Showing 18001 words to 21000 words out of 117648 words

Chapter 7 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

mai gajeren hannu, wanda ta bayyana damtsen hannunsa da gashi ya kwanta luf a jikinsa.




A gefen Didi ya zauna yana gaisheta cike da Kamala, idanunsa akan coolers d’in da suke zube bisa daddumar, dama ji yake kamar an wawashe masa kayan cikin sa kaf, ko don daga training wanka kawai yayi ya taho nan wajen Didi, kamar yarda ya saba tun a da, in dai Didin tana nan da safe nan wajenta yake karyawa.


Cup kawai suka ga ya d’auka ya fara tsiyayyar kunun da yake cikin flask d’in sai zabga k’amshi yake na lemon tsami da kayan k’amshi. Da turirin da komai ya kai bakinsa, har hakan ya ba Hamda mamaki ganin yarda yake cin k’osan da zafinsa cikin hanzari ko ta kan Irish d’in bai bi ba. Haka dama shi yake cin abincinsa a hanzarce musamman idan yana jin yunwa, shi yasa yake da k’akk’arfan jiki kuma ginanne mai d’auke da murjajjiyar fata.


Tsaki Didi tayi tana harararsa “Ni fa Hammadu bana son iya shege, waye ya gayyato ka nan kake shirin cinye mana abinci? Shi yasa ga kanan a tsaye k’ik’am da kai.”


Fuskarsa ya d’aure sosai kafin ya ture kwanan k’osan cikin fad’in “Alhamdulillah” Didi ta saka salati bayan ganin ya wawashe k’osan tas guda biyar kacal ya bari.


Murmushi ya sauke a fuskarta ya ce “Kin san rabona da irin abincin nan kuwa?” “Ina zan sani tunda ni ba Allahn musuru bace, kawai ka zo ka wawashe k’osan nan yarinyar nan ko ci ba tayi ba, tun safe take aiki akan digadiginta, ina ruwana y’ar uwarka ka cuta don wannan biyar d’in dai ba bata zan ba wallahi.” Ta fad’a tana dangwalar yaji ta cinyeshi tas.


Hamda mik’ewa tayi ta shige d’aki don dama ita ba gwanar karya wa bace da wuri. Yabi bayanta da kallo cike da tausayinta sai ji Didi tayi ya saki ajiyar zuciya ya ce


“Har yanzu uwarta bata karb’eta a matsayin y’a ba tamkar sauran y’ay’anta?”


Tsaki Didi tayi ta ce “Yaushe zata karb’eta ai Umaru ya cuceku da ya auro muku jahila, wannan zuwan ma da nayi haka na zo na tarar da ita a galabaice ciwon sanyi ya kwantar da ita, saboda tsabar aikin azaba da take bata. Allah wadaran dai Halin Sakina mai farar fuska bak’ar zuciya.”


Shiru Hammad yayi duk da fuskarsa ta nuna zallar b’acin rai bai ce komai ba, ya had’iye abinsa had’e da mik’ewa, ganin Didin na hamma alamar barcin hantsi take buk’ata.


Ko da ya koma sashensa, tararwa yayi su Nanna har sun shirya, gidansu zata je kuma ta rok’eshi kwana biyu zata yi da yaran gaba d’aya.


Mahaifiyarta Yayar Sadiya ce (Mahmah) uwa d’aya amma uba kowa da nasa. Ita dangin nata mahaifin a gwarzo suke ita kuma na Mahaifiyar Nanna anan Kano suke.






__________________________


Yana kwance a parlourn da yake b’angarensa yaji ana buga k’ofar da k’arfi tamkar za’a cireta.


Rintse ido yayi sam baya son tashi daga kwanciyar da yake, amma ya lura koma waye a uzurce yake daga yanayin bugun na rashin nutsuwa.






“Waye?” Ya fad’a cikin cunkusashshiyar muryarsa daga can b’arin aka ce bud’e ka gani”


Ba zai manta muryar ta ba, muryar shaid’aniyar matar nan ce k’awar Sakina wato Kady, ba zai manta wancan lokacin ba, da tare suka aikata abinda har yau yak’i barin zuciyarsa ta huta , bisa son zuciyarsu suka kuma buk’aci tilas ya rufa musu asiri.


Fuskarsa ya tamke sosai kafin ya bud’e mata k’ofar, don a shirye yake wannan karan ko da mai suka zo ya shirya karb’arsa.




Kallon-kallo suka shiga wurgawa juna bayan ya bud’e k’ofar, Mamaki ne ya kama Kady ganin yarda Hammad d’in ya zama wani ingarman namiji, kamar ba yaronnan da shekarun baya suka.....


Tayi saurin katse tunaninta ta hanyar sake kallon fuskarsa, sai taji tana shakkar zancen da tazo masa dashi, da alama bata tsammaci ganin sa haka ba, cikakken namiji da yake tashe da k’arfi da lafiya, daga yanayin fuskarsa ta san wannan karan ba zai d’au rainin hankali ba.


Da baya da baya ya juya cikin parlourn, wannan damar suka samu suka rufa masa baya.


Tuni har ya zauna kan kujera yana murza goshinsa da d’an yatsa, hakan ce take kasancewa a duk sanda ya kai matuk’a a b’acin rai ko tashin hankali.


Tsawon lokaci parlourn ya samu bak’uncin shiru, su sun kasa magana saboda yarda yayi musu kwarjini a parlourn, shi kuma ya runtse idonsa saboda sam baya son yayi ido da ido da su, ji yake tamkar ya shak’esu ya kashe su ya huta.


Idanun nasa a runtse ya ce “Me ke tafe da ku? Ko kuma kun zo kuyi abinda kuka saba ne?”




Da sauri Ammi tace “Subhanallah, ko d’aya wallahi, wancan karanma kamar yarda na gaya maka wallahi sharrin shaid’an ne. Don Allah ka manta ka d’auka ma kamar ba a yi ba wallahi rud’in zuciya ne da son haihuwar d’a namiji ta kowane hali.”


Idanun nasa a runtse yake sakin wani murmushi da kai tsaye zaka kira shi na takaici murya a kaurare ya ce “In manta da abinda ya faru fa kika ce? To idan na manta ita kuma yarinyar a wani mizani kuka ajiyeta? Ya zaku yi ku fahimtar da mutane cewa bata da gadon Abbu, a lokacin da ya rasu? Ko kuwa kuna son nayi shiru Allah ya kamani da laifi?
Dole ne ko ba yau ba in sanar da duniya wannan bak’in labarin.” Har zuwa lokacin da ya kai aya, idanunsa still a lumshe suke amon muryarsa ne kawai yake tashi a parlourn cikin isa da ginshira. Ammi ta kalli Kady kafin tayi mata alamun kinga taurin kansa ko? Jin shiru basu ce komai ba, ya bud’e idanunsa ya sauke su akan Ammi. “Yanzu yarinyar nan kina so kai tsaye na b’oye gaskiyar lamari a dinga kiranta y’ar Abbu alhali ni da ke mun san ba haka bane. Wannan karan a shirye nazo zan fallasa sirrinki, in huta da abinda ya tokare min k’irji shekaru da shekaru ko da kuwa Abbu ba zai yafe min ba........


Da sauri Ammi ta katseshi ta hanyar durk’ushewa a gabansa gwiwa bibbiyu “Don Allah kada kayi min haka Hammad, kamar yarda kace yarinyar zaka duba, zaka shafa mata bak’in paint mai wuyar gogewa.” “Kina son kice min kina son yarinyar da tun farkon haihuwarta kika nuna mata tsana muraran, yarinyar da kika so hallakarwa banda da kwananta a gaba, yarinyar da kike gallazawa tamkar ba jininki ba? Yaushe kika fara Sonta? Yaushe kika daina cutar da ita? Yarinyar da tun tana jaririya kika so mutuwarta akan wanzuwarta a duniya, yarinyar da ba kya son farin cikinta, ko ba ke na kama da shinkafar b’era zaki bata a tea ta mutu ki huta ba, saboda nayi shirin fallasa sirrinki kika min asirin da na gwammace nayi rayuwa a birmingham fiye da k’asata Nigeria Am sorry to say wannan karan ba gudu ba ja da baya wajen bankad’uwar sirrinki ko da hakan yana nufin kaf zuri’ar D’an Borno zasu d’ora min laifin akan rashin sanar da su da wuri, na kuma shirya karb’arwa yarinyar nan y’ancinta ta kowane hali.”
Ya fad’a yana bud’e idanunsa da suka kad’a suka yi jajir, ya zuba su akan fuskar Sakina da take durk’ushe a gabansa, idanunta ta sauke k’asa ruwan hawaye na ambaliya a saman k’uncinta.


Kady ce ta ja wani wawan tsaki ta mik’e had’e da janyeta. “Mik’e yaje ya gayawa duk uban da zai gayawa, sai me? Idan kika tubure ubansa ne yayi cikin akwai yarda za’ayi dake ne? Idan ma ya fad’a dole shima Za’a tuhumeshi....” haka tayi ta masifa kafin su bar parlourn da sauri, kana ganinsu ka san a hassale suke. Allah yaso gidan ba kowa Mahmah tabi su Nanna gidan iyayenta, ita Didi sun tafi asibiti ita da Hamda. Don haka suka samu wannan damar suka shiga wajen nasa.


Ya dad’e yana cizar leb’ensa na
K’asa kafin ya furzar da wani hucin numfashi ya mik’e. Wanka ya shiga yana fitowa kuma yayi shirin zuwa gaida surikansa, Gidan su Nanna.








_______________


Kady a zafafe ta sake duban Sakina kafin ta ce “Wallahi kina so ko ba kya so sai an kawar da wancan banzan a doron k’asa, don na lura da shirin tozartaki yazo, kina ganin yarda yake cika yake batsewa idan ya san wata ai bai san wata ba shashashan banza, ba dai kince yarinyarsa da ita take kama ba?”




Sakina ta runtse hannayenta kawai kafin ta ce “Ban so zata kaimu ga jallin kisan kai ba, amma idan haka ne mafita ba yarda zamu yi, sai dai zamu aikata hakan ta hanyar da ba za’a saka mana zargi ba, wacce hanya kike ga zamu bi.”
“Kunce burkin motarsa da k’usoshin tayar motar ta hanyar had’a baki da ma’aikatan gidan nan ko mak’udan kud’i sai mu shak’a musu.........
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe.


YA ABIN YAKE?


08033748387


Wattpad muna page 13




Follow me on Wattpad


@Nazeefah381






✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
11




*******************************


Idanunta jajir ta sake zubesu a fuskar kady “Wallahi har ga Allah bana son kalmar kisan nan ba yarda zan yi ne tunda ya riga ya kafe ne, tun yana shekarun yarinta dama yaron nan kafiya ce da shi da d’an banzan taurin Kai.” Kady ta ja tsaki kafin itama cikin takaici ta ce “D’an banza kina kallon yarda ya rufe ido yana magana a gadarance alamar ko son magana da mu baya yi, ni fa da zaki bar ni da kaina zan aika da shi lahira amma tunda kina tsoron kisan bari mu bi ta yarda kike so, zan
Aiko masa da fataken dare su ja masa kunne na k’arshe idan ya k’i yarda kuwa wallahi zai gane kurensa.”


Sakina ta d’an ja fasali kafin ta ce “Shikkenan, Allah yasa mu samu nasarar hakan, matsaloli sun yi min rufdugu a kaina, ga matsalar yarinyar nan da matar can ta saka musu ido akan lallai sai sun fitarda
miji, ga matsalar nan da muke ciki.


Kady ta dafa kanta murya a
raunane cike da tausayinta ta
ce "Komai zai daidaita Insha Allah, su yaran ki bar lamarinsu a hannuna zan samo musu mazaje na kece raini, tunda kyawawa ne ba zasu yi wuyar shigaba, nayi mamaki ma da har yau ba wani k'usan Gwamnati da yazo ya kawo musu hari, sai kace wad'anda aka yiwa asirin bak'in jini."




Ajiyar zuciya Sakina taja kafin ta ce Allah ya shige mana gaba, zan saka su tura hotunansu sai ki watsasu a status k'ila ta wajenki a dace tunda kina huld'a da manyan k'asar nan, da kuwa ranar nayi rawa da tsalle idan senator ko minister suka taya." Kady murmushi ta saki kafin ta ce "Ai
ba abin mamaki bane, kyawun da
suke da shi kad'ai ya isa yaja hankalin maza kansu, ki saka dai suje ayi musu makeup na
kece raini, sai a kira FARISH yayi musu hoto, don naga ya iya fidda
hotuna masu kyau." Ammi cike da
murna ta ce "Haka ma za'ayi wallahi kin kawo idea"






__________________________________


Daga ita sai Didi a parlourn, Didin tana taje mata dank’ararren gashin kanta da bata son gyarawa sai dai ta wanke, mita take tayi mata “Ke sai kace ba mace ba a haka zaki samu mijin aure, naga ko y’ar powderr nan ta y’an mata ba shafawa kike Ba kullum idanuwa a kod’e kamar nama, ai gwara ki dinga gyara jikinki ko kya samu saurayi kiyi aurenki ki huta da masifar Uwarki. Gobe zan baki kud’i dama ki siyo kayan kwalliya har da gazal da jam baki, don ance ko kana da kyau ka k’ara da wanka, amma lamarin tsoro yake bani ace har yanzu ba wanda yazo yace yana sonki, ko kuma don ana ganin y’an uwanki masu kalar larabawa, kema ai ba mummuna bace kawai da duhun fata ne da ke na kuma tabbata da rashin gyara.”




Shiru Hamda tayi mata, zuciyarta ta lula can tunani, sai yanzu da Didin tayi mata maganar sannan ta ankarar da ita, da sam ta manta a irin shekarunta ya kamata ace tana da saurayi ko da kuwa ace na wasa ne, ko me yasa ita bata da saurayin a tsayin rayuwarta ba wanda ya tab’a cewa yana sonta, ba mamaki rashin kwalliyar ne kamar yarda Didi tace idan kuwa hakane ya zama wajibi ta fara kwalliya, don da gaske itama tana son tayi aure ta bar gidannan fatanta da burinta ma bai wuce ta auri d’an wani garin ma, ta yarda zata dad’e bata zo gida ba.


Dai-dai lokacin da Didin take kame mata k’ak’k’arfan gashin nata ya turo k’ofa ya shigo, idanunsa a kanta, da tayi saurin sunkuyar da kai. Ya d’an tab’e baki had’e da zama gefen Didin.


Ta kuwa washe masa baki ganin ya turo mata leda shak’e da kaya gabanta. Kaya ne fal na ciye-ciye a ciki sai kayan tea da k’unshin ledar gasassun kaji a ciki, ga yoghurt masu sanyi.


Fara’ar Didi ta yawaita cewa take “Yanzu na san Hammadu ya dawo k’asar nan, wallahi da a zuciyata har na fara tunanin ko ka zama zumbuli ne kakan marowata, har na fara tsinewa Ingila gaba d’ayanta don na tabbatar su suka koya maka rowa, kai da kake kyauta kamar baka so, Ina matar taka ta dawo kuwa?” Ya d’an girgiza kai yana sakin murmushi ganin yarda take cin naman kamar wacce a shekara sau d’aya take ci. Tsaki taja kafin tace “Zancen banza zancen wofi, to zaman me take a gidan nasu? Ta barka anan wa zai kula da kai, idan kazo nan kaci abinci, cikin dare kuma wa zai gyara maka shimfid’arka, fisabilillahi A’a nifa bana son shegantaka daga kwana biyu shine za’a tafi har hud’u, ina ce tuni aka yi sadakar bakwan uban nata, wanda ya mutu ba ya mutu ba fisabilillahi na meye kuma zata rashe waje ta zauna kai kuma ta barka da rungumar filo cikin dare da mafarkai barkatai”


Tsaf ya had’e fuskarsa ganin zata yi masa b’aranb’arama a gaban Hamda, itama Hamdan kunya ce ta d’an kamata don sarai ta san inda zancen Didin ya dosa, ta mik’e ta shige kitchen gwara ta tsiri wanke-wanke akan ta zauna jin hirar Didi marar kan gado.


Tana jiyoshi yana yiwa Didin sababi, da sanar da ita shi ya amince matar tasa taje a zafafe yace “Kuma ni nace miki idan bana tare da matata ina rungumar pillow da mafarkai cikin dare?da zaki bani kunya gurin k’aramar yarinya.”


Tsaki Didi tayi ta ce “Zancen banza Zancen wofi Hamdan ce yarinya? Allah na tuba itama tun yaushe na gama gane aure take so, ai Ina lura da mafarkan da take yi da matse filo a k’irji, don haka ma zan sanar da ubanku ayi mata aure.”


Hamda da take kitchen ji tayi kamar ta nutse cikin k’asa saboda bala’in kunya da gaske yau Didi ta shammace ta ko a ina ta tab’a kamata tana rungumar pillow? ita ina ruwanta ma da wata soyayya, don takaici har wata y’ar k’walla ce ta zubo mata, yanzu wani kallo Didi take so Yaya Hammad yayi mata?


Shi kuwa don takaici kasa ce mata komai yayi, a fusace ya mik’e ya fice daga d’akin yana mamakin tsofaffi yarda ba ruwansu suke sakar zantukan da suke so son ransu ba tare da sun tauna abinda zasu fad’a d’in ba. Ya tabbata Hamda tana can tana jin takaicin furucin Didin. Shi kad’ai kuma sai ya saki murmushi ya girgiza kai kawai ya fad’a sashen mahaifiyarsa.








_____________________________


Hamda kuwa cikin takaici ta amsa kiran Didin da take ta k’walla mata.




Ta fito daga kitchen d’in fuskarta a had’e tana cono baki, ji take kamar ta rufe Didin da duka.


Didin data lura da b’acin ran kan fuskarta taje Tsuka ta ce “Kamar kumbo kamar katanta, shima haka ya fita yana muzurai dad’in abin dai a dake ba zan daku ba, a zage ba zan zagu ba sai dai a zageni a zuciya, wannan kuma mutum shi ya jiyo, k’arya aka yi miki ba auren kike so ba ranar fa ina kallonki kina barci kina faman matse k’afa.”


Hamda ta d’ago ta watsa mata wani kallon takaici kafin ta ce “Wallahi Didi ba kyau, Allah fa yana kallonki, ki ji tsoron Allah yanzu me kike so Yaya Hammad ya d’aukeni?”




Dariya Didin tayi ta ce “D’an nema, yazo da k’warin gwiwarsa da alama yunwa yake ji, anzo cinye min abinci,daga maganar gaskiya kuma ya fice, ba don halinsa ba d’auki abincinsa ki kai masa ko don himulin siyayyar nan da yayi mana.”


Hamda ta waro ido kafin ta ce “Ni zan kai masa abincin? Cabd’i ai kam ba dani ba. Da wani idon Zan kalleshi bayan kin gama kwaye min zani a wajensa.”


Didi ta zabga mata harara “Ni kike so in tashi in kai masa kenan ko? Da yake ni marainiyar wayonki ce, idan da Uwarki ce ai da ba ki fad’a mata haka ba, sai ni da kika ga na sakar miki ko? To ko ki d’auka ki kai ko nayiwa Gadanga waya yazo shi ya kai masa. Hammadun bai fi min uban kowa ba, duk cikinku wa ke kula da ni yarda shi yake yi, to wallahi ko ubanki sai na kira na saka shi ya kai masa abicin nan, tunda ke ban isa dake ba.”




Jin haka da sauri Hamda ta sunkuci tray d’in ranta fal da takaicin Didin.


Tana fita kuwa Didin ta saka dariya ta ce “Ja’ira y’ar nema banda nayi mata haka, ba zata je ba.”




Dai-dai zata shiga k’ofar sashensa shima ya sawo kai, ya dawo daga b’angaren Mahmah. Da sauri taja gefe kanta a k’asa murya na rawa tace “Didi ce tace a kawo maka abinci.” Banza yayi mata yana bud’e k’ofar. Ganin bai kulata ba ya sanya kanta cikin parlourn, da ba abinda kake ji sai k’arar Ac da sautin karatun alk’ur’ani daga bakin Sudais cikin suratul wak’ia, sai kuma sanyayyen K’amshin turarukan wuta, da suka gauraya da nasa turaren.




A dininig ta ajiye, cikin sauri har ta murza handle d’in k’ofar “Hamda” ya kira sunanta cikin ginshira wanda direct zata iya cewa shine karo na farko da taji sunan nata akan harshensa a dai yanzu da ta manyanta.


Kamar ba zata jiyo ba sai kuma ta juyo a hankali ta k’arasa inda yake zaune, tsawon seconds yana danna waya bai ce mata komai ba har ta ji ta gaji da tsayuwar sai taji yace “Aure kike so kamar yarda Didi tace?” Da wani irin shock take kallonsa kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login