Showing 93001 words to 96000 words out of 117648 words

Chapter 32 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

ta ji yace “Wani sabon salo kika samu? Sai kace sabon aure ba zaki dawo nan kusa da ni ki zauna ba? Saboda kina tsoron Didi ko?” Ya taune leb’ensa d’aya kafin ya furzar da huci ya ce “Idan kika ce haka zaki min wallahi a gadon Didin zan zo na karb’i hak’kina haka kawai saboda wata bidi’a ta banza da wofi ki yi ta d’aukan zunubi da azimin nan, ke kika jiyo ni ina da wata matar yau ma rashinta ne yasa nake binki duk da ba ni na jawoki ba, ke zaki je ki yi ta kwana rungumar filo ai dama Sabonki ne tun kina budurwa.”
Wani irin kallo take jifansa da shi kamar ta zunduma masa ihu jin abinda yake ce mata, ita zai gayawa wani yana da mata ai ta fisa sani dama ita ta kawo kanta har da zai tsaya ci mata mutunci, haushi da takaicin kalamansa yasa ta juya a zuciye ta fice daga falon duk da tana ji yana k’wala mata kira. Ya saki ajiyar zuciya yana jin takaicin yarda bakinsa ya ja shi ya sake b’allowa kansa ruwa ya santa sarai da d’an banzan kishi, ba waya a hannunta balle ya kirata.


Tana zuwa falon ta tarar da bak’i a falon Didin atamfofine da laces da shaddodi take ta bud’ewa, sai wasu akwatina biyu da kit a gefe, kasancewar zuciyarta ba dad’i yasa ta yi k’ok’arin shigewa d’aki bayan ta gayar da bak’in mazan da suke zaune. Didi ta ce “Ke Hamda zo nan ai sak’on naki ne, KK ne ya aiko ko da yake wannan ni ya aikowa ya ce a rabawa dangi, wancan akwatinan dai su ne naki.” Hamda ta koma ba don ta so ba ta hau bud’e kayan sabuwar wayar tafi tafiya da imaninta wacce take cikin kit d’in sai dantsatsetsiyar sark’ar gold wacce da gani babu tambaya dollars ta sha kuka wajen siyanta, akwatinan kuwa laces ne dandatsa-dandatsa da atamfofi super sai mayafansu HD Veils da jakunkuna uku da takalmansu, a ranta ta yi farin ciki da kayan amma yarda zuciyarta take tunzira da kalaman Hammad yasa fuskarta bata nuna ba, Sa’ada kuwa sai tsalle take tana d’aga Iphone 14 pro max tana cewa wallahi yarinya kin shigo gari. Bata tab’a komai a kayan ba ta mik’e ta shige d’aki, tana shiga ta yi wurgi da d’ankwalin kanta gashinta ya wargaje, sai sannan wani kuka mai k’arfi yazo mata, ji take da tana da hali da ta fasa auren Hammad d’in don ita tana daga cikin jinsin mata masu zafin kishi. Kuka ta yi sosai bata fito falon ba har sai da Sa’ada ta shigo kiranta Didi ta tara ayarin gidan wai zata yi rabon kayan sallahr da KK ya kawo.


Fuskarta a kumbure ta fita, duk wanda ya kalli idanunta ya san ba k’aramin kuka ta sha ba, shi kansa Hammad hankalinsa a tashe yake dubanta ji yake da da hali da ya kai mata runguma ya rarrasheta, amma ina ko arzikin kallo bata samu ba, sai ma harara da ta wurga masa ta yi k’asa da kanta. Abbu ne ya lura da yanayinta ya ce “Zo nan Hamda me ya sameki haka? Naga kamar kin yi kuka?” Girgiza kai kawai ta yi tana k’ok’arin mayar da hawayen da suke son sake zubo mata, murya a dashe ta k’arasa kusa da Abbun tana girgiza kai ta ce “Bakomai had’e da gallawa Hammad harara.” Didi ta ce “Kaima dai Ummaru da shirme ka ke, kukan me zata yi banda na farin cikin samun uba kamar KK ga uban kaya da ya d’and’aso mata ga shegiyar waya.” Hamda ta zabga mata wani kallo kafin cikin takaici ta ce “Ni ba kukan da nake ba kenan, ke wannan ya dameki ai dama tun kafin Ya zo Abbu yana mana duk abinda muke so.” Sosai Abbu da Ammi suka ji dad’in amsar da Hamda ta bawa Didi, idan ita ta manta gwara Hamdan ta mata matashiya kuma ya san ko nan gaba Hamdan ba zata gujeshi ba. Didi ta ce “Y’ar banza mai ido a tsakar ka, duk tsiyar Ki dai da KK d’in zaki tunk’aho..” ta sake zunb’ura baki “Ni wallahi da Abbu zan yi tunk’aho tunda shi ya yi d’awainiya da ni har na girma.” “Ke kika jiyo, ba wannan yasa na tara ku ba, kai Hammad tunda Sadiya ta k’i zuwa bak’in cikin duniya ya isheta kaje ka kira min ita ko zuciyarta zata buga sai ta ga wannan kab’akin arzikin, don ina lura da ita tunda lamarin nan ya faru shikkenan Sadiya halin uwarta ya fara bayyana tare da ita, yo uwarta banda dai idan taso mutuniyar kirki ce ai da ba ta zama aminiyata ba, don ko farar k’asa aka shafe min d’aki da ita sai hassadar ta ta nuna, ta dinga nurk’ufanci kenan, sai dai Akwai kyauta, kawaici da alkunya sumumu kasau ce ta gaske..” Hammad ya datsi leb’ensa banda idanuwan su Abbu yau kam da ya ganar da Didi kurenta. Ya saka kai ya fice yana ji tana fad’in “Sai dai hararar duka dai ba zan daku ba, ja’iri mai idanuwa kamar na muzuru.”




Yana saka kai d’akin Mahmah ya ji tana waya tana fad’in “Sakna nace miki yanzu fa zan je don na ji ance duk ta tara mutane wai za tayi rabon kayan sallah, to yanzu zan je wallahi nace and Atabau bana son auren…..” Hammad ya tura k’ofar idanunsa zube cikin na mahaifiyarsa yana jin takaicin yarda Salma take neman jirkita masa zuciyar Mahmahnsa mai adalci, baya son laifin da yake tsakaninta da Ammi ya shafi aurensa da Hamda, su d’in ma k’ok’arin sa kullum su fuskanci juna su zauna lafiya duka-duka duniyar ma nawa ce, ya saki ajiyar zuciya yana zama a kujerar da take gefen gadon a hankali ya ce “A sani na dake Mahmah uwace da za’a yi alfahari da ita, duk gidan nan an shaida cewa ba kya barin kishin da ke tsakaninku da Ammi ya shafi mu y’ay’a, abubuwa nawa kika shanye sai yanzu da rayuwar ta zo gangara za’a samu wasu can daga gefe su zuga min ke Mahmah, don Allah kada zuciyarki ta amince da zugarsu su zo su saka ki ki yi abinda zai zubar mana da
K’imarki da mutuncinki da
Ake gani, kowa fa ya shaida hak’uri da juriyarki a zaman aure wanda muke fata ya dalilin haka Ubangiji ya yi miki sakamako da jannatul Aaliyah. Don Allah Mahmah ki janye wancan furucin da na ji kina yi a waya ko ma da wa kike yi na tabbata Ba shawara mai kyau yake baki ba wacce duk wani mai sonki zai ba ki, ki d’auki Hamda kamar y’a insha Allahu ba za ki yi dana sanin aurenmu ba, sai kin yi alfahari da haka sai kince gwara da aka yi, kuma ni Mahmah wallahi ko wa na aura ba zan bari ta rainaki ba, Zan jajirce wajen kare martabarki da k’imarki, kuma in dai tana sona dole ta miki biyayya.” Sosai zuciyarta ta samu nutsuwa har ta ji tana jin kunyar abinda ta so aikatawa duk da Allah ya dubi zuciyarta bata aikata ba, ita kanta ta san ba halinta bane sharrin shaid’an ne da karakainar zuciya suka so dulmiyar da ita, ta godewa Allah da ubangiji ya kawo Hammad ya ankarar da ita abinda zuciyarta da tunaninta suka so su gusar mata, Sai ta samu kanta da jin kunyar Hammad d’in shi kansa ta yarda yana d’an cikinta shi ya zauna yana tunasar da ita abinda ta manta, kaiconta da ta so jawowa kanta da zuri’arta abin kunya, da da wani idon zata dubi Hamda yarinyar da ta rik’eta tamkar Uwa take ganin daraja, k’ima da mutuncinta, sau tari Idan Uwarta ta tunzirota tana kuka idan Didi bata nan, nan wajenta take zuwa ta samu sauk’in zuciya. Ta gyara zamanta tana sakin wata ajiyar zuciya ta murnar rashin aiwatar da k’udirinta ta tabbata da mutuncinta ya zube a idanun duk jama’ar gidan. Hammad ya saki murmushin samun nasara kafin ya mik’e da kansa ya yafa mata mayafin yana fad’in “Alhamdulillah, Da Allah yasa ki ka fahimceni yanzu ma Didi ce ke nemanki, kowa ya halarta banda ke.” Ta mik’e jikinta a sanyaye ta bi bayansa zuciyarta tana jin farin ciki a hankali ta furta “Madalla da kai ubangiji madalla da samun Y’ay’a na gari ko da su kad’ai aka barni ba abinda zance sai Alhamdulillah!”






A falon kowa ya hallara, ta samu zuciyarta da tsinkewa ta fad’i tunanin da tuni a cikin jama’ar nan zata zo ta zuba rashin mutunci. Didi ta zuba mata ido cikin takaici ta ce “Ba shakka Sadiya, wato nema ki ke duk wasu d’abiu na Sakina da ta zubar da su, ke ki tattara ki yayima ki zubawa kan ki, ana yabonki Sallah za ki kasa alwala, idan banda haka mutun nawa na aika kiranki ki ka yi burus da ni sai yanzu da d’anki ya je ya lallab’o ki sannan za ki zo ko?” Girgiza kai Ta yi kawai had’e da zama cike da kasala ta ce “Ki yi hak’uri Didi, ba k’in zuwa na yi ba bana jin dad’i ne.” Didi ta girgiza kai “Ko da na ji, nan ina nan ina mamakin yarda ki ke nema ki canja daga ainahin sunanki na Halimatu wato mai hak’uri, ai duk wata Halima da hak’uri aka santa idan ba so ki ke ki zama masifatu ba, yo fisabilillahi waye bai san kalar hak’urin da kika yi a gidan nan ba, k’iri-k’iri Umaru ya dinga banbanta ki da abokiyar zamanki kai wallahi Umaru ina jiye maka tashi ranar alk’iyama da shanyayyen jiki Idan Sadiya bata yafe maka hak’kintaba kai da matarka.” K’asa Abbu ya yi da kansa yana jin kunyar yaransa Su Hammad da suke zube a wajen, wani abu ne na tausayin Sadiya ya taso tun daga yatsansa ya lullib’e idanunsa, kunyarta yake ji sosai da ta yaranta, yau kam Didi ta b’aro masa aiki ta kuma ankarar da shi abinda ya dad’e yana son gyarawa son zuciya da sharrin shaid’an had’e da bin k’awace-k’awacen duniya ya hana shi ankarewa, sai yau da Didi ta taso da maganar takaicin kansa ya kamashi ya kasa had’a ido da kowa a d’akin musamman Sadiyar da ta sauke nata idanun a kansa tana son taga yarda zai yi, Ba shi da laifi a wani b’arin Sadiyar ce ta janyo koma mai ya faru, wata zuciyar kuma na k’addamar masa da laifinsa da hasko masa tarin kuskuren da ya tattafka a tsawon zamansu da Sadiyar, ya wajaba kam a gareshi ya nemi yafiyar ta kafin abinda Didin ta fad’a ya tabbata a kansa ya tashi da shanyayyen b’arin jikin, yana kallon idanun da Humaid ya zuba masa ya tabbata Ba tun yau yaron yake rik’e da shi a ransa ba, don duk ya fi su Hammad zafin zuciya. Ya gyara zamansa idanunsa cikin na Sadiyar yana sakar mata da murmushi zuciyarsa na hasko masa tarin kyawawan halayenta da nagartarta duk da ta b’angare d’aya take da cikas hakan ba zai zama hujja a gareshi da zai kasa yi mata adalci ba, d’auke kai ta yi tana fuskantar Didi da ta fara Rabon sufofinta, zuciyarta fes ta tabbata daga yanayin murmushin da ya sakar mata sak’on Didi ya isar masa burinta ya yi aiki da hakan su yi zamansu lafiya cikin aminci da k’aunar juna, abu d’aya ne Ba zata iya wannan kwamacalar soyayyar ta zamani, za dai ta k’okarta wanda ta ga zata iya, tausa, shafa masa mai amma banda duk wani kalar barikanci da Sakna take yi, wannan kam ta barwa yara ita da kanta ta yarda da maganar bahaushe da ya ce ‘In An girma a san an girma’






Jikar Nashe taku ce!




❤️❤️❤️❤️❤️🙏
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Zuciyarta fresh ta tashi tana jin ta wasai duk wani tarin shirgi na b’acin rai da aka dasawa zuciyarta tuni ya zagwanye. Wanka ta yi sosai ta hau gyara jikinta, yau kam da tunanin Hammad ta tashi ganin tun ranar bai sake neman keb’ewa da ita ba, bata sani ba ko fushi yake da ita ba, duk sai ta ji hankalinta ya tashi. Ta feshe jikinta da tsadadden turarenta duk da azimi ake amma sanin cewa ba inda zata yasa ta shiri na musamman. So take ta zagaya Sassan gidan ta gaishesu abinda ta dad’e ba ta yiba. Sosai ta yi kyau cikin sassauk’ar doguwar rigar da take jikinta ta yane kanta da mayafin rigar kafin ta goga lip stick.


Dama tuni ta gyare b’angaren Didin tun suna barci da safe. A falo ta samesu suna kallon wa’azi a tashar Sunna t.v. Tsananin kyan da fatarta ta sake ne yasa Asma’u sauke magananta a kanta tana mamakin canjawar Hamdan cikin lokaci k’ank’ani, da alama gyaran da ta fara mata magungunan suna bin jikinta yarda ya kamata, tana tunanin anya kuwa Hammad zai iya jurewa ya hak’ura har lokacin da aka d’iba na bikin nan? Didi kuwa fad’i take “Tubarakallah Masha Allah, yanzu da kina da wannan kyan duk bai bayyana ba sai yanzu, gaskiya dai Sakina ta musgunawa rayuwarki duk ta bi ta sukurkuta ki ba a ganin komai a tare da ke sai tarin manyan idanuwa wannan kam kamar kya kwashe mutum da su.” Hamda ta tsuke fuskarta tsam yanzu kam sam bata son a dinga zagar mata Amminta jinta take har k’okon ranta. Ta d’an gyara tsayuwarta kafin ta ce “Bari na shiga gida na gaishesu kafin time d’in d’ora abinci ya yi.” Didi za tayi magana Asma’u ta yi saurin cewa “Maza ki je, hakan ya yi kyau sai kin dawo. Y’an uwanki ma yau suna hanya.” Cikin farin ciki ta ware ido don ta san su wa UMMA Asman take nufi y’ay’anta da suke Dubai, kuma akwai sa’arta da suke mugun shiri a duk lokacin da suka Nigeria, zata iya cewa ma bata da aminiyar da ta wuce Sa’ada, da sauri ta ce “What time za su iso Umma?” Ta d’aga hannu tana nuna mata 4 da hannunta, Hamda ta yi saurin cewa bari na yi sauri na dawo na san mai zan dafa musu Sa’ada na san dambun shinkafa.” Asma’u ta girgiza kai had’e da cewa “Tabbas, shine favorite d’inta, amma su su Babana ai ba sa sonsa.” Ta d’an sosa kai tana son ta ce ina ruwanta amma kasancewar tunda can bata da wannan k’warin gwiwar yasa ta kasa furta abinda yake zuciyarta illa murmushi da sosa kai ta fice da sauri. Ta bar Didi tana zabgawa Asma’u harara kafin ta ja tsaki ta ce “Wallahi Asma’u idan kika ce haka zaki dinga min shishshigi akan yarinyar nan tsaf zan tattara komatsanki ki koma waccan shiyyar da ake sauke bak’i, saboda Allah ta ya zaki ce ta je ta gayar da mutanen gida? Ni fa bana son su shirya da uwarta balle ta samu fuskar da zata nuna min iko akan yarinyar da
Bata san yarda aka yi ta girma ba.” Asma’u murmushi kawai ta saki tana jaddada rigima irin ta Didi ban da haka ta ya zata yi ta raba yarinya da uwarta ta ce da ita kawai zata yi shiri? Sai dai bata tankata ba ta ja baki ta yi shiru duk da tana jin Didin na sake mita tana bala’i kamar ta ci babu.




A harabar sashensa ta hango shi a tsaye, hannayensa nad’e a k’irjinsa tunda ta hangoshi yanayin bugun k’irjinta ya sauya shi d’in ma da sauri ya kawar da idanunsa daga kanta, duk da tursasashi da zuciyarsa take yi amma ina ya san yarda yake azimin nan bai kamaci ya kafa mata maganai ba don tabbas aziminsa zai iya karyewa don haka ya d’auke kai ya cigaba da dannan waya. Haushi ya kama Hamda ganin yarda ya yi banza da lamarinta hakan ya sa zuciyarta ta k’untata ta fara tunanin menene kuskurenta? Da har ya jawo mata shagulatin b’angaro haka, ta ciji lab’ba in dai ita ce gidan ya tarar wallahi sai ta rama. Sashen Mahmah ta fara isa, tana zaune Nanna agefenta sai Asma’u da suke ta sake ingiza mata zuciya, ta ji a duniya ba auren da ta tsana sama sa auren Hammad da Hamda ta kuma ko wane hali sai ta mayar da shi labari. Sallamar da tayi da sanyin murya ya janyo suka zubawa k’ofar ido, ta iso ciki tana taku kamar wahainiya da yasa gaban Nanna bugu musamman ganin jikin da ake kira dirarren jiki, ta had’iye wani Abu da kyar da take barazanar toshe mata numfashi kafin ta kalli Hamdan kafin ta mayar da kallonta kan Mahmah da take ji itama kamar ta je ta rungume Hamdan saboda har ga Allah ita ba tun yanzu ba tana Jin son Hamdan amma ba matsayin surikarta ba, sharrin zuciya da zuga da ake mata be ya so ya makantar da zuciyarta, duk da yanzun ma ba wai ta janye k’udirin zuciyarta bane. A rakub’e Hamda ta zauna murya can k’asa ta ce “Ina kwananku?” Da kyar suka amsa kamar an musu dole jikinta a salub’e ta mik’e ganin kamar ba sa marabtarta, ta fice daga sasan zuciyarta cike da mamakin canjawar Mahmah a lokaci guda mace mai kyawun zuciya da kamala don ta tabbatar tafi Ammi sanin mutuncin d’an Adam da darajashi. Ta girgiza kai kawai idanunta na sake sauka kan Hammad da wannan karan ma ya yi kamar bai ganta ba, ta tura k’ofar shiga sassan Amminta tana tunanin ita kuma ko wani irin amsa zata yi mata?


Zaune ta samesu a tsakiyar falon, sun saka Ammin a tsakiya fuskokinsu d’auke da walwala da alama hira suke cikin nishad’i, suna ganinta suka sakar mata murmushi musamman Ammi da bakinta ya kasa rufuwa bata tab’a zaton Hamdan zata nemeta ba. Cike da rashin sabo ta tsaya a gefe, bata Saba ba, bata saba Idan suna irin wannan zaman ta yi musu katsalandan a ciki ba, Ammi cike da dana sani ganin ita ta sabar mata kafin ta shigo sai ta nemi iso, sai ga shi yau abin ita da kanta ya mata banbarakwai ta mik’awa Hamdan hannu fuskarta d’auke da kunya ta mata alamar ta taho. Da d’an murmushi a fusakr Hamdan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login