Showing 51001 words to 54000 words out of 55059 words
Chapter 18 - MATAR MAHAUKACI END Book Complete Document Writing Mrs Sadauki .txt
kula da su ɓangaren harakar kuɗi.
Ranar da Farida ta cika wata uku,tuni ciwon ya fara warkewa,babu laifi yanzu ta rage zage-zage sai ma hankali da ta maida kan Ɗan cikinta wanda cikin ikon Allah bai zube ba.
Safiyar da Hawali ta zo dubata ne ta riske su cikin tashin hankali wanda ba komai ya haifar da haka ba sai cutar ƙanjamau da aka tabbatar Farida na da ita ranar da aka fara yi mata awon farko.
Dan doli Abbasi ya sake dawowa saboda kiran gaggawa da Hawali ta sa aka yi mashi,jininsa aka auna aka tabbatar da lafiyar shi lau.
Cikin kuka Farida ke yi masu bayanin inda ta ke zaton ta samu H.I.V wato ga malam Jaye,tuni kuwa Hawali ta tura bataliyar sojoji dan ƙwamuso shi sai dai kash ƴan unguwa sun ƙona shi.
Farida na jin haka tayi ihu ta na cewa "wayyyo na shiga uku na lalace shikenan ba zai yi min aikin ba,dan Allah ku kai ni gidan wani malamin wlh in Abbas yayi aure mutuwa zan yi"
Abbasi wanda haushi da takaicinta duk sun cika shi,jin wai da igiyar aurensa taje ta kwanta da wani ƙaton banza.
Ƙanƙance ido yayi yace "ai kuwa sai dai ki mutu dan kuwa tuni Dr Halima ta shigo gidana yanzu haka ta na ɗauke da cikina,kuma ki sani na sake ki saki uku in kin haife min yaro zan zo na karɓe sa kar ki shayar da shi guba"ya na gama faɗa ya ajiye mata takardar sakinta.
Papa ya ja Mama suma suka bar ɗakin bayan Papa ya tabbatar ma Farida sun yarda ta taje can ta nemi wasu iyayen amman ba su ba,cikin kuka ta diro daga kan gadon sam ta manta ma da har yanzu ƙafafuwan ba su warke ba sai da ta ga suna fitar da jini.
Da sauri Hawali ta duƙa ta rungumeta tare da fashewa da kuka tace "ƙawata duniya ce ke haka,duniya juyin waina yau in ta na yayin ka gobe sai ta sake ka ta kama wani,a baya mun yi kuskura sosai shine na zuwa gidan boka wanda ban ƙara yarda ba sai da aka naɗa Jamal shugaban ƙasa nan na gane malam Jaye ba malami ba ne ɗan tsibo ne.Sannan lokacin da na samu cikin Ahmad duk a mafarki a nuna min komi,nayi neman ki dan na nusar da ke muhimmancin abota amman ban samu ba har gidan ku naje na tarar da su Papa sun tashi doli na haƙura.Dan Allah abinda ni ke so da ke kiyi haƙuri ki sa ma zuciyar ki dangana,sannan ki ƙudirci tuba tun yanzu ni kuma nayi maki alƙawarin zan kasance tare da ke har ƙarshen rayuwa"
Hawayen Farida ne suka tsaya cak jin kalaman Hawali "ƙawa duk irin cutar da nayi maki amman har yanzu ki na jin sona a ranki?kuma dagaske kin yafe min?"
Hawayen da ke kan kumcinta Hawali ta share mata kafin tace "bai komi bari na kirawo Dr ya duba ki "da sauri ta riƙo hannun Hawali kafin tace "dan Allah ki sa a cire min cikin nan ban so na haifo yaro mai irin cuta ta"
Hawali tace "a'a ai ba zai zo da ciwon ba ko kin manta akwai prévention ?"Farida ba tace komi ba Hawali ta fita ta kirawo Dr aka mayar da ita kan gado kafin a duba ta.
**** MARADI
Dr Halima ce zaune ita da Maryam wacce ta kawo mata ziyara, videos biki suke kallo yadda aka gabatar da bikin Dr Halima ɗin da Abbasi.Video na kaiwa ƙarshe sai wata ta shigo ashe na bikin Farida ne lokacin da aka yi party.
Dariya Maryam tayi tace "ashe ki na da shi"tayi maganar ta na kallon tv inda aka wano Mahomet duk ya ririƙeta kamar za'a ƙwace ta.
Dr Halima tace "eh wlh ashe Hubby ya na da shi,jiya na kalli video wlh in an ga Abban Yusu ba'a cewa bai da lafiya"
Maryam tace "a'a fah ana ganewa dubi yadda ya manne min,duk inda na yi ya na biye da ni"
Sallamar Atine ce ya katse su,da sauri Maryam ta miƙe ta karɓo Abdallah wanda tun zuwan su ya ke hannun Atinen "ki basa ya abincinsa, bawan Allah ya sha barci "cewar Atine da murmurshi Maryam ta karɓe sa ta na cewa "ai kuwa dai"kafin ta zo ta zauna.
A can gidan Daddy kuwa yau sosai suka ji dawowar Inna wacce tayi zamanin ta a Mai Jan Gero,wanda kuma tayi hakan ne dan baiwa Ammi da Daddy damar shaƙatawa tunda yanzu ita ɗaya ta rage cikin matan.
Yusu na kwance jikin Tantie Yusura wacce ke basu cigaban labarin nahiyar matsafa,da ɗan mamaki Ammi tace "yanzu wai dagaske naman mutum su ke ci?"
Tantie Yusura tace "Allah kuwa ,dama yadda tsarin ya ke su baiwa doguwa jini su kuma su ci naman to ni inda Allah ya yi min iyaka da su saboda ina yawan yin Azkar haɗi da karatun Alqur'ani.Lokuta da dama sai an shirya ni cikin kayan yanka sai shugaban matsafan yace wannan nemanta bai ciyuwa har yanzu mu ƙara bata lokaci"
Daddy yace "wlh har yanzu ina jin tausayin ki cikin raina,yadda kika yi rayuwa cikin aljannu to wai ake ma ki na yin sallah?"murmurshi Tantie Yusura tayi kafin tace "a sace ni ke yi saboda ko a can akwai mutanen da su na zaune ne kawai dan doli,akwai matar da ke taimakona"
Ammi tace "to wane irin abinci kuke ci ?"ta bata amsa da "irin wanda ake ci nan,sai dai babu nama"Inna ta tashi tace "dan Allah ku bar maganar nan tunda dai Allah ya kuɓuto mana ke,su kuma uwanda suka gina ramen muguntar sai su yi ta zama ciki"cike da jimami Daddy yace "wlh kuwa Inna kamar kin sani jiya-jiya nan na gamu da Balkisu tsakiyar kasuwa ta na hauka tuburan aka kuma samu maras imani suka yi mata ciki"
"Ah to ita ma ai ba imanin ne da ita ba shikenan dara ta ci gida"Tantie Yusura ke faɗa.
A ɓangaren Mahomet kuwa tuni ya fara aikinsa na haƙon zinariya,wanda tsantsar ilimi ne kawai ke aiki.Duk ƙarshen wata ya na zuwa ganin gida ,in kuma ya na Agadez duk dare na Allah sai sun yi waya da Maryam wacce a kullum ta ke yi masa kukan kewar sa.
Yanzu wata huɗu kenan da Mahomet ya fara aiki amman tuni rayuwarsu ta ƙara canzawa sosai ya ke samun kuɗi wanda ya saka masu babban buri.
A kwana a tashi babu wuya wajen Allah tuni Dr Halima an yi haihuwar farko inda ta samu Twins duk maza,murna gun Abbasi ba'a magana duk da kuwa ba wannan ba ne haihuwar shi ta farko dan tuni ita ma Farida ta haihu inda su ke samun kulawar Hawali wacce ta bada gudunmuwa sosai na ganin ƙawarta ta ba ta tozarta ba haka ma babyn wacce aka saka ma Hawa'u an ɗauki duk wasu matakan tsaro dan kar ta kamu da cutar ƙanjamau.
Farida ce zaune a bakin matelas ta na daidaita ƙafafun robar da Hawali ta sa aka yi mata, gundululun ta saka ma wata safa sannan ta ɗora ƙafar robar.Ta na gamawa ta tashi da tashi tsaye kai kace ƙafafunta ne,bakin mirror ta ƙarasa ta kalli kanta a take wasu hawaye suka zubo mata.Duk da ta kasance a gidan président hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba wanda kuma tsananin damuwa da ƙunci ne ke damunta.
Aka turo ƙofa,Laila ce mai kula da little Hawali .Saurin goge hawayen tayi ta ƙirkiro murmurshin doli ta karɓi yarinyar wacce ke barci an shirya ta tsaf cikin wasu ƴan kanti,"Madame tace in kin shirya driver na jiran ki"cewar Laila,kai kawai Hawali ta gyaɗa kafin ta goye yarinyar ta yafa mayafi ta ɗauki jaka.
A falo ta tarar da Hawali ta haɗe cikin gizner wacce ta zame mata kusan kayan jikinta a kullum, murmurshi ɗauke da fuskarta tace "exellency sannu da hutawa"Hawali ta ɗago ta dubi Farida ita ma ta sakar mata murmurshi tace "yauwa Barka da fitowa,na canza shawara ya kamata Laila ta raka ki shiyasa nace ta je ta shirya sai ku tafi tare"
Shiru Farida tayi kafin tace "miyasa har yanzu ba ki yarda da ni ba?wlh Allah ba zan taɓa baiwa Hawa nono ba nayi maki alƙawari can ma duk saboda ina a ruɗe ne amman ai yanzu na samu nutsuwa"
Hawali ta girgiza kai tace "ba wai saboda wannan ba ne kawai a'a,kin ga Homo/takwara ba ta wani saba da ke sosai ba kawai kuje tare da Lailar tunda ba jimawa za ku yi ba"
Ko kafin Farida tace wani abu Laila ta fito cikin shirinta ta na jaye da ƙaramin akwatin kayanta,miƙewa Hawali tayi duk suka fito waje.
Daidai bakin mota ta raka su sai da ta shafa kan Hawa wacce tuni Laila ta karɓe ta kafin ta dawo ciki su kuma driver ya fice da su zuwa aéroport.
***MARADI VILLE
Kasancewar yau weekend ce yasa Abbasi bai tafi aiki ba,su na zaune shi da Atine yayinda Twins Hassan and Hussain ke zaune daga gefe suna wasa.
Dr Halima ta fito daga kitchen ta na sanye da riga da siket na less wanda suka yi bala'in karɓar ta,dining ta nufa ta jera abincin da ta gama ta na jin Atine wacce suke kira da Hajiya na jera mata sannu haɗi da sa mata albarka saboda tunda aka kawo Dr Halima suke zaman lafiya.
Sallama suka ji a bakin ƙofa,Dr Halima da ke kusa ta karɓa haɗi da basu izinin shigowa.
Cak Farida ta tsaya ta na ƙare masu kallo kafin tayi ƙarfin halin cira ƙafarta ta ida shigowa ciki.
Abbasi ƙurrr ya kafeta da ido ya na kallo ya na jin tsohuwar soyayyarta na motsa mashi,Atine kuwa kawar da kai tayi gefe duk da ita ma ta nada mugun hali amman yanzu ai ta tuba.
Ganin sun yi tsaye Dr Halima ta shanye mamakin zuwan na su tace "ku zauna mana bari na kawo maku abun sha"sai bayan sun zauna ne Farida tace "ina wuni Hajiya?"Atine ta waigo ta amsa fuska a ɗan sake,nan kuma suka gaishe da Abbasi kafin Laila ta miƙa masa Hawa wacce ta buɗe ido tarau kan mahaifinta.
Kumatun ta ya shafa ya na jin wani tausayin ta,yanzu yarinyar ta na cikin wata kusan na goma amman sai yau kawai ya ganta.
Dr Halima ta kawo masu jus mai sanyi suka yi godiya suka karɓa,gefe ta zauna ita ma ta na jin wani tausayin Farida wacce ta aje duk wani jiji da kai da izza.
Dr Halima tace"yaushe garin?"Farida ta mayar da ɗacin da ta ke ji haɗi da kishi tace "yanzu mu ka sauka ai,driver da ya kawo mu daga aéroport ya na waje"ta faɗi hakan ne dan tabbatar ma da Dr Halima a jirgi ta zo har yanzu da sauran gatan ta.
Abbasi yace "ayya shine kuka baro sa waje?"Farida tace "eh da ya ke yanzu za mu wuce"Atine tace "kamar dai ana korar ku?ai ku bari ku ci abinci ko?" Duk yadda Farida ta so zillewa su bar gidan dan takaici amman sai da Atine ta tsayar da su suka ci abinci hatta driver ma sai da ya shigo ya ci.
Ba su yi wata hira ba sosai suka wuce gidan gwamna dama a can ne za su sauka,sosai suka samu tarba mai kyau daga wajen matar shi da masu yi mata hidima.
Kukan da ba ta samu ba ta yi ba ne ya kubce mata yayinda ruwan pampo suka fara dukan jikinta,sosai ta ke jin raɗaɗin ganin Dr Halima da mijinta wanda yanzu duk duniya babu wanda ta ke so sama da shi sai dai kash wutsiyar raƙumi ce yayi mata nisa.
Tuni Laila ta yiwa Hawa wanka ta kaɗa mata madara ta sha a nan barci ya ɗaukesu su biyun.Farida na fitowa ta shirya cikin kayan shan iska ta kwanta luf kan shimfiɗa ta na tunani da wannan barci ya ɗauke ta mai cike da mafarkan ƙarya,ko da ta farka sai taji haushin tashin da tayi saboda ta san in ba a mafarki ba babu yadda za'a yi ta ƙara zama ƙarƙashin innuwar aure kuma da Abbasi.
Washegari
Haka Farida ta ja Laila suka wuce gidan Daddy sosai suka yi mamakin canzawarta,neman gafarar su tayi suka kuwa ce sun yafe mata.Maryam wacce aka yi katari ta zo ganin gida sosai suka yi hira da Farida wacce rabinta duk ƙarfafa ma Faridar gwiwar ne ta na nuna mata girman ƙaddara wacce mutum bai iya kauce mata.Sosai Farida taji daɗin zuwan nata can,sai kuma yanzu ne ta gane tabbas tayi babbar asara da ba ta ƙulla hulɗa da Maryam ba tun farkon shigowata familyn.
Lokacin da ta tafi gidan Abbasi ma neman gafarar tayi kafin ta sa a sauko da akwatin kayan Hawa,ta na kuka ta na ƙari ta baro ma Abbasi Ƴar sa wacce tuni Atine ta ɗauki nauyin kula da ita.
Lokacin da Farida suka shiga jirgi dan komawa Niamey sosai taji kewar ƴar ta sai dai babu yadda za ta yi,ko da suka isa Niamey tuni an zo ɗaukar su.
Kamar yadda suka tsara har da Hawali aka zo tarbanta,daga hilin jirgi direct gidan su Farida suka yi tsinke.
Escort sai take ma Hawali baya suke har cikin gidan,a zaune suka samu Mama a falo ta na ganinsu ta je ta kirawo Papa.Ba su wani sha wahala ba iyayenta suka karɓi tubanta tare da yi mata nasiha mai ratsa jiki inda Papa ke cewa "duniya makaranta ce yanzu dai ko rayuwar ki da ta Hawali sun ishe ki ISHARA,a kullum burinki ki zamo sama da ita ya zamana kin fi ta sai dai Allah ne ke yi ba mutum ba.A ta dalilin son zuciyar ki kin rasa miji,ƙafafu uwa uba lafiya to ina son wannan ya zame maki darasi daga yau ki koma ga Allah"banda shashekar kukanta ba ka jin komi,nan dai Hawali tayi masu sallama ta tafi.
Washegari
Sai ga motoci kayan abinci aka sauke haɗi akwatunan kayan Farida,sosai su Papa suka ji daɗin haka inda suka kira Hawalin suka yi mata godiya.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Farida kullum ta na cikin kaɗaici duk da kuwa kusan kullum ta na tare da Ɗiyarta ta waya su na appel video da Dr Halima wacce ita sam ba ta riƙe Farida a rai ba tsakani da Allah ta ke kula da Hawa.
Wanka Farida tayi tsaf ta shirya,a falo ta tarar da Mama bayan ta gaisheta ta fice zuwa asibiti karɓar magani wanda ta ke zuwa ɗauka duk ƙarshen wata.
Yau ma ta tarar da layi,ta na nan zaune kamar an ce ta juya idon ta ya sauka kan délégué wanda ya ke cikin layin maza na masu karɓar maganin ƙanjamau.
Da mugun mamaki cikin ɗaga murya tace "délégué... ?"da sauri ya waigo dan muryar ta raɗau ta sauka cikin kunnen shi,fitowa yayi daga layin ya nufo ta mamaki ɗauke da fuskar shi yace "wai Dr Farida ce?"kai kawai ta gyaɗa masa ta na jin wata irin kunya ganinta da yayi cikin layin ƴan HIV .
Wayar shi ya fiddo dalleliya yace "saka min lambar ki"babu muso ta saka masa,ba tare da sun ƙara cewa komi ba ya koma layin shi.
Ya rigaita amsa hakan yasa ya zauna zaman jiranta, ta na fitowa yayi mata alama da hannu cike da kunya ta ƙarasa inda ya ke jingine da motar shi.
Ciki suka shiga yayi driving na su,inda a hanya ya ke bata labarin irin gurɓataciyar rayuwar da yayi a baya kawai dan Allah ya nufe sa da kuɗi yayi ta yawo da matan banza ya na ɓata ƴaƴan mutane har Allah ya jarabce sa da SIDA.
Har gida ya kawota,Farida za ta bashi labarin kanta ya ɗaga mata hannu yace "duk na san komi saboda can ma'aikata yadda kika san kaladan haka ko ina ake hirar ki har cire ƙafafun ki da aka yi,yanzu abinda ni ke so da ke in kin shiga gida ki zauna kiyi tunani da kyau in kin amince cikin satin nan azo ayi maganar komi a ɗaura mana aure"da "toh in shaa Allah"ta amsa kafin ta shiga gida.
Labarin délégué ta baiwa Mama cike da murna Mama tace "to ai babu wata matsala gwara ku yi auren zai fi tunda dukan ku séropositif ne"murmurshi kawai Farida tayi dan ta tsani ace ita séropositif ce.
Da dadare Mama ta shaida ma Papa,shi ma sosai ya nuna farin cikin sa hakan yasa Farida ta shaida ma Délégué yadda suka yi da iyayenta .
Cikin sati guda kacal aka zo aka yi magana aka ɗaura aure,auren da kusan Hawali ta fi kowa jin daɗin sa dan ita ta ɗauki nauyin kayan ɗaki.
Watan auren su Farida ta samu ciki,tuni aka fara ɗaukar masa matakan tsaro na kariya.Sosai suke nuna soyayya ga junan su tamkar uwanda ba su da cuta mai karya gangar jiki,a yadda suke gudanar da rayuwar su in ka gani sai sun baka sha'awa.
Lokaci zuwa lokaci Farida ta kan je palais in Hawali na gida,wani sa'in ma har gida driver ke zowa ya ɗauke ta.
Auren Farida a bakin Adamu Abbasi ya same shi ,shi ma Adamun yayi aure har da yaran sa biyu.
Hawa na cika shekara biyu babu wasu ƴan watanni Farida ta haifo ɗanta namiji wanda ya ci sunan Abbas.
Su Dr Halima da Maryam sai da suka tafi biki haka ma Abbasi ba'a barsa a baya ba,ya je yayi ɓarin kuɗi dan sosai ya yiwa takwaransa sayaya.
Da za su tawowa ne suka baro ma Farida Hawa,sosai kuma ta ji daɗin haka saboda ganin Ƴaƴan ta su ke mantar da ita duk wata damuwa.
A ɓangaren Hawali kuwa sosai hankalin ta ya kwanta musamman yanzu da Kalil ya dawo hannunta saboda matar da Deeni ya aura kullum cikin gallaza masa ta ke shine a ƙarshe ya kawo mata shi.Sosai rayuwar Hawali tayi haske ta na samun kulawar mijin ta Jamal wanda ya haska duniyar ta ya maisheta mutum,ya gina ma iyayenta gida mai doron zabo a Tillabery ya bata jarin kasuwanci kuma.
****MARADI
Bayan wasu shekaru
Tuni Tantie Yusura ta sake aure,Inna kuwa ta koma Mai Jan Gero inda ta ɗauki riƙon Yusu wanda tuni ya shiga makaranta.
Maryam ce ta fito hannun ta riƙe da kaji wanda Rabe ya aiko mata jin wai ta zo garin duk da kuwa idonsa na son ganin ta amman ya ƙi zuwa.
Bayan Boot ta saka kajin ta na ɗaga ma Inna da hannu wacce Yusu da Abdallah suka sata tsakiya,Mahomet wanda ya riga ta fitowa dan tuni ya ke zaune cikin mota ya na jiranta.Vitre ɗin