Showing 39001 words to 42000 words out of 54884 words
Chapter 14 - ZUMA A BAKI! Complet by Autar manya.txt
ta bullomin da rashin bani hakkin kwanciyar aure shima sena daureta da igiya na haye kanta nai bidirina hankalina kwance wannan dalilin yasa nakeson na kara aure na huta".
Gumine naji yana ketomin kota ina.
Seda na yarfe sannan nace mai.
"Amman tayaya kuna zaman haka har ka kai war haka da ita batare daka mata illah ba?"
Murmushi yayi.
"Ada batamin kowani hali wallahi seda ta shiga wata makarantar matan aure tofa daga nan ta haɗu da ƙawaye na grp suka soma ɗorata a hanya, abinda ze baki mamaki yawancinsu matan manyan masu kudine wannan dalilin yasa suke gasa a junansu har hakan ta kawo tana min korafin ita kaza da kaxa yay mata kaɗan da sauransu atakaice dai yanzu komi nai mata bata gani sabida hangen na sama da ita,iya hakuri ina hakuri da ita bazan iya sakinta ba sabida darajar haihuwa amman aure zanyi domin na sami nutsuwa, kullum cikin tsurfar anko waya kaza da kaza ta fito na sai mata take".
Ajiyar zuciya nakai mai karfi kafin naji ya cigaba.
"Daga karshe ma inna kawo mata kayan abinci setaki yin girkin wai ita baxataci kalar abinci kaza ba se kaza ke danaga abin ze daman kawai sena kulle store ɗina, na soma dire mata ƴar awo inta ga dama tayi in bata ga dama ba ta barshi ai cikinta ne nikam ina zuwa da take away ɗina daga wje naci na koshi, sabida ita naga nasiha da bada baki baya mata se an haɗata da masifa".
Wani tsoron Allah ne ya kamani daman haka mazan suke? ahaka nake fatan nai wani auren? dama haka ya umar yay hakuri dani? tabbas ba namijin daze dauki abinda naiwa ya umar koda kuwa waye, duk da zugar da sakina kemin amman nima nasan kaina ban kyautawa ya umar ba ashe haka yayta hakuri dani har haihuwa biyu, da auren sakina da jarabawar dana shiga bayan rabuwa ta da umar wallahi kaf isharace gareni haka zalika darasi ALLLAH ya nuna mini.
"Beby bakya jina?".
Naji muryarsa a kunnena.
Firgigit! na juyo na sauke ajiyar zuciya sannan nace mai.
"Amman nikam inda zaka ɗauki shawarata auren dazaka daɗa wallahi baze kawo maka gyaraba face illah da haɗari sabida daga lokacin daka fara kokarin kara aure to wallahi kawayen matarka zasu soma zugata akan tabi malamai daga nan sekaga wata barnar ta afku amman addu'a da nasiha sune zasu kawo muku gyara a tsakaninku haka nan abincin da kakeci kai ɗaya a ɗaki ka hanasu wallahi rashin adalci........".
Dannowar hancin wata shegiyar mota layinmune ya hanani ƙarasa maganar tawa.
*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_
*Albishirin ku masu son karanta ƙayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faɗakarwa to gada ma ta samu ki nemi waɗannan zafafan littatan waɗanda aka baje soyayya mai tsayawa a zuƙatan makaranta cikinsu*👇🏼
*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*
_Nemi wannan numbern 08142105218 duk ɗaya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba ɗaya xaki biya naira 1000 ɗaya ne_
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*47 & 48*
Dakatawa motar tai adai dai saitinmu domin tayar motar ma ta kusan takamin ƙafafuna da sauri najanye ƙafafun nawa na ɗagesu nai saman dakalin dasu ina mai kallon baƙar motar dataji uban baƙaƙen glass waɗanda ba,a ganin na cikinta, tsabar yadda motar ke sheƙi yasa ina kallon hoton fuskata ajikinta.
Tajima a tsaye batare dana cikinta ya fitoba haka nan ba,a kasheta ba, gaba ɗayanmu nida Alhaji daka tawa mukai tare da zubawa motar idanu muna kallon wanda ze fito daga cikinta musamman ni danakejin bada ban alhajiba da wallahi senaje na buga mai glass ɗin koda ɗan gidan ubanwaye domin rainin hankalin yakai ya komo ai.
Kamar daga sama naji anbude murfin motar da ƙarfi, gabana ne yay wata iriyar faɗuwa wanda yasa jinin dake zuwarmin na al'ada ya kuma zubomin aguje kamar an koroshi.
Sanye yake cikin wata ɗanyar gezner kalar sky blue anyi masa ɗinkin halp jamfa,babu hula a saman kansa se uban baƙin glass ɗin daya kafta a saman fuskarshi baƙin takalmi sau ciki ya saka aƙafafunsa, Ganin yana tunkaro inda mukene yasa nasha jinin jikina babu abinda ilahirin jikina yake face mazari yana kaɗawa da ƙarfi da ƙarfi,tsananin dokawar da kirjina keyine ya tsoratani domin da ƙarfi yake dokawar tamkar ze faɗo ƙasa.
Cikin nutsuwa naji sallamar sa acikin kunnuwa na.
"Amin wa'alaikassalam".
Cewar alhaji sa'eed.
"Ranka ya daɗe baka san da matar aure kake zaune ba in ita bata da hankalin gaya maka tana da aure ni gashi na gaya maka".
Da sauri na ɗaga idanuna na dubeshi yawani tsaya agabanmu ya harɗe hannunshi a saman kirjinshi.
"Ko kaɗan ban sani ba kuma bayan haka ni ai ɗan gida.......,
Bai barshi ya karasa faɗar maganar ba ya tari numfashinsa.
"Stop! malam kai wani irin mutum ne bada ban kaci darajar furfura ba da babu abinda ze hana na gaya maka magana marar daɗi, zaka wani kawo baki fal goro kana wani cewa kai nagidane karewa kaine raɓa,ƙarewar gida kekuma dallah tashi ki bawa mutane waje uban me wannan tsohon ze zuba miki inba majina ba".
Yafaɗa a tsawace.
"Wallahi ni ƙarya yake ba wani auren dake kaina kuma.......
Ya saka haɓar hannunshi ya bugemin bakina tare dajana ya wurga cikin motarshi wani irin razanannan kallo yake aika min kafin ya sakawa motar key yaja mubar wajan baki ɗaya.
Kifa kaina nai a tsakanin cinyoyina ina rafka kukan takaicin abinda yay mini.
Tafiya mukai mai ɗan banzan nisa kafin naji yayi parking alokacin na ɗago kaina naga ashe wajan wani shaƙatawa ya shigo damu wanda bansan sunan wajan ba sedai yadda naga jama'a ɗaiɗaiku suna shawagi abakin wata bishiya ya gyara parking ɗinsa sosai.
Amai makon naji maganarsa sedai naji tattausan hannunsa a saman haɓata ya ɗago fuskata.
Fuskarsa jajir da alamun zafin rai naji muryarsa.
"Aishahhh mai kike cewa a waya? zuwa nai mu fiƙe raini nida ke sekuma naga wancan tsohon, ke yanzu in banda abin kunya ki rabu da yaro sabon jini ki koma tsoho mai baki fal goro idan ramawa zaki ai seki auro ƙaninki kamar yadda na auri ɗanya jakaf, amman dai anci baya wato shiyasa naga kinci wannan farin hijabin kamar fatalwa, ke mai yasa har yau yadda nasanki haka kike ne".
Tsananin takaicin maganar tasane yasa na doke hannunsa ina yunƙurin fita daga motar ya saka hannu ya dannen cinyata ya kan kame alamun baze barni nai wani yunkuri ba.
Ɗago fuskata nai na zuba mai idanu.
"Ya umar mai na tare maka? katuna komi bawa zeyi ya tuna akwai mutuwa akwai hisabi nidai nasan baka da matsala dani a yanzu tunda bana aurenka".
Nafaɗa ina mai fashe mai da kuka!.
"Kabarni naji da abinda nakeji arayuwata kabarni naje nai rayuwata nima kamar kowace mace,ba tsohoba ko sa'an kakana zan aura ina tunanin a yanzu bakada da matsala da hakan ko kana da ita?".
Nafaɗa ina zaro mai idanuna waje.
Rintse idanunshi yay tare da zare glass ɗin idanunshi gaba ɗaya idanunshi ya haɗe da wani irin ja kamar gaushi wanda ya bani damar sunkuyar da kaina ƙasa domin bazan iya jurewa kallonshi ba.
"Bani da izini Aisha amma a yadda kike yakamata ki koma ɗakinki kiyi gadin ƴaƴanki".
Share hawayena nai sannan nace mai.
"Tun suna yara kake rainonsu wani abun bai cisuba se yanzu? nima aure zanyi bazanje gidan wani da agololi ba haka zalika xan koma makaranta nai ilimi na zama mace kamar kowa".
Dariya ya kece da ita wadda nake ganin kamar da biyu acikinta.
"Aisha baki dace da duk abinda kika lissafo ba haka nan bakin ki kaɗai ne yake furta hakan amman zuciyarki ta karyata hakan".
Kallonsa nai ina hango tsantsar rikici acikin idanunsa.
"Nidai na gaya maka koma dai maye kai kasani kaji dashi kuma nidai bana sonka kuma bazan koma gidanka ba ko mazan duniya sun kare".
Shafo tulin sumar dake kansa yay tare daɗan kallon gefensa kaɗan.
"Koda nai miki haka?".
Yafaɗa yana mai rungumoni ya hadeni da kirjinshi.
Ƙoƙarin tureshi nake amman hakan ya faskara sema kuma mannenin dayake da kirjinshi kamo cikin kunnena yay da mugunta yana cewa.
"Aisha!Aisha!! tawa duk duniya babu mai iya zama dake wallahi seni ɗin,haka zalika kem bazaki iya rayuwa da kowa ba seni nine na fara buɗe miki ido akaf mazan duniya baki da first love kamar ni, bazan ce ina sonki ba a yanzu amman ina son ki koma ɗakinki kodan kiyi gadin ƴaƴanki".
Yafaɗa domin son ya ƙular da ita.
Tureshi nai ina kuka! gashi bai bani damar maganaba.
Sema yamutsamin jikina danaji yanayi da hannunshi ɗago kaina yay tare da tsiran idanu yana kallon yadda fuskata ta jike da ruwan hawaye.
Tsintar bakinsa nai akan fuskata yana mai fito da harshe yana lashe hawayen nawa dashi.
Seda ya lashen tass sannan ya fito da harshen nasa sosai, ya haɗe da bakina yana kissing lip's ɗina kamar babu gobe.
Wata ajiyar zuciya na sauke jin haɗaɗɗan tattausan bakinsa acikin nawa yana sumbata yana zuban miyaun cikin bakinsa acikin nawa.
Gaba ɗaya mun shagala da hakan musamman shi danaji yay min rikon tsauri da karfi na fusge fuskata na cure waje ɗaya ina kuka! ina neman yafiyar ubangijina.
Shiko jikinsa a matukar mace naga ya mayar da kansa back seat na kujeran yana mai faman huro iskar bakinshi kamar mai cin yaji.
Munkai kusan mintuna biyar a haka sannan yaja motar muka bar wajan.
A kofar gidanmu yay parking tare da bude motar batare dayay magana ba sema rintse idanunsa dayay kamar mai jin kunyata.
Ina fitowa mukai kiciɓus da baba da baffa zasu fito daga gida.
Cak baba yatsaya yana nazarina.
"Humaira daga ina kike".
Tun kafin ma nai magana yay saurin bude kofar side nasa ya fito da sauri naji baba yana cewa.
"A,a Auda umari kuke kenan?"
Da gudu nai cikin gida batare danai tunanin komi ba nai ɗakinmu na barsu a wajan.
Haka na wanzu ina faman tunani abu guda har dare ban fitoba seda anty ta gaji sannan ta leƙo anan naji tana ta min tsiya wai daman nasan umar zezo nacewa alhaji yazo dama ai tasan munafurcine shiyasa jiya naita kuka ashe da biyu nake.
Bance mata komi ba na koma ɗakinmu wajan karfe goman dare anisa tazo take cemin baba na kirana.
Hijabi na saka jikina yana rawa na nufi ɗakin nasa.
Zama nai ina mai kallon baba kafin na mayar da kaina kasa.
"Humaira ranar ita yau lahadi zaki koma gidan tsohon mijinki mun gama magana gobe za,a daura aure idan ya kammala aikin daya kawosa nan zaku wuce tare bana son doguwar magana kije ki rike ƴaƴanki sabida naga alamun kema kinfison hakan sabida yadda kika share alhaji ɗazu kika tafi wajan uban ƴaƴanki to Alhamdulillahi maganar makaranta babu bare maganar wani auren domin haka ki koma ɗakinki yafi miki alheri".
Kukane ya kufcen da sauri nai ɗakinmu ina mai cewa.
"Burinka ya cika umar nasan kasheni zakuyi kaida sakina daman nasan plant ka haɗa a ɗazun yasa ka ɗauken a motar ka".
Nafaɗa ina mai fashewa da kuka............
***************
Cikin nutsuwa ya ƙarasa gabansu baba adake kamar wani soja,yana kuma kunshe dariyarta aransa na yadda yaga tasaka gudu kamar wadda ta fito daga gudun hijira.
"Baba barka da yammaci................
Gamai buƙatar karanta littafina sabo wanda zezo a farkon sabuwar wannan shekara mai zuwa ze biya
*BAƘAR FATA*
(Romantic story)
Norma grp#300
VIP#500
Sp#1000
Complt#1000
Accnt#0078174806 starling bank then show me your evidance of payment ina maraba da masoyana ƙashin bayan nasarata one love❤️💯
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*
*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹
*49 & 50*
Cikin sakin fuska baba ya dubi umar yace masa.
"Barkan kadai Umar, dafatan kana lafiya yaya iyalin naka?".
Murmushi ya sauke yana mai saka hannunshi ya shafo sumar dake saman kansa.
"Lafiya lau nima nazo wani ɗan aikine kanon dafatan kuna cikin koshin lafiya?".
"Alhamdulillahi umari ashe kaida humaira ne, shiyasa naga tai gida aguje ja'irar yarinya".
Cewar baffa ƙananin baba yana dariya.
Cikin tausasan kalamai yacewa baba daman magana ce dashi in babu damuwa ze dawo nan da magari ba.
"A,a umari haba sekace bako muje shagon zaure mana muyi maganar tunda naga da sauran lokaci kafin ayi magaribar".
Bai misaltawa baba ba haka suka rankaya sukayi cikin gidan a shagon soro baba ya gyara mai wajan zama kana ya zauna.
Cikin nutsuwa ya kalli baffa domin baze iya duban baba da maganar ba sabida kunya wadda tunda ya saketa bai taɓa waiwayarta da sunan biko ba se yanzu.
"Baffa daman mungama magana da Aisha akan cewar ita tafi son ta koma sabida ƴaƴanta shine nazo na baku hakuri baba ataimaka Aisha ta koma wajan yaranta".
Tsit! shagon yayi kafin baffa yace mai.
"To Alhamdulillahi Umar daman mu a kullum gyara mukeso ba ɓarna ba sabida haka tunda har ita humairan da kanta tace taji tagani zata koma ai babu wani abu semuyi muku fatan alheri Allah ya saɓa hali".
Da amin baba ya amsa.
Anan suka gama maganar da zasuyi kuma atake anan baffa ya amshi wakilcin humaira akaro na biyu shikuma baba ya amshi na umar sadaki ya bayar bayan haka suka bar maganar akan gobe za,a daura aure.
To bayan kammala wannan gidan imran ya wuce ya sami kanwarsa maryam ɗauke da tsohon ciki ko ruwa ma bai tsaya yasha agidan ba yayi gidan inna sabida imran ɗin baya nan yana wajan aikinsa wanda bayan kammala karatunshi shima ya sami aikin banki anan wani sabon banki shiyasa haduwar tasu take wuya sabida yanayin aikin kowa sedai duk wata tattaunawa suna yinta a waya.
Innah tana tsakar gida tana faman gyara zogalan ,dazatai miya sallama yayi ya shigo tare da neman guri ya zauna a gefenta yana gaisarta.
kada ran kada han ta amsa mai domin ya bata haushi jiya akan abinda yay ma humaira a waya.
Bayan wajan yay shuru kamar babu kowa inna ce ta dubeshi.
"Umar umarni nake baka akan kaje ka dawo da uwar yaranka wallahi a wannan karon bazan ɗaga maka ƙafaba nagama magana ta".
Tafaɗa ranta a ɓace.
"Inna yanzuma daga gidansu nake kuma insha Allahu gobe zata zama matata akaro na biyu".
Jiyowa tai ta dubeshi.
"Kai dan Allah umari da gaske kake?".
Cikin tsantsar mamakin soyayyar da innah kewa aurenshi da humaira ya dubeta yau ta soma kiran sunanshi domin bata faɗa sabida kara irinta ɗan fari.
"Innah da gaske mana nake kedai ki mana fatan alkairi wallahi innah tunda na saki yarinyar kawai rayuwa nake amman komai baya min daɗi".
Yafaɗa cikin damuwa.
"Yo daman kai waya gaya maka ana saɓawa Allah a zauna kalau? ai saki baya daga cikin abinda Allah yakeso musamman idan anyishi cikin ganganci da kuma sauri shin wai mai ma yasa tun lokacin bakai tunanin mayarta ba?".
Ransa aɗan ɓace idanunsa jajir ya dubi innah.
"Wallahi innah lokacin na kasa controlling na kaina ne sabida abinda ya faru".........tas ya kwashe duk abinda yagani alokacin da abinda humaira kemai ada ya sanar da ita.
"Inna na rufeki ne sabida kada kiga baƙinta har watarana nazo nace zan mayarta kiƙi yarda, sannan kuma nima daga baya nai nadamar saurin sakin danai domin anan shine kaɗai laifina tare kuma da rashin bincike inna se jiya data ganni a datti wanda banga ƴa macen dazata ganka a haka ta kulaka ba inba mai tsananin sonka ba innah inkinga yadda Aisha taita kuka akaina abin ze baki mamaki".
Ya dakata yana lumshe idanunsa.
Innah kuma cewa tayi.
"Allah sarki yaro ashe har yau kana nan da wannan xurfin cikin naka? shin mai yasa bakai kokarin sanar dani komi ba alokacin ai da tuni maganar ɗanka na wajan huɗu ake da humaira domin bazan zuba ido aurenku ya salwanta ba da tabbas zanyi iya karfina domin ganin na tare wannan ɓarnar".
Da sauri ya tari numfashinta.
"Innah bazaki iya ba! domin babu wani mahalukin daya isa ya tarewa wani bawa ƙaddarar da Allah ya ƙaddara zata sameshi sabida haka ƙaddarar aurena da humair tun fil azal samammiyace dan haka innah babu wanda ya isa ya gyara abinda Allah ya raba gashi nan se yanzu da lokacin dai daiton yayi Allah ya ƙullah komai cikin nutsuwa".
Mayar da ajiyar zuciya innah tayi.
"To hakane yaro Allah na tuba da wancan kalamin nawa na ɗazu, to amman mai yasa kai lokacin daka ganta da wannan bakai nazarin wani abuba kawai ka saketa sannan mai yasa baka tambayeta akan mai ya kawosa ba? dan kawai kafin ta aureka suna soyayya seya zama cewar da auren nata ma zasuyi kenan? kai ganganci yaro domin zartar da hukunci babu bincike bakaramar illah bane arayuwa hakanan yana kawo nadama mai yawa".
"Wallahi innah sam kaina bai kawo hakan ba se bayan dana rabu da ita sannan naga rashin adalcina nayin biris da bincike akan abinda ya kawo afkuwar hakan amman yanzu alhamdulilahi tunda zata koma ɗakinta".
A ɗage ta dubeshi tana murmushi.
"Amman koda ta dawo ɗin yana da kyau kai bincike akan abinda ya haidar da waccan matsalar domin muddin bakai bincike ba ina mai tabbatar maka da cewa wallahi setaga tafi ta baya illah".
Gabansa ne ya faɗi baki sake kuma yana kallon mahaifiyar tashi.
Ƙarar wayarsace ta dawo dashi a tunanin daya afka.
Bayan ya ɗaga bayani ogansa kemai akan amfa gano ɗayan mutumin nan na naija wanda suke haɗaka da habu ɗan ƙwai wajan garkuwa da mutane, yanzu yana son ya kuma turamai da bayanan cigaban da aka samu anan ɗin.
agurguje yaywa inna sallama ya fita daga gidan ya kama hanyar hotel a daren ranar ya kammala tura bayan sa sannan ya afka tunanin mafita akan umarnin da innah ta bashi wanda zuwa washe gari yagama yanke shawarar zebi komi a sannu har Allah ya bashi sa'a gefe ɗaya kuma ga tarin damuwar kewar yaranshi wanda kullum ya kira sakeena a waya setace mai bata kusa wanda hakan ya kuma hasko mai akwai abinda yaran ke fuskanta game da zaman gidan nasu tare da ita.
MONDAY MORNING.
Cikin shiga ta alfarma ya kintsa kansa kallo ɗaya zakai mai kasan yana matukar farin ciki ayau ɗin amma tsabar basar da abu arai yasa baxaka fahimta ba.
Waya sukai dasu salim suna mai shaƙiyanci wai ungulu ta koma gidanta na tsamiya haka yayta biye musu kafin ya sauka ya faɗa mota seda ya biya gidan innah yay break fast sannan sukai waya da tsoho kakansa wanda yay masa