Showing 78001 words to 81000 words out of 117648 words
Chapter 27 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
ya jawo Sakna ta janye bakinta daga cikin na Abbu idanunta cikin na Sadiya da take tsaye ranta a matuk’ar b’ace. Sakna ta yi murmushi tana cewa “Ki yi hak’uri don Allah.” Daga haka ta saka kai ta fice.
Sadiya cikin tsananin b’acin rai ta juya zata tafi sai ji ta yi Abbu ya kirata “Zo nan SADIYA.” Ya fad’a cikin wata iriyar murya da ta tabbatar tsananin matakin sha’awa da yake kaine ya sanya muryar ta shi jirkicewa ta sauya launi. Tsananin kishi ya sa ta ji kamar ta zunduma uban ihu, da kyar ta had’iye abin da ya tokare mata a k’irji ta ce “Ba sai na zo ba, da na san ma ka samu lafiya har kana iya kusantar mace da ban dawo ba.” Ya lumshe idanunsa yana jin takaicin Sadiya a ransa sam bata iya kula da miji ba. “Ta yarda y’ar uwarki ta fiki kenan, me yasa ba zaki yi koyi da ita ba? Laifi ta yi min ta zo bani hak’uri ta hanyar da ta san duk girman laifinta Zan hak’ura na yafe mata. Tana kula da ni fiye da ke ta san soyayya kuma kullum a cikin nunan kulawa take fisabiliallahi ta yaya kike zaton Zan iya rabuwa da ita? Alhali ko da yaushe akwai salon kulawa da take sabuntawa ta ba ni, ko zuciyar k’arfe ce da ni ba dole ta narkar da ita ba, Zan gaya miki gaskiya ki canja halayyarki, ki na min biyayya sau da k’afa ta nan kam kin fi Sakna amma zan gaya miki gaskiya Sakna ta fiki sanin sirrin shimfid’a ta san ta yarda zata kautar min da duk wata sha’awar y’a mace, don haka zuciyata take kasa rabuwa da ita…. Yanzu tunda ki ka saka k’afa kika fice ba ki sake dawowa ba sai yanzu kuma tun safe kayan nan suke jikin ki haka ki kaga ita Saknan tana yi? Da an yi magana ace asiri..”
Cikin takaici take kallonsa wasu hawaye suna zubo mata, ya dad’e yana fad’a mata kuskurenta amma na yau yafi tsaya mata, ita kunya ce take mata dabaibayi ta hanata aikata wasu abubuwan, magungunan gyaran jiki kuwa gani take asarar kud’i ne siyansu, ita sam ba zata iya wannan zubin dashin da ba biya ba, akan me ma girma ya riga ya kamasu. Bata san shi Abbu ba ruwansa da girma ba, kullum jinsa yake kar in dai akan wannan harkar ce. (Don haka wallahi mata a dage da gyara, a kuma dage da sanin sirrin kwanciya, domin sune maganin mallakar miji sadidan ki dinga juya abinki son ranki sai ki ji ana ai wance asiri ta yiwa mijinta ga shi nan ta mallakeshi. Mhmn ba su san abin ba anan take ba, shi namiji yana son a kula masa da b’angaren shinfid’a ga dai Sadiya nan ta mayar da kanta borar k’arfi da yaji a wajen miji, Allah yasa mu dace.)
Muryarta na rawa ta ce “Yanzu duk girman laifin da ta yi maka ka yafe mata kenan?” Ya girgiza kai cike da takaicinta ga maganar da ake mata ita kuma ga zancen da take masa “Ban ce miki na yafe mata ba, amma kaso mafi yawa daga haushinta da nake ji ya zagwanye. Hukunci kuma ina nan ina tunanin hukuncin da ta dace da shi. Zo ki zuba min abinci yunwa nake ji.” Ta bi abincin da Saknan ta kawo da tsaki kafin ta janyo nata abincin ta fara k’okarin zuba masa, duk da yana son cin abincin Saknan haka ya hak’ura ya dinga cin na Sadiya wanda sam bai zama daga cikin irin cimar da yake so ba. Har yanzu ta kasa gane kalar abincin da ya fi so, tsawon shekarun da suka d’auka tare sab’anin Sakna da haddace tsaf a kanta, ta san cimar da yafi ci da safe, ta san ta rana hakanan ta dare. Kad’an ya ci abincin ya ce ya isheshi. Jira yake ya ga ko zata yi hankalin had’a masa ruwan wanka, sai ya ga ta yi zamanta kamar ma a k’agare take ta tafi, ya kau da b’acin ransa had’e da cewa “Diyayye saura ruwan wanka.” Ta d’an kalleshi kawai had’e da cewa “Yau kuma wani sabon salon suna ne ya tashi menene kuma wani Diyayye kamar wata yarinya?” Dariya ya yi kawai ya lura har abada Sadiya ba zata canja hali ba, madadin ta d’an rungumoshi ta ce masa “Umaruru, nima na rama, kamar yarda Sakna take masa idan ya kirata da Saknene. A zuciyarsa ya ce MATA SUNA SUKA TARA.. ruwan kawai ta had’a masa ta fito had’e da ce masa na kai.” Ta kamashi ta raka toilet d’in, tana k’okarin ficewa ya janyota “Ba zaki taya ni ba? Na ga kema ko wankan b kiyi ba tun na safe ne ko?” B’ata fuska ta yi had’e da cewa “Wankan zan je in yi.” Ya k’ura mata ido “To mu yi tare mana.” Ta yi saurin kallonsa kafin ta ce “Allah ya sawwake sai kace wata yarinya.” “Sakna yarinyace kenan da muke yi tare?” Haka ya so yace mata sai dai ya gintse ta hanyar tab’e bakinsa ya kuma sakar mata hannu, a zuciyarsa ya raya ba ta yarda za’a yi ya rabu da Sakna alhali ita Sadiya bata waye ba, da an tashi zance kuma ace baya adalci a tsakaninsu ta ina kuwa zai yi adalci? Ya tabbata da Sakna ce tsaf zata wankeshi kamar yarda ake wanke yara har ma ta shafe shi da mai ba wani kunya, to dama ai ba kunya tsakanin mace da mijinta. Haka ya dinga wankan zuciyarsa fal da tunanin Sakna da Sadiya da suka zama masu mabanbantan halaye. Sakna irin matar nan ce da Hausawa kai tsaye suke kira karuwar gida yayin da Sadiya ta zama irin matan nan masu duhun kai da basu san komai ba a harkar auratayya.
_____________
Sanin cewa tana b’angaren Didi yasa kansa tsaye ya nufi sashen, jikinsa sanye da doguwar rigar jallabiya coffee colour da ta saje da fatar jikinsa. Fuskarsa tas da alama bai dad’e da fitowa daga wanka ba, hannunsa rik’e da carbi na dannawa yana matsawa a hankali. Sai zabga k’amshin turaren Miyaki d’an asalin yake.
Daga Didi sai Asma’u a falon suna baje tana shafawa Didin man zafi a k’afa. Suka tsinkayi muryarsa ya shigo. Baki sake Didi take kallonsa ya zauna a gefenta had’e da gaisar da Umma Asman, sannan ya juya yana kallon Didin da ta yi kicin-kicin da fuska, “Tsohuwa mai lan k’alfe an sha luwa lafiya?” Harara ta watso masa jin yarda yake kwaikwayan maganarta. Cike da shak’iyanci. Ta yi k’wafa a ranta ta ce “Zaka ci ubanka ne zan lama, ba dai matalka tana nan ba.” A fili kuwa cewa ta yi “Umalu dai ya haifo mana jalaba, ko da yake duk wani iya shegen da ya yi kwatankwacinsa ka ke yi, ga shi nan kai ma baka damu da b’acin lansa ba, kamal yalda bai damu da nawa ba, ka je ka yi aule bai tani ba, tannan ka b’oye ma ta abu mai mahimmanci. Ai idan bai yi wata ba te ka taka mata hawan jini.” Daga haka ta mik’e d’akin Hamda ta je ta kulle ta zare mukullin ta tura cikin bujenta “Ban ga dalilin biyo ta nan ba, tunda uwalka ta ce bata ton aulen to wallahi ba zan bali ka tumulmusheta ba, ni ce nan gatanta wallahi, kaje ka shilyota da uwalka idan ta amince da aulen falillahi hamdihi a had’o lefe a zo ayi biki kowa ya shaida tannan a kai mata ita gidanka ka je ka tumulmusheta a can jalababbe kawai.” Sunkuyar da kai ya yi yana murmushi kunyar Umma Amsa ya hana shi k’watar key d’in ta k’arfin tsiya don da gaske a matse yake da son jin d’umin Hamdan a jikinsa ko da ba za su aikata komai ba. Ya mik’e ya fice kawai yana tuna wunin yau sir bai ganta ba bai san a wani hali take ba, ga shi ba waya a hannunta ya zama dole ya siyo mata waya ko muryarta ya dinga ji.
Direct b’angarensa ya nufa dole ya je ya nemi sulhu da Nanna tunda Didi ta rufe masa waccan k’ofar. Tana zaune a d’akinta ya shiga ta d’ago tana mamakin ganinsa a d’akin kafin ta tab’e baki ta ce “Lafiya?” Ya k’arasa wajenta ya zauna daf da ita yana shiga jikinta sosai. Da sauri ta mik’e dama wannan damar take jira, ya d’ago yana kallonta “Me ye haka Nanna?” “Kai zan tambaya meye haka? Ina matar taka da zaka zo jikina ai gwara kaje can ta baka abinda ni bana baka da yasa ka aureta.” Fuska a had’e ya ce “Na san da itan ai na zo nan.” Ta yi wata iriyar shewa kafin ta ce “Amma kuwa Hammad ka sha haushi don ina tabbatar maka wannan jikin nawa k’walelenka matuk’ar zaka dinga had’a jiki da waccan sannan ka zo ka had’a da ni, idan zaka yi gaggawar sakinta ka saketa kafin zuciya ta ta tunzira na sanar da Mahmah sirrin da kake b’oye mata game da Kamla…” zancen da ya shiga kunnen Sadiya kenan kasancewar ta shigo neman Hammad tana ta k’wala kira ba su ji ba, tana sa kai zata fita ta jiyo kamar fad’a suke ai kuwa ta tsinci wannan maganar, gabanta yana fad’uwa ta zaro ido ta ce “Kamla kuma innalillahi wa inna ilaihirrajiuna mai kunnuwana suke shirin ji?”
Jikar Nashe✍🏽✍🏽📖
❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: K’ok’arin tureshi take yi, amma bai bata damar hakan ba, duk da ya ga Didin na kusanto su sake manna bakinsa ya yi cikin nata, fatansa Didin ta gansu ina ruwansa tunda ya san ba haramun ya aikata ba, ya manna ta da jikinsa sosai ta yarda ba zata samu damar tserewa “Nutsu Malama, kada ki sake tureni da fushin Didi da na mala’iku wanne ki ka fi tsoro?” Hawaye kawai ta ji suna zubo mata ganin Didin dab da su, cikin gigita ta runtse idanunta tana jiran jin saukar sandar mopperr a jikinta. Sai ta ji Didin ta saka salati “Innalillahi, wace jalaba ce wannan cikin dalennan kazo kana lalubeta kai dai an yi tanbad’adde k’warai da gaske.” Bai kulata ba, ya mik’e da Hamdan a jikinsa ya sake rik’ota sosai idanunsa cikin na Didin ya ce “Haramun na aikata?” “K’anin haramun ka aikata tunda ni ban amince da wannan tambad’adden auren naka ba.” Ciki-ciki ya yi da idonsa kafin ya ce “Kada ki sake tambad’a min aurena, aurena na halak ne da shaidu da komai..” Didi ta wurgi Hamda da take k’ok’arin k’wace hannunta daga nasa da harara “Munafuka da kika ganni ba, ke wato har kin iya biyo dare ki samu namiji saboda kina jin dad’in tumurmusaki da yake yi, tun kina budurwa ai na san kema jalababbiya ce yadda kike kwana kina matse filo a jiki, ba zaki wuce ba tai na maka miki tandan nan.” Da sauri Hamda ta fincike Hannunta ta shige d’aki wata kunya da bata san daga inda ta taho ba ta had’u ta rufar mata. Didi ta bi shi da kallon banza kafin ta ce “Wallahi Hammad na sake ganin k’afafunka a nan tai na taka Umalu ya yi mana tsakani da kai.” Shiru ya yi mata don gaba d’aya Hamda ta tafi da duk wata nutsuwarsa jin sa yake da kyar yake mayar da numfashinsa ga Didi na neman sake caza masa kai, ya mik’e cike da k’warin gwiwa yake kallonta “Saboda lefe kika rik’e min mata? Idan na yi lefen a gobe za ki bani Matata?” Kallon banzan ta sake watsa masa kafin ta ce “Ai idan kaga na baka ita, an had’a an yi bikinta da na y’an Uwanta da za’a yi ana tallacewa tannan za’a kaita d’akinka, don ban yarda ka sameta a gantale ba.” Kallon baki isa ba yake mata kafin ya yi k’wafa ya sa kai zai fice ya jiyota tana fad’in “Ni Za’a kawowa itkanci wallahi ka take zuwa ma tai na fad’awa Tadiya ta titseyeka ka taketa ai dama ba son Auren takeba, na ma
Yi mamaki da hal yanzu bata take tada balli ba.” Jikinsa a mace ya wuce sashensa gaba d’aya jallabiyarsa ta nad’e k’amshin jikin Hamda tsaf,
K’amshin da yake sake tada masa zafaffiyar sha’awarta. Wanka ya shiga kafin ya fito ya kwanta gefen Nanna da ta juya masa baya, zuciyarta cike taf da jin haushinsa don ta tabbatar daga gurin Hamda yake tunda ya shigo ta ji k’amshin turaren mata a jikinsa, tsaki ta ja a hankali ba tayi zaton zai ji ta ba, ga mamakinta sai ji tayi ya birkitota yana jifanta da kallo da manyan idanunsa “Allah yasa dai tsakinki ba dani kike ba?” Tsoro ne fal ya cikata shi yasa ta k’i biyewa zuciyatta da take ingizata tace Da shi d’in take sai me? Amma madadin haka sai ta girgiza kai cike da tsoronsa “Magana za ki min, Bana son raini.” Murya a shak’e ta ce “Ba da kai nake ba, kaina ne ya ke min ciwo.” Ya sassauta rik’on da ya yi mata ta hanyar shafa kan sai ya ji da d’an zafi da alamar da gaske ciwon kan take, sauka ya yi ya samo ruwa da paracetamol ya b’alla yana cusa mata bakinta ta samu ta had’iye da kyar, suka kwanta yana d’an murza mata kanta yana k’okarin yakice tunanin Hamda da ya tsaya masa a k’irji.
Hamdan kuwa fad’a ta sha gurin Umma Asman sosai akan yarda ta yi kunnen uwar shegu da jan kunnen da ta yi mata. “Ba zaki bari a siya miki mutuncinki na y’a mace Ba? Ba zaki bari ya dinga d’okinki Ba, zuwa kika yi kika sake sakar masa jiki, kin kyauta to.” Kunya ce ta kamata sosai har ta ji takaicin yarda ta fita ta sameshi ta tabbata rigar da take jikinta ce ta janyo ya kasa hak’uri sai da ya jata jikinsa, tunda idan har zai ganta a haka ta tabbata Ba zai iya d’auke kansa ba, dama ya lafiyar giwa, dole kuwa ta ja jikinta da shi, musamman da bata san makomar auren nasu ba, daga yanayin yarda Mahmah take amsa gaisuwarta ta tabbata ba tayi na’am da aurensu da Hammad d’in ba, za kuma ta iya datse shi a duk lokacin da ya yi mata. Ba zan sake kusantarka ba har sai Mahmah ta amince da aurenmu shine tunanin da take a zuciyarta.
__________________
Duk fushi take da Ammin amma tana jiyo muryarta falon Didi sai da ta ji zuciyarta na son ta ganta, tana son Ammi fiye da kowa a rayuwarta, zuciyarta na son fita ta ganta ko da zata yi mata hararar da ta saba, amma tana tunanin lokutan da Ammin ta d’auka tana wahalashsheta akan laifin da Ba nata ba, ashe duka kuskuren ma idan za’a tankad’eshi a taskaceshi na Ammin ne kacokam ba nata ba, ita tabi son zuciyarta Allah kuma ya nuna mata ikonsa ba dai d’a namiji take so ba, to shi kuma Allah bai so ta haifa ba. Kasa jurewa ta yi sai da ta mik’e ta fita jin kukan Ammin a gaban Didi kamar ranta zai fita tana jiyo sautinta tana fad’in “Don girman zatin Allah Didi ki yafe min, Umar ya ce ba zai cigaba da zama da ni ba har sai idan ke kika amince masa, wallahi zan gyara kuskurena zan zauna da kowa Lafiya, zan yi biyayya a gareki Didi ki tuna ko Allah muna masa laifi ya yafe balle d’an Adam, Didi watan azimi muke ki dubi girman Allah alfarmar watannan ki yafe min.” Yawan magiyar ya sa Didi taji tausayinta da sauri ta d’aga mata hannu “Ya ita Takina, dama ni ban tab’a k’ullatarki ba, kuma sai a godewa Allah da ba ta hanyar banza kika samar da cikin nata ba, Zan yafe miki amma tai kin ja y’alki a jiki kin nuna mata soyayyar da duk bata samu ba, kin wanke mata wancan bak’in painting da kika goga mata a zuciya, daga yau kuma nake ton na fala ganin canji shima Umalun zan gaya mata. Abu na gaba ki zauna da kowa lafiya, mu nan da kike gani ba wanda yake k’ullatarki kowa son ki yake, ke ki ke ganin kamal ina fifita Tadiya a kanki ko d’aya ba haka bane, Idan kin gyala halinki za mu zauna da ke k’alau. Allah ya take tiltyal da ke alfalmal muhammaduna manzan Allah.” Murna da tsananin farin ciki ne yasa ta fara kwararar da hawaye tana furta “Nagode Didi Asma’u ki taya ni godiya.” Murmushi Umma Asma’u take ta kuma k’walawa Hamda da take tsaye a bayan k’ofa kira. Farin ciki yasa Hamda tahowa a guje ta zube a gabansu tana sakin hawayen murna, bakinta ya kasa rufuwa wani kallo kawai takewa Ammin tana kallon hannayen da Ammin ta bud’e mata alamar ta taho, Ba tayi wani jinkiri ba ta fad’a cikin k’irjin da ta dad’e tana son jinta kwance a cikinsa tana kuka har mafarkin hakan take, cikin wata iriyar soyayya mai zafi Ammin ta rungumeta tsam a k’irjinta hawayen farin ciki yana zubar musu, tana jin kuma yarda zuciyoyinsu suke bugawa kusan lokaci d’aya. K’aunar nan ta tsakanin uwa da d’a ta taso ta lullub’e zuk’atansu. Daidai Lokacin da Abbu da Hammad suka shigo kamar had’in baki farin cikinsu ya yawaita ganin Hamda rungume a jikin uwarta karo na farko a rayuwa Hammad bai san sanda ya danna wayarsa ba ya shiga yi musu vedio fuskokinsu cike da walwala. Didi fad’i take “Hukumullahi la ajabun, Yanzu kin yarda haihuwa a wajen Allah take ko? Shi yake da ikon bayar da namiji ko mace yanzu haka ita da baki to haihuwarba, ita zata zame miki Tanyin idaniya”
Abbu girgiza kai yake kawai jin dad’insa d’aya Didi ta yafewa Saknansa, shi dama tun a daren jiya ya yafe mata, bayan ya tabbatar da sakin da yake tunanin yi mata shine babbar wautar da zai yi a rayuwa.
________________
Kwana biyun da Mahmah ta bashi bai manta da su ba, ya kuma tabbatar da ita ma tana sane da shi, a yau kuma shi da kansa ya yarjewa zuciyarsa bayyana musu wacece Kamla da kuma ubanta kai