Showing 54001 words to 55059 words out of 55059 words

Chapter 19 - MATAR MAHAUKACI END Book Complete Document Writing Mrs Sadauki .txt

mota yayi ƙasa da shi ya na kallon yaran na sa wanda duk duniya bai da kamar su,murya a ɗan raunane yace "shi ma Abdallahn ta riƙe sa ne ko miye?"da sauri Maryam ta dube sa tace "eh yace zai zauna ne "cike da jin haushi ya kawar da kai,Inna da ke bakin ƙofar gida ta na kallon su tace "uwar mi ce ya ke cewa?"Maryam ba ta ce komi ba ta shige mota ya ja su.






Su na zuwa gida ya shige ɗakinsa,jikin Maryam ne yayi sanyi duk sai taji babu daɗi.Part ɗin ta ta wuce,wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa.
Ɗakinsa ta nufa,a zaune ta tarar da shi ya na duba syst dab da shi ta zauna ta ɗora kanta kan kafaɗar sa.Bai kulata ba ya cigaba da aikin sa,ta turo baki ta kai hannu ta na daddanna system ɗin.Tsayawa yayi hakan yasa tace "kayi haƙuri"ba tare da ta kalle shi ba,"haƙuri?da aka yi mi?"ya tambaya,amsa ta bashi "da na baro Abdallah can wajen Inna "ɗan ture ta yayi yace "a'a dan mi ai Ɗan ki ne tunda kin yanke hukuncin barin sa a can miye nawa?"a yadda ya yi maganar za ka gane ya na cikin fushi.
A shagwaɓe tace "dan Allah kayi haƙuri Allah zan haukace "Mahomet ya miƙe yace "daidai kenan sai mu yi ta haukan a tare dama mijin ki mahaukaci ne kin ga sai mutane su ce *MATAR MAHAUKACI* ta haukace "da sauri ta tashi ta na dire-diren ƙafafu haɗi da kukan shagwaɓa "Allah kar ka sake ce min matar mahaukaci tunda dai mijina lafiyar sa lau"da sauri Mahomet yace "a'a inda lafiyar sa lau da ba za ki bayar da yaron sa riƙo ba alhalin kin san nan da wani week..."saurin huging na shi ta baya tayi hakan ya sa shi ƙyalewa.






Lokacin da ya juyo ƙuri suka yi ma juna,kafin ya ɗan busa gashin idonta da sauri ta lumshe ido.A hankali ya ranƙwafo ya sa bakin sa cikin nata,halshen sa ya zura ya fara shan yawunta.
Jikinsa ta ƙara shigewa kafin ta ririƙesa da dukan hannuwan ta,tsawon lokaci kafin ya cire bakin sa ya ɗago haɓarta ya na dubanta da idon shi suka canza launi.Da sauri tayi ƙasa da kai,zip ɗin rigarta ya ja tare da yin ƙasa da rigar,da sauri ta faɗa ƙirjinsa saboda har kullum ta na jin kunyar Mahomet.Kan bed ya direta ya fara sarrafa ta,har zai shigeta ya fasa da sauri ta buɗe idonta jin ya kwanta kusa da ita ya na sauke numfashi.
Ido cikin ido suke kallon juna,kafin ya ɗaga mata gira ita kuwa ta turo baki ganin haka Mahomet ya rage masu hasken ɗakin kafin ya ziyarce ta.










Haka rayuwa ta cigaba da kansacewa yau daɗi gobe akasin sa, ɓangaren Dr Halima sosai ta samu nutsuwa zumuncin su da Maryam ya ɗore sosai kamar yadda ya ke wajen Hawali da Farida wacce aka naɗa shugabar mata ta masu HIV .


Taron buɗe asibiti M.M AGAJI ya tara dubbunan likitoci da iyayen su,likita ce ta azo a gani wace ta tara ko wane ɓangare na kiyon lafiya.
A gaban ɗumbin mutane Mahomet ya taimaka ma Maryam ta datse ɗan ƙyalen da yayi masu iyaka da shiga harabar asibitin,taɓi aka yi Mahomet ya ja hannunta suka shiga, Daddy da Ammi da su Tantie Yusura da Inna ma suka shiga kafin sauran jama'a .
Atine sosai taji haushin ganin asibitin Mahomet ta fi ta Ɗanta Abbasi amman da ta tuna hassada babu kyau sai tayi ta Istigfari,su Dr Halima da Abbasi sai duba waje suke suna yaba kyawun sa gami da yin addu'a.
Mahomet kuwa hannun matar sa ya jaye suka silale wani ɗaki,Maryam ta waro ido tace "Chouchou wai miye nufin ka mun baro baƙi a can fa"wani irin jawota yayi yace "babu ruwana da su uzuri ne ya taso dan haka a taimaki patient please Dr "dukan wasa ta kai masa a ƙirji ta na cewa "babu wani patient wayo ne kake son yi min"cak ya ɗauke ta ya ɗorata kan wani ɗan madaidaicin gado ya na mai cewa "ina son zama patient na farko da za'a duba matsalar shi ne"Maryam na murmurshi tace "to bari na fara gwada alƙalamin ka in har dagaske ya shiryar karɓar traitement ɗin Dr Maryam "fuska ya shagwaɓe yace "ai kuwa dai tamkar ya ji ki har ya fara..."saurin kai bakinta tayi kan lips ɗin shi tayi shi kuma yayi baya da su ya zamana ita ke bisan sa,har zai cire mata kaya yace "bari dai na rage hasken ɗakin ta yadda ƴan gulma ba za su ganin mu ba"Maryam ta turo baki tace "wlh kuwa kamar ka sani Mrs SADAUKI na nan ta laɓe ta na ɗaukar duk abinda mu ke ta na kaiwa can *MATAR MAHAUKACI* PAID"Mahomet ya waro ido yace "kai haba wannan tonon asiri har ina,kice duk ta tonare mu?"Maryam tace "sosai fah ba ka ga Halimatu tun daga Diffa ita da M Shakur ta Katsina da Lawiza suke sauraren kalar soyayyar mu ba?"da sauri yace "ke an yi fah haka dan kuwa haka na ritsa Queen Fulani ta na gulmata wai ashe har dukan ki na taɓa yi lokacin da ina hauka?"Maryam ta ƙyalƙyace da dariya tace "ai kuwa dai Mrs Shugaba da M Yusuf Dabo sai da suka ta yi min dariya, Princesse Aichatou da wasu ɗaiɗaikun FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS kawai suka tausaya min"Mahomet ya jawota yace "ke haba dan Allah?ki na nufi Real Aïcha da Sajida da Najaâtou Haladou duk ba su cece ki ba?" Baki ta kwaɓe tace "ai fah sai kayi ba su ne ƴan *GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR 🇳🇪* ba?to duk dariyata suka yi"Mahomet ya ɓata fuska yace "ok tunda ma haka ne bari na ida kashe duk hasken ɗakin gaba ɗaya ,Mrs SADAUKI ba za ki sake leƙen asirin mun ba tunda har mun gano ki mi za mu ce Qalbi?"yayi maganar ya na tambayar Maryam haɗi da sake janyota ya manna jikinsa sosai a tare suka sauke wata sanyar ajiyar zuciya suna masu furta "Alhamdullah!"


To Ni ma Mrs SADAUKI 💫 a nan Ni ke cewa:


*ALHAMDULLAH !!!*




A nan na kawo ƙarshen labarin matar mahaukaci,godiya ta tabbata ga Allah mai kowa kuma mai komi da ya bani ikon gama sa lafiya.Ina godiya da dukan masoyana na gode sosai da kuka kasance tare da ni kuka fidda kuɗin ku kuka sayi book ɗina,na gode sosai da kuka nuna soyayyar ku gare ni😍😍😍

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login