Showing 27001 words to 30000 words out of 54884 words
Chapter 10 - ZUMA A BAKI! Complet by Autar manya.txt
ta bani shawara.
Tsayin kwanaki gashi na tafi shekara an saka bikin ya imran da maryam kanwar ya umar haka nan an saka bikin nafisa mai bina, a wannan lokacin na rame na fige su islam na gidan inna hutu amman kunyar inna ya hana naje na gansu domin ni a tunanina ya gaya mata yadda muka zauna.
Seda ana ya gobe zasu tafi nasai omo da sabulai anisa ta rakani gidan a saka makon takuramin da anty tai akan naje na gansu a karo na biyu.
Tunda na doso layin jikina ke rawa sanye yake da bakar t.shirt se bakin wando yay wani haske ya karo kyau matasan layin zaune gefensa suna masa fadanci yana raba musu kudi gidan inna an gyareshi har wani gate aka saka domin rabona da gidan tun daya saken anisa ce ta gaishe sa nikuwa wucewa nai na shiga gidan inna maryam tana zaune tanawa islam wanka shiga nai muka gaisa da inna sannan na fito wajan islam sabida kukanta ya dauki hankalina kusan a tare muka isa gareta nidashi ajiyar zuciya na sauke ina mai kallon maryam.
"Maryam meke damun Aisha?"
Nafaɗa ina kallon yadda ƴar keta kuka!
"Wallahi anty humairah wanka ne bata so"
Kokarin kai hannuna nake jikinta yay saurin ɗauke ƴarsa ya makawa maryam harara tabar wajan.
A kokarina na kuma kamo islam saukar mari naji a kuncina.
"Kada ki kuma saka wannan jakin hannun naki ajikin ƴata banza marar zuciya uban me ya kawoki gidanmu wallahi nakuma ganin wannan ramammiyar fuskar taki sena la'antaki".
Yafaɗa yana mai tofan miyau a saman fuskata yaja yarsa suka bar wajan.
A tsakar wajan na zube nama kasa kuka dan takaicin tozarcin dayamin a wannan kadamin bana hango so se dunbin ƙi gareni.
Haka anisa tazo tajani mukai gida dan tsabar bala'i har zazzaɓi nai ranar tundaga wannan lokacin ban kuma saka ƴaƴana a idanuna ba haka zalika inyazo baya zuwa inda muke sedai aikensa haka zalika matarsa ma bamu taɓa ganinta ba kwanaki ma tai ɓari amman batazo nan ba kuma a gidan inna tai jinyar, haka lamarin nawa yay ta tafiya har zuwa wannan lokacin dayau ya kawosu gidanmu wanda shine zuwansa na biyu tin bayan rabuwarmu.
Wannan shine tarihinmu dafatan makaranta labarina zasu fahimta.
*DAWOWA LABARI*
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*27 & 28*
Nisawa nai bayan na gama tunanin tarihin abinda ya shuɗe a shekara ɗaya da rabin data gabata.
Share hawayena nai idanuna jajir na fito daga ɗakinmu, bakin rijiya naje na ɗauro alwala nazo na tayar da sallar magariba,bayan na idar na zauna nan ma tunanin bayan iddata na faɗa.
Wanda babu kalar ƙalubalan da ban ganiba, har wankau seda nai sabida baba yayi rantsuwa a lokacin akan baze ciyar dani ba tunda na kaso aurena haka nake xama nai wankau nai gogau na sami kuɗin abinci haka al'amura sukaita faruwa wanda har akai bikin nafisa mai bina tare da ya imran daya auri maryam duk ina cikin wannan ƙuncin rayuwa seda ayiya kakata tazo da kanta taiwa baba faɗa sannan ya janye ƙudirinsa lokacinne umma taiwa matar ƙaninta magana aka saman koyarwa nan wadda ake biyana dubu bakwai a duk wata.
Da kuɗin nake taimakon anty nake taimakon ƙannena,nima naɗan sai wani abun.
Haka al'amura suka cigaba da wanzuwa a tsakanina da mahaifana wanda seda aka kai ruwa rana kafin baba ya soma amsar gaisuwata.
Gaba ɗaya ni yanzu wannan rayuwar ta fita akaina bani da bazzawari bare na sami mai ɗeben kewa ga shi ban san gidansu sakina ba.
Na jefa wayata masai bare muyi waya da ita haka na nisa a tunanin lokacin danaji sallamar anisa a ɗakin.
Amsa mata nayi tare dajan bakina na tsuke.
"Yaya humairah"
Ta kira sunana.
"Na'am Anisa".
Gyara zamanta tai a gabana tare da cewa.
"Ɗazufa naga yaya umar dasu aslam wallahi fafur sukaƙi yarda dani wai su akaisu wajan inno".
Ban ce mata komi ba naja jikina nai saman gado.
Babu yadda anty batai dani akan na fito nasha iska naci abinciba amman naƙi haka nai kwanan kuka
Washe gari kuwa kaina ya tashi da mugun ciwo,idanuna yay jajir sallar asubahi nai na koma baccina.
"Ke humairah yau bazaki aiki ba sekin makara"
Naji muryar anty akaina.
Ban motsaba nifa wallahi in akan ƴaƴana ne sena zubar da komai na makashi kotu domin bana jin a yanzu zan iya rayuwa babu su.
Fafur naki tashi bare na shirya nai makaranta haka naita juyi agado wajan karfe goman safiya naji kamshin turarensa tare da sallamarsa da sauri na mike na nufi gaban taga ina leƙen ƴaƴana.
Waige naga islam nayi tare da turjewa waje ɗaya taki shiga ɗakin anty.
"Daddy ina maman?"
Tafaɗa tana turo baki irin na shagwaɓaɓɓun yara.
Shafa tulun sumar dake kansa yay tun jiya islam ta hanashi sukuni ita yakaita wajan mamah mai kuka ta jiya har dukan ƴar yay akan nacin data kafa masa amman taƙi shuru ganin haka yasa ya tattarota sukayo nan( ɗada mahaifi se Allah).
"Tana ciki muje mana"
Yafaɗa murya ƙasa-ƙasa.
Amai makon ta shiga seta saka mai kuka wanda ya janyo hankalina nayo tsakar gidan,sabida daman ni ɗayace a ɓangaren namu su anty suna ɓangaren ummah.
Kaina babu ko ɗan kwali haka na zube a gabanta na ware hannuna ina kuka.
Da gudu ta shige jikina tana sakin ajiyar Zuciya.
Shafa kanta nai da hannuna ina jin wani irin nutsuwa a tare dani.
Kafin na soma kici-kicin ɗagata nai ɗakinmu da ita.
"Wait dakata! ina zakimin da yarinya kinga ajeta zamu wucene"
A dake na tsaya da ita a hannuna.
"Bazan bada ba ainima ina da hakki akanta dan jaraba ƴa nason wajan mamanta ka hanata zuwa"
Nafaɗa cikin rashin kunya.
A gabana ya tsaya yana zuban kallon banza.
"Bani ita Aisha bana son hauka"
Yana kokarin kwatar ta.
Seta saka kuka.
"Ni wallahi daddy bazani wajan mommy ba ita bata kuka akammu dukanmu take mommyn abuja".
Cak naga ya tsaya ya zuba mata ido yana kallonta kafin naga ya juya yabar tsakar gidan.
Yana gab da fita na ɗaga murya.
"Allah ya isana ga duk ƙatuwar data dokarmin ƴaƴana ubangiji yabimin hakkina"
Da gudu najata mukai ɗakinmu ina dariyar farin ciki.
Shima anasa ɓarin maganar islam ta kaɗashi batun yau take cemai mommy na dukansu ba amman yadda take nan nan dasu agabansa yasa ya kasa yadda da maganar islam ɗin sabida ance ba,a kama maganar yaro gefe ɗaya ga takaicin rinjayen da humaira tai mai na amsar islam wadda yaji kamar ya gaurawa islam mari sabida yadda take ƙulafucin uwarta.
Haka ya koma gidan inna aslam daman bayajin dadi yana bacci dan haka shima fita yay zuwa gidansu sakina wadda ya kasa gane kanta sam yanzu in sukazo kano bata yadda ta sauka gidan inna kamar da sedai shiya bita can gidan nasu.
A gado na ajeta na fita waje shayi na haɗo mana mai kauri nazo na zuba mata muka baje muna sha muna gamawa na tsefe mata kanta da kaina na wanke mata sannan na shiga ɗakin anty da ita se lokacin suka san an kawon ita nanfa anisa ta amsheta ta soma yarfa mata kitso mai kyau da yamma nai mata kunshi ja wanda ya haskata.
Sosai baba yay farin cikin ganin islam a gidan haka yayta sabga mata siyayya kala kala, a daren kuma har aka rufo kofar gida baizo ɗaukarta ba dan haka na cire mata kayanta muka kwanta tare washe gari ranar juma'a nafita aiki tare da ita.
Lokacin naga tashin hankali domin karfe goman safiya da rabi segashi a bakin gate ɗinmu koda naje cin mutunci yahau min akan me xan fito mai da yarinya.
Sunkuyar da kaina kasa nai ina mai wasa da yatsuna haka ya gama bala'insa yaja ƴarsa suka tafi ajiyar zuciya na mayar domin yanzu naɗanji dama sabida yadda islam ta ɗeban kewa a daran jiya.
Sedai maganar dukan da matar ubansu ke masu ita ta tsayan a raina na kasa mantawa.
Haka na yini a makarantar sannan na dawo gida bayan an tashi lokacin naji labarin sun wuce abuja.
Hmm ashe wucewa zasuyi can ɗin shiyasa yazo a burkice.
Watsar da sabgarsu nai a ranar na shiga sabgata washe gari na tashi da shirin tafiya gidan shugabar makarantarmu kamar yadda ta umarcen.
Shikuwa daman da yaran kaɗai ya tafi domin zasu koma school ne ita kuwa sakina taƙi binsa sabida fushin datake dashi tun jiya akan yace mata islam na wajan mamanta.
Wannan dalilin ne yasa ta dauki fushin dayasa har shima yay fushi ya tafi yabarta haka nan koda ta kira wayarsa bai dauka ba domin ta ɓata mai rai sabida yadda tace mai ai daman tasan munafurcin mazane amman yanasan matarsa har yau wannan maganar yasa yaji haushinta sosai.
Hankalintane ya tashi a washe garin asabar tai gidan inna domin tasakata ta basa hakuri akan laifin datai mai har yay tafiyarsa ya barta.
Shikuwa daman da biyu yay hakan na farko maganar islam na tana dukansu na biyu kuma furucinta gareshi wanda ba daban yakai zuciyarsa nesaba dase yay mata illah a daren.
Ita kanta inna, tai mamakin yadda sakina batazo gaisheta ba,amman dan rashin kunya tazo mata da wannan maganar agabanta inna ta kirasa ta hau yimai faɗa akanme ze tafi yabar matarsa.
Hakuri ya bata sannan yace gobe ta bata kudin mota ta tawo haka inna ta kirga kudi ta bata sukai sallama ba kunya ta kama hanyar fita.
Magana mukai akan sabon bazzawarin da shugabar makarantar mu ta sama min na taho inata tunani mai ƴaƴa takwas da mata ɗaya amman yana da kuɗi hawayene yake zubomin lallai rayuwa yau ni ake jonawa da wani duk irin soyayyar da umari ya nuna mini.
Cak na tsaya lokacin dana zo giftawa ta gidan inna ganin sakina tana fitowa daga gidan.........!
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*29 & 30*
Cikin tsananin ɗauki na ƙarasa gareta fuskata a sake naja na tsaya a gabanta.
"A,a sakina daman ana ganinku a duniya? se yanzu kika tuna dani wallahi nayi faman nemanki amman rashin sanin gidanku yasa kikajini ɗiff gani ba waya akwai tarin damuwa a zuciyata".
Nafaɗa ina mai riƙo hannunta.
Zame hannunta tai daga cikin nawa tana mai jefamin ƙazamin kallo kafin ta kwashe da wata irin dariya.
"Hmm yaro!yarone yaro man kaza komi girman jikinka idan babba yafika tofa ya fika"
Ta numfasa tana mai cigaba dayin dariyarta.
"Humairah kenan ai bani da buƙatar ki bani wani labari akan mutuwar aurenki domin ina da labarin komi akanki ba kowa bace ba ke face bazzawara marar ƴanci mai baƙin jinin da tunda Umar ya rabu da ita batada mashin shini sabida tsabar baƙin halinki"
Jikina ne yahau tsananin rawa dajin kalamin da aminiyata take jefamin amman jin maganarta a karo na biyu ya kuma hargitsamin lissafina.
"A yanzu bani da buƙatar wata alaƙa dake humaira sabida daman buƙatar maje hajji sallah to alhamdulillahi ni naje hajji har umara ma naje ta dalilinki ƙawata"
Ta kwashe mini da wata shegiyar dariya.
"Da farko sunana sakina kuma ni haifaffiyar garin kano state ce mahaifina aiki ya kawosa garin kano, amman ɗan asalin garin nasarawa lafiya ne, har Allah yasa ya auri mahaifiyata umma, anan unguwar chiranchi suka zauna har Allah yasa umma ta haifi anty hadiza daga kan anty hadiza bata kuma samun haihuwa ba har seda ta shekara takwas sannan ta haifeni ni sakina, nayi primary da secondry a wata makaranta a gadon ƙaya daga nan babanmu ya rasu wannan tasa ban cigaba dayi ba bayan nai candy ita kuwa daman anty hadiza tuni tai auren ta anan kusa da gidanmu, babarmu mace ce mai hakuri hakama anty hadiza amman nikam inada zafi ina da kishi haka nan zuciyata mai riƙo ce da bin diddigin abinda take so shekaruna ashirin da huɗu da haihuwa amman bani da saurayi bare nai tunanin yin aure sabida akwai wanda na ƙwallafa raina akansa tun ina zuwa makaranta a gadon ƙaya nake haɗuwa dashi inze tafi BUK wannan tasa bana sauraran kowani ɗa namiji, sanin inada ƙaramin jiki yasa ummana bata damuwa da rashin aurena domin inna fita kamar yar shekaru sha bakwai zakaganni sedai ta idanu inada nuna shekaruna, Akwai watarana dana fito daga gidan anty hadixa kawai senaganshi hannunsa ɗauke da wata baƙar yarinya mai girman jiki tana ta mai sangarta ze tafi makaranta a ranar dana ganshi kasa bacci nai........
Washe gari nabi ta hanyar danaga yabi anan na sami makocin sa nake tambayarsa akan labarinsa atake anan ya gayan sunansa da kuma alaƙarsa da wannan yarinya wadda naji zata zaman Garkuwa a wajansa, Mataki na farko dana fara ɗauka shine na yaga takarduna gaba ɗaya na makarantar sakandire na sake neman sakandiren da wannan yarinyar take na koma daga farko ma'ana jss one.Cikin sa'a aka haɗamu aji guda da ita, da bin diddigi da shishshigi na samu na shiga jikinta ta zamen aminiya na fuskanci yarinyar batada wata magana seta masoyina wadda dukkan maganar da zatai akansa takan tafine da dukkan zuciyata.
NAZIR
Naje sabon gari nemo ankon bikin ƙawata xan gifa mukai clashing dashi adai dai wajan gidan gala, da sauri yazo gareni yana mai min magana akan yana sona sedai kallo guda nai masa na shaida cewar ƙwararran ɗan duniyane da wannan damar na amshi numbernsa wanda najewa wannan yarinyar dashi a matsayin yayana wanda na lasa mai wata ZUMA A BAKI wadda takaisa ga bani haɗin kai wajan cikar muradina, nayi amfani da ƙawancenmu ne na cika burina akan abinda nike so haka nan naje mata da wani irin salon yaudarar ƙawa wanda bata san dashiba......
Yaudarar kuwa itace.
Najenye jikina daga halaƙa da ƴan gidansu ma'ana koda wasa ban shiga jikinta a gida ba ta yadda har mahaifanta zasu lura dani su rabamu, nima kuma ban kaita gidanmu ba bare mahaifiyata da ƴar uwata su lura da shirina nabar ƙawance na da itane a iya school daga nan kuma se ranar dana taɓa satar jiki naje gidansu ranar da nazir yazo se kuma ranar daurin aure danabi zugar jama'ar biki na faɗa gidan nasu batare dana bar wani ya ankare ba, nayi amfani da tunanina sosai kafin wanzuwar hakan sannan koda wasa ban jata jikina ba amman ita ta jani ajikinta"
Seta juyo tana kallona.
"Tunda na sanki humaira sau biyu na taɓa xuwa gidanku abotarmu a iya makaranta ta tsaya wadda yawanci iyaye basa sanin dawa ƴaƴansu suke mu'amala a makarantunsu kinga kuwa hakan ke sawa yawanci burin ƙawa ke cika akan ƙawarta musamman mai wayo irin nawa, Tun bayan da kika auri Umar na shiga halin damuwa kullum bani da buri face ganin na rabaku"
Ta kuma kallona.
"MATAKI NA BIYU Nasha matukar wuya kafin na gano maye halin umar! na fara karantar cewar bayan ke baya da wata macen dayake so aduniya inka cire mahaifiyarsa daga ke kuwa se ƴaƴan da kika haifa wanda bayan na gama amfani da uwarsu a matakin farko na cikar burina senai amfani da su wajan ƙarasa ƙudirina, wanda bayan mun haɗa baki nida nazir mun fahimci lokacin dawowar umar gida nazo akan zan miki sallamar tafiya abuja har yazo ya rike hannunki se kuma nazo nabi naxir abuja akan an saceni wanda duk nazir ne ya bincikon inda umar ke aiki da hanyar sa ta komawa gida da ƴaƴan cikin ki nai amfani har umar ya auren wanda hakan bakaramin kunci kesa ruhina ba domin bana kaunar abinda ze raɓeki bare naci albarkacin ki a wajan Umar, humaira a yanzu burina ya cika shiyasa ma na ɓata lokaci wajan warware miki zare da a bawa domin bana shakkar kisan nice matar umar mariƙiyar ƴaƴanki aminiyar ki ta bogi domin nayi amfani da daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarki nai miki muguwar illah kuma ina miki albishir da cewa umar nawa ne for now an always dan haka sekibi wani sarkin badai nawa ba".
Tafaɗa tana mini dariya.
"Koda wasa umar bai san na sanki ba bare yay tunanin ni ƙawarki ce haka nan inna bata sanni ba haka zalika dattijawanki suma basu sanni ba bare ai tunanin naci amana sabida haka ina da fredom na shiga duk inda naso a dangin mijina batare da anyimin kallon mai cin amana ba bare naji kunya".
Tafaɗa tana ɗan rangwaɗa agabana kamar wata ƴar duniya.
Wani irin rawa jikina ya ɗauka kamar mazari kafin nai yunƙurin........................
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*31 & 32*
Ɗora tafikan hannuna biyar a saman fuskarta bata gama dawowa a hayyacinta ba na kuma wanketa da wani bahagon marin, kafin ta sosa na ƙara mata uku a jere masu ɗan karen zafi.
Da azabar ƙunar zuci na dubeta.
"Wallahi sakina sekinyi mamakin yaudara ta da kikai zan nuna miki ni ƴar kano ce cikakka ba zuwau ba kuma sena nuna miki wacece ni! cikin ilimi da nutsuwa irinta ƴaƴa masu tarbiya daga ƙarshe kuma ina mai tabbatar miki da cewa GANGAR JIKIN UMAR KIKA AURA ba zuciyarsa ba domin zuciyar umar ta AISHA HUMAIRA ce da ƴaƴanta har abada sakina bazaki mallaki umar ba matukar ina raye nai gabanki nai miki gudun wuce sa'a a fagen soyayyar umar domin ni sona yake daga zuci har baki haka zalika sone daga Allah ba boka ba malam ba kirsa bare bariki soyayyace ta asali ƴar gaske wadda turawa kewa laƙani da Pure love wadda ba algus cikinta kuma ko yanzu na mutu nagodewa Allah dayasa kika ci arzikin ƴaƴana har kika sami soyayyarsa koda haka seki bawa jakar ƙwaƙwalwarki amsar wacece aisha a zuciyar umar? bazan ji komi dan kinmin haka ba,domin sau tari daman makashinka yana tare dakai sedai kuma ta yaro kyau take bata ƙarko mu zuba"
Nafaɗa a dake.
Tare da saurin barin wajan zuciyata na suya na nufi gidanmu.
*SAKINA*
Azabure ta dafe fuskarta da dukkan tafukan hannayenta tsananin mamakin humaira ya hanata tafiya bare ta ɗago daga dogon suman wucin gadin azabar zafin marin data afka sosai humaira ta bata mamaki yaushe humaira ta zama jan wuya haka? yaushe humaira ta zama mai dakakkiyar zuciya haka wadda harta ɗaga hannu ta zuba mata maruka biyar lallai ɗan