Showing 90001 words to 93000 words out of 117648 words

Chapter 31 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

kukan da ta dad’e tana neman inda za ta saka kanta ta yi kuka ko ta samu k’uncin da nadamar ta jawo mata ya sauk’ak’a a zuciyarta, Muniran ta rungumeta itama nata hawayen suna sauka tausayin Ammin take ji tausayin da yake nad’e duk wani k’arfin zuciya, Uwarta mai kyawun zuciya ce ta tabbatar kuma ba don gado take son ta haifi namiji ba, don dai ta sharewa Umminta bak’in cikin rashin haihuwar d’a namiji da har aka dinga mata gori a rayuwa. Sun dad’e a haka kafin Ammin ta d’ago tana matsa hannun Muniran kafin ta ce “Ta wace hanya kike ga Zan ja Hamda a jikina? Da sam ba zata kawo zargin Dan naga ubanta da kud’i bane.” Munira ta girgiza kai “Wannan zargin ba zai kau daga zuciyarta ba har abada, haka nan daga zuciyar mutanen gidan nan, abu d’aya da zaki tuna ki kwantar da hankalinki shine idan kika tuna don Allah ki keyi ba don jama’a ba, to sai ki samu sauk’in zuciyarki, abu na gaba ki d’auke kai daga dukiyar KK kada ki sake ki nuna zalamarki a kansu.” Amma ta girgiza kai tana jin zuciyarta ta samu nutsuwa daga shawarwarin da Munirat d’in ta bata, duk da ta bi ta Munirat d’in da abin bai kai tsawon haka ba, to sharrin shaid’an duk shi ya jawo mata komai. Munirat ta sake share mata hawayenta had’e da cewa yanzu ki je ki sake bawa Abbu hak’uri na tabbata zai hak’ura duk da ya sakko dama.” Ammi ta d’aga kanta alamun amsar shawarar y’ar ta ta.


Tsaf ta yi wanka, kamar yarda ta saba bata tunkarar tirakrshi sai da daddad’an k’amshin da ita kanta ta san yana wargaza tunanin Abbu, a wannan turbar take son saka duk yaranta har Hamda kuwa daga gobe zata fara koyar da ita karatun mallakar miji, ta yarda ba zai iya rayuwa idan ba bu ita ba, harta da gashin kanta sai da ta turara shi sannan ta zumbula dogon hijabinta ta fice zuwa b’angaren Abbun.


Lokacin yana zaune jikinsa yake jin ya masa nauyi, sosai yake son a mammatsa masa, ya san kuma Sadiya ba zuwa zata yi ba musamman sanin cewa ba girginta ba ne. Sakna ta tura k’ofa ta shiga da sallama. Abbu ya saki ajiyar zuciya yana amsa mata sai dai babu yanayin walwala a tare da shi. Bata damu ba ta k’arasa ta zauna a gefensa fuskarta d’auke da murmushi burinta ta gusar masa da wannan fuskar da ta gusar masa da duk wani kyansa. Ta saka kanta a kafad’arsa yana jin yarda numfashinta yake hawa da sauka a kunnensa “Ka yi Hak’uri Faruk’u na please ka yafe min mu koma kamar yarda muke a da, wallahi ba na jin dad’in yanayin nan sam.” Ta fad’a tana matsa masa cinyarsa a hankali ta bi duk wata hanya da zata bi na ganin ta shayar da shi duk wani farinciki a wannan daren kafin ya sauko bisa tilashin zuciyarsa ya fara mayar mata da martani gangar jikinsa na nuna mata yarda ya yi bala’in missing d’inta ta hanyar rawa da jikinsa yakeyi, tsammaninsa zai iya rayuwa ba Sakna sai dai yau jikinsa da ruhinsa sun k’aryata tunaninsa kansu tsaye, don idan a zahiri ya nuna mata ya bazangatar da lamarinta sai dai yau bad’ininsa ya nuna mata itace dai mahad’insa itace Saknansa da duk wani numfashinsa da d’igon k’aunarta yake dira. Shikkenan zancen ya mutu murus ya koma tamkar ma ba ayi ba, madadin jin haushinta wata sabuwar k’aunarta ce ta sake maye gurbin tsanar a zuciyarsa ko bakomai yau ta bashi wata irin zuma mai wuyar fasalta zak’inta a harshe, yana jin tamkar ya sake mayar da ita ciki. Ba boka ba Malam Sakna ta sake dawo da martabarta a zuciyarsa, ta hanyar da mata da yawa kunya ba ta barinsu aikatawa JIKAR NASHE zata sake fad’a babu kunya a rayuwar aure da haka matan waje suke janye muku hankalin maza, ko a auro wacce take da masters a wannan fannin ta samu kan miji sai ki ji ana ta mallakeshi, ta asirceshi alhali ita kad’ai ta san yarda take sarrafashi a gado ta yarda zai zame mata rak’umi da akala wannan ake kira ‘Karuwar Gida’😆.








___________________


Babu komai a ranta ta tashi da safe, kafin Salma k’anwarta tazo ta wargaza mata duk wani tunani mai kyau na zuciyarta, ta kuma amince da gurguwar shawarar da Salman ta bata, ba tare da tsinkaye da tunanin mai lamarin zai jawo ba. “Yanzu ke Anty Sadiya sai ki amince Hammad ya had’a zuri’a da jinin macen da k’iri’kiri ta mayar da ke bora a wajen mijinki, waye bai san irin cutarwar da waccan matar take miki ba, ai wallahi idan nice yanzu za’a fara wasan ba KK ba ko shugaban k’asa ne ubanta ba zan bari d’ana ya maye mata gurbin miji ba, ai ko don na cusawa uwarta bak’in ciki ta d’and’ana itama ta ji sai na tuje wannan auren Hammad da ikonki ne, kema a yanzu za ki ja zaran na ki mulkin, ki nuna power da ikonki haba Anty mana kada ki bada ni mana.” Sadiyar ta yi tsai da ranta tana jin shawarar da y’ar uwarta ta bata abar d’auka ce, ya kamata itama ta wargaza farincikin D’an Borno musamman Sakna ta cusawa ta ta y’ar bak’in ciki, abinda ta so yi da kenan wata zuciyar ta dinga kwad’aita mata kud’i da arzikin KK sai dai yau Salma ta farkar da ita daga mafarkin da take, ya kamata itama ta murd’a kambunta ta ja zarenta tabbas! Ta saki ajiyar zuciya “K’warai Salma, kin tunasar da ni abinda zuciyata da hasashena suka manta, saboda kwad’ayin dukiya, amma ta ina kika ga zan fara?” Salma ta saki murmushin jin dad’i ta ce “Ta yau zaki fara ana shan ruwa ki tarasu a falon Didin ki sanar da su buk’atar Ki Hammad ya saki Hamda, ke ba ki amince da auren ba, kuma duk juyin da za’a yi ki kafe a kan hakan, ai kin gane, yanzu za kiga kema kin zama sarauniya an zo ana lalla’ba Ki, ki jajirce kice wallahi za ki tsine masa idan bai saketa ba.” Sadiya ta saki murmushi ta kuma amince da shawarar da jaririyar k’anwarta ta d’orata a kai saboda rashin wayo, jaririya mana tunda Salma sa’ar d’anta na uku ne wato Hameed, ta saki dariya tana tuno yarda Sakna da Didi za su durk’ushe a gabanta suna neman ta amince da auren, ita kuma ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya tana izzar mulki da rantsuwar Hammad d’in sai ya saki Hamdan…🤣🤣




Jikar Nashe ce!
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Wani kallo Hammad ya dinga jifan Didi da shi jin tana shirin aikata b’aranb’arama, kafin ya d’auke kansa Didi ta ja tsaki ta ce “Yo aikin banza da wofi Gadanga kake harara ba ni ba,
Don uwarka ce sai na kasa fad’ar gaskiya, ina ce masifa ta dinga yi sai ka saketa, to yanzu ba sai ka saketan ba mu gani..” Sadiya k’asa ta yi da kanta tana wasa da yatsun hannayenta, Ji take da tana da dama da ta janyo wancan furucin ta mayar da shi cikinta, amma sam Didi bata kyauta mata ba, da har ta fad’i hakan a gaban KK, ba ta yarda za’a yi ace ta k’i Hamda a yanzu alhali zata haifa mata jikoki daga tsatson KK, tun farko da ta san Hamdan jinin KK CE da ba ta soma ma cewa sai ya saketa ba, Kai ko a zuciyarta ta tabbata da ba za ta yi wannan tunanin ba. KK ya saki murmushi kawai yana girgizawa Didi kai a hankali kuma ya ce “Duk abinda ya wuce ya wuce Didi a daina tayar da shi.” Didi ta jinjina kai kafin ta ce “Amma kuwa tabbas ka jawa Hammad kunne dama kada na ji kada na gani don ban shirya makanta ba, ya bari Idan tare a can ya je su ci tsiyar da za su ci, idan ya so ma ya gutsire bakin nata k’arewa tand’ewa.” Gaba d’aya gurin ba wanda bai ji kunyar furucin Didi ba, kada Hamda ta ji labari ji take da da hali da ta narke ta bi k’asa akan wannan kunyar da Didi take bata. Shi kansa Hammad d’in sai da ya gallawa Didi harara ta k’asan ido. Har waje ya raka KK kafin ya dawo wajen su Abbun, idanunsa na laluban inda zai gano Hamda sai dai sam bata wajen da alama ta shige d’akinta, ya ciji leb’ensa na k’asa yana takaicin yarda Didin take so ta saka masa shamaki tsakaninsa da matarsa.


Cikin kamala ya durk’ushe a tsakiyar falon, idanunsa a k’asa muryarsa ta raunana sosai kafin ya ce “Don Allah Abbu ka yafe min, na Dan an aikata maka ba daidai ba, ta hanyar b’oye maka wad’annan sirrikan wallahi ba yarda Zan yi ne..” Tsawon lokaci Abbu yana masa wani irin duba kafin ya saki murmushi ya dafa kafad’arsa yana girgiza masa kai “Da fari kam na ji haushinka Hammad, amma yanzu na gane dalilinka na aikata haka Allah yayi maka albarka.” Ameen ya amsa a hankali idanunsa cikin na Mahmah da itama ta kafa masa na ta idon tana mamakin zurfin cikinsa ta yarda ya iya b’oye wannan sirrin mai girma cikin zuciyarsa shekara da shekaru. “Mahmah kema ki yi hak’uri please!” Ya fad’a yana dunk’ule hannayensa waje d’aya alamar rarrashi, kafin Mahmahn ta ce wani abu Didi ta ce “Zancen banza, zancen wofi to ita kuma hak’urin me zaka bata? Me ka yi mata? Ai itace ma taso cutarka ta raba maka aure da y’arnan kaga samu ka ga rashi haka kawai.” Ya d’ago a fusace har zai mata rashin kunya sai kuma ya ga fuskar yaranta a wajen don haka ya gintse abinda ya so fad’a mata, ya kama hannun Mahmahn kawai yana matsawa idanunsa cikin na Nanna da ta rasa yarda zata saka kanta saboda tsananin takaici, idanunta ya yi jazur dalilin tashin hankalin da take ciki da matsanancin ciwon Kai, take a wajen wani irin tausayinta ya kamashi ya ji k’aunarta na d’an tab’a shi kad’an da gaske bai tab’a jin tana burgeshi ba, yana zaune da ita ne kawai saboda itace zab’in mahaifiyarsa amma yau ya d’an Ji wani Abu mai kama da k’auna da yake so ya yi tasiri a zuciyarsa. Nanna bata da laifi ko kad’an tana kuma kyautata masa fiye da zaton mutum a rayuwarsa tana gudun b’acin ranta, yana kuma ganin kima da mutuncinta musamman da ta rik’e masa Kamla tsakani da Allah duk da bata da tabbacin ba y’arsa bace, sau d’aya ya tab’a ganin laifinta Akan Hamda da ta kafawa d’anban tsana tun ma bata san wacece ita a wajensa ba. Shi kansa ya san mai laifi ne a wajenta ya kuma wajaba k’warai da gaske ya amsa laifinsa ta hanyar kyautata mata da gudun b’acin ranta ko zai samu zaman lafiya a gidansa. Murmushi ya sakar mata yana d’aga gira d’aya, inda bata kula ba, hakan da ya yi bai yi tasiri a zuciyarta ba, ko kad’an bata ji sauk’i daga rugugin bak’in cikin da yake addabar zuciyarta ba, da gaske tana takaici tana kishi tana kuma bak’in cikin zamowar Hamda d’iyar KK, a da tana tunanin bata da asali har tana shirin goranta mata idan ta tare a gidan mijinta sai ga shi ashe ta fita asalin ma, hawaye ya silmiyo mata tana jin tsana da Kishin Hamda matsananci, a lokaci d’aya kuma tana jin k’aunar mijinta ba ta ga kuma wanda zata barwa mijinta ba wallahi, zata zauna da shi za kuma su goga kishin a ga wa ke da nasara? Ita ko Hamdan?
Ganin tana jifansa da wani irin firgitaccen kallo ya sa shi d’auke kallonsa daga kanta, shi da kansa ya san yanzu aka fara? Kishiya itace yak’in mata ya tabbata ba aure ba.


Haka duk jama’ar wajen suka watse ganin dare ya lula. Shima Hammad haka ya fita jikinsa a salub’e duk da yana son ganin Hamda ya san Didi ba zata ba shi wannan damar ba, ko ba haka ba bai shirya janyowa kansa idanuwa ba, zuciyar kowa fes ya tafi gida yau dai k’udundunenen Sirri ya fashe kowa ya ji asali da tushen komai.




Hamda tsaye ta yi a gefen mudubi hannuta d’auke da towel tana goge sumar kanta, ta saba duk dare sai ta yi wankan take jin dad’i. K’amshin turarukan wanka kawai take zabgawa a jikinta. Umma Asma ta shigo da cup a hannunta ta mik’a mata “Maza kafa ki shanye shi tas, don wannan mijin naki ban hango wasa a lamarinsa ba duk da dai yana da wata Matar. Matsananciyar kunya ce ta sa hannunta ya fara rawa duk da tun farkon aurenta bata tab’a sha ba ta san menene ta kuma san amfaninsa, tabbas ita kanta ta san lamarin Hammad ba wasa dole ta tashi tsaye wajen gyara kanta. Umma Asma ta sake jan kunnenta sosai akan kada ta sake ta sake rab’arsa har sai an gama shiryata sosai. Ta amince da hakan kafin ta kulle d’akin ta juyo tana daka uban tsalle, murna fal cikinta da ta tabbatar ko wanene mahaifinta. Ta lumshe idanunta tana hango yarda Hammad yake sakar mata murmushi kafin ta ja filo ta rungume a jikinta. Asuba ta gari Hamda.






_____________


Tunda ta shiga d’akinta take zagaye tsakar d’akin cikin tashin hankali zuciyarta ce kawai take duka, neman mafita kawai take mafitar da zata hana Hammad auren koma wacece ba ma Hamda ba da take ganin ta zarceta a komai, kyau dirin jiki kyawun fata abu d’aya zata bugi k’irji ta ce tafi Hamdan shine kyawun gashi don ita ko relaxing kanta ba tayi saboda tsabar santsi da yauk’insa, kuma sarai ta sani Gashi yana d’aya daga abinda yake burge Hammad a sasan jikin y’a mace. Ta runtse idanunta da zuciyarta ta hasasho mata yarda Hammad d’in yake maitar k’irjin y’a mace anan kam Hamda ta mata zarra don a cike take taf daga saman ta har k’asanta, tashin hankalinta ya k’ara hauhawa har ta ji kamar ta kurma ihu da ta tuno yarda Mahmah ba kunya ba tsoron Allah ta yi mubaya’a ga auren duk da cika bakin da ta dinga yi a kwanakin baya, itace hope d’inta ita kuma take saka ran za ta tirje ta k’i amanna ga auren sai ga shi a lokaci guda fuskarta ta nuna tana farin ciki da hakan, hawaye na ziraro mata cikin buga katifa ta ce “No No No Mahmah dole ke za ki yi min maganin abin nan, ko kina so ko ba kya so.” Ta zaro wayarta ta shiga kiran Anty Salma da ta zamo k’anwar su Mahmahnce ta kuma san ita kad’ai zata iya lankwasata ta saka Mahmahn ta yi abinda take so ta shirya ko ba ta shirya ba, duk da ta ga dare ya tsala bai hanata doka mata kiran ba, tunda ta san dare ne na azimi goman k’arshe kuma ta tabbata kowa idonsa biyu.
Zatonta kuwa ya yi daidai don bugu biyu Anty Salman ta d’auka cikin tsoro ta ce “Nanna lafiya?” Kuka ne ya k’wacewa Nannan, kukan da take neman inda zata saukeshi sai yanzu ta samu. Anty Salma ta saka salati ta ce “Lafiya Nanna?” Nan Nannan ta shiga bata labari da k’arya da gaskiya. Anty Salman ta dakatar da ita ta hanyar cewa “kan uban can, ita kuma Yayar ta amince? Hamda fa kika ce ya aura jjnin Sakna? Saknan da ta mayar da ita bora a gidan miji to wallahi ba zai yiyuba da safe Zan zo gidan, ki ma share hawayenki ba y’ar KK MuD’allab ba ko d’iyar shugaban k’asan Amuruka ce sai ya saketa, da ni ake zancen ban da abin Yaya ba yanzu bane zata nunawa Sakna kuskurenta..”
Farin ciki da murna ya cika zuciyar Nanna, ta tabbata Anty Salma zata aikata duk abinda ta saka kanta, don haka barcin za tayi har da munshari…..
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Kusan mintuna biyar suna knocking a bakin k’ofar sashen nasa bai bud’e ba, kamar ya san da ita aka zo ya d’au lokaci kafin ya bud’e, fuskarsa a d’aure yake dubanta, yana mamakin yarda lokaci d’aya ta birkice masa kamar ba Hamdan da ya sani ba, mai son sa da jin maganarsa, ta bi ta hau maganar Didi ta zauna a kai kamar wani fad’ar annabi, idanunsa cikin nata yana k’are mata kallo, kallon da ya takurata ta sunkui da kai, gaba d’aya kallon ya saka mata wata irin nutsuwar da bata shirya yinta ba, ita kuwa Sa’ada dariya ce take son kamata ganin yarda ma suka manta da ita a wajen har sai da ta yi gyaran murya sannan Hammad ya ankare ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya kafin ya mik’a hannu ya amshi basket d’in abincin da yake hannun Sa’ada ya ce “Je ki abinki Sa’ada akwai aikin da
Zata min yanzu zata taho.” Hamda tayi raurau da idonta kafin ta ce “Wallahi Didi tace min kada na dad’e ka ga fad’a zata min.” Ya watsa mata wani irin kallo da yasa Sa’ada wata irin dariya ta so kub’uce mata ta juya da sauri ta wuce don ba su saba y’ar wasa da Yaya Hammad d’in ba, amma kallon da yake jifan Hamdan da shi abin so ne ga kowacce mace mijinta ko saurayinta ya dinga mata shi, kallo mai nuna zallar so da nuna kewa ga wanda akewa shi, hannunta na rawa ta mik’a masa flask d’in kunun “Please Yaya Hammad ka karb’a kafin kasa Didi ta tara min mutane…” “Masifar Didi da tsinuwar mala’iku wanne kika fi gudu? Idan ba zaki shigo ki je kawai.” Hawaye ne ya fara k’ok’arin zubo mata kafin ta saka k’afa cikin falon gabanta na fad’uwa, ta tsaya cak a bayan kujera shi kuwa tab’e bakinsa ya yi ya cigaba da zuba abincinsa lura da yayi da ko cewa ya yi ta zuba masa yarda take a tsorace ba zata zuba ba, shi har mamakinta ma yake kada fa ta zamo masa bagidajiya ba irin Nanna da take kanainayeshi ba, da sonsa da ba son ransa take fincikar ra’ayinsa sau tari. Ya fara kurb’ar kunun idanunsa suna yawo a kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login