Showing 108001 words to 111000 words out of 117648 words
Chapter 37 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
shugaban k’asa ai sai haka.” Hamda tab’e bakinta ta yi tana cigaba da danna wayarta haka kawai ta samu kanta da gushewar murnar lefen daga zuciyarta. Ganin bata son magana ya sa Sa’ada ficewa daga d’akin.
Didi ta ja kayan fad’ar kishiyar Nanna gabanta akwatina set biyu ga mukullin dank’arareyar mota tab’e baki ta yi kafin ta ce “Ni fa ban ga dalilin wad’annan kaya da za’a laftawa waccen matar ba, yo fisabillahi ai ba son Hamdan take ba, yanzu kuma don rashin kunya sai ta saka hannu ta karb’i kyautar ubanta.” Ba wanda ya kulata sai bambamin fad’a take kafin ta ce “Ke Sa’ada tafi ki kira min ita na kafa mata sharad’ai idan ta amince falillahi hamdihi idan bata amince ba kuwa wad’annan kayan ba rabonta bane.” Lauratu ta ware ido kafin ta ce “Wani sharad’i kuma Didi ai ita kamata ya yi a lallasheta musamman an mata laifi wallahi.” Didi ta watso mata harara kafin ta ce “Lauratu ki fita idona mutuniyar banza laifin uban me aka mata? Auren da ya yi ne laifi?” Shigowar su Nannan ce ta sa Didi jan tsaki murya a k’asa ta ce “Haka kawai mata tana zaune shirin a wani bata kaya.” A fili kuma sai ta washe baki “To zauna ki ga kab’akin arziki Uban Hamda dai ya k’watarwa y’arsa y’anci don haka kada in ji kada in gani wallahi kin wa Hamda wani abu irin wannan dukiya da ya narka miki na tabbata don ki zauna da y’arsa lafiya ne, idan kuma ba kya son zaman lafiyar a mayar masa.” Nanna fuska a had’e take kallon kayan kafin ta ja ajiyar numfashi ta ce “Allah ya bamu zaman lafiya ya kawar da y’an ba ni na iya a cikin lamarin.” Didi ta kalleta shek’ek’e “Su waye y’an ba ni na iyan? Eeh lallai wuyanki ya isa yanka. Ta wulleta da mukullin kafin ta ce “Kin yi da uwarki Sadiya da Maryama da kuke kira Dida. Rasa kunya.” Murmushi Nanna ta yi kafin ta ce “Ni fa Addu’a na mana Didi.” Daga haka ta mik’e tana bud’e kayan ta yaba k’warai da karamci KK ta masa addu’a sannan ta saka su Sa’ada su tayata kwasar kayan.
__________
A kashegari Hammad suka tafi da matarsa Birmingham don su tattaro kan iyalinsu zuwa gida Nigeria. Ba k’aramin kai zuciya nesa ya yi ba, da ya k’i neman Hamda so yake ya d’orata akan saiti ta san zaman aure suke yanzu ba zaman saurayi da budurwa ba, hakan da ya yi kuma ba k’aramin hassala zuciyar Hamda ba, ta tattara lamarinsa ta watsar suma suka fara shirin tafiya Umara.
______________
Tsawon sati biyu suka yi a Umarar a wannan gab’ar kuma a hanyar dawowa Hamdan ta fara wani irin zazzafan zazzab’i da haraswa ta galabaita sosai don komai bata son ci sai Apples da grapes hakan ya sa ta yi guzirinsu da yawa daga Saudi. Duk da Asma’u da Amminta sun gane ba su furta mata ba su tsoronsu d’aya ma
Ranar da Didi zata fuskanci akwai cikin sun san akwai tab’argaza don haka suka yi shiru, Ammi dai ta mayar da hankalinta sosai kan kula da autarta gaba d’aya yanzu burinta ta ga Hamda ta kama zuciyar Hammad yarda ya kamata don ta lura kamar har yanzu basu kai matakin da take so ba, tunda har zasu iya d’aukan lokaci Suna gaba, don tana d’aukar wayar Hamdan ta ga ko Hammad d’in sun yi waya sai ta ga ba kiransa haka nan
Text messages sai abin ya fara bata tsoro ya zama dole ta sanar da Hamda sirrin kame zuciyar d’a namiji. Tun a daren ranar da suka dawo ta rutsata a d’aki “Hamda me ke tsakininku da mijinki?” Hamda idanunta ya kawo ruwa ta d’ago tana kallon Ammin kafin murya a dashe ta ce “Ni ma fa Ammi ban sani ba haka kawai ya daina min magana.” Ammi ta girgiza kai “labari kike Hamda ta yaya kina amarya miji zai yi wannan dogon fushin da ke? Ki fito ki gaya min gaskiya ni mahaifiyarki ce.” Kuka ne ya fara zuwa mata cikin muryar kukan ta shiga ba wa Ammin labari. Ammin tana gama jinta ce “bud’e kunnenki ki ji da kyau ba ‘a kama zuciyar miji ta hakan da kika b’ullo na tabbata k’in bari ya kusanceki kike shi yasa ya yi wannan dogon fushin dake idan kika bari ya saba da kusantar jikinki shine ba zai iya dogon fushin da ke ba, saboda ko ya yi dole ya sauko ba ‘a wa miji rowar kai kina ji na?” Tana hawaye ta d’aga kai “Yauwa Yanzu na ji ance gobe zai dawo kuma saura kwana biyar a fara biki ban ce ki bari ya kusanceki yanzu ba, ki bari akwai had’in da zan miki da zarar an kaiki gidansa ya kusanceki ina tabbatar miki ba zai sake iya d’aukan ko awa biyu yana fushi da ke ba, ki kuma dage da
Shan zuma da tsumin da na baki turaren tsuguno kada ki yi wasa dashi kin ji ai.” Hamda a kunyace ta d’aga kanta duk da ta ga ita Ammin ba abinda ya dameta kamar ma da k’awarta take magana. (Haka ake so yanzu iyaye su zama ki zama k’awar y’arki, kafin wata can ta d’orata a turbar rashin hankali ta kashe mata aure a banza a wofi, amma wasu iyayen sai su zauna kunya yaranki su rasa inda za su kai matsalarsu su ji sanyi sai wajen k’awaye.) Ammi ta d’an harareta “Ki bar wani sunkuyar da kai ban amince ki yi aminiya da wata ba da ya zarce ni ko yayyenki indai a fannin aure ne.” Hamda ta d’aga kai tana karb’ar cup d’in da Ammin ta mik’o mata damammen nonon Shanu ne da ya sha had’in magani na su na y’an Jordan, Hamda kuwa sai da ta shanye tas sannan ta mik’a mata cup d’in. “Ki ajiye hankalinki sosai akan mijinki ki fahimci abinda yake so d wanda baya so ki san ta sigar da zaki bi ki kwantar masa da b’acin ransa ko fushinsa ta yarda koda daga waje wani ya b’ata masa rai zai ji ba inda yake son ya zo sai wajenki. Ban da d’aga murya fiye da ta miji yana rage k’ima da martabarki a idanun miji, ban da kai k’ara yana wanzar da rashin zaman lafiya a rayuwar aure ko fad’a kuka yi ku sulhunta kanku ba tare da third party ba.” Sosai nasihar Ammin ta shiga zuciyarta sai ta samu kanta da alfahari da samun mahaifiya kamar Amminta. Har bata san sanda ta shige jikinta ba tana jin wani farin ciki, ita ma Ammin sosai ta rungumeta a jikinta dukkansu nutsuwa na saukar musu.
_______________
Da safe KK ya yi niyyar zuwar wa danginsa da lamarin da ya kira da bazata, ya san tabbas yau zai gigita tunaninsu da hankalinsu gaba d’aya.Hamda da Didi ya sa Driver ya d’auko masa da suka zo ya ce su zauna kada su shiga hall d’in taron familyn na su da suka saba yi duk shekara sai ya aika da kansa an kirasu. Ya shige d’akin taron ya bar Hamda da Didi zaune a cikin mota Didi dariya kawai take tana son ta ga yarda idanun y’an banza yake.
A falon gaba d’aya ahalin K. Mud’allab sun hallara ana ta gaisuwar zumunci kowa ya yi masa jawabin kafin a mik’awa KK mic d’in ana sauraran nasa jawabin, burinsu su ji wannan shekaran nawa nawa zai ba su kamar yarda ya saba basu duk shekara. Gyaran murya ya yi kafin ya ce “Alhamdulillah yau ina tafe da albishir mai dad’in ji.” Sosai bakunan mutanen wajen suka dinga washewa tamkar gonar auduga burinsu su ji daddad’an albishir d’in. KK ya cigaba da kallonsu yana sakin nasa murmushin da suka rasa musabbabinsa “Alhamdulillah, Ina farin cikin sanar da ku auren y’ata ta cikina Hamda Kamal Kabeer Mud’allab……..”
Jikar Nashe ce.
[1/12, 7:47 AM] Nazeefah Nashe: Tsit d’akin taron ya samu bak’uncin shiru, zuk’atansu d’auke da mabanbanta tunani da gaske lamarin ya zo musu a bazata, idan ba kunnensu ne ya ji ba daidai ba kamar KK Mud’allab ne yake sanar da su yana da y’a ta cikinsa wacce yake shirin aurarwa, mutumin da suke ran mutuwarsa nan kwana kusa don ma hak’ansu ya kasa cimma ruwa a duk sanda suka yi yunk’urin kisan na sa basa samun nasara sosai yake samun kariyar ubangiji daga duk wani sharri su da makircinsu. KK ya sake sakin murmushi ganin yarda duk fuskokinsu suka nuna zallar tashin hankali da rud’ani, ya cigaba da magana cikin nuna k’arfin k’udirar ubangiji “A shekaru sha tara da suka wuce bayan tsawon lokaci ina neman haihuwa Allah ya na d’aukar ransu dabarar auren Sirri ya zo zuciyata haka ya sa na d’aura aure da Mahaifiyar Hamda, na kuma b’oye bayyanuwar hakan har zuwa yanzu da halin bayyanawar ta yi, bayan Hamda kuma har ila yau ina da k’anwarta Kamla da matata ta yanzu ta haifa min aka kuma raineta a gidan da Hamda ta taso, sun tashi ne duka a k’ark’ashin tarbiyya d’aya.” Kafin ya k’arasa duk wad’annan bayanin tuni zuciyoyinsu sun cunkushe sun kuma rine da tsananin b’acin rai ji suke lamarin yazo tamkar wani irin almara zuciyoyinsu bugawa suke da tsananin k’arfi suna jin tsanar KK na k’ara gauraye jini da b’argonsu duk wani shiri na su ya tashi a banza kenan, ba su sare da lamarin ba sai da KK ya umarci d’aya daga cikin body guards na sa su je su shigo da bak’in da suke mota. Zuwa lokacin tuni zuk’atan y’an uwan nasa sun tafi akan yarda za su yi su kawar da zuri’ar ta KK kusan dukkansu tunaninsu d’aya ne tun ma kafin su Hamdan su shigo falon. Ko k’aunar ganin tsatson KK d’in basa yi illa basaja da suka yi da fuskarsu zahiran suka nuna farin cikinsu yayin da bad’inin zuk’atansu suke cikin wani irin k’unci da rad’ad’i mai barazanar bugawar zuk’atan nasu.
Sassanyar muryar da ta yi musu sallama da ita ne ya sa dukkansu suka d’ago suna mata kallon mamaki musamman ganin yarda tsananin kamarsu da KK ta bayyana zahiri ba sai ka tambaya ba ka san jininsa ce. Babu inda ta bar komai na KK illa k’irar jikinta da tata ta zamo ta mata shi kuma tasa kuma ta zamo mai cikakken zati irin ta y’an maza. In banda haka harta da k’wayar idanunsu iri d’aya ce. Bisa tilas suka shiga k’ak’alo murmushi suna binta da shi duk da kana ganin murmushin zaka saka shi a mizanin yak’e wanda bahaushe yake cewa ya fi kuka ciwo. KK ya dinga bin fuskokinsu da kyakykyawan nazari yana sakin murmushi mai nufin ma’anoni da dama. Ma’anar da kai tsaya zaka iya fassarata da sun k’i Allah ya so. Har da masu tashi da k’ok’arin rungumar Hamdan daga cikin y’an uwansa Mata, Hamdan dai fuskarta a sake take bin su d’aya bayan d’aya tana gaishesu bisa umarnin mahaifinta. Didi kuwa gefe guda ta ja ta zauna a kujera ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya tana jifansu da kallon da kai tsaye zaka fassarashi da na neman tashin hankali mamakin su take sosai ganin yarda suka yi basaja a cikin rigunan mutanen kirki alhali zuciyarsu fal take da bak’in ciki k’yashi da hassada. Wata yarsa tana k’ok’arin jan Hamdan a jikinta Didi ta yi saurin cewa “Ahir wallahi me ye had’inki da ita za ki wani k’wakumata a jikin ki, wannan y’a ai ita sunanta An k’i Allah ya so.” Jikin mutanen wurin sosai ya fara rawa ganin Didi na shirin zabga musu rashin mutunci da alama KK ya sanar da ita wani labari daga cikin sashen labaransu. Ganin Didi na shirin bayyana musu alamun ya san wancan sirrin yasa KK cewa “Wannan itace Hamda kuma wannan tsohuwa da kuke gani itace matsayin mahaifiya gareni a yanzu…” Didi ta b’antari goro ta sake gyara zama tana turo d’auri ta ce “Gaya musu d’an albarka a yanzu da kuma har abada, ba kuma wanda ya isa ya nufoka da sharri matuk’ar ina raye na Riga na zagayeka da ayatul kursiyyu ko sarkin aljannu nan zai ganka ya bar ka eehe.” Gaba d’aya kallonta suke suna mamakin k’arfin hali irin na tsohuwar KK ya cigaba da cewa “Da izinin Allah kuwa Didi, Hamda da kuke gani itace matar jikan Didi wanda yanzu yake matsayin d’a a wajena a yanzu da kuma har abada tun tuni aka d’aura auren tariyar ce nan da kwana hud’u bayan an gwangwaje bikinsu da angonta Hammad dafatan za ku halarci bikin?” Gaba d’aya jikinsu sanyi ya yi baka jin komai sai ajiyar zuciya fahimtar da suka yi KK ya san duk wani makircin da suka dinga k’ulla masa da zubar masa da cikkunan yaransa da suka dinga yi, ashe duk ya sani shiru kawai ya yi, wasu daga cikinsu tuni kunya ta musu k’awanya yayinda wasu suka d’aura d’ambar sake wani shirin na ruguza duk wata rayuwar jin dad’i ta KK Mud’allab d’in. Ciki kuwa har da kawar da gudan jinin nasa da shi kansa daga doron k’asa. Didi ta ce “Ba dole su je ba musamman an san ba zuwan banza za’a yi ba, sai dai ina son ka ja musu kunne bana gayyar mugu ko maha’inci a wajen taron bikin jikokina shi kuwa munafuki dama ko ido hud’u da ni baya iya yi haka nake da wannan kwarjinin daga rabbil izzati yauwa dafatan an ji da kyau.” Ta mik’e hannunta cikin na Hamda suka saka kai suka fice KK ma ya bi bayansu inda tsirari daga cikinsu suka mara musu baya, inda saura suka zauna jigum-jigum ga shi kowa yana da abin cewa amma a lokacin bakunasu sun gaza furta ko da kalmar ‘A’ illa jan numfashi da furzar da wani irin huci daga bakunansu.
Suna fita KK ya sake raka su mota had’e da sanar Didin zuwa yamma su Hammad za su iso daga Birmingham Didi ta ja tsaki “To Allah na tuba ni meye had’i na da shi bayan tunda ya tafi bai neme ni ba, ai idan aure bai kawo shi ba shika zai kawo shi ina nan ina jiransa.” KK dariya kawai ya yi yana jinjina rigimar Didi a ransa.
Tunda suka shiga motar take jin haraswa sakamakon sanyin A.cn da ya had’u da k’amshin freshner da yake dukan hancinta kasancewar ba a wannan motar suka zo ba a waccan da suka zo ba wannan k’amshin tun tana kawar da kai har lamarin ya gagareta ta shiga k’unshe baki tana yiwa Didi alamar a tsaya amma kan kace mai ta Kelaye aman gaba d’aya a jikin Didi, da sauri ta ja gefe don ba k’aramin k’yamar amai bane da ita, ita kuwa Hamda sosai ta yi amanta Didi fuskarta kamar ta yi kuka ta shiga sababi “fisabilillah Hamda ba sai kice amai ki ke ji ba sai ki daddage ki kelayo min shi a jiki, ba ki san yarda nake k’yamar amai ba to ma fisabilillahi me ya sameki? Na ga dai k’alau muka taho daga gida.” Hamda bata bi ta kanta ba ta fita daga motar bayan drivern ya tsaya ya bata ruwa ta wanke jikinta itama Didi haka ta fito tana kyab’e baki kamar ta ga kashi ta shiga wanke aman da ya b’ata mata hijab da leda a hannunta k’arshe ganin ya k’i fita ga wani k’arni da yake ya sa ba shiri ta cire Hijabin ta wurgar da shi, Driver yana zare ido ya ce “Hajiya ya ki ka wurgar?” Didi ta ja tsaki “Wallahi duk k’aunata da Hijabin gwara na yar da shi to me zan yi da shi bayan ta kelaye shi da amai Kuma da tsada na siyi abuna dama idan ka je ka fad’awa KK duk abinda ya faru na san zai saka a d’inka min sababbi ke kuma wuce mu je burina in je toilet na yi wanka.” Hamda ta koma motar duk jikinta ya yi weak har wani duhu-duhu take gani. Didi gaban motar ta koma ta shige tana fad’in nan zan zauna ina dalili na shiga ki sake kelaye ni da amai sai kace mai yaron ciki.” Gaban Hamda ya fad’i jin abinda Didin tace ta fara tunanin rabo ta da period tabbas da alamun k’amshin gaskiya a zancen Didi idan kuwa ta tabbata ciki ne da ita da wani ido zata amsa wa Didi tarin tambayoyinta? Ta ce mata a ina Hammad ya yi mata ciki? Ta d’an lumshe idonta kawai tana jin wata irin kasala ina ma ta samu mai mata tausa?
Suna komawa gida suka tarar da bak’in jordan sun zo, mamaki ya kama Hamda ganin yarda suke haba-haba da ita mutanen da da sam ba su damu da ita ba, bata tsinke da lamarin sai ganin tarin kab’akin kayayyakin da suka kawo musu ita da yayyenta kayayyaki ne na gani na fad’a na mutanen jordan. Ammi ta zaro wani material mai masifar kyau Milk colour mai ratsin ja ta mik’awa Hamda an turarashi da turarukan wuta y’an asali sai zabga k’amshi ya ke. “Maza ki masa ado da wannan yau ance za su dawo ki tabbata kuma kin shanye duk abinda na baki don bana son wasa Sam a cikin lamarina.” Hamda ta karb’i kayan idanunta cikin na wata sistern Ammin da ta mik’o mata wata k’aramar kwalbar turare ta ce “Idan kin yi wankan ki shafe wannan a duk sassan jikin ki, turare ne na jan hankalin miji.” Hamda ta saka hannu biyu ta karb’a sannan ta fice.
Tsaf ta shirya cikin rigar da ta fito da ainahin surorin jikinta masu barazanar fasa rigar su fito saboda yarda Suka cika rigar taf suka kuma bayyana wani sashe na su daga saman wuyan rigar da ya kasance round, a tsuke rigar take don haka harta cikakken k’ugunta sai da ya bayyana kansa, sam bata wani ji kunya ba kamar yarda take ji a lokutan baya idan ta yi makamanciyar shiga irin wannan burinta ma Hammad d’in ya ganta ta koya masa hankali. Don zai san ya d’au tsawon lokaci bai nemeta ba. Gashinta ya sha gyara sosai ga wani tsawo da ya sake yi na asalin mutanen Ethiopia. Babu kwalliya a fuskarta illa