Showing 39001 words to 42000 words out of 117648 words
Chapter 14 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt
take hanata huld’a da Hamda, saboda tana son ta sosai. Hakan yasa dole Khairi ta zauna ba tare da ta kira Hamdan sun shiga d’aki ba.
Har ya watsa ruwa ya kwanta don
Ya huta, sai ya tuna da ita ya san bai zama lallai Nanna ta kaita masauki ba, ba ma wannan ba yana lura da ita a jirgi ba wani abincin kirki ta ci ba. Don haka ya mik’e da sauri ya fita. Hasashensa kuwa ya zama gaskiya don tana rakab’e a kujera ta lula duniyar barci ita kad’ai ce a parlourn kamar mayya, ta takure jikinta da alama sanyi take ji sosai.
Hannu yasa ya d’an buga bayanta da sauri ta mik’e a d’an firgice idanunta sun yi nauyi saboda barcin da yake cikinsu. “Me yasa baki shiga d’aki ba?” Ta ware idonta kafin ta ce “Ba’a nuna min d’akinba ai.” Tsaki ya ja ya mik’e hannunsa jaye da trolley d’inta ya ce “Biyo ni.” Murd’a d’akin su Khairi ya yi ga mamakinsa sai ya ji shi a kulle abinda ba a yi kenan rufe d’aki a gidan ko menene dalilin hakan. Ya shiga Knocking k’ofar da d’an k’arfi. Cikin barci Khairi ta farka tana fad’in “Waye?” “Bud’e” ta ji muryar Daddynta, hannu ta sa ta murd’a sai ta ji d’akin is locked sai sannan ta tuna Mommynsu ce ta gark’ame d’akin duk don kada Hamda ta shigo. Murya a tsorace ta ce “Daddy Mom ce ta rufe da key.” Da k’arfi ya ce “For What reason?” Jikin Khairi ya soma rawa don sam bata son tashin hankali a rayuwarta ga shi ta ji Daddy kamar ransa ya yi mugun b’aci, ta kasa cewa komai sai zare ido take. Da sauri Hammad ya juya ga Hamda kawai ya sake ce mata biyo ni.”
Direct d’akinsa ya wuce da ita, dole ne ma ya yi maganin Nanna. Ya bud’e wardrobe ya d’au abinda zai buk’ata ya kalleta “Zauna anan kafin na gyara miki wancan d’akin.” Ta bi d’akin da kallo had’uwa da tsaruwar d’akin kad’ai ya isa ya burgeka balle yarda d’akin ya rik’e turarensa k’am tamkar anan ake had’a samfurin turaren kafin ta yi magana ya fice daga bedroom d’in nasa. Ta bi bayansa da kallo kafin ta sauke wata sassauk’ar ajiyar zuciya. Da zata iya kwanciya za tayi kawai amma ta fi so ta watsa ruwa tukun. Don haka direct ta fad’a had’adden toilet d’in nasa.
Shi kuwa yana fita d’akin Nanna ya wuce direct, Fuskarsa a had’e sosai. Ya tura k’ofar ya shiga. Nannan tana zaune gaban dressing mirror ta na shafa mai ta ganshi ya shigo da kaya a hannunsa ya zube kan gado. Sannan ya hau gadon ya yi kwanciyarsa ba tare da yayi mata magana ba. Cikin mamaki take kallonsa “Ban gane ba Yallab’ai, ina naka d’akin?” Ba tare da ya kalleta ba ya ce “Yana wajen Hamda.” Da sauri ta mik’e har towel d’inta yana shirin zamewa ta ce “Wani irin abu ne wannan zaka d’au master bedroom ka bata alhali akwai guest room.” Ya d’ago yana tsatstsareta da ido da tilas ya sata risnar da nata idon “Na fiki sanin da guest room d’in na bata nawan. Saboda ita ba guest ba ce yarda kike tak’ama da gidan nan itama haka take tak’ama da shi.” “Wallahi k’arya ne ni da nake matar gida har ka had’ani da ita?” Murmushi ya saki kawai ya ja filo ya kwanta “zuwa ki fitar da ita daga bedroom d’in nan shine kuskure mafi girma da zaki aikata a rayuwar aurenmu, duk ba ke kika jawo ba da ba ki tilastani zuwa Nigeria ta ya kike tunanin duk wad’annan abubuwan za su faru, don haka duk abinda ya faru ke kika janyo.” Daga haka ya lumshe idonsa ya bar ta a tsaye zuciyarta na kissima mata al’amura da dama. Da kyar ta ja sillan k’afafunta ta zira doguwar riga mara nauyi sannan ita ma ta bi gefensa ta kwanta, kusan zata iya cewa wannan shine karo na farko da ya kwanta a d’akinta, kullum ita take kai kanta wajensa. Tsaki ta ja tana tunanin Hamda kwance can a lumtsumemen gadonsu.
Sun sha barci sosai don sai da yunwa ta fara nuk’urk’usar ko wannensu sannan suka tashi. Hamda ma yunwar ce ta farkar da ita sai dai tana tsoron fita parlourn, ta ci karo da Nanna, bata san wannan kallon da take jifanta da shi.
Da kansa ya mik’e ya fito tunawa da yayi haka ta kwanta bata saka komai a cikinta ba, gwara ma su sun ci abinci a cikin jirgin. A kitchen ya taradda Khairi da Nanna suna dafa noodles don ita kad’ai ce da su a gidan komai sun fitar da shi kafin su tafi. Ya lek’a tukunyar sannan ya juya ya fice.
Direct d’akin da take ya nufa har ya murd’a zai shiga sai kuma ya tsaya ya d’an k’wank’wasa. Da sauri Hamda ta zari veil d’in da yake gefenta ta nad’e himulin gashinta da shi. Har yanzu ta k’i amincewa zuciyarta cewa muharraminta ne. Ya tsaya daga bakin k’ofa yana nazarin fuskarta, gaba d’aya yunwa ta riga tasa ta fara fita daga hayyacinta. Ya ja tsaki yana sakin handle d’in k’ofar “Kina jira a zo a baki abiinci ne? Ba zaki zo ki samu abinda zaki ci ba.” Da kyar ta mik’e jiri na d’an d’ibarta kad’an ta saka k’afa zata fito daga d’akin sai gani ya yi tayi baya ta fad’i.
Da hanzari ya juyo ya d’aga cak yana mamakin wauta irin tata. Fuskarsa a d’aure ya ce “Wai ke wace irin shashashace? Kin san ba zaki iya tafiya ba wa yace ki taso?” Ya zaunar da ita a gefen gadon sannan ya fice. Tea mai madara had’ad’de Nanna ta ga yana had’awa mamaki ya kusa kasheta a tsaye don dai ta san baya shan irin wannan tea d’in zallar black ko green tea yake sha. Ta kuwa tsatstsareshi da ido “Me zaka yi da shi?” Bai kulata ba ya fice da mug d’in a hannunsa da sauri ta bi bayansa sai taga ya shige d’akinsa, wani irin tuk’ukin b’acin rai ya shigeta. Da sauri ta juya d’aki tana lalubar wayar aminiyarta da take zaune a garin Uk.
A tsaye ya mik’a mata mug d’in hannunta na rawa ta saka hannu ta karb’a ta kai bakinta da sauri take zuk’a alamar tana jin yunwa sosai. Juyawa kawai ya zari key d’in motarsa gwara ya je ya samo solution akan Hamda don ya lura zamanta da Nanna ba abu ne mai yiwuwa ba. Shopping zai yi saboda ba su da komai a gidan, zai biya kuma wajen abokinsa Mustafa da suka fara maganar Hamda da shi a waya su yanke shawarar yarda za su b’ullowa Ammi. Da safe kuma yaje makarantar da ya riga ya samar mata admission.
__________
Cikin dare Gwaggo Asma’u jirginsu ya sauka daga k’asar Dubai. Duk da gajiyar da tayi amma a daren ranar ta matsantawa mijinta Sheikh Abdallah akan sai sunje sun ga jikin Didi.
Ba kowa a wajenta sai Sadiya da Lauratu. Da murna suka tareta bayan an gaggaisa Sheikh Abdallah ya tambayi yanayin ciwon nata. Don ya ga Didin bata magana sai dai kallo da ido. Sai da suka bashi labarin kaf abinda yake faruwa sannan suka ga ya saki murmushi kasancewarsa masani akan cutittuka na shafar jinnu ya tabbatar musu ciwon Didin bana asibiti bane da safe a neman mata sallama shi zai sake dubata. Daga haka ya yi musu sallama ya tafi ya bar matarsa a wajen. Suka cigaba da jajanta lamarin. Asma’un ce ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “Amma Sakina an yi y’ar banza, su kuma su Yaya fisabilillahi ya aka yi suka yarda da wannan tatsuniyar da ta shirga. Duk ma ba wannan ba yanzu ina Hammad da yarinyar me yasa ba’a gwada k’wayoyin halittarsu ba a tabbatar shin y’ar da gaske tasa ce ko sharrinta ne.” Mahmah ta ja mayafi ta goge hawayen fuskarta kasa magana ta yi sai Lauratu ce tace “Ai zancen da nake miki Hammad ya tafi da y’ar Birmingham bayan da Yaya ya koresu.”
Rik’e kai kawai Asma’u tayi kafin ta ce “Kash Na so Na zo na sameshi amma bakomai idan ta san wata ai ba ta san wata ba da kaina zan nemo gaskiyar lamarin.”
Tun bayan da ya kawo mata abinci da kansa cikin d’aki bai sake waiwayarta ba har safiyar Ranar.
Ya shigo fes da shi cikin shigar bak’ar Rigar Hilfiger da brown trouser. Sai jibegegiyar rigar sanyi bak’a a jikinsa kansa kuma sanye da bak’ar hular sanyi da ta rufe masa har kunnensa. Yana shiga tana share hawayen da yake sauko mata. Ya san kukan me take kukan maganganun da Nanna ta dasa mata take, yana jin su. Sharewa ya yi kamar bai gani ba “Mik’e mu je makarantar da za ki fara zuwa.” Ta mik’e cikin sanyin jiki suka fice daga gidan.
Sai da suka isa harabar makarantar Aston University da ke Birmingham cikin wata irin murya ya ce “Saura ki shiga kina wannan sussunne kan, kuma kin iya turanci ko?” Sunkuyar da kanta kawai tayi tana jin takaicin maganarsa. Ya fice daga motar ita kuma ta bi bayansa.
A hanyarsu ta dawo ya kalleta yana reverse da mota zai shiga layinsu ya ce “Zamanku da Nanna ba zai yiwu ba, don haka na yanke shawarar aurawa Amini na ke.... kin amince?” Da sauri ta d’ago tana kallonsa kafin ta ce wani abu yace “Shine abinda yafi kamatarki a halin yanzu.”
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: YA ABIN YAKE?
LAST FREE PAGE INSHA ALLAH
Normal group 300
Vip 500
Special people 1000 sending privately.
Payment via 2118666253 U B A
Sai a tura shaidar biya ta (08033748387. Ga wanda suka biya akwai kyautar free book d’ina Na Zumuncin Zamani.)
_____________________
Kallonsa kawai take tana mamakin furucinsa, shin da gaske auren zai yi mata, me yasa ya taho da ita k’asar da bata san kowa ba alhali ya san matarsa ba zata iya rik’eta ba? Aure dama an tab’a aure haka ba tare da matar ta san mijin ba, ko kuwa don k’addara ta hau kanta sai a samu koma waye a lik’a mata shi a matsayin miji? Shikkenan ita bata da damar soyayya kenan? Ta ina mijin zai ga k’imarta da mutuncinta. Hannu tasa ta share hawayen da ya kwaranyo kan fuskarta da gaske lamarin ya yi mata zafi k’warai da gaske. Shikkenan duk mafarkinta na tsalelen mijin da take so ta aura ya bi iska, ko zunnuraini da ta amince zata aureshi ne kawai ba don ya zama irin mijin da take so ba. Irin mijin da take so sirri ne a zuciyarta da kuma tunaninsa take kwana a koda yaushe.
A fili ya ja tsaki “Idan ba kya son auren ba sai ki fad’a ba me ye na zama kina min kuka. Kin san da yaya ya amince zai aureki ma tukun?” Ya fad’a daidai yana parking a k’ofar gidansa “Aurenki shine abinda yafi alheri a yanzu a rayuwarki, ko bakomai za kiyi karatunki cikin nutsuwa, don haka ki share wannan hawayen idan kin amince gobe zai zo ku ga juna zai kuma kawo miki sadakinki da duk wani abu da za ki buk’ata, Nan da kwana biyar za muje masallaci da su a d’aura miki aure ki tare a gidan sa.” Tana shashshek’a ta share hawayenta had’e da d’aga kanta cikin wata irin murya ta ce “Shikkenan bakomai Allah yasa haka ne yafi alheri a gareni” idanunsa cikin nata ya ce “Haka ne ma insha Allah, kina da suffa da halayen da za ki saka namiji ya so ki ko bai shirya ba, don haka ki k’addara za ki zama star a zuciyar abokina.” Yatsun hannunta kawai take wasa da shi kafin ya mik’a mata jakarta ya ce “Mu je gida.” Ta fita daga motar jikinta a salub’e haka kawai kuma gabanta yake dukan Tara-tara. Tana mamakin yarda lamarin auren nata ya zo kamar auren y’ar tsana.
A parlour Nanna take zaune cikin hamshak’iyar shiga, fuskarta sam ba walwala take jifansa da wani kallo ganin yarda suka shigo gidan. Ba tare da ya kalleta ba ya zauna yana d’iban lemon tataccen inibin da yake gabanta a jug. Ta d’ago tana kallonsa kafin ta ce “Ban da dai yarinyar nan y’arka ce da sai nace ko soyayya ku ke?” Fuskarsa a had’e ya d’ago tare da zuba mata wani matsiyacin kallo, sai kuma ya girgiza kai kawai ya cigaba da kurb’ar juice d’insa “Ka kalleni ka yi shiru, na lura kular da kake bawa yarinyar nan ta na nema ta wuce muhallinta don ko ni matarka ban samu kwatankwacin kular ba, kada dai bayan an gama da uwa a zo a koma bibiyar y’a.” Ji ta yi kawai ya yi cilli da Glass tumbler d’in hannunsa cikin matsanancin b’acin rai ya dubeta “Na rantse da Allah idan kika sake min kwatankwacin wannan furucin I will show You who I am. Wani irin iskanci ne wannan kawai don na zuba miki ido kina duk abinda kika ga dama doesn’t meant kin fi k’arfina ne.” Daga haka ya fice daga gidan zuciyarsa a tunzire har hakan ya d’an firgitar da Nannan ta tabbatar yau ta kaishi mak’ura amma zuciyar shaid’an na sake tunzirata. Ta mik’e da sauri ta nufi d’akinsa inda Hamda take.
Tana zaune a gefen gadon hannayenta zube a k’uncinta, gaba d’aya zuciyarta ta ruga tunani. Mamakin yarda rayuwa ta yi mata juyin waina take. Turo k’ofar da aka yi da k’arfi ne ya sata saurin d’aga kai, idanunta suka sauka cikin Na Nanna da take tsaye tana huci tamkar zakanyar da ta kwana da yunwa “Ki tattaro duk wani kayanki ki koma d’akin yara, duk da babu space ki dinga bajewa a k’asa, haba yarinya kin shigo rayuwata kin zame min bala’i ina zaman lafiya da mijina yanzu abu ya gagara shegiya kawai, na tabbatar uwarki ce ta yiwa mijina fyad’e saboda jarabarta ta son haihuwa d’a namiji amma aka tattare laifin duk aka jibge masa.” Ganin Hamda ba ta ce komai ya sa ta cigaba da zabga mata masifa “Kuma last warning da zan miki ba ke ba shirgin yara ne ki tsaya a matsayinki na shegiya su ma su tsaya a matsayinsu na y’ay’an Sunna da aka haifa da aure. Sai na bi na sanar da kowa matsayinki wallahi idan ba ki bar gidan nan ba, sai na goga miki bak’in fentin da zaki kasa auruwa ki fito yanzun nan na gaya miki.” Daga haka ta fice daga d’akin ta bar Hamda tana wani irin kuka tabbas Yaya Hammad ya yi gaskiya da ya ce aurenta shine abu mafi alheri a gareta. Ta lura idan har zata cigaba da zama a gidan nan Nanna sai ta saka mata ciwon zuciya da bak’ak’en kalamanta. Ta rasa me ta yi mata da har ta tsaneta haka? Duk abinda ya faru itama fa ba laifinta bane.
Tsaf ta had’e kayanta ta mayar da su d’akin su Khairi. Gado uku ne a d’akin daidai kwanciyarsu don haka dole ita a k’asa zata dinga kwanciya ba bak’on abu bane a gurinta, amma ya zama dole ta amince da mijin da Hammad ya zab’a mata ta huta.
________________________
Cikin farin ciki Sakina da yaranta suke, saboda yau aka kawo kud’in auren yaranta su biyu Najma da Nasma kuma gaba d’aya aka had’a har saka rana. Duk da k’annen Abbun sun nuna a bari Didi ta samu lafiya amma Sakina ta ce Sam ayi kawai ko Didin da zata iya magana ai cewa kawai za tayi ayi tunda ta fi kowa son yaran su yi aure. Nan fa shirye-shiryen biki ya kankama don bayan Sallah da sati biyu za’a yi bikin. Lokacin kuwa Azimi saura kwana goma aka saka ranar. Bakin Ammi yak’i rufuwa saboda ba k’ananan kud’ad’e take shak’a a wajen Angwayen da uban gayya Abbu ba. Don sosai ta sake samun kansa ta hanyar bankawa kanta magungunan mata da suke sake zautashi. Dole wannan karan ma Sadiya ta sake zama y’ar kallo don ko ranar girkinta sau tari ya sha kiranta da sunan Sakina ta. Sakina kaza Sakina kaza. Tun abin baya damunta har yanzu ya soma damunta don da tayi masa k’orafi ma cewa ya yi “Ki yi hak’uri Na rasa yarda zan yi na kwatanta adalci tsakaninku, amma ke ma da laifinki ko y’an dabarun nan na mata ba kya yi.” Ranta a b’ace ta fice masa daga d’akin tana ayyana in dai ba shi ya nemeta ba ba zata sake kawo kanta gareshi ba. Ranar ku san kwana ta yi b’acin rai na nuk’urk’usar zuciyarta. Sai daga baya ta ja tsuka don ta bawa kanta a haushi a yanayin shekarunta ma ya kamata ace ta tattara wannan matsalar ta saka ta a gefe tunda tun a lokacin yarinta ma ba ta tata yake ba ta Sakinarsa y’ar Gold k’irar diamond. Dama haushinsa take ji tun akan maganar Hammad don dai su Asma’u da Gadanga sun ce ta saka masa ido ne su ga iya gudun ruwansa.
Didi kuwa tunda aka dawo da ita daga asibiti ake ta abu d’aya duk malamin da yazo sai ya ce Sammu ne amma insha Allah bakinta zai bud’e kuma suna ganin alamun nasara. Don haka su Lauratu suka sake dagewa da tsare sashen Didin don sam ba sa haufi akan cewa Sakina ce ta yi mata asiri. Ko abinci ta kawo ba bu mai ci don lamarinta yanzu tsoro yake ba su.
_____________
Sai dare ya dawo gidan, Hannunsa d’auke da takardun makarantar ta ya nufi bedroom d’in sa. Don ya san ace zai sameta. Yana murza k’ofar d’akin ya ji wani k’amshi ya doki hancinsa, ba ya haufi k’amshin turaren Nanna ne. Mamaki ya kamashi da ya kunna fitila ya ga Nannan kwance akan gadonsa cikin wata fitinanniyat rigar barci da duk ta bayyana surorin jikinta. A tunaninta ta yi kyau sai dai ina shi bai gani ba muninta kawai ya gani da bayyanar halittunta da suka sauya sabida haihuwa kasancewr Nannan mai teb’a da zubabbun Mama. Tsaki kawai ya ja ya shige toilet kamar ya tamabayeta ina Hamdan? Sai dai ya kyaleta don ya san rigima take nema. Wanka ya yi da brush ya fito sanye