Showing 15001 words to 18000 words out of 55059 words

Chapter 6 - MATAR MAHAUKACI END Book Complete Document Writing Mrs Sadauki .txt

kowa sanin yanzu ban kula kowa balle na tsayar ɗin,kuma ni wlh tsoron auren nan ni ke"cewar Farida kamar za ta yi kuka dan har ga Allah ta na masifar son mahaifiyarta ba ta son ta rasa aurenta .
Mama ta girgiza kai tace "ki dai yi tunani ai ba'a rasa masu son ki sai ki zaɓi ɗaya"da sauri tace "Mama ɗazu wani yace ya na sona da aure har da lambar wayar sa ya rubuta a jikin letter yace in na amince sai na kirasa"da murna Mama tace "to ki kirasa mana"Farida ta ɗan yamutsa fuska tace "a'a sai zuwa dare kar yace dama jira ni ke" nan suka cigaba da tsara yadda komi zai kasance.








A ɓangaren Abbasi kuwa sosai yayi ta masifa miyasa Adamu ya rubuta mata lettre ba tare da ya shawarce sa ba,kamar mai naƙuda haka yayi ta zagayen ɗaki ya na cewa "shikenan ka dagula min lissafi ai ga shi ta ƙi kiran yanzu wajen awa biyar"Adamu ya ja tsuki yace "kai fa ka na da matsala ƙila ma ba ta buɗe saƙon ba"harar sa Abbasi yayi yace "duk laifin ka ne uban zanzari ai da bari ka yi har na samu lafiya 💯 sai na tunkareta da maganai"baki Adamu ya taɓe ya kishingiɗa ya na mai cigaba da kallon tv,Abbasi kuwa zaunawa yayi ya rabka tagumi suna nan zaune har aka kira sallar la'asar.
Bayan sun gama sallah Abbasi yayi zamansa masjid ya kama roƙon Allah ya na kai kukan sa tare da wuridi.
Duk text ɗin da ya ji sai gabansa ya faɗi yayi tunanin ko Farida ce,ganin zai zauce yasa shi saka wayar a silencieux.








Farida kwance bisa gado ta na tunanin yadda za ta shaida ma Abbasi ta amince ba tare da ta zubar da ajin ta ba,text ta ke ta na gogewa a ƙarshe dai ta rumtse ido ta tura masa.Ajiyar zuciya ta sauke ganin saƙon ya tafi a zuci tace "ko ba komi shi ba jarababe ba ne kuma ba ta da wani girman zai ji min ciwo"sai kuma tayi murmushi tuna délégué a fili tace "ina son laɓanka zan rinƙa tsotse su kullum kafin ayi aurena"ta ɗauki pilow ta rungume.


Abbasi kuwa sai bayan sallar isha ya fiddo wayar sa appel manqué ya gani dayawa har da na Atine,sai da ya fara maidawa mutane kiran sannan ya shiga duba saƙonni ```NA AMINCE DA AUREN KA.SIGNE FARIDA``` duk takaici da baƙin cikin da hajiya Atine ta ƙumsa masa sai yaji ya kawar.Wani ihu yayi na murna ya na mai ƙwalawa Adamu kira wanda ke share masu ɗaki "abokina ta amince yaushe za mu je gidan su?"Adamu yayi tsaye riƙe da tsintsiya ya na murmurshi yace "alhamdullah,yanzu sai ka kira ta har ku ɗan hiranta sai ka faɗa maka za mu je gidan su"kamar wani sakarai haka Abbasi ya wuce ɗaki ya na cewa "toh,toh abokin ƙwarai"






Sai da Abbasi yayi mata kira na uku sannan ta ɗaga,sanyayar ajiyar zuci ya sauke yace "amincin Allah ya tabbata ga sarauniyar kyawawa "tayi wani far da ido tace "tare da ɗan fillo "murmurshi mai sauti Abbasi ya fitar sannan yace "ai kema Fillon ce"tace "a'a fah ni bazabarma ce mai surki da Bugaje "yace "to daga yanzu kin zama Fillo tunda har kika kasance tsokar bafulatani sannan kika zamo fitilar sa "shiru Farida tayi dan ba ta saba jin irin wannan kalaman ba saboda ita ba ta taɓa soyayya ba.
Ya ja dogon numfashi yace "na gode sosai da kika amsa Bara ta,ina godiya da kika dubi maraicina kika karɓe ni a matsayin miji"tace "babu komi Allah shige mana gaba"yace "amen"nan ya fara janta da hira.








★★★ *MARADI VILLE*




Sanyayar ajiyar zuciya Maryam ta sauke ta na mai ƙara buɗe ƙofofin hancinta ta na shaƙar turaren wuta da na ruwar da Ammi ta saka ɗakin.Kamar wani mai hankali haka Mahomet ya ƙureta da ido ya na kallo tare da sakar mata murmurshi wanda ya ke har ƙasan zuciyar sa,dubanta ta kai gare sa sai kuma ta kawar da kai saboda faɗuwa da gabanta yayi.
Toilet ta shiga ta tsaya kallon tsarin wajen,an jera towel manya da ƙanana color biyu blue da kuma rose sai ƙaton baignoire wanda ya ke kamar ƙwarya mai rond.
A hankali ta taka zuwa shower kafin ta cire kayan jikinta,pampon ta kunna ruwa suka fara tsatsafowa kan fuskarta da sauri ta lumshe ido ta na shaƙar iska.Sai da ta jiƙe jikinta sannan ta jawo soso rose kamar yadda Ammi ta yi mata bayanin ita ke da komi rose Mahomet kuma blue tun daga towel,soson wanka da kuma brush.
Sabulu ta goga mai ƙamshi kafin ta fara gogawa a fuskarta,ƙarar buɗe ƙofa yasa ta juya da sauri cikin rashin sani ta buɗe ido ai kuwa kumfa ya shige idon da sauri ta juya ta murɗa pampon ta fara wankewa.
Dariyar Mahomet taji ƙyalƙyalƙyal har da taɓa hannuwa,"fita har na gama"ta faɗa cikin ɗaga murya ta na rufe ƙirjinta.Kamar wani ƙaramin yaro ya maƙe kafaɗata tare da soma cire jallabiya jikinsa,kyarma Maryam ta fara ganin ya raba kansa da kaya ya nufota.Da sauri ta rumtse ido ta na jin hucinsa,shower ya kunna masu tare da jawota zuwa ƙirjinsa ta ja ajiyar zuciya ta na jin wani yammm saboda gargasar ƙirjinsa da ta gogu da fatar ta.






"Das.Das.Das!"haka zuciyar Maryam ke yi,wanka ya fara yi masu da sauri ta ƙara rumtse ido jin ya na cuɗata,wa'azin malamin su ta tuna inda ya ke ce masu *« هن لباس لكم وانتم *لباس لهن* matanku gonakin ku ne,ku sutura ne gare su suma haka."dan haka ku kasance masu sirri ga mazajen ku,kar ku bari ku fitar da sirrin da sai da kuka rufe ƙofa kuka yi saboda Manzon Allah SAW yace bai hallita ga mata ko miji ba su sanar da wani wata magana alhalin kafin su yi sirrin sai da suka saki labule bima'ana ba su yi zancen ko wani abu ba sai lokacin da suka kasance su ɗaya kamar kwanciyar aure,faɗar wasu kalmomi da ma'aurata kan gaya ma junansu na sirri»


A zuci tayi tunaninta da ba za ta manta ba lokacin da malam yayi wa'azin ba ta fahimta sosai ba,ta na ta yi mashi tambayoyi har manyan Ajin suka katse mata hanzari saboda sun san ba ta yi girman da za'a kawo ta ajin su ba kawai dan ta na da ilimi ne sosai.
Da sauri ta dawo daga tunanin jin Mahomet na matsa breast ɗin ta,ido ta buɗe ta sauke su kan fuskar shi daidai lokacin ya ɗago shi ma ya dubeta jin ta tsayar da shi,idonsu suka sarƙe cikin na juna.Matsawa ya sake yi ita kuma ta ƙara riƙe hannunsa ta buɗe baki za ta yi magana da sauri ya sunkuyo ya sauke laɓansa kan lisp ɗin ta......
[14/02 à 11:40] Mrs SADAUKI 💫: *PAID PAGE 19-20*




*Littafin kuɗi ne ki biya ki karanta hankali kwance ƴar uwa ba tare da kin shiga haƙina ba ki biya 200₦ kacal ki sha karatu in kin shirya kin tuntuɓe Ni ta WhatsApp* +22795045822




MATAN ALBARKA HERBAL MEDICINE


INA KUKE ISASUN MATA MASU AJI MASU DARSJA DA GIRMA MU MATSO KUJI GA GYARA NA MUSSAMN NA ISASUN MATA MASU AJI


INA MAI MATSALAR SAURIN KAWOWAR MAI GIDA KI ZO GA HADIN NE DA KAI ZAKU SAMU QARFI DA ISASHEN RUWA
MAI FAMA DA BUSHEWAR GABA
MAI BUDEWAR GABA
MAI QAIQAYIN GABA
MAI FITAR RUWA BA KAN GADO
INA MAI SO TA MATSE MUNA DA MAIDA TSOHUWA YArinya
Kuma muna gyara amare gyaran da zai shekara a jikin su ina masu jego
Kuma ga naku gadin ISASUN MATA
Muna gyara dukan matasalolin mata na cikiy Dana waje kedai ki tuntubemu a wanna nombar kuma muna wa,azin aure 08163199051


Sign manager c,e o maman shukura
____________






Tsawon lokaci ya ɗauka ya na embrassé ɗin ta kafin ya cire bakinsa ya ƙura mata ido,baki ta turo tayi masa harar wasa shi kuma ya tuntsire da dariya ya na laƙuto kumfar da ke jikinta.Shower ta kunna ta fara tsaftace kanta,ya ɗan tureta shi ma ya shiga ruwan na dukar sa towel ta jawo ta ɗaura ta fice ta barsa ya na ihun yadda ruwa ke tsatsafowa.




Mai ta ɗauka ta shafe jikinta sannan ta murza humra,ta na shirin saka kaya Mahomet ya fito ɗaure da towel har ƙirji yadda ya ga tayi dariya Maryam tayi sai kuma ta nufo sa ta fige towel ɗin tace "wannan ba na ka ba ne,sai ka koma ka ɗauro na ka blue"kafaɗa ya maƙe kamar ɗan yaro ya fara ƙoƙarin ƙwata da ta ƙi bashi shi ma ya fige wanda ke ɗaure ga jikinta.
Ta na gunguni ta ɗaura wanda ta ƙwace ɗin kafin ta nufi drower kayanta,riga da zane na atamfa ta saka ba tare da ta ɗaura ɗan kwali ba.Ya matso kusa da ita kamar a mafarki taji yace "kaya na ki saka min"waigowa tayi ta tambaye shi "wai kai mahaukaci ne kuwa?"kai ya girgiza mata tare da wani murmurshi, ɓangaren inda kayansa suke ta buɗe kaya ne sosai na maza ta taɓe baki tace"ashe kai ma ka nada kaya shine kullum kake fama da jallabiya?"bai tankata ba ta fiddo riga da wando na jean,da taimakon ta ya shirya tsaf ya fito Mahamadu ɗin sa kai kace kwanyarsa daram ta ke.
Mai ta murza a tafukan hannunta ta shiga murje masa fuska kafin ta saka masa turare,ja da baya tayi ta ƙare masa kallo kafin ta kama hannunsa su sauka ƙasa.








Da murmurshi Ammi ta tarbe su ta na cewa "ah yanzu kuwa ni ke shirin shiga na ga ko lafiya daga ki tai ki yi wanka ki fito"murmurshi kawai Maryam tayi ta na son rabe hannunsu amman Mahomet ya riƙe ta gam.
"To ku je ku zauna kafin Daddyn ku ya fito"kamar jela haka suka jera suka nufi salon,wani banzar kallo Balkisu ta watsawa Maryam wanda taji gabanta yin mummunar faɗuwa kawai sai ta fara ambaton Allah.




"Ina kika baro ɗan kwalin?salon ki jawo mana aiki ko?to tashi maza ki ɗauko shi"Inna ke magana cikin faɗa, Maryam tace "dan kaina ya sha iska ne in na dunkume sa ai wari zai yi"kallon da Inna ta jefa mata ne yasa tayi saurin tashi ta na gunguni, Mahomet ma ya bi bayanta😹






A tsakar ɗaki ya ja ya tsaya ya na kallon yadda ta ke ɗaurin,yayi huging na ta yace "Masha Allah"haka kawai taji wani sanyi ya ratsata,juyowa tayi suna facing juna tare kallon juna ido cikin ido.Murmushi ya sakar mata har point beauté ɗinsa ya lumtsa,ta shafi gurin kafin tace "kai ma yau kayi kyau"ta ja hannunsa suka sauko.


Tuni Daddy ya hallara,sosai yaji daɗin sakin jikin da Maryam ta yi.Sai da ta gaishe da Daddy sannan suka zauna, Hajiya Atine ita ke da girki hakan yasa ta fara servir ɗin kowa da ta zo daidai su Maryam sai ta ɗauki babban plate ta zuba masu tace "ki baiwa mijin ki abinci a baki ki fara samun ladar aure"ta na sakin wani murmurshi wanda ita kaɗai ta san ma'anar sa.
Ƙureta da ido Inna tayi ta na son gano wani abu amman sam Atine ba bayar da hanyar ba, Maryam ta ɗebo abinci ta kai bakin Mahomet ya na kallonta haka ya buɗe baki ta saka mashi.
Ta na shirin kaiwa bakinta ya dakatar da ita ya ɗebo zai kai bakinta Balkisu tayi wani irin tari wanda yasa duk kowa kallonta dan sam su ba su san wainar da su Mahomet ke toyawa ba kowa abincin sa ya ke ci.






"Sannu ki sha ruwa koko mai yayi yawa ne?"cewar Atine ta na miƙowa Balkisu kofin ruwa,ta karɓa ta na hararen Atine a zuci kuma ta na tsine mata tunda ita ta basu shawarar haka"
Ganin tarin ya lafa yasa kowa ya cigaba da cin abincin shi,Maryam kuwa Ayar tambaya ta ɗora kan Balkisu ganin ta kuma ƙure su da ido.
Plate ɗin ta ɗauka tare da kama hannun Mahomet suka koma tsakiyar salon,wani maƙoƙon baƙin ciki ya turniƙe Balkisu tsabar jin haushi yasa ta miƙe ta nufi ɗakinta.
Cikin kuka ta kira Momynta ta na cewa "wlh Momy na gaji haba in ba ayi wasa ba sai dai ki tarar da gawata gidan ga,tun farko na gaya maki Ɗan ni ke so ba uban ba amman kika nace na aure shi yanzu ga shi nan wata banza na shirin ƙwace min shi"daga can ɗayan ɓangaren Momy tace "ki kwantar da hankalin ki mai gadon zinari ai na kusa dawowa,da zarar na dawo ki sa a ranki mahaukaci ya zama na ki kuma wannan yarinyar tun can baya na faɗa maki ki bar damuwa da ita"Balkisu ta goge ƙwalla tace "to ni dai na gaji na baki damar ƙarshe in har ba ki nemo min mafita ba ni zan nemawa kaina"ƙit ta kashe kiran ta nufi toilet ta sakarwa kan ta shower ko taji sanyi.








★★★ *NIAMEY*




Da kwatance su Abbasi suka isa gidan su Farida sun samu tarba mai kyau,Papa yayi mashi tambayoyi a ƙarshe yace a basa wata ɗaya in shaa Allah zai gabatar da iyayensa su zo nema masa aure.
Farida ta fito rakiyar su,Abbasi sai wani rawar jiki ya ke kanta tare da yi mata godiya ta na shirin magana wayarta ta ɗau ringing ta na ɗagawa taji ihun Hawali ta na cewa "ƙawata na samu aiki wlh na samu buƙata ta biya"Farida tayi murmurshi tace "zan kira ki an jima ina tare da baƙi ne" "ok to babu damuwa gobe zan je office ɗin ki akwai hira ƙawa,yanzu nima frite zan soya ma babban Kalil"cewar Hawali ta na kashe kiran.
Ta rausayar da kai tace "sorry wlh wata ƙawata ce ke gaya min ta samu aiki" Abbasi yace "Masha Allah,haka ai ake so Allah sa alkhairi mu za mu wuce Adamu na jira na"ya miƙa mata wani ɗan ƙaramin akwati ta karɓa ta na mai cewa "amen!in kun isa gida lafiya ka kira ni"yace "ok babu damuwa gobe za mu koma Maradi Bus ɗin 09h "Farida tace "eh haka Adamu ya faɗa min wai, please ba ku bari ko 2week ku yi?"Abbasi yace "a'a gwara da na koma na shaidawa su Daddy maganar auren mu"Farida ta rufe ido da gudu ta shige gida.
Abbasi na dariya ya nufi gun Adamu wanda tuni ya samar masu abun hawa wanda za su koma,su na isa gida kuwa Abbasi ya kira ta suka sha hira kai kace dama sun yi wani sabo.




Washegari
09h cicif motar su Abbasi ta ɓaga zuwa Maradi cike da kewar masoyiyyar sa suka bar garin.
A ɓangaren Farida kuwa hakincewa tayi cikin office ɗin ta , délégué na gefenta ta na lalube shi tare da tsotse sa shi kuwa kamar wani soko haka ya zauna.
Su na tsaka da kissing Hawali ta banko kai da sauri duk suka ɗago,ajiyar zuciya Farida ta sauke ganin Hawali ce.
"Ka tashi ka tafi sai kuma na neme ka"cewar Farida ta na shafar laɓan délégué,ba dan ransa ya so ba haka ya fita.
Hawali tace "amman kin cika ƴar iska ke yanzu ba ki jin tsoron asirin ku ya tonu?a office fah kuke ba gida ba"Farida ta harareta tace "ke dallah Malama ki zauna in ba ke ba akwai uban da ya isa ya shigo min office ba tare da neman izini ba"Hawali ta taɓe baki tace "to ki shafawa Ɗan mutane lafiya tunda kin ce tsoron aliyarsa kike"Farida ta sheƙe da dariya tace "Allah kuwa wannan mugun abu ai doli naji tsoro amman Abbas tashi daidai ni ce"Hawali ta zauna tace "wai dagaske ƙawa aure za ki yi?"Farida ta ɗaga gira tace"Yes !Har ma sun yi magana da Papa jiya"cike da murna Hawali tace "alhamdullah!yanzu mu yi zancen abinda ya kawo ni kince abinda yasa Abban Kalil ke nuna halin ko in kula a kaina saboda rashin aiki ne kullum sai na roƙesa kuɗi to yanzu da na samu aikin ya zan yi?"Farida ta gyara zama tace "eh sosai saboda yawan roƙon miji ya na sa martabar ki ta zube,yanzu abinda za'a yi kayan jiki na faɗa a gani za ki saye da mayuyuka masu kyau gami da turare ki rinƙa tsantsara mashi kwalliya sannan kuma ki rinƙa yi masa abinci jefi-jefi wanda ba daga aljihun sa ba kuɗin suka fita"Hawali ta sauke ajiyar zuciya tace "in shaa Allah zan gwada yi Allah sa ya karɓe ni"Farida ta ja tsuki tace "in bai karɓe ki ba sai ki kai banza wajen Malam "Hawali ta tunzura tace "Allah kiyaye da na yiwa mijina asiri sannan mijina ba banza ba ne ki iya bakin ki"abu kamar wasa Farida ta hasala nan suka fara caca baki har Hawali tayi zuciya ta bar ta nan.








★★★ *MARADI*




Kwana ɗaya tal da su Maryam suka kasance ɗaki ɗaya da Mahomet sun samu fahimtar juna,alaƙar aure ba ta shiga tsakanin su amman sun raba dare su na wasanni da sassan jikin juna.Abun ka da tashen balaga sosai Maryam ke jin daɗin yanayin shiyasa ta biye masa ba tare da tsoro ko kunyarsa ba,abu ɗaya ya bata mamaki yadda Mahomet yayi masu wankan tsarki.




Zufar gaban goshinta ya goge mata da hannunsa ya na sake kallon zallar kyawun da Allah ya yi mata,ɗan motsawa tayi gami da miƙa sai ta ɗan buɗe idonta Mahomet ya sakar mata murmurshi ya na son tayar da ita zaune.Bisa fafaɗan ƙirjinsa tayi luuu ta kwanta ta turo baki kaɗan tace "bacci ni ke ji ka bar ni na huta,jiya kai ka hana mu rumtsawa"rungumeta yayi ya na ɗan jijigata kamar wata baby hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya yiwa Maryam ba nan take barci ya kuma ɗauke ta.






Kamar daga sama yaji muryar da duk duniya babu wacce ya ke tsoro da kuma tsana kamar ita,cikin takaici Balkisu ta kuma cewa "Mahomet haka za ka yi min?"cike da tsoronta ya shimfiɗe Maryam ya koma gefe ya na zanzana.
Tunkarosa tayi da sauri ya zube ƙasa ya kama kunnuwansa alamar ya tuba,miƙar da shi tayi tsaye ta shafi sajen sa sannan ta kai bakinta kan lips ɗin sa ta fara kissing.
Tureta Mahomet yayi ya girgiza mata kai,ta saki murmurshi tace "Daddyn ka ne dama yace azo a duba a gani ko lafiya ba ku fito ba?"bai ce da ita komi ba sai kallonta da ya ke ya na karantar halin ta "munafuka na tabbata in kika san da ɗan sauran hankalina ba za ki fito da true color ɗin ki ba,da sannu zan kawo ƙarshen ki kafin ki aiwatar da nufin ki"Mahomet

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login