Showing 51001 words to 54000 words out of 54884 words

Chapter 18 - ZUMA A BAKI! Complet by Autar manya.txt

da ita ya mikon koda na duba kayan baccine kala biyar masu shegen kyau, da taimakonsa na kuma shiryawa ina tura mai bakina naya ɓatan kwalliyar ɗazu shima jallabiya ya saka dark blue mai adon golden ɗin zare muka kashe kammu da turare mai kamshi seda muka biya ɗakinsu islam na ɗauko aslam shikuma ya ɗaukota mukayo falo.
Duk inda na gifta domin haɗa mana abinci idanunsa nakaina dayake rigar dana saka irin mai santsin nance mai hannun shimi seta lafe ajikina musamman daga wajan kirjina kuma bawani tsayi gareta ba, domin dukkanta iya gwiwatane.
Seda nai sarving ɗin yara na tura musu gabansu sannan, na juyo kan daddy shima na haɗa mai, sannan na haɗa wani plate ɗin daban.
"Ƙawata"!
"Jeki kira anty tazo muyi dinner".
Na umarci islam, ga mamakina senaga yarinyar ta sauya yanayinta amman bata musamba seta mike.
"My happiness koma ci abincinki".
Ya faɗa cikin kulawa.
Kokarin tashi yake yaje ya kirata na ɓata fuskata tare da danne hannunsa na hanashi tashi da ido na nuna rashin amincewata.
Murmushi ya sakarmin mai ƙayatarwa kana ya zaro wayarsa daga aljihun rigar ya lalubi layinta.
Cike da yanga ta ɗauka batare datai magana ba.
"Ki fito falo muna jiranki".
Yana faɗin haka ya katse kiran wallahi seda naji babu daɗi domin nifa ina da zafin kishi akan abinda nakeso bare na buɗi idanu naga ƙawata a matsayin kishiyata wadda na bawa dukkan yardata.
Idanuna na lumshe batare danai dogon nazari ba hawaye mai ɗumi ya soma zubomin batare dana bari yagani ba.
Tun kafin ta shigo turarenta mai kamshi yay mana sallama gabana ne ya yanke ya faɗi ganin ƴar iskar shigar datai da nononta kamar na bare taci wata uwar vest mai karamin hannu se guntun skirt kanta babu ko ɗankwali.
Agabansa ta tsugunna ta kamo hannunsa ta sumbata sannan ta nemi guri ta zauna a kusada kujerar dayake kenan mun sakashi a tsakiya yara kuma na ɗayan ɓarin.
Bata kalli inda nake ba bare taimin magana.
Murmushi nai mai ciwo rayuwa kenan wai sakina kemin haka amman sena share tashi nai ina rangwaɗa tare da nufar gaban plate ɗin dana haɗa mana abincin na tura mata nata gabanta.
Murmushin mugunta nai tare da cewa.
"Anty sakina ga naki wannan kuma zamuci da daddy".
Nafaɗa ina mai jefa masa kallon da tun ina yarinya idan nai masa shi yake manta dawa yake tare.
Harshena nake juyawa acikin bakina ina ɗan tsotsa kaɗan kaɗan ina kallonsa a shagwaɓe.
Jikina naɗan matsar gabansa ganin yaran sun gama cin nasu har sun nufi gaban tv suna kallon tom and jerry,tattausan hannuna nakai saman sajensa naɗan shafo tare da hura mai iskar dake bakina kaɗan abincin na matsar gabansa sosai, sannan na ɗauki spoon na ɗibo madai daici na soma ciyar dashi, babu shiri yahau amsa yana ci yana lumshe idanu kamar babu halittarta a garemu haka na zage na ciyar dashi wanda rabin soyayyace seda nagama basa sannan nima ya soma bani.
Tunda suka soma soyayyar agabanta taji komai ya fice mata akanta tayaya tai sake humaira ta dawo? bayan tasan daman yadda humaira take a zuciyar umar hawayen bakin ciki ta share amman tunowa da target ɗinta akansu yasa ta saki ranta batare dataci abinci ba ta mike.
"Hy ina zaki kijara nagama bawa beby abincin akwai magana"
Taji muryar umar akanta wadda take rawar jarabar bukatar humaira.
Ba damar musu domin ta tuno matsar jiya dan haka seta tashi tsam ta koma kujerar falo tai kasa da kanta tana nadamar zuci.
Seda na ɓata lokaci ina jansa da soyayya seda na tabbatar kafarta ta gaji da zaman jiranmu sannan na bashi damar mikewa still hannuna na kasan mararshi ina masa tausa wadda yaketa faman miƙa.
A kujera ɗaya muka zauna dashi muna kallonta wadda take kai gaba ɗaya rabin jikina yana jikinsa hannuna yana jikinsa ina mai wasanni.
Lumshe idanunshi yake cike da ƙarfin hali ya dubi yaransa.
"Ku tashi maza aje ai alwala a kwanta a kashe ƙwai".
Ba musu suka mike da sauri na kirasu suna zuwa na ɗaga kowa nai masa kiss sannan nace.
"Ayi balaƙi da nasi maganin miyagu"
Da sauri ta ɗago muka haɗa ido na kashe mata ɗaya ina jefa mata kallon dani kike zancen.
Shiko bai fuskanci komai ba illah murmushin dayay yaran suka amsa dato.
"Mammah"
"Kuyiwa anty sakina seda safe as from to day ta koma anty nikuma mammah kunji yarana?".
Da to suka kuma amsamin sannan suka nufeta sukai mata seda safe amsawar yake tai musu sannan suka wuce.
Seda ya dai dai ta nutsuwar sa sannan ya dubeni.
"Humairah ga sakina nan ku zauna lafiya kece babba amman anan kece karama domin ta rigaki zuwa nan ɗin nasanki bakida matsala dan Allah ku kwantar min da hankalina".
Tura bakina nai gaba naki cemai komi.
Baibi takaina ba.
"Sakina ga matata nan ku zauna lafiya zanyi kwana uku a ɗakinta yakama litinin zaki amshi girkin ki kamar yadda ake kwana uku a ɗakin wadda ba budurwa ba".
Ga mamata nan ta mai maita wannan furucin ya kona ranta har seda ta nuna.mai a yanayin maganarta.
"Ni daman ai bance ba matarka bace Allah kyauta".
"Look sakina bana son dogon turanci nagama magana ta sannan kuma ina miki godiya ga abinda kikaiwa yarana amman komai yazo karshe tunda ga mahaifiyar sunan nasan zata basu dukkan kulawar data dace wallahi kin bani mamaki ban taɓa tunanin zaki haka ba".
Rau rau tai da fuska.
"Kayi hakuri wallahi kuskure nai amman bazan kuma ba".
Tafaɗa ranta a ɓace.
"Babu komai komi ai na rayuwa yiwa kaine".
Yafaɗa tare da kamani muka tashi sallama yay mata muka nufi ɗaki.
Zame jikina nai anasa na raɓe nai bayi nayo alwalar sallar isha wadda banyi ba amman yara sukam sunyi tasu shima yacemin yay tasa awaje.
Na shinfiɗa abin sallah na tayar ina idarwa nai addu'oina na koma na dauro ta kwanciya sannan nazo na wuceshi nai kwanciyata.
Yana zaune saman sopa dagashi se ɗan guntun wando ya biyoni bayan ya gama komai nasa ya kwanta abayana yana gogamin sajenshi a bayana.
Banza nai masa hannunshi yasa ya jawoni.
"Mai akai mikine naga kamar kin sauya".
Doke mai hannun nai na koma na kuma juya mai bayana.
Harshen sa yasaka yana lasar fatar dake bayan kunnena yana min tafiyar tsutsa da hannunshi.
"Bakai kace wai ita na sama a gidan nan na to amman waya fara ɓareka a leda?".
Nafaɗa ina kukan ƙarya.
Jikinsa na wata irin rawa ya janyoni jikinsa akuma rude yace.
"Wato nida ke kamar bansan wayafi kishin ɗan uwansa ba hakika naiwa Allah godiya daya nuna ranar da Aisha take nunan so mai zafi tare da kishi haka nan muka kwanta tare muna faranta ran junanmu tabbas wannan rana ta daban ce, ki ɗauka sakina kamar ƙaddararta ce ta rabamu wallahi inda ina tare dake babu macen data isa ta shigo rayuwarmu amman kaddarar rabuwar mu ta shigo da aurena da waccan badan ina sonta ba kauna zallah ke nakewa ƙanwata ina maki mahaukacin son dayake tafiya da dukkan bugun numfashina"
Yafaɗa yana tura harshensa a cikin kunnena.
"To nuratu fa?"
Nafaɗa a bazata.
Murmushi yay mai sauti.
"Aishata rigima nifa nuratu itake haukan sona ammani nagaya mata gaskiya idan na aureta zumuncinmu xe lalace sabida matiƙar kina tare dani wallahi babu macen dazanwa adalci ki tayani da addu'a naiwa sakina adalci domin harga Allah kece da zuciyata".
Hawayen daɗi na zubo sannan nace to mai tace?"
"Ta fitar da miji nan da two weeks bikinta amman badan taso ba tace ni takeso".
Yafaɗa cikin zolaya.
"Ai seka aureta mayan mata".
Hannunshi yakai saman kirjina yana shafosu.
"Mata ababan sone kokinga laifina amman dai serious nur zatai aure nan da two weeks nima innah ke gayamin domin tunda nai mata maganar bazan aureta ba bata kuma kirana ba".
Juyowa nai ina fuskantar sa.
Nakai hannuna kan kirjinshi na shafo nippy ɗinshi.
"Wai dan Allah bayan rabuwar mu wani hali ka shiga?sannan tayaya kai tunanin mayar dani gidanka? sannan tayaya ka iya sakina duk da tarin son da kake min?".
Haɗeni yay da jikinsa ɗumin jikinmu na kuma haduwa.
"Bayan rabuwar mu wallahi har ciwo na kwanta kafin na dangana da rashin ki kuma wallahi duk abinda nake maki ada kawai dauriya ce amman har ƙasan raina bana so musamman ranar dana koreki kin tuna ranar da kika kawowa yara sabulu munzo hutu wallahi ganin kina kuka nima seda nai ranar seda nasha maganin zazzaɓi sabida damuwar hakan ta haifar min da zazzafan zazzaɓi akanki na daina zuwa hutu kano sannan na zuba securities masu yawa akan shige da ficenki hatta school ɗin da kike zuwa koyarwa na sani ke sau uku maza na biyoki bakya sani nike saka waɗanda kemin gadinki na korarsu, Hatta wannan tsohon nasan da zuwansa kuma dalilin zuwansa yasa nazo kofar gidanku ranar, duk da yadda kema na hango sona a idanunki ranar danaje wani bincike nai shigar mahaukata kokin tuna yadda kikaita kuka akaina? to wannan ma ta karamin ƙarfin gwiwar tunkarar auranki duk da daman na barkine ki ɗan gasu amman daman nasan zan mayar dake domin da shirin hakan nake kwana nake tashi nadai barkine ki gasu da sona kamar yadda lokacin danaga wannan guy ɗin na kasa samun nutsuwa wanda har yau ina hango hoton komi ki dauka kaddara ta rabamu amman bana zarginki da komi face sharrin shaiɗan dayay nasara sarrafa zuciyata a lokacin na sakeki sorry my dear".
Atakaice hatta yadda ya auri sakina seda ya gayamin alokacin na kara shan mamaki da rashin amanar ɗan adam lallai sakina ta nunan darasi arayuwa.
"Wallahi nima banson ina maka mugun soba seda muka rabu kasan nima kullum senai kuka akanka hatta anty tausayina take ji akan yadda taga ina damuwa dakai dayawan tunaninka kai hakuri sharrin shaiɗan yasa waccan lokacin naita munana maka amman wannan karon na shirya tsaf domin neman aljanata".
"Nima ban rikeki ba domin lokacin harda kuruciya akanki sannan nafi zargin akwai mai zugaki domin ada ba haka kike ba".
Ban bashi damar cigaba da maganar ba na jefa bakina ana sa na soma bashi hot kiss mai narkar da zuciyar masoyi.
Ranar mun jiyar da kammu daɗin aure da asuba ma seda akai kafi shayi sannan muka koma bacci.
Tsawon kwana uku muna kashe kammu da love domin ko falo bama fitowa seda ya more missing ɗina dayay wanda kullum buga harka muke ba dare ba rana ba yamma dayake mun shiga week end.
BAYAN KWANA BIYU.
yakama litini makamar aiki da wuri ya mika yara school shima ya wuce office wanda inya dawo ze wuce ɗakin sakina wadda tundaga sau ɗayan nan ban kuma ganinta a gidan ba domin bata fitowa falon.
Tsaf na gama gyara ko ina na gidan na koma ɗaki na gasa cinyoyina domin yadda ya hanani sakat a kwanaki ukun nan, dagani se tawul na fito na kwanta, sabida baccin gajiyar danake ji, jinai ana taɓa kofar ɗakina sena tashi naje na saka key na koma na kwanta banjima ba bacci ya kwasheni.


Umar kuwa sosai ya sami shaidar karin girma tare da karramawa akan aikinsa sosai ya taso gida cikin farin ciki sabida yadda aikinshi yay kyau ma'ana an kama waɗan nan ƴan garkuwar ta dalilin binciken dayay harma an mikawa alhaji wada mai wake yaransa su habu ɗan ƙwai kuma an mika su ga hukuma wannan namijin kokarin da umar yay ne yasa hedqauter ɗinsu ta ƙara masa girma tare da shaidar karramawa harma da hutun sati biyu agida.
Haka ya taso gida batare dayaje dauko yaransa ba sabida lokacin ba,a tashesu a school ba.
Ahanya nekuma alhaji wada ya kirashi bayan sun gaisa yay masa godiya sosai sannan yace yana mai albishir daya basa sabon gidanshi dake kano anan unguwar gaida sannan kuma ya biya masa hajji bana kujera biyu.
Mamakin wannnn kyauta umar yay amman seyay masa godiya ya kashe wayar yanata mamaki daman wannan karon yakeson yasai fili ya soma gini kuma segashi Allah ya kawo masa ta hanya mafi sauki harda kyautar kujerar makka biyu wadda atake anan yay sadaukarwarta ga baba da innah.
Tabbas yasan yaywa alhaji wada kokari akan yaransa amman bai ɗauka zemai irin wannan kyauta haka ba tabbas wasu mutanan sunsan alkairi komai kankantarsa.
Da ɗaukin waɗan nan albishir ya fafari motar yay gidansa.


Nazeer karfe goman safiyar litinin tai mai agarin abuja bayan yaci dogon kudiri aransa kai tsaye a kofar gidan umar ya yada zango.
Sakina dubarar aiken mai gadi tai kafin ta leko ta shigo da nazir gidan sabida bata tunanin umar ze dawo a wannan lokacin.
Ɗakinta takaisa taɗan tura kofar tana masa bayani.
Tunda ta soma masa magana ya kafe da mici micin idanunsa yana ayyana lallai sakina jakace.
Tashi yay tsam ya kamota ya wurgata saman gadon aurenta na sunna yabi ya haye kanta yana lasar fatar wuyanta.
"Lallai sakina ke dabba ce kin manta furucinki na karshe gareni? mai kika mayar dani daƙiƙi koko soko? to yau nazo dominki na dauki fansata wadda naketa shirinta segashi kin bani hanya mai sauki akan ɗaukar tata".
Da wani irin tsoro ta tureshi.
"nazir kana hauka da aurena mai zakai min dan Allah kada ka ketan haddi na tuba dan Allah dan Allah".
Dariya ya saki.
"Hmm sakina mai tsoro ga ban tsoro ke wace irin marar imanine da auranta zaki rabata da yaranta da mijinta akaro na biyu? alhalin ke bazaki iya rike masu suba? au ke kinsan darajar naki auren amman baki san na wani ba kawarki aminiyarki kika yaudara aidaman kinsan karshenki koba afaɗa ba"
"Niba burina nazo nai zina da matar aure ba domin duk barikina nasan gejin yinta nazone domin mijinki yazo ya kamamu ahaka har hakan tasa asirin da kika rufe ya tonu".
Wannan furuncin yay dai dai da lokacin da umar ya shigo gidan ya tura kofar dakin humaira yajita arufe seya nufi na sakina tura kofarsa yay dai dai da sanda yaga katon gardi akan matarsa akuma kan gadonsu.
Jikinsa yana rawa ya bugawa nazer tsawa wadda tasaka nazeer dira daga saman gadon jikinshi yana faman mazari.
Wata shaka yakaiwa nazeer wanda ya kusan kaisa kiyamata kafin ya haɗesu shida sakina yahau jibga abinka da tsohon ɗan tauri gakuma kirar karfi seda ya tabbatar sun daku sannan ya watsosu falo.
Ihunsune ya farkar dani da gudu naja hijabi nai falo ganin yana kokarin kisan kai yasa nasha gabansa.
"Hy umar control your mind sekai kisan kai"


Idanuna arufe seda na bude nai katari da nazeer durkushe bakinsa yana ɗigar jini sakina kau tana kwance tana mayar da numfashi.
Da mamaki na dubesa.
"Nazeer mai ya kawoka gidan nan?".
Da rarrafe yazo gaban umar ya rike mai kafarsa.
"Kai hakuri officer kozaka kasheni wallahi sena faɗi gaskiya.............................."
Komai AtoZ seda nazeer ya faɗawa umar tundaga haduwarsu da sakina da komai hatta kawancenmu kai wani abunma ban sani ba ni kuka ma kasa zuwarmin nai saɓanin ya umar dayake kuka kamar mace.
Kafin nazer ya fito da wayarsa ya kunna recording ɗin daya dauka na makircin datake shirin haɗamin ya kunna afili a wannan karon kuka na saka wato bani da laifine yasa Allah yay gaggawar kawon sakayya domun wallahi inda nazeer bai amsa mata ba da wani xata nemo tunda bata da imani.
"Tayaya rayuwa zatai dai dai bayan na jikinka dashi ake cutar dakai tayaya duniya zatai lafiya bayan zamba acikin aminci yay yawa macuta sun yi yawa maha'inta sunyi yawa tayaya zamuga dai dai bayan muna bakin ciki ga junanmu hassada ƙyashi sun mana katutu ƙawarki aminiyarki kikaiwa haka wadda ta baki dukkan yarda wallahi nai tirr dake daman ina kan binciken silar bayyanar wannan saurayin a kofar gidana sekuma Allah ya sawwaqa komi lallai sakina kin cika macuciya sakamakon cutarki kije na sakeki saki biyu kuma gaki ga duniyar nan".
"Kaikuma kaje idan zaka shiryu ka dai daita rayuwarka kamar kowa kayi idan kuma bazakai ba kaje duniya ce tafi bagaruwa jima".
Gabana nazeer ya nufo yana kuka yana neman yafiyata akan yaudarar dayay min da kuma sanadin kisan aurena na farko.
"Nazeer na yafe maka wallahi kodan namijin kokarin dakaimin kaje Allah ya yafe maka amin".
Da gudu yabar falon yana kuka.
Itako sakina wata janyowa umar yay mata ya wurga waje bayan ya naɗa mata matsiyacin duka babarta ya kira awaya ya sanar mata sannan ya kira innah yana kuka yana shaida mata.
"Hmm yaro kenan aini tun ranar da humaira tabar gidan nan naji komi abakin sakinar inda take gayawa humaira bata san ina jiyosu ba wallahi yaro abin yay min zafi karka manta wannan dalilin yasa nace maka kaita bincike domin ni babbace bazance komi ba to Allah yasa rabuwar takuce tafi alkairi".
Tafaɗa sukai sallama.
Zubewa yay agabana yana kuka a saman kafafuna.
"Dan Allah ki yafan aisha ban kyauta ba nai aiki daka ashe makashinki yana tare dake amman why baki taɓa sanar dani ba?".
Nima zubewar nai gaban sa ina kuka na cusa kaina a kirjinshi
"Allah na barwa nake addu'a gashi nan cikin sauki ya bayyana gaskiya karka damu daman rayuwar ta gaji haka ba,a taɓa samun nasara se an fuskanci kalubale nagodewa Allah dayasa tafiyar batai nisa ba da tuni an cutar dani fiye dana baya".
Rungumeshi nai mukai ɗaki na taimaka mai yay wanka har lokacin ransa yana ɓace.
Da dubara nake jansa da hira anan yake shaidamin abinda ya faru gareshi fatan alkairi nai masa tare da mikewa na fita na gyara falon na wuce kicin raina fess.
Tsahon kwanaki rayuwa muke mai cike da farin ciki kayan ɗakin sakina yasa an fitar dasu ɗakin ya koma nawa nasa kuma ya zama nasa kenan sekuma na yara.
Kwanci tashi har nai wata biyu agarin abuja maryam ta haihu bai barni naje ba haka akai bikin sadiya nanma ya hanani zuwa nuratu kam abuja aka kawota da zama kusan kullum ma muna tare domin tana yawan zuwa nikam tunda na koma banzo kano ba sabida yanayin danake fama dashi na juna biyu.
Bayan wata biyar.
Sakina kam da barance ta sami kudin motar kano gaba ɗaga rayuwa ta juya mata tai danasanin cin amana domin bata kwashe mata da daɗi ba agidansu kuwa uwarta tai mata tass takuma ce sedai ta bar mata gidanta da ƙyar makota suka saka baki ta zauna sedai abincin dazata cima setai wankau da gogau take samu takai bakinta.


Gaba ɗaya ta koma wata iri ta rame ta fige ta ƙanjame tai bakikkirin kamar gawayi kamar ba sakina yar gayu ba nadama kam tayita takuma la'anci sharrin shaiɗan daya ƙawata mata mijin kawarta ta aura gaya nan tana girbe abinda ta shuka.
Cikin haka babarta ta soma yi mata zancen aure domin tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login