Showing 54001 words to 54884 words out of 54884 words
Chapter 19 - ZUMA A BAKI! Complet by Autar manya.txt
idda, anan gaban gidansu ta sami wani mai mata da ƴaƴa cikin sati akai bikinsu wanda adaran ranar taci ubanta wajan uwar gidan domin har karyata yaran sukai a hannu sannan kuma mijin baida lokacinta haka ta wanxu cikin kuncin rayuwar datake jin dama ta mutu ta huta, wajan wata guda mijin yay bai kusance taba domin matarsa tafi karfinsa ganin hakan da cutarwa yasa ya saketa takuma dawowa gida cikin rayuwar kunci.
Ahaka nazeer ya waigota shima duniyar ta juya mai domin agarin harkar barikinsa ya gamu da wata iyamura tai mai shegen duka ta karyasa a ƙafa yanzu haka ya nakasa bara yake wannan tasa ya waigo wajan sakina a farko ta bijire amma ganin yadda itama hannunta da ƴaƴan mijinta sukai mata duka ya nakasa yasa ta amince ya aureta suka tare gidan gado inda mahaifin nazeer ya rasu ya bari ɗaki ɗaya suka samu da bayi rayuwa suke a ƙazance da kunci domin abinda zasukai bakinsuma rasashi suke ahaka ta hafi ya mace da nazeer ɗin komai ya juya musu kamar ba nazerr da sakina ba daman haka Allah yake.
Bayan shekaru biyar.
Yanxu haka mun dawo kano da zama ya umar ya sami rufin asirin Allah haka nan ya zama fitila acikin ahalinshi da nawa yarana huɗu abayan su aslam na haifi mai sunan baba da anty, soyayyarsa gareni kullum sabuwace bani da wata matsala da danginshi haka nawa shima, yakai mahahifiyarshi makka tare da babana sannan nima ya kaini Allah yaywa ayiyah rasuwa haka zalika tsoho ma ya rasu rayuwa tana tafiya mana yadda ta kamata anyi bikin anisa kanwata harta haihu nafisa ta kara haihuwa nuratu ta haihuwa sannan kuma maryam ma ta kuma haihuwa.
Zaune nake a babban falona ina taiwa islam faɗa sabida tai latting fita school sabida suna placement ne ta shiga ss1 sallama mai aikina tai tare da cemin hajiya kinyi baki suna karamin falo.
Fita nai na tarar da wata tsohuwar mace baka da wani gurgu suna zaune a kasan carfet.
Zama nai muka gaisa batare danai ƙyamarsu ba,"Mammah sena dawo" islam yarinya mai shekaru goma sha biyu take gayamin.
"To adawo lafiya bakiga baki ba".
Gaisarsu tai ta wuce naga wannan tsohuwar tana bin islam da kallo.
"Islam zo baki gane nine bako?".
Dawowa tai tana ɗan ɗage hancinta gani.
"Islam ina kaninki?".
"Yana madina daddy ya kaisa makarantar haddar kur'an"
Tafaɗa a gajarce.
"Islam nice antynku ku yafen yaran nan dan Allah cutar danai tai muku abaya ita Allah ya nunan domin nai auren mai mata da wata ɗaya ya sakoni harda karayar da ƴaƴansa sukai min wadda ita ta nakasan rayuwa kinga hannun baya sarrafuwa ta sauki inko ya kama min ciwo kamar zan mutu".
Kamar islam zatai kuka tace.
"Na yafe miki mommy mammah ki bata magani na tafi school"
Tafita ta barmu tunda ta soma magana nake mamakin yadda Allah yake ikonsa daman sakinace wannan?
Sautin kukanta ya dawo dani daga tunanina tana kuka tana bani hakuri tare da gabatar min da nazeer atake anan tsoron Allah ya kamani tabbas bazakai sharri kaji daɗi ba haka bazakai alkairi kaji rashin daɗiba yanzu tun aduniya ake sakayya wallahi ba'a bari aje can.
"Nazeer sakina na yafe muku kuma Allah yasa wannan ya zama darasi akaina dama sauran alummah sabida haka kuje na yafe muku".
Na faɗa ina tashi naje ɗaki inata mamaki kayana na hado mata harda na islam dayake tace tana da yarinya sannan na basu kudi kimanin dubu hamsin mukai sallama sunata godiya kamar zasu ari baki
Dawowa nai na zauna aini sakina ta koyan hankali shiyasa tunda na dawo nan ban yarda sabga ta haɗani da kowa ba face mutuncin gaisuwa babban abokina mijina ƴaƴana kawayena.
Koda ya dawo na tareshi da maganar bai wani damu ba haka ya shantakar da abin yana cewa daman ai karshen alewa ƙasa.
Islam kwa data dawo tana basa labari harda kuka rarrashinta yay yana tsokanarta wai mai irin zuciyata.
Kafin ya dawo kaina ya ribacen muyi master room tun a bakin kofa yake faman kissing ɗina tare da ɗagani cakk yay saman bed dani ya shiga ya mutsamin jikina.
"I love you wfy"
Yafaɗa yana kafa bakinsa a na shanuna.
"I love you hubby"
Nima na faɗa ina ɗora a hannuna a lantarkinsa kafin mu lula duniyar ma'aurata
*TAMMAT BIHAMDIHI*
Anan na kawo karshen littafin zuma a baki.
Jigon labarina:
Yarda da ƙaddarah mai kyau da marar kyau sannan kuma sadaukarwa da cin amana wanda yay girma acikin alummarmu.
Uwa uba soyayyar gaskiya wadda tai aiki acikin labarin.
Kuskuren danai ya Allah ka yafen abin da nai dai dai kuma kabani ladan
My fans abinda kuka gani na dai dai ku ɗauka amman abunda kuka gani na rashin dai dai ku watsar!
Allah ka ƙarawa mahaifiyata lafiya ina godiya sosai gareku da jimirin bina daki daki.
Godiya ga wahidin ahadun daya bani ikon rubutun ya kuma haskan tunanin ya kuma bani karfin gwiwa ya kuma buden ƙwaƙwalwa yakuma haɗani da masoya ta hanyarsa nagode maka ubangijina ina rokon ka daka ƙarawa annabin(s.a.w) daraja da wasila da fadila fil jannatul firdausi amin.
End of zuma a baki on sat/25/december 2022.
*AUTAR MANYA*
Marubuciyar.
*MURADIN ZUCIYA*
*TAURARO*
*HASKE*
*RABON WANI*
*KOBA SO*
*ƊAN MAJALISSA*
*DA IZZATA*
*AUREN BARE*
*ZUMA A BAKI*
Sekuma........
*BAƘAR FATA*
Love and romantic story 2022 da yardar Allah ze faso.
BAƘAR FATA
Kalar fatar jikina!
BAƘAR FATA!
Daga fitattu huɗu🔥
BAƘAR FATA!
Launi daga cikin halittta
BAƘAR FATA!
Takun na musammane
BAƘAR FATA!
Hmmm bazance komai ba amman zance wannan karon sekun wanke hannu kun tanadi ruwan ɗumi kusa sabida😜..........
More information akan BAƘAR FATA DAMA SAURAN CHART ME UP! 08142105218
Autarku ce😘