Showing 84001 words to 87000 words out of 117648 words

Chapter 29 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

ta ce “Wace irin masifa ce wannan take bin jinin D’an Borno daga wannan sai wannan ka gaya min ita Kamlan y’ar waye?” Kansa a k’asa kafin ya d’ago ya kallin duka d’aukacin mutanen falon, Abbu ji yake kamar numfashinsa ya sark’e saboda tsabar firgici da razani, k’irjinsa sai kai da kawowa yake, tausayin Abbun ya sake shigarsa a karo na biyu, ya san tunanin da yake baya son a gwada abinda ya faru a kansa da Hamda, ya mayar da kallonsa kan GADANGA da shima yake kallonsa cike da firgicin goshinsa sai zufa ce take keto masa, murmushi ya d’an saki akan fuskarsa ganin yarda Didi ta daddage ta zuba masa mari a gigice muryarta na rawa ta ce “Ka fad’a min ita kuma KAMLA wacece? Kafin jini na ya hau, ko ciwon zuciya ya kamani, tabbas da na san wad’annan matsalolin za su faru da tun mutuwar Usmanu na rok’i Allah nima yasa na bi shi.” Ita kanta ba zata ce ga ta yarda aka yi maganarta ta dawo daidai ta daina wancan gwarancin da take. Murmushi ya saki yana duban Ammi da itama take masa kallon mamaki da razana a fuskarta. Ya girgiza kansa a karo na biyu ya ce “Da gaske ba y’ata bace, UBANSU D’AYA DA HAMDA.” Wannan karan da sauri duka falon suka zuba salati Hamdan da sauri numfashinta yake sark’ewa tana wa Hammad wani irin kallo. Didi kuwa k’asa tayi da kanta gabanta yana wani irin fad’uwa ta mik’e tana kallonsa kafin tace kana nufin itama BUZU ne Ubanta?” Ya d’auke ganinsa daga kan Didi yana zagaye mutanen falon da ido, kafin ya zube idanunsa akan GADANGA da shima yake kallonsa a kid’imen, zuwa lokacin kad’an ne daga cikin mutanen falon ba suyi suman wuncin gadi ba. A zafafe Asma’u ta kalleshi ta kalli Gadanga cikin wata irin tsawa da ba su san Asma’u na da ita ba ta ce “GADANGA, HAMMAD ku fad’a min abinda yake faruwa ku daina b’oye mana don na lura da rainin hankali a tare da ku.” Gadanga Ya ware idanunsa sosai akan Asma’u ganin yarda take masa magana kamar bata cikin hayyacinta. Hammad kuwa d’ago idanunsa ya yi still yana sake kallon jama’ar da suke falon, da murmushi a fuskarsa da kai tsaye za’a iya kiransa na rainin hankali.




****************************


Lokacin da duka abubuwan suke faruwa, lokaci ne da tabbas zan iya cewa k’iris ya rage zuciyata ta buga, tsananin yarda tunani yayi min yawa da matsanancin b’acin rai sam ba ni da walwala a lokacin hakan yasa na zama kamar wani zautacce.


Ganin har a lokacin ba su bayyana kansu ba yasa nima na kasa furtawa, da kaina wani lokacin cikin dare na isa har d’akinsa yana zaune cikin tunani duk da bai bayyana damuwa k’arara a fuskarasa ba, na tabbata shi kansa yana cikin damuwa da tarin da na sani. Na isa a hankali na zauna bisa tursasawar zuciyata duk da gangar jikina bata son na rab’e shi saboda ganinsa mai tarin laifi a wajena, cikin wata iriyar murya kansa a k’asa ya ce “Kuskurene Hammad kuskurene kuma da sharrin shaid’an wallahi ina cikin dana sani, don Allah kada ka furta kalmar nan ga kowa.” Tsananin takaici ya sa na shanye maganar da na shiga yi masa ina kallonsa da raunannun idanuna na ce “Kuskure ne tarawa da matar aure matar da ba taka ba, Zina fa kenan.” Ya girgiza kai “Wallahi ba zina mu kayi ba Hammad Da aurena a kanta amma ba wanda ya sani, sai dai akwai shaidu da suka tabbatar da hakan.” Cikin takaici kamar na mak’ureshi nace “Aure kan aure kenan ka yi, tabbacin k’arancin ilimin addini a tare da kai.” Ya sake girgiza kai “Ya saketa duk da sakinnata da ya yi shima cikin sirri ne.” Ina girgiza kai had’e da furta “Sirri Sirri Sirri! Komai Sirri ni har na gaji da jin wannan zancen na Sirri, me yasa ba zaku bayyanawa duniya Sirrin da kuke k’udundunewa ba, ba kwa tsoron ranar da mutane zasu jefa ayar tambaya a kanku, nifa ina ganin kamar hakan SON ZUCIYA ne.” K’asa ya yi da kansa sosai kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Akwai wani Sirrin ma da nake son fad’a maka, ina fatan zaka min alk’awarin ba zaka bayyana shi ga kowa ba, sai dai idan ni na amince maka.” Na girgiza kai “Ban karb’a ba, na gaji da ajiyar sirrikanku da suke barazanar babbaka min zuciya, ku rik’e sirrikanku a cikinku.” Ya kamo hannuna ba don na shirya ba, sai dai ina saka k’wayar idanuna cikin nasa na ji zan amince ya fad’a min sirrin nasa, sabida wani irin kwarjini da ya yi min. “Dole zan gaya maka sirrina, kuma na tabbata idan ka jishi tilas zaka amince ka rik’e min shi gam, har sai na yarjewa kaina fallasashi gaban zuri’ar D’AN BORNO..”




Kafin ya gama gaya min, tuni duk wasu k’ofofin numfashina sun d’auke, na dinga kallonsa wani iri, ina jin yarda gumi ke tsiyaya a jikina, fatana a lokacin a ce mafarki nake ba ido bud’eba, wani irin abu nake ji, da gaske zahiri za’a samu kwatankwacin wannan abin da ya fad’a min a rayuwa, zuciyata ta tsananta bugu ina jifansa da wani irin kallo, da na san hakan zan ji daga gareshi da ban
Amince masa na saurari abinda ya fad’a min ba, yanzu ya sake d’ora min wani irin nauyi da ba mamaki ya saka zuciyata ta buga…”


Hammad ya saki ajiyar zuciya yana jifansu da kallo, yanayin da suke ciki ya tabbatar masa k’iris ta su zuciyar take jira ta buga. Sai ya gyara zama yana d’ora wa daga inda ya tsaya.




Tunda na tafi k’asar waje na mayar da hankalina kan business d’in da nake, burina na manta da waccan badak’alar rayuwar da maganar da ta bi ta dabaibaye min zuciya.
Na samu nutsuwar zuciya sosai a lokacin, bana tare da tension ko kad’an, sai wani lokaci ina office a zaune na samu kiran gaggawa daga wani asibi ana nemana.


Ina zuwa asibitin na ganshi cikin tashin hankali ya kasa zaune ya kasa tsaye. Ya cafki hannuna yana duba na da idanunsa da suke min kwarjini “Haihuwa zata yi Hammad!” Gaba na na ji ya buga, a hankali muryata a dashe nace masa “An kuma?” Ya jijjiga min kai don son tabbatar min da hasashensa An kuma Hammad, amma wannan karan ma ya zama Sirri tsakanina da kai kuma ka yi min alk’awarin rik’e y’ar ba tare da sanar da kowa ba kai ka haifeta ba, har zuwa lokacin da Sirrin zai bayyana a idon duniya…” cikin takaicin lamarin na cije leb’ena Ina dartse shi da k’arfi har wani gishiri na ji a bakina alamar na fasa shi jini ya fito, na dafe goshina kawai sai na samu kaina da jijjiga masa kai, alamar na karb’i alk’awarinsa koma mai zai faru ya faru.


A cikin daren ya min waya ta sauka, a cikin daren kuma na d’auko y’ar na dank’awa Nanna tare da yi mata kyakykyawan kashedi. Mun kai ruwa rana kafin ta amince da buk’atata bisa tursasawar zuciyarta ta cigaba da kula da KAMLA. Wannan shine abinda ya faru.


Takaicine yasa Abbu mik’ewa ya kai masa mari, “Me kake so ka fad’a mana, wani sirri ne da ba zaka fito ka fad’e shi ba kake kewaye-kewaye, don ubanka waye mutumin da kake zancensa tunda duk a cukurkud’e ka yi maganar BUZU ko GADANGA?” Idanunsa ya jefa cikin na GADANGA kafin ya runtse idanunsa ya bud’e ya d’aga hannunsa ya nuna shi. A bakinsa zaku ji komai, don alk’awari na d’aukar masa ba zan fad’a ba kuma na cika masa… mutanen wajen suka bi inda yake nunawa da kallo kafin cikin matuk’ar mamaki kowa ya ce “GADANGA!”






Ina yin ku mutanena.




Jikar Nashe taku ce, iya wuya ana tare one love kawai.
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: Shi kansa Gadangan a razane yake kallon jama’ar da suka zuba masa ido, da gaske furucin Hammad d’in yazo masa a bazata jin kuma sun ambaci sunansa yasa gabansa fad’uwa, idanunsa cikin na Hammad yake masa kallon tuhuma.


Wani irin had’adden k’amshi ne ya ziyarci k’ofofin hancinsu k’amshin da kai tsaya za’a iya kiransa na tsadadden turaren da ya lashe mak’udan kud’i wajen siyansa. Gaba d’aya ya maye duk wani k’amshi da yake falon, kafin k’ofar falon ta bud’u. Kammalallen mutumin mai fuskar dattawan k’warai ta bayyana. Fuskarsa ba b’oyayyiya bace a kaf fad’in Nigeria an sanshi kasancewarsa na gaba-gaba a sahun masu arziki da suke k’asar. Ko yaro k’arami ka haskawa hotonsa direct zai fad’a maka sunansa kai tsaye K.K MUD’ALLABI, Dogo ne sosai mai cikar zati da Haiba gami da kamala. Excort d’insa ne a bayansa suke biye da shi suna sanye da bak’aken kaya wuluk kafin ya murza yatsun hannayensa alamar da take nuna musu baya buk’atarsu a wajen su fita. Suka sara masa had’e da juyawa da sassarfa. Hammad da sauri yazo ya tareshi cikin matuk’ar girmamawa shi kuma ya ja Hammad d’in jikinsa ya bashi kyakykyawar runguma, jin Hammad d’in yake kamar jininsa kamar shi ya tsuguna ya haifeshi.


Idanun d’aukacin mutanen da ke falon zube suke a kansa suna mamakin mai ya kawo KK Mud’allab gidansu. Mutumin da yake wahalar gani a K’asar sai kana da babban matsayi sannan kake ganinshi, shima d’in on appointment, ba su gama wancan mamakin ba wani ya kashesu, ta yarda ya rungume Hammad tsaf a jikinsa tamkar zai mayar da shi cikinsa. Hammad ya ja hannunsa ya isar da shi har tsakiyar falon aka sama masa waje ya zauna, fuskarsa d’auke da matsanancin murmushi mai bayyana tsananin farincikinsa. Zai iya cewa bai tab’a riskar kansa a farinciki kamar na ranar ba. Nan aka shiga gaisheshi idanunsa yake zagaye falon da su kafin ya sauke idanunsa kan Hamda, ko ba’a fad’a masa ba ya san ita ce, ya san Hamda ce ba ya neman k’arin bayani, ji yake tamkar ya jata jikinsa ya sanyata a k’irjinsa ya rungumeta. Shiru suka yi, d’aukacin mutane falon suna jiran k’arin bayani daga bakin Hammad, da shima tasa fuskar ta kasa b’oye murna da farin cikin da yake yi, ko bakomai yau zai huta da ajiyar wannan gundumemen sirrin da yake, da kullum tunaninsa ranar da zai fallasu, ya dad’e yana jigatar da shi duk dare da abin yake kwana yake ta shi.


Ya sani jiransa suke ya yi magana, amma kwarjini KK Mud’allab ya kasa barin kowannensu ya d’aga baki ya furta.shi kansa karo da dama kwarjinin mutumin ne yake masa togaciya daga dukkan komai ko da kuwa ya yi yunk’urin hakan. Ya saki d’an murmushi ganin suma sun fad’a kwatankwacin wancan yanayin nasa a karo na farko da suka had’u da KK Mud’allab d’in. “Na san zuka’tanku suna cike da son sanin me ya kawo gawurtaccen d’an kasuwa gidan nan, abinda baku tab’a zata ko kad’an a rayuwa ba.” Ya ja fasali kafin ya ce “Abinda zan iya ce muku kawai KK MUD’ALLAB shine mahaifin HAMDA DA KAMLA.” A razane mutanen wajen suke kallonsa, Hamda kuwa tsananin rud’ani bata san sanda a sukwane ta iso gaban KK d’in ba, tana ware idanunsa a kanta, ko da Hammad bai furta ba, tsananin kamannin da suka d’auko nasa mai taken kwabo da kwabo ya isa ya bayyana wa duk wani mai tantama cewa shine mahaifinsu. Mutanen falon kansu abinda suka lura da shi kenan, mamaki da ta’ajjibin lamarin ya cikasu, burinsu kawai su ji yarda aka haihu a ragaya. KK d’in bud’ewa Hamda hannu ya yi alamar ta taho ya rungumeta. Ba mutanen kad’ai ba hatta Ammi lamarin ya firgita ta, ta ina suka had’u da KK d’in har suka yi tarayyar da suka samar da cikin Hamdan, tabbas bata san shi ba za kuma ta iya rantsuwa a rayuwa banda tana ganinsa a hotuna a waya ko yayinda yake hira da y’an jarida bata tab’a ganinsa ba a zahiri. Ta ja fasali tana jin kokwanton lamarin a zuciyarta ko dai fashin yarinya zai mata. Sosai ya rungume Hamda a jikinsa yana jin wata irin nutsuwa da k’aunarta suna gauraye dukka jikinsa, wannan ranar yake jira ranar da zai ji gidan jininsa a jikinsa, ranar da shima zai bugi k’irji ya kira kansa UBA. Ita kanta Hamda nutsuwar da ta samu da ta jita kwance a jikinsa ya tabbatar mata da cewa shine mahaifinta. Ta gefen kunnenta ta dinga jin zubar ruwan hawayensa da suke d’igar mata akan fatar kunnen da zafinsu, lamarin da yasa Hammad sunkuyar da nasa kan yana zubar da nasa hawayen na tsantsar farin ciki da murnar sauke damin nauyin alk’awarin da ya d’auka a rayuwarsa. Didi ta gaji da zuba musu ido, sai ware ido take tana kallonsu cike da son k’arin bayani. Hammad ya sake girgiza kai yana jaddada musu “Idan kukayi la’akari da zallar kamanninsu ya isa ya tabbatar muku da gaske shine uban Hamda da Kamla, ba ni ba ba BuZu ba, ba kuma Gadanga da duk hasashenku suka fi tafiya kansa ba, KK dai shine UBA idan nace Uba ina nufin uban da ya samar da k’wayar cikin HAMDA DA KAMLA.” Kaf nutsuwa ta d’aukewa ahalin D’AN BORNO musamman Ammi da lamarin yake shirin bugar mata da zuciya, wace irin kalar shirme Hammad yake fad’a ne? A ina taga KK d’in balle har wata mu’amala ta had’a shi da ita.
KK d’in ne ya gyara zamansa cikin tarin kamalarsa ya ce “Tabbas, abinda yaron kirki ya fad’a gaskiya ne, HAMDA da KAMLA y’ay’ana ne, kuma jini na da na samar da su ta hanyar da ake samar da cikin kowani yaro, ko asibiti aka je aka gwada za’a ga k’wayoyin halittarmu d’aya ne da su, Ni ne Ubansu ni na samar da k’wayakwayan haihuwarsu a mahaifar iyayensu mata, ba uwarsu d’aya ba amma ni ne ubansu.” Wannan karan dukan da zuciyar Ammin take ta tsananta, idan har hakane KK yana nufin Hamda ba y’arta bace kenan? To ita ina tata y’ar ya aka yi duk hakan ta faru? Ta runtse idanunta tana jin lamarin kamar almara kafin ta ji KK ya fara magana cikin wata irin kammalalliyar murya mai nutsar da zuciyar mai sauraro.








*****************


Sunana Kamaluddeen Kabeer Mud’allab, wanda d’aukacin mutane suka fi kira da KK Mud’allab, na tabbata kun sanni a ido sai dai ba ku tab’a gani na a zahiri ba, Mu sha bakwai ne cif a wajen mahaifinmu da muka fito daga mabanbanta iyaye mata, ni kad’ai jal mahaifiyata da muke kira Ummu ta haifa, daga kaina kuma bata sake haihuwa ba, ina da y’an uba sha shidda kenan, na taso a ware musamman ina da shekaru bakwai mahaifiyata ta rasu ta barni, kuma bata da kowa a garin nan, danginta kaf mutanen ethiopia ne wato k’asar Habasha, da ta mutu sun so tafiya da ni sai dai mahaifina ya nuna rashin amincewarsa saboda soyayyar da yake min mai girma ce, wannan soyayyar kuma ita ta jawo min tsana mai girma a cikin y’an uwana basu da buri irinsu kassarani daga su har iyayensu kuwa. Na taso cikin wata iriyar rayuwa mai wahalar magantuwa, ni kad’ai na san a yarda na taso kafin na girma na je k’asar Habasha inda su kuma suka gatantani fiye da zatonku, suka d’ora ni akan kasuwanci bayan sun shak’a min mak’udan kud’ad’e inda daga nan ne asalin arzikina tun daga lokacin na zama mai kud’i sai kuma a lokacin y’an uwana sabida rashin tsoron Allah suka fara k’ok’arin ja na a jiki da son nuna min soyayya. Ban bi ta tasu ba na amince da su na dinga kyautata musu.


Lokacin da na yi aure sai ya zama duk matar da zan aura sai sun d’orata a turbar son ta zalinceni ko ma su bata guba da zummar ta bani na sha na mutu, duk don son su gaji dukiyata kamar yarda hasashena ya bani. Hakan yasa tun bayan sakin matata ta hud’u sai ban sake aure ba sai na je garinmu na auro y’ar uwata da iyayenmu suka zo duniya k’ark’ashin mahaifa d’aya, na san ba ta yarda za a yi wani bare ya had’a baki da ita ta cuceni.


Da suka ga haka, sai suka canja salo ta hanyar duk sanda matata ta samu ciki sai sun san ta yarda suka yi suka zubar da shi idan kuwa ba su nasara ba har ta haife sai sun san yarda suka yi suka salwantar min da yaro ko yarinya. Haihuwa biyar banda juna biyu da suka zubar min, hakan ya fara d’aga hankalina na fara tunanin mafita. Duk yarda na bi sai naga hanyar ba mai b’ullewa bace, har lokacin da na yanke shawara ta k’arshe….




Tirk’ashi masoyan jikar Nashe wai YA ABIN YAKE NE?🙆🏿🤦🏿‍♀️🤷‍♀️




Vip and special mu had’u a posting dare.


Ana tare Love you irin da yawa d’in nan, masu tambayar zumuncin zamani ina nan tafe ba na iya typing biyu ku bari na gama wannan a tsanake insha Allah shima zai zo muku cike da salo mai nishad’antarwa da farantawa had’e da fad’akarwa gaba d’aya.




JIKAR NASHE TAKU CE!
[1/12, 7:45 AM] Nazeefah Nashe: “Hukumullahu la ajabun..” shine abinda Didi take ta fad’e tun bayan jin maganganun KK d’in da suka zame musu tamkar labarin irin tatsunuyoyin nan, ko hikayoyi, idanu duk d’aukacin mutanen wajen suka zuba masa, zuk’atansu cike da ta’ajibin lamarin. Hamda kam farin ciki ne ya cika zuciyarta, jin Mahaifinta shine KK, ta kuma tabbatar da hakan musamman da taji ya ce a kashegari zai gabatar da duk wasu shaidu da za su tabbatar da auren su da Sakna. Gaba d’aya ta ji ta sake k’ank’ame jikinsa tana mayar da ajiyar zuciya da sauri, shi d’in ma cikin tarin k’aunar d’iyar tasa ya sake rik’eta sosai yana jin tamkar ya mayar da ita ciki, k’aunar da ta rasa ta shi tana k’arama ita ce yanzu ya d’auki d’amban shayar da ita da dukiyarsa da jikinsa da duk wani abu da ya mallaka. Ammi kuwa idanu ta zuba masa cike take itama da matsanancin mamaki ko a mafarki bata sawa zuciyarta ganin KK Mud’allab ba sai gashi ashe a zahiri ma har shimfid’a suka had’a ba tare da ta sani ba, suka had’a
Jini ta hanyar haihuwar Hamda,
Abinda bata tab’a kawowa ba ko a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login