Showing 3001 words to 6000 words out of 117648 words

Chapter 2 - YA ABIN YAKE Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe .txt

ya shayar da ita ruwan mamaki shi yasa ma bata ɗauketa ba don idan ta ɗauketa tabbas Sakina taci riba a wajensu tunda ta bayyana ƙarara kenan ita take juya su.


Shirye-shirye da gyaran ɗakin ya hana Mahmah zuwa asibitin sai bayan ƙarfe biyar, sannan ta tafi bayan ta tura Humaid gidan yayansu na biyu Hamidan ya kwana, don idan ta barshi da Saliha wahala zai sha, da Hamood yana nan ne ma da sauƙi to ya tafi karatu can ƙasar Egypt.







Da Abbu suka tafi asibitin, suka bar Ammi a jikin window sai cizon yatsa take ganin yarda suke tafe cikin nishaɗi sai tuntsira dariya suke, wato ita ya mayar ƴar banza bai damu da ɓacin ranta ba tana sane taƙi fita gyaran ɗakin Didi, duk don ta samu ya kulata amma kamar ya san manufarta ya tattara ya watsar da ita da kansa ya zage aka yi aikin dashi da Mahmah don a dokarsa bai yarda ƴan aiki suyi masa aikin uwarsa ba don ƙarara ta nuna masa bata son hakan kasancewarta mai tsafta da tsantseni.


Kamar ya san tana lafe a window tana kallonsu ta taga ya buɗewa Sadiya ƙofar motar yana jifanta da wani irin murmushi da ya tunzira zuciyar Ammi taji wani kishi yana katantawa da ita, har yau ta kasa iya danne kishinta akan Sadiya duk da ta fita da komai amma haushinta take ji sosai tana tunanin duk duniya ba wanda ta tsana sama da Sadiya musamman da tayi mata zarra wajen haihuwar ƴaƴa maza don ita kaf ƴaƴanta biyar maza ne ba mace ko ɗaya abinda yake sake baƙanta ran Ammi kenan musamman idan kalmar ‘ Sadiya taci gida’. Ta faɗo dodon kunneta da mafi yawan akasarin mutane suke faɗa musamman a wajen taron biki ko suna na dangin mijinta, kai har da ma na mutuwa ta sha ji ana mata gori ko don mutanen sunyi la'akari da yarda maitarta ta fito a fili na son haihuwar ƴaƴa maza ne shi yasa ake jifanta da zancen? Da sauri ta saki labilan tana runtse ido tuno da maganar da likita yayi bayan haihuwar Hamda ya tabbatar mata da ba zata sake haihuwa ba saboda mahaifarta ta taɓu dole aka juyata haka dole tana ji tana gani burikan ta suka bi iska, tayi burin haihuwar ƴaƴa maza ita ba don gado bama don son taje gidajensu ta shimfiɗa mulki kamar yarda Didi take shimfiɗa mulkinta a gidajen nata yaran.
Tana jin tashin motarsu ta saki tsaki haɗe da furta zaka biyo dare ka nemeni ne wallahi kayiwa kanka sai nayi sati ban baka haƙƙinka ba, ta tabbata kuma sai ya kusa suma don idan tayi masa yaji ko na kwana ɗaya ne ranar girkinta zama yake yayi mata kuka yana roƙonta, don da gaske shi kaɗai yasan ruwan zallar daɗin da yake kwankwaɗa a jikinta balle sati! ta saki murmushi da ta tuna haɗaɗɗiyar zumar da ta siya da zata kusa zautar dashi a zahiri tace gidan ka tarar.










_____________________________


Da sauƙi sosai suka sameta don likita ya tabbatar musu zuwa safiya ma idan drip ɗin da ake saka mata ya ƙare za'a iya sallamarta. Mahmah da kanta ta zauna tana bata kunun gyaɗar da ta damo mata ta sha kuma sosai har sai da tayi gyatsa. Abbu murmushi kawai yake yana sake jaddada kimar Sadiya a zuciyarsa, da gaske ɗin ita ta dabance zuciyarta mai kyauce,Mai halin mutanen farko shi yasa kullum yake mata kirari da Hali dubu.






Kashegari kuwa aka sallamesu, ko kafin suje gida tuni Mahmah tayiwa Saliha waya ta ce ta gyara mata ɗakin da yake kusa dana Humaid nan zata saka Hamda a ciki, duk da bata da tabbacin uwarta zata yarda sai dai wannan karan Abbu ya tsaya kai da fata ya ce dole nema ta yarda tunda ita bata sonta bata isa ta hana wani riƙeta ba.




Suna shigewa sashenta Ammi ta fito a sukwane cikin bala'i ta shiga ɓangaren Sadiyar tana zuwa ta shiga surfa bala'in sai an fito mata da ƴarta ai ba uban wanine ya haifa mata ita ba matar shige kawai borar gida"
Sadiya murmushi ta saki kafin ta girgiza kai ta ce"Wallahi ba zata fito ba sai dai idan Ubanta ne yazo ya fitar da ita da kansa, kuma alhamdulillah borar gida ita ta zama uwar mazan gida mowa kuma ta haifi mata...... Wani kukan kura Ammi tayi, tayi kanta yasa na runtse ido don na tabbata ba za'a kwashe da daɗi ba.
[1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE




YA ABIN YAKE ?


LIttafin Nazeefah Nashe.


08033748387










Follow me on ArewaBooks


@nazeefah


https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e




ELEGANT ONLINE WRITERS


(Haɗin kai shine takenmu.)
_3






















Ya abin yake?




Daban yake da sauran.




Da sauri Sadiya ta fincike wuyanta
haɗe rai sosai tayi ta ce "kada ki fara kada kiyi wannan kuskuren, ko ina yarinya ban yarda da dambe da kishiya ba, balle yanzu da nake da ƴaƴa da jikoki har da surikai."


A zafafe Ammi ta ingijeta tare da ɗaga hannu zata zabga mata mari dai-dai lokacin da drivern Didi ya danno hancin motarsa cikin gidan tare da sakin gigitaccen horn, bisa bin umarnin Didi don sanar da masu gidan zuwanta, wanda hakan shine tambarinta.


Cak Ammi tayi da hannunta cikin matuƙar ɓacin rai da haushin bayyanar jarababbar tsohuwar, tayi tsaki ta fice daga sashen Mahmahn da sauri don ta san tabbas Didi tazo ta tarar da wannan tashin hankalin ranar na lahira ma sai yafi ta jin daɗi. Mahmah tayi murmushi kafin ta furta “Gaba da gabanta”da ki tsaya mana. Sannan tayi azamar fita don tarar Didin.






Fuskar Didin a washe take kallonta, da duk jama'ar gidan tana amsa gaisuwarsu cike da murnar samunsu lafiya, ahalin Sakina ne kawai bata gani ba. Bata damu kanta ba ta san dalilinsu na ƙin zuwa bai wuce ba sa son tayi musu gorin rashin aure ba, alhali ba mijin suka rasa ba suna dai jiran wanda ya ci ya tada kai.


Murya a cunkushe ta kalli Sadiya ta ce"Ita hakimar kishiyar taki tana ina?"
Mahmah ta ɗan yi jim kafin ta ce "Ina ji sallah take tunda baki ganta ba." ta samu kanta da gillara ƙarya duk don ta gyara lamarin. Didi ta kalli agogon hannunta kafin ta ce "Sallahr walaha take Kenan da sha biyun rana? Sadiya kenan kishiya kike karewa don kada nayi mata sababi? ai ba tun yau na san Sakina bata ƙaunar taga nazo gidannan ba, saboda bata son na sawa yaranta ido to wannan karan a shirye nazo tsaf wallahi ba zan bar gidannan ba sai na aurar da iyayen matan da ta girke a ɗakinta, su ba zawarawa ba su ba ƴan mata ba, shi kuma soloɓiyin mijinku ya saka mata ido sabida baya son laifin balarabiya."


Sunkuyar da kai Sadiya tayi kafin ta ce "Kiyi haƙuri Didi ai aure lokacine da zarar lokacinsu yazo ko suna so ko basa so sai sun yi."


Dai-dai lokacin da Ammin ta shigo kuma duk wani sababin Didin akan kunnenta take yi ranta ya sake ɓaci shikkenan wannan matar zata zo ta ɗaga mata hankali.


Fuskarta ba yabo ba fallasa tayi sallama haɗe da faɗawa cikin parlourn. Didi ta zuba mata ido tana jijjiga kai ganin yarda Sakinan ta cono ɗankwali har gaban goshi,alamar dake nuni da cewa a shirye take da amsar duk wani rashin mutunci na Didin.
Murya a cunkushe ta fara gaisheta Didin ta yamutsa fuska kafin ta ce "Ai Sakina da kin bar gaisuwarki tunda ba dole nace sai kinzo kin gaisheni ba, ba buƙatar ta nake ba gaisuwar da za'a yiwa mutum ana faman ɗaga hanci dai-dai nake dake wallahi, ki bini a hankali kafin ki kaini bango." Sakina dai ɗan murmusawa tayi wanda direct zan iya kiransa dana rainin hankali ta miƙe cike da izza tace "A huta lafiya Didi" daga haka ta kaɗa zaninta ta wuce ta bar Hajja Didi da hangamemmen baki don kuwa ta hango raini tsagwaronsa a fuskar Sakina, girgiza kai tayi kawai tana kallon Sadiya tace "Shahara iyye! Cabd’i jam" girgiza kai itama Sadiyar tayi ita kanta tana mamakin yarda Sakinah ta fetsare har haka? Didin da ko ido mutane basa iya haɗawa da ita idan tana magana. Ita dai murya a sarƙafe ta hau bata haƙuri sannan ta miƙe don ta bawa Didin waje ta huta har ta kai bakin ƙofa Didin tace "Ina Hamda ne ban ganta ba ko bata gama gallafirin makarantar kwanar bane?" Sadiya ta girgiza kai ta ce tana ɓangarena bata da lafiya ne yau ma aka yi discharging ɗinmu daga hospital ai da tuni kin ganta ta fito."


"Subhanallahi me ya sameta haka? Yanzu haka shaiɗaniyar uwarta har yau bata san annabi ya faku ba ko? Wannan mata sai kace wacce tazo a zamanin jahiliyya ƙiri-ƙiri ka ƙi ƴarka ba laifin tsaye ba na zaune, muje in ganta ai gwara da aka mayar da ita ɓangaren naki, naga uban da zai ce sai ta koma gurin wulaƙantacciyar matar can da ta zamewa mijinki matar jaraba." Ita dai Sadiya murmushi kawai ta saki ta bi bayan Didin tana tafe tana riƙe zaninta da yake shirin faɗuwa.






A kwance suka sameta idanunta a lumshe lokaci guda ta sake zabgewa dama ita ba jikin arziki ba kyalan-kyalan take tamkar ta faɗi ko don bata da kwanciyar hankali ne Allahu ya alamu. Didin da sauri ta ƙarasa gefen gadon ta zauna tana dafa goshin Hamdan, da kyar Hamdan ta buɗe idanunta da suka zama tamkar garwashi ta zuba su akan Didi tana sakin wani malalacin murmushi, tana shirin miƙewa Mahmah ta ce "Koma ki Kwanta Ke da ba kya jin daɗi." Wani kallo Didi ta zabga mata kafin ta ce "Ta zauna a ina? Bayan Allah ya kawo ni, ke tashi dahalla mu wuce idan banda kafirin iyayi na Sadiya me ye haɗinki da ita da har zaki rabamu? Sadiya ta gumtse dariyarta ta ce "Ayi haƙuri Didi bari na taimaka mata ta koma ɓangarennaki" "Ya dai fi, in banda shegantaka ba ita take taya ni hira ba, sai kuma a barni can a zaune ni kaɗai kamar wata mayya dama ku gidannan ba wani yawan arziki ba kowacce ta tsaya ragwanta daga haihuwa biyar kawai ni sai da na haihu sau goma sha huɗu ke da kanki kin sani zama ne kawai Allah baiyi zasu yi ba, Huɗu kacal Allah ya raya min na kuma gode masa a hakan ma, muje dahalla kin tsaya min wani iyayin banza."




Ammi da take tsaye a jikin window ta hango fitowarsu ana rirriƙe da Hamda wani abu mai kama da tausayi yaso shiga ranta amma sai tayi tsaki kawai ta saki labilan zuciyarta na sake ɓacin ran ƙin barinta ta cigaba da wahalar da Hamda da aka yi, yarinyar da ko sunanta bata son ji bare karo da baƙar fuskarta.






Didi suna shiga ɗakin ta hau damawa Hamda fura da nononta mai kyau da tazo da shi, sai garin fura mai ƙanshi da aka yi mata dakan hannu sai zabga ƙamshi yake. Sosai damun yayi kyau sai ƙamshi take bata saka mata sugar ba sai zuma farar saƙa.




Da kyar Hamda ta miƙe ta karɓi furar ta fara sha dama Allah ya zuba mata son fura don dai bata samu ne sai Didi tazo, don wani lokacin da gangan Ammi take dama furar kuma ta hanata ta bawa masu aiki saboda ta san tana tsananin son furar. Ta lumshe ido tana jin daɗin zuwan kakartata da ta tabbatar soyayyar da take mata babu algus. Sosai ta samu ƙwarin jikinta har ta miƙe da kanta ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada sallah a gefen Didin da take sallahr itama.




Suna idarwa suka jiyo sallamar su Muneerah Najma da Nasma fuskar Muneerah ce kawai a washe banda ta su Najma da suka yi kamar an aiko musu da saƙon mutuwa.




Muneerah da sauri ta isa wajen Didin tana gaisheta, itama cike da kulawa take amsawa tana son Muneerah musamman da yake ita sunanta taci "Ina kika shiga tun ɗazu ban ganki ba?" Muneerah tana ɗibar fura ta ce "Wallahi Didi Islamiyya naje da na gaji da tsimayin zuwanki.".Didi ta ce "Masha Allah ubangiji ya bada nasarar karatu. Ku kuma asararru ina kuka shige ana nan dai ana haɗa kafaɗa da iyaye an ƙi aure ko? To ku kwana da saninku wannan karan da shirina nazo inma ku fitar da miji ko ni na fitar muku acan Gwarzo cikin dangi ko abokan arziki, na baku wata ɗaya kacal wallahi wannan karan ba zan karɓi uzirinku ba ko kun wuce azimi ba zaku wuce sallah ƙarama ba insha Allah ku haƙura ku zaɓi ko waye tunda govenor da shugaban ƙasar har yau ba su ganoku ba, sai ku rungumi haƙuri kafin furfura ta fara bayyanar muku a gida, don kyan da kuke taƙama da shi zagwanyewa zai yi matuƙar babu aure shashashai kawai." suna gama gaisheta suka miƙe ransu a. ɓace da tijarar da take musu suka ƙarasa wajen Ammi Suna shiga taga alamun Didi ta kunnosu tsaki tayi kawai tayi kafin ta tambayesu mai ya faru? Najma ta zauna tana zuba tagumi ta ce "Jarrabar tazo yaushe zamu ga dai-dai daga zuwanta har ta fara zancen aure wai mu zata haɗa da ƴan gwarzo kurt da kuwa sai ta gwammaci kiɗa da karatu wallahi don ba mai saka ni auren mutumin ƙauye."
Tsaki Ammi tayi kafin ta ce "Ya zama kuwa dole na tashi tsaye wajen samo muku mazaje na kece raini ko da kuwa zanyi yawo tsirara burina naga kun auri mazan kece raini da zanyi tunƙaho dasu a matsayin surukai tunda dai Allah bai bani yara mazan da nake burin naje gidansu na baje mulkina ba, kamar yarda waccan tsohuwar take baje nata, tun ina yarinya ban fi shekara sha shidda ba nasa wa raina son haihuwar ƴaƴa maza ganin yarda yayar Mamma na take baza mulki a gidajen ƴaƴanta maza Ita kuwa Ummi mu kawai ta haifa mata bata da inda take zuwa tayi tunƙaho sai daga baya ta haifi ƙaninmu shikkenan na sawa zuciyata burin haihuwar maza amma Allah bai cika min burina ba, duk da ƙoƙarin da nayi tayi akan haka."




Tana faɗar haka hawaye ya shiga gangaro mata akan fuskarta wanda hakan yake nuni ƙarara da zallar ɓacin ran da yake zuciyarta.




Ko da Abbu ya dawo zancen dai ɗaya ne Didi ta tareshi da shi ta kuma tabbatar masa wannan karan da gaske take dole ne ta aurar dasu da son su ko ba son su, su suka kawo mijin ko akasin haka ta sake jaddada masa "Idan har kaga hakan bai faru ba tabbacine na rashin rayuwata, amma ko sharafa nake a gadon asibiti sai na aurar dasu banda tsiya ko Munirah da Hamda sun kai munzalin aure. Shima kuma Hammad ka sanar dashi ya tattara ya dawo gida Yaro shekara sha uku yana can zube a ƙasashen masu jajayen kunnuwa yayi sammakal ko matarsa yana can aka Kai masa ita, ai barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. To wannan karan da shirina nazo ƙwal uban kowa zan ci har shi Hammad ɗin da ku iyayensa." Abbu dai sunkuyar da kai yayi yana jaddada mata za'a yi yarda take so.






Haka nake so Didi, ki soyawa kowa gyad’arsa a hannu y’an k’wal uba..
[1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE




YA ABIN YAKE ?


LIttafin Nazeefah Nashe.


08033748387




Follow me on ArewaBooks


@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e




ELEGANT ONLINE WRITERS


(Haɗin kai shine takenmu.)
_4










*******************************






Da asubar fari, da tayi sallah bata
koma ba, tana zaune gefen Didi suka yi azkar kafin ta karanta abinda ya sawwaƙa daga Alƙur'ani mai girma. Bata koma barcin ba, kasancewar ta ɗan ji sauƙin jikinta gyara sashen Didin tayi tas. ta wanke toilets uku da suke sashen ɗaya a Parlour biyu a sauran bedroom ɗin da suke sashen Didin inda ta mayar da ɗayan bedroom ɗinnata duk da dai Didin bata yarda su raba ɗaki ba tare suke kwana. Tas gurin ya fito sai zabga ƙamshi yake farin ciki ya lulluɓe Didi yana daga dalilin da yasa take son Hamda, sam bata da ƙiwa ko kaɗan. Wanka Didi ta shiga tana faɗin kema sai ki shiga kiyi wanka ga sabbin kaya nan da na ɗinko miki don na san waccan gallafirin uwar taki ko kayan ubanku yayi muku ba bari take ki saka ba, ta gwammaci ta haɗaki da gwanjo ina nan Ina jiran ranar da zata zo tana neman gafarar ki, to ko cikin shegen Ki tayi ai iya ɗiban albarkar da zata yi kenan, balle laifinki ɗaya wai kinzo a mace, shikkenan tun ranar da aka haifeki ake gumurzu da ita bari muyi walaha mu karya na baki labarin da kika daɗe kina son ji na san yanzu shekarunki sun kai sha bakwai tsab kwanyarki zata ɗauki labarin takaicin uwarki mai hali kwatankwacin na jahiliyya, na tabbata ita da kanta banda an saka mata ido tsaf zata iya hallakaki a lokacin, kai mun ga tashin hankali Ƙiris fa ya rage ta zauce sabida masifa.




Daga haka ta shige wanka wannan damar Hamda ta samu tayi saurin ficewa tana mamakin surutun Didin.




Sashen mahaifiyarta ta shiga, dama da spare key a hannunta ta buɗe a hankali, shiru ta tarar da parlourn da alama barci suke tabi gurin da kallo duk datti ɗan kwana biyun da tayi bata yi shara ba. Dama ita Ammi sam taƙi yarda ta ɗau mai aiki don tace gata bata buƙatar wata mai aiki. Ta ɗaure Hijabinta a ƙugunta ta shiga wanke kwanukan kitchen ɗin ta gyarashi tsaf burinta ta faranta mata ko ta samu ta goge tabon ƙiyayyarta a zuciyar Ammin.


Kan kace me? Ta gyare gidan tsaf banda ɗakunan barcinsu ta wanke har toilet ɗin parlourn sannan ta saka turarukan wuta a burner da humidifier tuni gidan ya ɗau wani irin Ƙamshi daga haka tayi sauri ta fice ta koma sashen Didi.




A saman sallaya ta tarar da Didin da alama sallahr walaha tayi, ita kanta Didin ita Ta koyar da ita sallahr walahar, tana sake jaddada mata ɗimbun ladan da yake cikin Sallahr walahan da tarin nutsuwa da mai yinta yake samu a zuciyarsa, ga shi Allah yana amsa addu’arsa ba da jinkiri ba.




Wankan itama ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login