Showing 27001 words to 30000 words out of 117648 words
Chapter 10 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
cikin da ya murd’awa Muneerah cikin dare da misalin Sha biyun dare ne ya sata fitowa daga bedroom d’insu don ta samo magani a first aid box da yake d’akin Amminsu.
Kasancewar dare ne kafin ta murd’a k’ofar d’akin ta ji sautin muryar Ammin da alama waya take jin tana kiran sunan Hamda yasa ta dakata da bud’e k’ofar ta kara kanta sosai a jikin k’ofar sai taji Ammin ta cigaba da cewa “Kin san sarai ta yarda aka samar da yarinyar nan? Ta yaya kike tunanin hankalina zai kwanta idan ban kawar da ita ba, duk ranar da Umar ya san maganar nan na ha’intarsa da nayi ha’inci mai muni ina tabbatar miki Mami ba zan kwana da igiyar aurensa ba, don Allah Mami ki nemar min mafita wallahi kaina ya k’ulle, na rasa yarda zan yi, don na lura yaron nan bai k’i ya fallasa sirrin nan ba ko da shi zai kwana a ciki, na tabbata akwai abinda Hammad ya taka shirunsa ba yana nufin ya hak’ura bane musamman da na san ya kwana da sanin cewa ni na turo mutanennan suka yi masa duka cikin dare.......
Wata irin hajijiyace ta fara d’iban Munirat ji da ganinta duk suka d’auke na wuncin gadi, a take ta kurma wani uban ihu........✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
Jikar Nashe//
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE
(Mai tak’ama da ikon Subhana)
YA ABIN YAKE?
08033748387
Follow me on ArewaBooks
@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e
On Wattpad @Nazeefah381
Last free pages.
15
✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
__________________________________
Da sauri Sakina ta fito daga bedroom d’inta, hankalinta a tashe dafatan Munira bata ji abinda take cewa mahaifiyarta a waya ba.
Turus tayi ganin Muniran a k’asa tana dafe da gwiyoyinta hawaye shab’e-shab’e a fuskarta, alamarta ya nuna kamar fad’uwa tayi. Sakina ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Ke kuma lafiya cikin darennan kike kurma uban ihu?” Munirat ta tattaro duk wata nutsuwa Ta saka a fuskarta, bata son Ammin ta fahimci ta ji zancen da take, ta san idan har ta gane zata iya d’aukan ko wane mataki a kanta, don haka murya na rawa ta ce “Ciki na ke azabar ciwo, kuma na zo amsar magani sai na zame anan.” Ammi ta saka hannu ta mik’ar da ita had’e da fad’in Ayya muje ki sha maganin to, ko dai period pain ne?” Ta girgiza kai jikinta a salub’e, kafin ta bi bayan Ammin zuciyarta na sake mamakin halayyar Ammin.
Tana shan maganin tayi saurin ficewa daga d’akin, nutsuwa take buk’ata gami da dogon nazari akan maganar nan da ta jiyo, tabbas biri yayi kama da mutum, amma waye uban Hamdan shine abinda ta kasa ganewa.
Ta dad’e tana juyi a saman gadonta dafatan barci ya kwasheta amma ina wannan dare kam tuni suka yi hannun riga da barci, ciwon cikin ma tuni ta neme shi ta rasa, k’wak’walwarta ta tafi dogon nazari, tunaninta ya tsaya cak zuciyarta na wani irin bugu bata son abinda take tunanin ya tabbata, bata fata ko kad’an idan hakan ta kasance ba Ammi kad’ai ba su kansu abin kunya ne a wajensu.
HAMMAD zuciyarta take ta bata a matsayin uban da yayi cikin Hamda, idan ba haka ba me zai saka y’arsa tayi kama kwabo da kwabo da Hamda, kamar da kana gani ko ba’a fad’a maka ba zaka san sun had’a jini d’aya. Ta runtse idonta wasu hawaye na zubo mata, ya zama dole ta fallasa sirrin nan, ko Ammi Ta hankalta ta nemi tuba ga Allah, Sannan zuciyarta itama ta huta da dogon tunani, idan ba haka ba kuwa tabbas zuciyatta zata buga. Ranar dai kam akan idonta aka yi kiran Assalatu abinda bata tab’a yi ba kenan a rayuwarta.
_________________
Sukuku ta tashi da safen, duk da barcin da yake rinjayar idonta, amma ba zata iya yi ba, Neman wanda zata tunkura da zancen take direct zuciyarta ta amince ta jewa da Anty Lauratu da zancen idan yaso ta gaya mata kada ta sake ta ce ita ta gaya mata.
Ko da ta fito parlour suna zaune suna karyawa gudun kada Ammin ta jefa ayar tambaya a kanta yasa ta zauna ta fara tsakurar abincin, tana turawa da kyar kafin ta mik’e tana zarar tissue, Ammi ta kalleta “Ke kuma sai ina ina ce yau baki da
Lectures?” Munira tayi saurin girgiza kai tana gyara farin glass d’in da ke idonta ta ce “Ammi ina da group discussion amma ba zan dad’e ba zan dawo.” “Ai shikkenan ki dawo da wuri don mu zamu je gidan Kady yayunki suna da bak’i kuma kin san bana son barin shiyyata ba kowa.” Da sauri ta d’aga kai tana ficewa daga parlourn tana jin Najma na cewa ta tsaya tayi dropping d’inta a motar Ammi amma ta zura da gudu, gwara ta shiga napep ba ta san kowa ya san inda zata, musamman Lauratu da bata shiri da Ammi, shi yasa ma Ammin bata bari suje gidanta.
A bakin gate d’in gidan mai a daidaita sahun ya ajiyeta ta zaro d’ari biyar ta bashi kafin Ta saka kai Ta shige had’e da cewa ya bar canjin.
Lauratun ce kawai a gidan duk yaran sun tafi makaranta, dama babbar y’arta sa’ar Hamda ce. Cikin mamaki take kallon Muniran ta ce “Ikon Allah yau kece a gidan amma dai Sakina bata san nan kika zo ba? Kuma fa yanzu da kika ganni mayafi nake shirin yafawa yau nace a wajen Didi na zan wuni”
Munira murmushin yak’e ta saki kafin ta ce “Ya naji gidan shiru?” Lauratu ta ce “Wa zaki samu duk sun tafi school daga ina haka?”
Tana murmushin ta ce “Daga gida mana” Lauratu ta sake gyara zama ta ce “Amma dai ba lafiya ba? Don haka kawai Sakina ba zata bari kizo gidan nan ba, haka kawai ta cusa muku k’iyayyata.” Munira ta ja fasali kafin ta ce “Wallahi, Amma ba k’alau ba wata gagarumar magana ke tafe dani amma ban san ta yarda zaki d’auki abin ba, ko ma ta yaya kika d’aukeshi please kada sunana ya shigo.” Nan ta shiga bata labarin da ya hautsina kayan cikin Lauratu kafin ta gama kuwa gumi ya jik’ata sharkaf duk da sanyin a.cn da yake parlourn, hankali tashe ta mik’e tana struggling a parlourn ta ma rasa abin cewa illa zuciyarta da take wani irin duka, fatanta da burinta a lokacin kada Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya, duk da komai ya nuna kansa k’uruk’uru tun a lokacin da ace sun kasance mutane masu tsinkaye da sun fahimci abinda yake tsakanin Sakina da Hammad, kafin cikin Hamda ya bayyana, me yasa idanunsu suka rufe suka kasa gano dalilin takun sak’ar Sakina da Hammad, lokaci d’aya yaron ya juye ya zama mai bak’ar zuciya, ya kuma tsani had’a inuwa d’aya da Sakina Why? Lauratu ta fad’a da k’arfi had’e da rotsa wani verse da yake gefe a fili ta furta tabbas Sakina ta cucemu idan har hasashen mu ya zama gaskiya, tayi wa zuri’ar d’an Borno mummunan tabon da zai bi mu har kan tattab’a kunnenmu a ina aka tab’a yin haka?
Ganin yarda hankalinta ya tashi ne ya kad’a hanjin cikin Munira, sam ta manta zafin ran k’anwar ubansu Lauratu, me ya kaita zuwa ta bayyana mata wannan gungumemen sirrin? Cikin rawar murya ta ce “Please Amma, don’t include my name, don Allah.” Ta fad’a tana durk’ushewa a gabanta hannayenta a had’e alamar rok’o. Fuska ba annuri Lauratu tayi mata wani irin kallo kafin ta mik’e ta zari Car key, da wata iriyar murya ta ce “Ba abinda zai saka ni fad’ar sunanki, amma am sorry to say ba abinda zai hanani tonawa Sakina asiri yau, sai dai idan kafin na k’arasa gidan na mutu.”
Gaban Munira ya shiga duka, ganin har Lauratu ta kira Umma Asma’u ta rattaba mata bayani, kasancewar ita a dubai suke zaune da yaranta da mijinta ba damar ta zo ji tayi kawai Umma Asma’un ta saka kuka tana fad’in “What a nonsense Lauratu?” D’if ta kashe wayar ta mayar da kiranta kan Gadanga, kafin ta kira Babansu Hammad ta ce tana da meeting da su a sashen Didi kuma urgent ne, hankali tashe duk suka dinga barin wajen aikinsu, suna tafiya gida.
A hanya ta sauke Munirat “Ki wuce School kamar yarda kika sanar mata, ba zan ce ke kika gaya min ba Allah yayi miki albarka.”
Munirat jikinta a sanyaye ta fice daga motar, tana fatan Allah yasa ba gagarumar matsala ta janyo a familynsu ba sai yanzu take da na sanin fitar da maganar da Ta sani barinta tayi a ranta ko da zata zama ajalinta.
⭐️
Kamar an jehota haka ta shiga b’angaren mahaifiyarta Didi, tana zaune da casbaha a hannunta tana latsawa, idanunta akan a k’warin talabijin tana kallon tashar Saudi Sunna, kasancewarta masoyiyar madinatul munawwara, girgiza kai kawai take tana sauraran hadisai tamkar tana gane larabcin da suke yi.
A fitgice ta d’ago tana zube idanunta a kan Lauratu y’ar autarta, cikin masifa ta ce “Amma Lauratu baki da hali ko kad’an wallahi, fisabilillah banda rana ce b sai nace gamo nayi ba ki shigo min haka bagatatan ba sallama, haba kina girma kina cin kashi, wallahi sai da gabana ya yanke ya ce ras Allah ya raba mu da mugun halinki Lauratu.”
Da Didin ta dubi yanayin fuskarta da bata cigaba da kwararato ba, sai da ta dasa aya sannan ta d’ago tana duban idanun Lauratun da suka yi jajir kamar gauta, da sauri ta ce “Hasbunallah, Allah yasa
Dai ba mijinki bane ya sako ki.”
Lauratu ta ja ajiyar zuciya kafin tace “Gwara min ace sakina yayi wallahi, da wannan gundumemiyar masifar da ta tunkaro mu.” Tuna k’irjin Didi ya shiga luguden daka jin zancen Lauratu wace masifa ce da har ta fi saki? Ta jefawa Lauratun tambaya ba tare da ta shirya ba, Lauratu ta saka gefen mayanfinta ta goge hawayenta, Didi ta ja tsaki shikkenan ta faru ta k’are Wata yayi wa ciki, ya tafka miki tsiyar halin mazan kenan? Ko kuwa Kishiya zai yi miki?” Tsaf Lauratu ta shanye kukanta tana girgiza kai ta ce “Wallahi, duka Didi gwara wannan akan masifar da ta tunkaro zuri’armu ta D’an Borno.” Kafin kace me sai ga Didi ta shige toilet da sauri saboda juyin da cikinta yayi, anya Lauratu tana cikin hankalinta kuwa? Ta dad’e a toilet d’in kafin ta fito tana yarfe gumi ta kalli Lauratu “Kinga Lauratu tun muna shaida juna da ke ki gaya min me ya faru? Kafin ki kaini gadon asibiti.” Lauratu ta shiga dube-dube kafin ta ce “Ina Hamda?” Didi ba baki sai d’akin Hamda data nuna mata, Lauratu ta saka baki ta k’wala mata kira, sai ga Hamda ta fito da sauri, don ta san Amman tasu bata son jira.
Ido kawai lauratu ta tsira mata ba tare da amsa gaisuwar da take mata ba, ta ce “Kirawo min d’iyar Hammad, Kamla.” Hamda da sauri ta koma d’aki don can ta baro Kamlan tana game da sabuwar wayar da zunnuraini ya kawo mata.
Kamo hannunta kawai tayi suka taho parlourn, Lauratu ta k’ura musu ido tana sake jin fad’uwar gabanta na k’aruwa kafin ta ja fasali ta ce “Didi k’ura musu ido ki gano min ko akwai banbancin da ni na kasa ganowa.” Tsaki Didi ta ja kafin ta ce “Kaji min zancen banza, da wofi to tun yaushe ake fad’ar kamanninsu, wani abu ne don ta yiyo kamannin k’anwar ubanta, bana raba d’aya biyu a can ahalina na farko sai kayi shishshigin d’ebo kamannin wani, wanda ba mamaki tun tale-tale kafin a haifeni ma suka zo duniyar suka yi rayuwarsu suka koma, shine Me don Hamda tana kama da Kamla?”
Dai-dai lokacin Abbu da Gadanga suka shigo, ido suka zubawa Lauratu don duk hankalinsu a tashe suka taho, sun zata wani abin ne ya samu Didin, ita d’in ma ido ta kafa musu kafin ta ce “Kuyi hak’uri na tasoku rana tsaka, wani abu ne mai firgitarwa yasa na fito da ku daga office, Yaya ka dubi Hamda da Kamla ka gaya min akwai banbanci a zubin halittarsu.” Ta fad’a tana kallon Gadanga, da yayiwa su Hamda k’uri da ido, sai kuma ya girgiza Kai, “Sam ba wani banbanci sai yau ma na sake tabbatar da zahirin kamanninsu da ake ta fad’a a dangi, wani abu ne ya faru?” Girgiza kai tayi kafin ta ce “Hamda ku shiga ciki.” Suka wuce
Kuwa suka shiga duk da Hamda hankalinta ya kasa kwanciya, sai da ta rab’e jikin k’ofa.
Lauratu taja ajiyar numfashi kafin ta ce “Abbu Kayi hak’uri da abinda zan fad’i amma Hamda ba y’arka bace, y’ar Hammad ce!
Kafin tayi aune suka ga Didi tayi wani irin mik’ewa ta kai mata damk’a cikin matuk’ar tashin hankali, da sauri Gadanga ya rik’ota yana k’ok’arin zaunar da ita ta fisge jikinta “Bar ni Gadanga barni in shak’e yarinyar nan ta mutu na daina jin wannan zantukan banzan, mu zata b’atawa sunan dangi wace irin maganar banza ce wannan?”
K’arar da suka ji da fad’uwa a k’asa ne yasa suka bazama ciki. Hamda suka gani kwance a corridor ba alamar numfashi tattare da ita hakan ya tabbatar musu da taji zantukan da suke fad’a. Didi ta saka salati tana b’allawa Lauratu harara “Shikkenan kin yi kisan kai, na tabbata yarinyar nan ta ji wad’annan banzayen zantukan naki to wallahi ba zan rufa miki asiri ba, y’an sanda zan kira yanzu su gark’ameki.” Gadanga dai bai ce komai ba ya d’aga Hamda cak ya shigar da ita cikin bedroom ruwa ya shafa mata kafin ta kawo gauran numfashi. Idanunta a runtse ta damk’i hannun Gadangan fad’i take “Baffa da gaske ne abinda kunnuwa na suka jiyo min? Da gaske ne ni y’ar Yaya Hammad ce ba y’ar Abbu ba?” Gadanga ya share zufar da take karyo masa don shi dai a hasashensa akwai k’amshin gaskiya a zancen Lauratu, baya son ya gasgata ne gudun afkuwar wata matsala. Ya kama hannunta duk da idanunta a runtse suke ya ce “Ba gaskiya bane ki kwantar da hankalinki, ba ta yarda za’a yi labarin nan ya zama gaskiya, kina jina?” Hawayen ta share da kyar ta d’aga Kai, shi kuma ya mik’e ya fita parlourn jikinsa a salub’e, gaba d’aya gwiwoyinsa sun sare da kyar yake jansu kada Allah ya tabbatar da wannan zancen na lauratu a bigiren gaskiya.
Zaune ya samesu jigum-jigum banda Didi da take ta yiwa Lauaratu masifa kamar zata cinyeta, ita kuma Lauratun ta kafe akan abinda take fad’e gaskiya ne, Abbu dai yana zaune kansa a k’asa shi kad’ai ya san halin da zuciyarsa take ciki a lokacin bai k’i Allah ya d’auki ransa ba kafin tabbatuwar lamarin a bigiren gaskiya. Idanunsa sun kad’a sun yi jazur, fuskarsa kuwa tamkar bai tab’a dariya ba tunda aka halicceshi, kan nasa a sunkuye ya d’ago yana sauke ganinsa akan Lauratu kafin su ji ya ce “A ina kika ji maganar nan?” Lauratu da ta tsorata da ganin yanayinsa musamman yarda ya tsatstsareta da manyan idanunsa da suka jirkita suka koma mata wani iri murya na rawa ta ce “Wallahi ina zaune a gida Munira ta zo ta same ni da zancen..........” kafin ta gama bada labarin tuni zuciyar Didi ta daina aikinta yarda ya kamata fata take ace mafarki take ba gaskiya kunnuwanta suke jiyo mata ba. Shi kuwa Abbu gaba d’aya yaji ana wata irin hajijiya da shi kafin ya kalli Gadanga ya ce “Ka kira min Sakina da Hammad ka kira kuma Sadiya.” Daga haka ya mayar da kansa jikin kujera ya runtse ido da gaske duk da a zaunen yake jinsa yake kamar zai fad’i wannan wace irin masifa ce tayi musu dirar mikiya a zuri’ar D’AN BORNO? Tambayar da yakewa zuciyarsa kenan da yaji tayi masa nauyi kamar Dutse. Didi kuwa bata uhm bata uhm-uhm sai wani irin kallo take bin lauratu da shi tana tunanin anya kuwa Lauratun jinin ta ce da suka haifa ita da mijinta Usmanu? Ban da a gida ta haifeta tabbas da tace an musanya mata Lauratu, saboda halayenta kaf ya sha banban da na yayunta, duk da bata tantama nata halayen ta d’ebe kaf har ma tana tunanin nan gaba kad’an zata shanyeta.
Mahmah ce ta fara zuwa jikinta a sanyaye ta shigo tana mamakin dalilin wannan zaman da rana tsaka gagal haka, bata ce komai ba ta zauna tana amsa gaisuwar Lauratu da ta ganta tamkar a firgice.
Ita kuwa Sakina (Ammi) da sak’on ya sameta wata iriyar mummunar fad’uwar gaba ce ta sameta hakan ya tabbatar mata koma kiran menene ba alheri bane. Jiki na rawa ta mik’e tana lalubar mayafi don ta san bata da damar da zata kaucewa kiran Didi.
Hammad ya rigata zuwa, shigarta parlourn ta hangoshi zaune kan kujera duk da a yanayi na rud’ani yake ba zaka tab’a gane hakan a tare da shi ba, ya san za’a rina ya kuma san irin wannan ranar ko mu dad’e ko mu jima zata zo, ranar da yake mafarkinta yau ga shi ta zo ko da wani ido Sakina zata dubi mutanennan ta basu labarin abinda ya faru? Ya sauke gwauran numfashi lokacin da yaci karo da fararen k’afafun Sakinan tana shigowa falon, sune dai wad’ancan fararen k’afafun da ba zai tab’a manta a yanayin da ya gansu ba a wancan lokacin, ya runtse ido bayan ya hango shigowarta tana taku tamkar bata son taka k’asa haka halittarta take tun fil’azal Sakina mai yanga ce. Tabbas yau zai fito ya fad’i Gaskiya ko ya huta da bak’in cikin da yake kwasa a zuciyarsa shekara da shekaru.
Tun kafin ta k’araso taji kanta ya sara ta tabbatar kuma wannan zaman ba na lafiya ba, Allah dai yasa zaman ba akan wancan b’aragurbin k’wan bane da idan ya fashe warinsa sai ya addabi duk wani ahalin zuri’ar d’an Borno zai kuma girgizasu matuk’a da gaske.
A can gefen Abbu ta zauna duk da tun da ta shigo bai d’aga kansa ba. yanzun ma bai d’aga ba ya tabbatar dai itace tun bayan da
Ya shak’i k’amshin turarenta.
Shirun da yaji gurin yayi ya tabbatar masa da cewa ba za su iya tunkararta da zancen ba, hakan yasa kansa na k’asa cikin wata iriyar murya da sam ba tayi kama da ta Abbun ba saboda kaurinta da bud’ewarta ya ce “Sakna ina so ki fad’a min Hamda y’ar waye?” A firgice ta d’ago ta