwabje min baki wai na raina Anti Wasila da nace ta yi tsayuwar dare ta mallake Ummati.
Kan Ummati na fada da kuka na “Ummati da gaske kin yarda a tafi da ni a raba mu? Ummati nice fa Azumin ki, Boodon ki, Asshenki, Siyamar ki”. Ummati tayi azamar ture ni daga kan kafafun ta tace
“Allah yasa Sabira ce ba Siyama ba. In kin zauna wace tsiyar kike taimaka min da shi? Banda ki nade kafa a gado ki ci ki tashi hatta kwanon da kika ci abinci sai ni zan dauke miki, idan kuwa kashi kikayi sai dai in kora miki, hayya ratata Allah ya raka taki gona, Wasilar ce abin tausayi ba ke ba, sabida yadda zaki je ki maida mata daki matattarar kazantar ki. Faruqu kawai zan yi kewa”.
Gefe na koma na saka kai cikin cinyoyi na na soma gunza kuka, na ki hada kayan na ki yin komai, maganganun Ummati sun bakanta min ba dan kadan ba, sai ga Antin ta yi sallama tana tambayar Ummati wai na kammala hada kayana? Abba ya na jera su a trunk din mota ne tun yanzu da daddare, don da assubah zamu kama hanya sabida sai mun kwana a hanya.
Ummati ta ce “gata nan sai kuka take wai bazata bi ku ba” Anti ta karaso inda nake ta tsugunna cikin lallashi tana cewa “Oh ni Wasila bakin jinin nawa har ya kai haka gun Siyama?! To ki sha kurumin ki duk hutu da kaina zan kawo ki Mambila ki yi hutun ki tare da Ummati”.
Na dago idanuna jajir, jagab dasu da hawaye na dube ta “kada ki kara tube min zani, babu kyau wani ya ga tsiraicin wani, in kin ce in yi ko menene zan yi, sannan don Allah kada ki kara saka ni girki” Anti tace “kece kika yi gardama in da kin yi salin alin ba zan yi miki da kai na ba, girki kuwa sunnar kowacce mace ne”. Na yi sharbe na ce “ai ba dole bane, tunda ni din bana so, kuma kada ki kai ni makaranta, bana so bana son karatu wallahi”.
Anti ta yi dan jim! Kafin ta ce “ban yi wannan alkawarin ba, sabida ba ni ke iko da ke ba, alkawarin da zan yi shine ko iya sakandire kika yi zan roki Abba ya kyale ki ba lallai sai kin je jami’a ba, sai ku yi auren ku da Omar ki yi ta sullubowa Ummati kyawawan tattaba kunne”.
Ummati mikewa tsaye ta yi don lallashin da Anti Wasila ke ta faman yimin ya fara bata haushi tace “da ke da mijin naki da tattaba kunnen naki da Antin naki duk ku tattara ku bar min daki kafin in miki tabon sallama da Mambila a kan farar fatar ki, ki koma birnin da dabbare-dabbare, kin san dai ban taba gwada kai hannu na jikin ki ba kada kisa mu yi sallama da shi yau (duka)”.
Anti tace “yi hakuri Ummati, kukan sallama take miki, bari in hada mata kayan da kaina”.
Anti ta shiga dakina tana hada min kaya amma ko nisa bata yi ba da ta ci karo da wanduna masu busashshen menses a jiki ta watsar ta fito tsigar jikin ta na tashi, tana ce da Ummati.
“A tattara kayan Siyama duka a wanke a bada sadaqa Ummati” “to me zata saka in kuka tafi?” Ummati ta tambaya cikin mamaki, sai Anti tace “babu matsala zan diddinka mata wasu”.
Shi kam Ya Omar sosai yake murnar komawar sa Abuja sabida jami’a da zai fara a can, nikadai nake bacin rai na da fama da kuncin zuciya. Da asubah muna idar da sallah muka kama hanyar barin Gembu, Gembun Mambila, Gembun da ta tattara duk wani dabdalar kuruciya ta. Zuwa birnin da ya bude sabon shafi na rayuwa a gareni, wanda mafarki na na shekara da shekaru ne yayi min sanadin sa.
Da gaske Aunty Wasila has become my lifestyle influencer…. ta yi nasarar mai da ni MUTUM!
Na farko ta raba ni da rayuwa mara ma’ana dana ke yi a baya. Amma da na san actualizing mafarkin dana ke faman yi shi ke jira na a birnin da ko kusa ban yarda na bi Wasila ba, gara na dauwama a dakin Ummati na, cikin kwarkwata da amosani da kirci, doyi da hamami na da gashin hammata ta. Hausawa suka ce wai zama lafiya ya fi zama dan sarki ta kowanne fanni.
Abu daya nake tunani akan hanyar mu ta zuwa Abuja yake nutsar da bacin raina na rabo ni da Mambila da Wasila ta yi; watakila in hadu da shi…… Watakila silar haduwar mu kenan da mijin mafarki na, tunda na tabbata ba a Mambila yake ba, da a can yake, da tuni na ganshi a tsayin shekarun dana dauka ina mafarkin sa.
Bai yi kama da Mambilawa ba ya fi kama da 'Black-Nigerians', don haka kila kaddara ta da shi ita ke sarrafa kanta a kaina. Na kuma tabbata kaddarar ce har ila yau ta sa Wasila fizgoni daga mahaifa ta zuwa birnin gamayyar ‘yan Najeriya. Domin na yi amanna da cewa Allah na nufin wani babban al’amari a tsakani na da shi wanda ba’a mafarki zai kare ba.
Wanda kuma ban san farkon sa ban san karshen sa ba. Addu’a ta guda daya bazata taba canzawa a kan sa ba ta Allah ya bayyana min shi. Ya hada fuskokin mu ko da sau daya ne in gan shi a zahiri don cire kishirwar ganin sa da ke addabar idanu na dare da rana, in gaya masa tsahon shekarun dana dauka ina mafarkin sa…da mafarkin zamowar sa miji a gare ni. In kuma gaya masa cewa ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba.
Hakika an halicci zuciyata sarqafe da tasa ta yadda na ke da assurance na cewa zukatan mu are undoubtedly connected, an yi min jarrabawa mai girma a kan sa tun kan in gan shi, tun kan in san shi, tun kan in mallaki hankalin kai na.
******
“TAFIYA MABUDIN ILMI”
T
un ina karama nake jin Ummati na yawan fadin wannan zancen na hausawa, "tafiya mabudin ilmi" ban taba yarda ba sai yau da na fito daga alkarya ta ta ainahi wadda ban taba barin ta ba tun haihuwa ta, na ke keta garuruwa da jihohin Arewa maso gabashin Najeriya cikin lafiyayyar motar Abba (4-Matic) baka wul. Sanyin A/C ya addabe ni sai da na roki Ya Umar da ke tukin motar akan ya rage, Abba ne zaune a gefen sa yana karatun Al’qur’ani ni da Anti muna kujerar baya. Anti na ramuwar barci ni kuwa idanuna tangaran ko son kiftawa bana yi kada a wuce wani garin ban tambayi Ya Umar sunan sa ba. Shikuma baya gajiya da gayamin har da karin bayanin karamar hukuma ce ko kuwa jiha. Da sunan gwamnan garin mai ci idan ya sani. Tafiya sosai ta kwana guda da yini guda kafin mu isa FCT Abuja. A hakan ma mun tsaya a Kano ne mun kwana a wani gidan saukar baki (Tahir Guest Palace) washegari da safe muka dauki hanya.
Tunda aka haife ni ban taba fita daga garin Gembu ba sai wannan karon, hana rantsuwa na je Gashaka tare da Ummati wajen dangin mahaifiyata ba sau daya ba ba sau biyu ba dana yi wayo, don haka yau da na rinka ratsa jihohin arewa bude ido nayi kawai na yi ta shan kallo ina mamakin wasu gine ginen wadanda ban san da irin su a Najeriya ba.
Da muka shigo Abuja kuwa manyan titunan ta masu fadi da gadojin sama da kasa su suka fi daukar hankali na domin cigaban dana tarar ya kai ya kawo. Sai yamma lis muka shiga wata kebantacciyar unguwa wai ita Jahi, inda anan gidan da Abba ya saya yake, gidan na mu ba wani babba bane kwatakwata (three bedrooms duplex) ne, dakuna uku kacal ke da gidan biyu a sama daya a kasa sai BQ inda anan Ya Umar zai zauna. Amma tsari da ilmin da aka zuba wajen tsara komai na gidan abin burgewa ne matuka. Ana kiran wadannan gidajen duplex, wadanda duk kusan iri daya ne cikin estate din, an kwaikwayo su ne daga gidajen kasar Sweden.
Dakin kasa Anti ta bar min, inda a can babban falon gidan yake, da main kitchen, ita da Abba suna sama, Ya Umar na daga waje shikadai a BQ sai maigadi a nasa dakin can a jikin gate din shigowa.
Kwana biyu kawai Anti ta bar ni na huta daga gajiyar mota daga ranar kuwa a gabanta nake wanka ina kuka ina komai ba ruwan ta, komai koya min take kamar ta samu katuwar jahila, tun daga alwallah har wankan tsarki, da wankan sabulu da yadda ake gyaran gashi, ta sayo min hand dryer ta koya min busar da gashi inna wanke, ta saya min shampoos ds conditioners samfurin Dr. Teal’s, komai na amfani na har man shafawa da bath foam dina samfurin (Dr. Teal’s) Anti ke zabar min, sati daya da zuwan mu ta kai ni H-MEDIX inda acan ta hada min set din su, daganan sai Grandsquare inda ta saya min undies farare sol sol da kayan barci kala biyar da dogayen riguna suma biyar biyar, Egyptian Jilbaabs kala-kala don zuwa islamiyya, maclean kuwa daga ni har ita dana Longrich muke amfani.
Zuwa sati biyu na fara da rage kin shiga kitchen don kuwa Anti bata bari na in yi zaman banza irin wanda na saba a falon Ummati ina kallon talbijin, idan har zata shiga to dole ta biyo ta daki na ta sako ni a gaba, tare muke shiga safe, rana da yamma mu yi girki sau uku a rana.
Aunty bata raga mini, ba ta sassauta min sai ta ga na yi komai daidai kamar yadda ta koya min shi a kicin. Haka da ta samu lokaci ta dauke ni muka je tayi min shopping kayayyaki na dinkawa kala kala atamfa, shadda, leshi da materials, ta bada a dinka min a gidan su bayan telan gidan su ya auna ni, sannan ta saya min kayan masarufi dana tsaftace jiki iri - iri, turaruka da deosprays masu dadin kamshi na Dolce&Gabbana, haka ta ke bata lokacin ta wajen nuna min yadda zan ke amfani da komai, yadda zan gyara fuskata, hatta shafa lipstick ita ta nuna min, kasancewar tana hutun aure bata zuwa aiki sai bayan wata daya.
Amma duk da haka ni kullum cikin jin haushin Aunty Wasila nake. Gani nake ta takura rayuwa ta ta canza ta iyakar canzawa, ta matsa mini.
"Me yasa ta damu da sai ta canza min tsarin rayuwa ta?"
Idan ina yi ma Ya Umar wannan korafin sai ya girgiza kai ya ce “nan gaba kadan zaki gane babu mai son ki a duniya bayan iyayen ki sai Antin ki, Wasila”. Nace “au kai baka so na?” Yace “ni ba na cikin lissafin su, soyayyar miji daban ta iyaye daban. Aunty wasila da Abba iyayen ki ne”.
Sai bayan ya fada yayi nadamar subutar bakin sa, yayi maza ya gyara da cewa “soyayyar Yaya daban take da ta kowa, kin ji? Ki daure ki daina korafi kan Antin ki, ki bata dukkan goyon baya da hadin kan ki. Bata nufin ki da komai sai tarin alkhairi.
Ina tabbatar miki duk kudin da ta ke kashe miki ba Abba ne yake bata ba, hasali ma bai san tana yi ba. Don Abban namu Economist ne ba zai salwantar da kudi masu yawa har haka a kan ki wai don ki zama 'yar birni ba.
Had you know how beautiful and radiant you have become now, da kin gode mata iyakar godewa. She is indeed your lifestyle influencer!”
Murmushi nayi. Ban san takamaimai ma’anar kalmar da ya fada ta karshe a wancan lokacin ba, illa zuciya ta da ta fassara ta yadda ta ga dama, na san dai kawai Omar yana yabon kirkin Anti Wasila ne.
Da hutun Anti ya kare ta koma aiki sai na samu saukin ayyukan gida, ni kadai nake wuni a gidan, kuma sai naji gidan ya yi min fadi babu dadi kamar da, kewar ta ta dame ni. Kasancewar har zuwa lokacin admission dina bai fito ba daga ‘Regent College’ inda Abba ya nema min.
Ya Umar kuwa yanata zirga zirgar registration din sa tsakanin gida da Gwagwalada inda zai fara level 1 a tsangayar da Abban mu yayi nasa karatun wato tattalin arzikin kasa (economics). Don Abba so yake a komai Umar ya gaje shi tunda dai bai da dan da ya fi Umar din, amma shi a ra’ayin sa karatun likita ya so ya yi, likitan zuciya, amma tunda Abba yace ga abinda yake so ya karanta ya karba da hannu bibbiyu. Ko dama can shi mutum ne mai muhimmanta ra’ayin wanin sa a kan nasa, a haka kowa ya shaide shi.
Kullum Anti ta fita aiki zaka same ni ne ina gyaran gidan mu ciki da bai din sa, bani kicin bani falo bani saman bene har sai naga ko’ina yayi kal-kal, tsaf-tsaf, yana daukar ido, sannan in dora mana abincin rana, zuwa yanzu kam ba laifi na iya girki daidai gwargwado na zamani amma banda na gargajiya wadanda Anti su tafi koya min.
Direban ofis din su Abba na zuwa daukar masa abinci karfe biyu daidai na rana kasancewar Abba tunda ya auri Wasila bai iya cin abinci