Showing 39001 words to 42000 words out of 55059 words
Chapter 14 - MATAR MAHAUKACI END Book Complete Document Writing Mrs Sadauki .txt
ne kuyi fatan dai Allah fidda ku daga wanga baƙin wajen"
Duk suka amsa da "amen" Lami ta wuce yayinda Maryam ta fara shayar da yaron ta.
A asibiti kuwa mai gadi ne ya shigo da wani dattijo wanda duk yayi furfura ga uban gemu da ya tara,bayan sun gaisa da su Abbasi yace "na je can gidan ku na farko aka ce kun tashi nan aka gamo ni da wani ya kawo ni sabon gida sai kuma na tarar babu kowa sai mai gadin ke faɗan Issufu ne babu lafiya"Abbasi ya amsa masa "eh wlh ya na ciki yanzu haka Dr mu ke jira ya bamu izinin shiga yace mu jira sa"dattijon ya jinjina kai.
Can Dr ya leƙo yace "Bismillah"ai kuwa suka runguɗa,a kwance suka tarar da Daddy ya rame sosai yayi haske.
Da sauri ya tako inda Daddy ya ke kwance yace "Issufu?"Daddy yayi murmurshi yace "welcome back Mahmud sai yau Allah yayi nufin ƙarasowar ku?"Mahomet yace "Daddy wane Mahmud ɗin?"
"Baban Balkisu Uba mahaifi" cak suka tsaya su na kallon juna Balkisu da kuma Mama uwanda shigowar su kenan su na addu'ar Allah basu iko su ƙarasa kashe Daddy kafin ya tona masu asiri.
"Mahamud?"Mama ta faɗa shi kuwa ya juya ya na kallon mata ma fi soyuwa a rayuwar sa....
[03/03 à 13:55] Mrs SADAUKI 💫: *43-44*
Hayaniya da koke-koken su ya saka Dr shigowa fitar da su daga ɗakin aka bar Mahomet shi kaɗai,hannun Daddy ya riƙe yace "ya jikin na ka ?ka na jin wani canji kuwa?"Daddy ya lumshe ido ya na jin wani sanyi na ratsa sa sannan ya buɗe su yace "alhamdullah!ina takwara na?"
Mahomet ya sunne kai dan bai son ɗaga ma Daddy hankali "ya na can tare da mahaifiyar shi"ya faɗa dakyat
"To a kawo min shi nayi missing na shi sosai"Daddy ya faɗa ya na mai massaging hannun Mahomet da ke cikin na sa.
Da "toh Daddy"ya amsa kafin ya jefo wata tambaya "amman Daddy miyasa ba ka faɗa ma iyalansa ya na raye ba ka ɓoye masu?"Daddy ya bashi amsa "saboda inda ya ke da shi da matacce sunan su ɗaya,ka bari in na fita daga nan duk zan faɗa maku komi"shiru kawai Mahomet yayi.
Turo ƙofa aka yi tare da shigowa,Inna ce da Ammi.Cike duk da murna su ke tambayar sa jiki ya na amsa masu "to ai yanzu shikenan tunda ka farfaɗo sai ka faɗa ma ƴan sanda ba Maryam na ce ta so kashe ka muguwar matar ka ce dan haka a sako min jika ta"cewar Inna .
Da mamaki Daddy ya tambaya"Maryam ɗin na hannun su?"Ammi ta basa amsa da "eh! Bilkisu tace wai ita Maryam ɗin ta baka guba ka sha shine ƴan sanda suka kamata"
Daddy ya kalli Mahomet da sauri yace "yi haƙuri Daddy dan kar na tayar maka da hankali ne"Daddy yace "ok tashi ka je can police station ɗin ka tawo da ɗan sanda guda nayi mashi bayani"da murna Mahomet ya fita.
A harabar asibitin ya ga Mama sai kuka ta ke yayinda Bilkisu ke taya ta, Mahmud kuwa ya koma gefe ya na kallonsu dan shi ya zata kukan murna su ke.
Tsuki Mahomet ya ja ya na jin wata tsanar duka ahalin kafin ya wuce,babu jimawa suka zo shi da ƴan sanda wanda ganin su ya kaɗa hantar su Mama.
Cikin halin ciwo Daddy yace "ku saki baiwar Allah ba ta san komi ba,ku kama mahaifiyar Balkisu ita ta tsara komi in na ƙara samun lafiya zan yi maku bayanin komi"haka kuwa aka yi Mahomet ya yiwa ƴan sanda jagora har wajen Mama.
Da mugun mamaki Mahmud ke kallon su,a ruɗe ya fara tambaya "lafiya?mi matata tayi maku da za ku kamata?"
Mahomet ya bashi amsa "saboda ta so kashe mutumen da yayi ma rayuwarta da ta ƴarta halaci,duk tsawon shekarun da Daddy ya ɗauka ya na kula da su hakan bai sa tayi farin ciki ba sai ganin bayansa da ta ke son yi ta dalilinta ga shi an saka masa hanji roba .Ku tafi da ita."Mahomet na gama faɗa ya juya.
Mahmud kuwa zaman ƴan bori yayi tsabar tashin hankali ya kafe Balkisu da ido alamun ya na son jin ƙarin bayani dan alamu sun nuna ta san komi.
"Wlh Abba ba laifina ba ne Mama ce ta ban wani magani na saka ma Alhaji a tea tace min da zarar ya sha to sai yadda nayi da shi komi yawan kuɗi kuma zai bani ashe guba ce ta saka"wani gigitacen mari Abbas ya ɗauke ta da shi kafin yace "miƙe maza"tashi tayi jiki na ɓari,kamar wata ƙaramar yarinya haka ya kama hannunta suka fita ya tsayar da adaidaita jin ya ambaci comsariat ya saka Bilkisu ƙara ɗaga murya ta na kuka tare da bashi haƙuri.
Da isar su ya ce ma ƴan sanda a haɗa da ita a kulle, Mahomet wanda ya ke tsaye kusa da Maryam yayi murmurshi dan tun farko ya so a haɗa da ita sai dai gudun ɓacin ran Daddy ne.
Lami har da kukan ta jin Mahomet ya ɗauki nauyin zai biya duk bashin da ake binta,in kuma lokacin fitar ta yayi zai zo su ɗauke ta dan tuni matar da ta ji ma ciwo ta dawo hayyacinta.
Sai da suka tafi gida tayi wanka ta ci abinci kafin ta shirya Yusu, Mahomet ya wuce da su asibiti.
Daddy ya karɓi Yusuf ya na yi masa wasa sosai ya ke son yaron,Atine da Farida uwanda su ke zaune daga gefe baƙin ciki kamar zai kashe su .
Maryam na son yi ma Farida magana irin na tsakanin matar ƙane da magajin nan amman babu dama Farida sai cika ta ke ta na batsewa a doli ta shafa ma kanta lafiya.
Satin Daddy biyu a asibiti aka sallamo shi,tun daga nan rayuwar gidan ta koma wata iri saboda zuwa yanzu kowa ya gane tuggun Mama ne da Balkisu .
Ɓangaren karatun Maryam tuni ta fara zuwa school,in za ta tafi gida ta ke barin Yusu.Mahomet kuwa shi ya karɓi ragamar kasuwanci Daddy sosai ya ke tafiya da lamurran kamar yadda ake so.
A can comsariat kuwa Abba ya bada umarnin a hora su sosai duk da Daddy yace ya yafe,Balkisu tuni ido ya raina fata duk tayi baƙi haɗi da rama saboda azaba saboda babu mai kai masu abinci wanda ake raba ma ƴan kaso shi ne su ke ci.
Sai da suka yi wata uku cur sannan aka sako su, Mama zubewa tayi gaban Daddy ta na neman gafara.
"Kin ji kunyar duniya wlh,duk da ban kasance mutumen kirki ba haka bawan Allah na ya kula da ni tun farkon kama mu da aka yi da ƙwaya a hanyar Jos.Babu wata hanya da bai bi ba dan a sako ni amman abu ya cuttura saboda sabon D.P.O da aka naɗa mai shegen zafin kai,sun ci kuɗin shi sosai fiye da yadda kike tunani dan kawai a sassauta min horo.A yadda tsarin ya ke duk wanda aka kama da irin manya ƙwayoyi halbe shi za'a yi ko kuma yayi kason rai da rai,duk tsawon shekarun da na ɗauka a kurkuku jiran mutuwar mu ne ni ke sai kwatsam aka ce an fidda uwanda ake fitarwa Zakka ciki kuwa har da sunana.Bayan mun fito ne d.p.o ke shaidan Issufu ne ya roƙi alfarmar a sakaya da sunana bayan maƙudan kuɗi da biya na cin hanci"Abba na kawowa nan kawai sai ya fashe da kuka kafin ya cigaba da cewa "abokina na gode sosai kuma ina mai sake neman afuwar ka kuskuren baya da na yanzu,haƙiƙa kai abokin kirki ne shiyasa ko da aka kama mu kai ne mutum na farko da nace a tura ma hotunana ko Allah yasa ka ji tausayina ka zo gare ni sai kuma Allah ya amsa roƙo na"da sauri Daddy ya riƙe masa hannuwa ganin Abba na shirin kama ƙafafun sa "babu komi aboki ai yiwa kai ne,sannan ka yafe masu nima da laifina a ciki da ban sanar da su tun farko ba amman Allah na gani na ɓoye hakan saboda kar na tashi hankalin su"
Mama tace "haƙiƙa ɗaukar mataki ba tare da ƙwaƙwaran bincike ba ya na tattare da dana sani marar amfani, lokacin da na ga hoton Mahmud ɗakin ka cikin mawuyacin hali na zata aiwatar furucin ka ne kayi wanda kace za ka ganin bayan sa shiyasa na fara bin duk wata hanya da zan toshe farin cikin ka a ƙarshe kuma na baiwa Balkisu guba"
"Laha'ilah to aniyar ki ta biki kuma daga yau ko sawun ki na gani sai na tara maki mutane,kai kuma ka sakar masu Ƴa tunda abun ba mutumci"Inna ke magana ta na kallon Daddy wanda dama tun tuni ya rubuta ma Balkisu takardar sakinta.
Balkisu na ganin Daddy ya miƙo mata farar takarda ta saki ihu ta na kiran ta shiga uku ta lalace "nayi maki saki ɗaya"shine abinda Daddy ya faɗa kafin ya miƙe Abba ma ya miƙe yace "sai ki san inda zaku nufa ke da ƴar ta ki"
Kowa ya watse ya barsu su biyu a nan falo, Mahomet direct makarantar su Maryam ya nufa dan lokacin tashin su yayi tun tuni har ma ya gota.
Ya na tsayawa da mota ya tsinkayo ta ƙarƙashin icce sai turo baki gaba ta ke,sarai ta gan shi amman ta juyar da kai.A hankali ya soma takawa zuwa gare ta bayan ya rufe motar,"ran ki shi daɗe kaina bisa wuya am sorry"ta juyo ta dube sa tace "sabidar Allah ka kyauta ?tun fa ɗazu mu ka tashi shine sai yanzu za ka zo?"
"Réunion mu ka yi fah,kin san tunda Abban Balkisu ya dawo ba'a yi maganar komi ba sai yau,mu je na sauke ki gida"
"Ok naji,na san bbna yayi ta kuka na haura lokacin da ya saba gani na"
Mahomet ya taɓe baki yace "au shi kawai kike tausayi kenan banda uban shi?"dariya tayi ta buɗe seat ɗin gaba ta zauna, driving ya ke su na hira har suka zo gida.
Yusu na ganin ta ya miƙe ya fara takowa cikin irin tafiyar nan ta ƴan koyo,ɗaukar sa tayi ta cilla shi kuma ya fara dariya haɗi da yi mata gwaranci ya na nuna mata Inna .
Mama da Balkisu sosai suka yi nadama babu ranar da ba za su ban haƙuri ba akan Daddy ya mayar da Balkisu ɗakinta duk da dai har yanzu ba ta ra'ayin sa Mahomet ta ke so.
Sai da aka ruwa rana sannan ya maido ta duba da ba ta taɓa ra'ayin cutar da shi ba,tun dawowarta jiki yayi sanyi yanzu ta bar duk wata ɗagawa saboda ko ta gaishe da Inna ba kasau ta ke amsawa ba kuma yanzu Inna ta kasa ta tsare addu'o'in tsari ta ke ba kowa na gidan musamman ta sa Daddy ya ɗauki malumai duk wata a na biyan su,da wannan duk sihirin da ke jikin Abbasi ya baje kuma sosai shi ma ya gane irin sakacin da yayi a baya.
Bayan wasu shekaru
Tuni Maryam ta kammala karatun ta har ta fara aiki a asibitin Abbasi,Yusuf cikin shekara ta uku ya ke da wasu watanni tuni kuma Maryam ta samu wani ciki wanda sam bai bata wahala.
Tunda ta fara zuwa aiki maganar kirki ba ta haɗa su da Farida ba kowa sabgar gaban sa ya ke,dama can ba ɓangaren su guda ba.
Maryam ce tafe ta na daddanna waya kai taji tayi karo da mutum,ta na ɗagowa ta ga Dr nan ce wacce ta taɓa amsar number ta.
Murmushi ɗauke da fuskarta tace "Dr Halima ko?"kai ta gyaɗa tace "ashe ki na nan?wlh nayi neman lambar da kika bani sam ban ganta ba ashe da rabon za mu sake gamuwa"cewar Dr Halima .
Maryam tace "ayya bari na baki ,ya ne ko nan kike aiki?"
"A'a zan dai fara ne,ina ne office ɗin Dr Abbas ?"Dr Halima ta tambaya,kwatanta mata Maryam tayi ita kuwa tayi godiya ta tafi bayan sun yi masayar lambobi.
Knowking tayi daga can ciki aka amasa,shiga tayi bakinta ɗauke da sallama da sauri Abbasi ya ɗago jin zazzaƙar muryata sai kuma ya mayar da kansa ya amsa tare da bata izinin zama.
Dossier ɗin hannunta ta miƙa masa ya shiga dubawa,cike da jin daɗin ganin CV ɗin ta célibataire ce ba ta da aure Abbasi ya ɗago karaf idonsu ya sarƙe cikin na juna a tare kuma zukatan su suka buga......
[05/03 à 13:11] Mrs SADAUKI 💫: *45-46*
"Takardu sun yi kyau gaskiya kamar mai su"cewar Abbasi murmurshi tayi tace "na gode kenan za'a ɗauke ni aikin?"
"Eh har ma an ɗauke ki,ko yanzu za ki iya farawa "Abbasi ya bata amsa da murnarta ta shiga yi masa addu'a tare da fatan alkhairi wanda hakan ya sa ta sake shiga zuciyar Abbasi.
"Bari na baki system ɗin da za ki rinƙa amfani da ita,za ki ga komi da komi da ke ciki da yadda tsarin zai rinƙa tafiya.Sannan bayan sakatariya za ki rinƙa kama wani aikin in ana buƙata musamman in bani nan"Abbasi ya faɗa ya na ɗauko wata computer wacce lokacin da ya sallami sakatariyar shi ta farko ya karɓe abar sa.Kunnawa yayi kafin ya juyo ta zuwa gaban ta yace "ki kula sosai ina son mutum mai amana duk da Adamu ya shaida min ba ki da matsala kuma ko ina ana yabon ki"
Dr Halima tace "in shaa Allah DG za ka same ni mai riƙon amana da yardar Allah kuma za ka ji daɗin aikina fatana dai Allah shige mana gaba"
Abbasi ya amsa da "amen"nan Dr Halima ta fara duduba abubuwan da ke ciki daga ƙarshe dai Abbasi ya gwada mata office ɗin ta wanda sai an zo nan sannan a shigo nasa.
Zama tayi ta fara aiki kamar agogo a ƙasan zuciyarta sai godiya ta ke ma Allah da ya kuma bata wani aikin.
A kiɗime Farida ke kallon labarun ta na fiddo ido waje,tabbas in dai ba gizo idon ta ke yi mata tabbas wannan shine Jamal mijin Hawali.
Murya cike da tsantsar hassada da baƙin ciki ta ke cewa "wai dama Jamal ne yayi coup d'État😱 na shiga uku na lalace ni Fatima Bintu,ana nufin Hawali ta zama 1ère dame/first lady ? Innalillahi wa'inna iley raji'un bari dai na kira Mama na ji "ta ɗauki waya ta kira Mama babu ko gaisu tace "Mama sojan nan da ake cewa yayi juyin mulki dama Jamal ne?sai yanzu ni ke gani a journal da aka sa maimaici"Mama tace "eh mana nima jiya na gani a tv ko kin san shi ne?"kuka Farida ta fashe da shi tace "Mama mijin Hawali ne fah wannan ƙawata wacce na ce maki na goge lambar ta bayan na sakata liste noire"
Mama tace "to mine ne na kukan ?tun yaushe ni ke yi maki faɗa ki bar duk wata shiririta ki koma ga Allah amman kika ƙi?yanzu ai ga irin ta nan"kashe kiran Farida tayi ta na jin wani irin matsanancin haushi,rabon da tayi tunanin Hawali tun lokacin da tayi ma malam Jaye maganar ya zubar da cikin jikinta yanzu kusan shekaru uku kenan duk da ta na zuwa Niamey amman ko sau ɗaya ba ta taɓa neman Hawalin ba.
Abbasi kuwa lokaci ɗaya duk ya rasa sukunin shi,wani irin son Dr Halima ne ya shige sa lokaci guda sam bai san yadda zai yi da ruhinsa ba.Dossier ɗin ya duba ya ɗauki numérota da ke jikin lettre ɗin neman aiki,tunanin yadda zai ɓullo ma lamarin ya fara kafin kuma ya tashi ya na murmurshi.
Abbasi kamfanin layin Moov ya tafi ya sayo sabon Sim da kuma ƴar ƙaramar portable,zama yayi a mota ya haɗa komi kafin ya tsara text ya tura ma Dr Halima.
Ita kuwa baiwar Allah ta na can ta na faman gérer abubuwa a computer sam ba ta tsaya bin ta wayar ta ba har sai da lokacin tashi yayi ta rufe office ɗin ta wuce gida.
A gajiye ta shiga gidan,Moma na ganinta ta saki murmurshi ta ce "sannu da zuwa Sa'adiyana ga ruwan wanka can na zuba maki a bokiti dan su sha ɗan iska"zama tayi bisa tabarmar kaba tace "Washhh!na gaji wlh ,babu ƙanƙara ne ƙishi ni ke ji"
Moma tace "a'a fah ban samu yaron da zai sawo ba sai dai ki sha na tulu"
Safar ƙafarta ta cire kafin ta miƙe ta nufi tulun ruwan,moɗa ta cika da ruwa ta tsugunna ta shanye su tas ajiyar zuciya ta sauke kafin ta aje moɗar ta wuce ɗaki.
Zane ta samu tayi ɗaurin ƙirji kafin ta fito ta ɗauki ruwan da ke cikin bokiti ta shiga banɗaki,ba ta wani jima ba ta fito.
"Ga abincin ki nan ki ɗauka ki ci,ni zan tafi gidan Rahamu in yi mata barka kuɗin auren Ƴar ta da aka kawo"cewar Moma ta na gyara luluɓi.
Halima ba tace komi ba sai kujerar katako da tajo ta zauna kafin ta buɗe kwanon abinci,wake da shinkafa ne sai ƙamshin albasa ke tashi.Bismillah tayi ta fara ci tayi kamar ba ta san Moma na kallonta ba,cike da tausayin Ƴarta ta Moma ta fice bayan nazari da karantar halin ta Halimar ta shiga.
Ƙwalla ce ta fito daga idonta ta zuba cikin kwanon abincin,duk uwar yunwar da ta ke ji sai taji sam ta ɓace.Tashi tayi ta wanke hannunta ta shige ɗaki,bisa ɗan gadon ƙarfe ta haye ta kwanta tare da lumshe ido.
In ba ta saɓa lissafi ba yanzu shekarunta sun haura talatin amman shiru babu wani tsayayen saurayi balle ayi tunanin mijin aure.
Bayan hannu ta sa ta goge hawayen da suka zuba a kumatunta a fili ta furta " *WAMAN YATAWAKAL ALALLAHI FAHUWA HASBUHU* ```Duk wanda ya sanya yaƙininsa ga Allah ba zai taɓa da na sani ba,duk wanda ya yarda da Allah ba zai taɓa tozarta ba``` "
Tashi tayi ta ɗauko wayarta daga cikin bag,lambar Maryam ta danna ma kira babu jimawa kuwa ta ɗaga.
Gaisawa suka yi kafin su fara taɓa hira wacce duk akan aikin da Halimar ta samu ne,sosai Maryam ta taya ta murna tare da alƙawarin gobe za taje har office ɗin Dr Halima.
Katse kiran tayi ta na jin haka kawai Maryam ta shiga ranta, messagerie ta shiga ta fara dubawa har ta iso ga wata lamba wacce babu suna.
"Amincin Allah ya tabbata ga sarauniyar kyau,fatan ki na lafiya" shine saƙon da ta gani,Halima ta taɓe baki ta fito ba tare da tayi reply ba.
Tamkar wanda ƙwai ya fashe ma a ciki ko kuma mace mai naƙuda haka Abbasi ya kasa tsaye ya kasa zamne.Duk da