Showing 42001 words to 45000 words out of 55059 words

Chapter 15 - MATAR MAHAUKACI END Book Complete Document Writing Mrs Sadauki .txt

Farida ta na cikin damuwa sai da ta tambaye shi lafiya amman yace mata ba komi,ganin zaryar ba za ta fishe shi ba ya shiga toilet ya yo alwala kafin ya fito ya fara yin Sallah.
Ya na gamawa ya zauna kan tafi ya na ta tasbihi da hailala daga nan barci ya kwashe sa,Farida na ganin haka ta ɗauki wayar shi ta kama ɗan yatsan shi ta cire empreinte take wayar ta buɗe.
Bincike ta shiga yi masa ta na duba duk wani sirrin sa amman ba ta ga komi ba,tsuki taja ta ajiye wayar ta na harar sa.Hasken ɗakin ta rage bayan ta haye gado,da ta rumtse ido Hawali ta ke gani cikin gizner wacce ta sha wani tsadadden ɗinki.Ta ja tsuki ta tashi zaune,sam a rayuwarta ta tsani wani ya fi ta ko gidan biki ta tafi ta fi son ace ta fi kowa haɗuwa.








****


"Lafiyar ki wai tun ɗazu kike a nan zaune?"Mahomet ya tambaya ya na kallonta,yanayin fuskarta ya ƙara canzawa zuwa kalar tausayi tace "in na kwanta ban jin daɗi duk sai na ji cikin nan ya takura ni"
"Ok taso na rungume ki,sai ki jingina da jikina"cewar Mahomet ya na mai zama bakin bed ya miƙe ƙafafunsa.
Tashi tayi daga inda ta ke ta zo ta shiga tsakanin ƙafafun sa ta jingina da ƙirjinsa,kamar wata baby haka ya ke dadaɓa bayanta yayinda hannu ɗayan ke bisa kan cikinta ya shafawa bakinsa kuma ɗauke da addu'oi a haka barci ya ɗauke Maryam shi kuma Mahomet yayi gadin ta.




Washegari
Bayan sun yi breakfast Mahomet ya sauketa *ALFARMA CLINIC* wato asibitin Abbasi wacce yanzu ƙaurin sunanta yasa mutane da dama kan zuwa daga sauran gararuwa.
Ta na tafe ta na Azkar wanda ya zame mata abokin hira kullum cikin yin sa ta ke,direct office ɗin Dr Halima ta nufa.A zaune ta tarar da ita ta na aiki a computer,ta na ganin Maryam ta rufe ta na murmurshin da ya zame mata sabo.
Cikin kujerun da ke ajiye a office ɗin Maryam ta ja ɗaya ta zauna ta na mai gaishe da Dr Halima "ina boy ya na lafiya ko?"
"Lafiyar shi lau ya na can ya na barci bai farka ba lokacin da na baro gida,ya naki yaran?"ita ma Maryam ta tambaya ta na murmurshi,yanayin fuskar Halima ya canza tace "a'a ai ban da aure ma,am ke ina ne office ɗin ki?"tayi tambayar cikin son kawar da zancen auren ,fahimtar haka yasa Maryam ma ta bar batun.
"A'a banda office ai,sai dai an keɓe mana ɓangaren mu ni da sauran abokanan aikina da sannu duk za ki saba da su"Halima na shirin magana aka banko ƙofa.
Ƙamshin turarenta ya fara yi masu iso kafin ta shigo fuskar nan a murtuƙe an sha uwar kwalliya,ba tayi sallama ba haka kuma ba ta gaishe su kwata-kwata ma ba ta kalli inda suke ba.Har ta kama handle ɗin ƙofa Dr Halima ta ɗaga murya tace "keee!"cak Farida ta tsaya kafin ta juyo a tsiyace ta zuba idonta bisa farar fuskar Halima mai ɗauke da dogon hanci irin na fulanin asali.
Dr Halima ta miƙe tace "ki jira nayi maki iso ba haka ake shiga ba babu neman izini"ƙugu Farida ta riƙe kafin ta yi mata kallon ƙasa da bisa tace "ke a suwa?wace ce ke da har za ki min katsalanda da shiga bureau mijina?"
Murmushi Halima tayi tace "sorry Madam DG dokar aikin ce ke haka,bai sanar da ni za ki zo ba shiyasa kuma nan ba'a gida ba ne ma'aikata ce"
Ganin dai kamar Halima daidai ta ke da ita yasa ta tura kofa da ƙarfi ta shiga ita ma ta take mata baya ta na dakatar da ita.
"Wace irin ƴar iskar sakatariya ce wannan da har za ta samu zarrar dakatar da ni ?"Farida ta tambayi Abbasi wanda ya tsaya ya na kallonsu ita da Halima.
"Dokar aiki ce kuma sannan ta yaya za ta gane ke matata ce tunda ba'a rubuta a goshin ki ba,Halima koma bakin aikin ki"cewar Abbasi,"ok"kawai tace kafin ta fita.
"Saboda sakatariya kake gaya min magana?"Farida ta faɗa a hasale,tasowa Abbasi yayi ya rungumeta cike da kissa irin ta su ta maza yace "haba Hubbyna miye haka saboda ƴar aiki za ki ɓata min ran ki a banza, please ban so.Yauwa faɗa min wannan kwalliyar nawa aka sayar min ita"ya ƙare maganar ya na mai kai laɓansa bisa na ta.






Sai da Dr Halima ta fito ne Maryam ke shaida mata yadda suke da Farida,ai kuwa Halima ta jinjina irin rashin mutumcin Farida da kuma rashin wayo.
Su na nan zaune Rahila ta shigo,kamar yadda tsarin ya ke dama kowa sai ya zo ya gaishe da Abbasi.
Nan ita ma ta zauna aka shiga hirar duniya kafin wani lokaci office ɗin Halima ya cika da jama'a a sannu kuma wasu suka watse jin Oga na tare da Madam ne .
[07/03 à 10:21] Mrs SADAUKI 💫: *47-48*










Kafin wani lokaci Dr Halima ta saba da sauran abokanan aikinta sai dai jinin su ya fi haɗuwa da Maryam dan ku san kullum sai sun yi waya bayan sun tashi daga aiki.Ɓangare guda ta fara kula ɓoyayyen masoyi wanda cikin lokaci guda yayi nasarar sace zuciyarta ,sosai Halima ke jin son sa.








Yau a tare suka shigo office ɗin da Maryam wacce yanzu cikinta ya tsufa sosai,cikin yanayi na tsokana Maryam tace "oh!na matsu na ga wannan Guy wanda ya sace zuciyar ki har haka,amman fah ina gudun ki hanasa komawa in ya zo"Dr Halima tayi dariya tace "Allah ki kiyaye ni,ba fah matsuwa nayi ba juste ina son ganin sa ne ido da ido yace min zai yi shigar Black ta yadda zan shaida sa amman ba zai fito yace min shi ne ba"
Maryam tace "kuma a nan CLINIC zai zo?"Halima ta bata amsa da "eh haka yace "Maryam ta ja kunera ta zauna tace "to Allah kawo sa lafiya"ta amsa da "amen "ta na mai buɗe system amman sam ta kasa yin aikin saboda ganin lokacin zuwan na sa ya gabato kamar yadda yace kafin ƙarfe takwas na safe ya buga zai zo sai ya kirata ta fito.




Su na nan zaune bini-bini sai ta duba agogon hannunta shiru har saura minti biyar kawai ya rage,Maryam ta miƙe tace "bari na tafi har zuwa heure ɗin pause sai na dawo" "ok to babu damuwa in ya zo zan kira ki ta waya"a haka dai Maryam ta fito cikin sauri ,sai kuma ta tsaya cak ganin Abbasi tsaye ya na waya yayi shigar baƙaƙen kaya tunda daga takalminsa har izuwa agogo.






Zuciyarta ce ta fara bugawa amman sai ta kawar da tunanin ta nufi ɓangaren su,gaisawa tayi da su Rahila wacce ta cika tayi fam a tunaninta Maryam ɗin ba za ta zo ba yau dan kar ta barta da aiki.
Kan hijab ta ɗora farar rigar su ta likitoci,Rahila ta taɓe baki tace "Ni kam Maryam ki na bani mamaki ke a ko ina sai kin gwadi ke Malama ce, lokacin hutu ki saurari karatu ko wa'azi wanin sa'in dan kiciyi ƙur'ani kike buɗawa a likita ki na karatu yanzu kuma hijabin ma ba za ki iya cirewa ba ki saka rigar ?"




Tunda ta fara magana Maryam ta kafeta da ido har sai da ta gama sannan ta bata amsa da "eh saboda karatun Alkur'ani cikin jinina da zuciyata ya ke,tun ina ƴar jaririyata da shi ake min tawai in ina kuka kuma a kunna min.Maganar kuma ban cire hijabi wannan ra'ayina ne saboda Musulunci yace a saka"




Duk da maganar tayi mata zafi amman sai da ta maida martani wajen cewa "Allahu Akbar to yayi musulmai shi dai imani a zuci ya ke kuma na ga dukan mu nan mata ne babu abinda za ki gwada mana sannan in forme ce da ƙugu ko ni na fi ki"
Maryam ba ta tankata ba ta fara duba wasu takardu,su kuwa sauran matan biye ma Rahila su kayi suna ƙara girmama lamarin wanda duk habaici ne ake yi ma Maryam ita kuwa da ta lura kamar dama sun daɗe su na baƙin cikinta sai ta share su.




Su na tsaka da yin hirar Barira ta shigo fuska duk a haɗe,Maryam tace "ke lafiyar ki yau?"ta tambaya bayan sun gaisa , "lafiya lau na fito daga gida waccan baƙar macen mai shegiyar izza ta zo ta ɓatan rai"
Maryam tace "wa fah?"
"Matar DG mana ni miye sunan ta ma?"da ya ke gulma ce da sauri Rahila tace "Farida ,hum ai wannan matar ta iya masifa ga shegen kishi sai kace ita ɗaya ke da miji"
Barira tace "wlh kuwa yanzu ma fah masifar ce ta ke wai ta kama sakatari na kallon shi har da ririƙeta yayi za ta kai ma Halima duka"jin an ambaci Halima ya sa Maryam cewa "da fatan dai sun kashe hutar?"
"Allah sa sun buga"cewar Rahila
Barira tace "a'a ba su buga ba saboda yadda Halima ta zabure ta nuna ita ma masifafiya ce yasa Farida ta sha jinin jikinta"ajiyar zuciya Maryam ta sauke kafin ta cigaba da aikin ta.






Rahila tace "ai naji haushi sosai wlh so nayi su ci bura ubar juna dan na san Halima sosai ta na da sanyi amman in ranta ya ɓace akwai bala'i"ai kuwa suka shiga yin zancen kowa sai zagin Farida ya ke ya na faɗin rashin mutumcin da tayi mashi.






Ganin hirar na ta hauhawa har ta koma kamar gulma ya sa Maryam ɗan tsayawa daga aikin da ta ke na ƙirgen magani tace "dan Allah ku bar maganai,nan fah zunubi ne kawai kuke rage mata sannan ba ta san ku na yi ba"ai kuwa suka yo mata caaa amman banda Barira wacce tace "kuma fah gaskiyar ki Maryam bari na tafi na duba patients"








HALIMA POV




Ta na nan zaune duk ta damu sai taji an taɓa ƙofa da sauri ta ɗaga idonta ta zuba su kan ƙafafunsa uwanda su ke sanye cikin baƙaƙen takalmi,a sannu ta fara ɗaga idonta zuwa baƙin wandonsa har ta kai ga baƙar rigar sa murmurshi tayi ta lumshe ido lokacin da zuciyarta ta raya mata shine ɓoyayyen masoyinta.
Lumsashun idon ta buɗe ta zuba su kan fuskar sa wacce ta ke ɗauke da annuri,da sauri Dr Halima ta waro ido ganin fuskar Abbasi ya na sakar mata murmurshi,ta miƙe kenan za ta takowa inda ya ke tsaye tun ɗazu Farida ta shigo ita kuwa kan fuskar Halima wacce ta ke fyau babu kwalliya face baƙin kwalli da man leɓe a nan idon Farida suka sauka da sauri ta maido dubanta ga Abbasi wanda ta lura shi Halima ke kallo.








"Uban miye kike kallo a fuskar mijina?shegiya munafuka fara mayya"cewar Farida cikin masifa da sauri Abbasi ya riƙo hannunta,cikin masifa ta ke aiko mata zagi da ta lura da Barira wacce ke tsaye bakin ƙofa ta ƙara da "duk mayyatar mace kama da jawaru ko ƴan mata sai sun bar min mijina,munafukai ai dama na daɗe da ganewa gaishe sa da kuke zowa ba na Allah da Annabi ba ne"




"Keee!ki iya bakin ki wlh in kin ɗauka ke wata tsiya ce to ni takalme na ma ya fi ki daraja banza sakarai kawai,ke har mace ce?kije gidajen daraja ki duba mata uwanda suka san darajar kan su da ta mijin su"cewar Halima jikinta har rawa ya ke wanda ya baiwa saharin jikinta damar zamewa dogon gashin kanta ya bayyana,wanda ganin sa ba ƙaramin ruɗu Farida ta shiga ba.






Cikin Halima ta sake ƙoƙarin yi Abbasi ya daka mata tsawa wacce tunda ta ke da shi ba ta taɓa sanin Abbasi mafaɗaci ba ne sai yau.
"Kan ki guda ?miye ke damun ki ?ke har kin isa ki zo ki zubar min da ƙima gaban ma'aikatana?yanzu da kike zanen ƴan mata da zawaru kawai dan kin ji mijin Barira ya mutu ne sai aka ce maki sona ta ke ko mi?"juyawa Farida tayi bakin ƙofa sai ta ga ashe tuni Barira ta bar gun.




Wani abu ta haɗiye mai ɗaci tace "Abbas ni kake gaya ma magana?"Abbasi ya hayayaƙo mata yace "eh ɗin an gaya maki ke wace ce?"tsabar baƙin ciki Farida ta zube a sume.
Cike da tashin hankali ya ciciɓeta ya shiga da ita wani ɗaki wanda an yi shi ne domin duba lafiyar shi ne kawai halin en cas.
Kan bed ɗin ya shimfiɗeta,Dr Halima wacce ke bayan sa ya baiwa umarni "Hubby kirawo min Maryam"fita Halima tayi ta na juya kalmar Hubby a zuci ta ke tambaya "ko dai dagaske shine ɓoyayyen masoyi?"ta na shiga Infirmerie duk suka juyo su na kallonta ita kuwa ba ta kula su ba dan ta lura tuni Barira ta shaida masu shine gulma ke ciciyar su.








Hannun Maryam kawai ta jawo ita kuma ta fara tambayar ta lafiya,sai da suka fito waje ne sannan Dr Halima ta gaya mata abinda ke faruwa.
Ɗakin da Farida ke ciki suka shiga,dubata suka yi ta dawo daga sumen da tayi Maryam ta ɗibi jininta ta fita zuwa labo tsawon lokaci kafin ta dawo ta na murmurshi ta miƙa ma Abbasi takardar sakamakon tace "congratulations na kusa zama Tantie Farida na da ciki na wata biyu"kamar almara haka Abbasi ya ji furucin karɓar takarda yayi ya na dubawa kafin ya gwale idon Farida wacce ke barci ta na sauke ajiyar zuciya da huci.
Dubawa yayi ya ga tension ɗin ta ya hau,kanta ya shafa yace"kin cika rigima ne babyna"da sauri kuma ya juyo sai ya ga ashe su Halima sun fita,ya sauke ajiyar zuciya.








"Hum!kin ga kamar almara ashe DG ne ɓoyayyen masoyi"cewar Halima,Maryam tayi murmurshi tace "ina taya ki murna domin duk wacce ta samu Abbasi matsayin miji ta huta dan dai kawai Allah ya jarabe sa da matar ƙwarai ne amman Abbasi bai da wata matsala"Halima tayi dariya haɗi da kai ma Maryam dukan wasa tace "wai matar ƙwarai,to miye na sakayawa kawai kice ƴar iskar mata ni kuma ko kallo ba ta ishe ni ba sannan yanzu ma na ƙara jin son sa dan tunda ni ke kishiya ba ta taɓa ɗagan hankali ba"Maryam ta ja baki tace "sai kuma fah ni sgiyasa da nace ki auri Abban Yusu kika ƙi amincewa"Halima ta harareta tace "ke yanzu in nace maki zan auri Abban Yusu sai ki yarda?"Maryam ta ɗaga kafaɗu tace "mi zai hana kuwa?kin ga kuwa da daidai kenan tunda yanzu na tsufa sai na bar maki miji ku sha amarcin ku har sai na haihu nayi arba'in"
Halima ta girgiza kai tace "eh na ga alamu ki na buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa"a sanyaye Maryam tace "dan ina *MATAR MAHAUKACI* ko?"da sauri Halima tace "Innalillahi wlh ba da nufi nace ba,dan Allah kiyi haƙuri wlh tallahi ban faɗi haka da wata manufa ba"
Maryam tace "laaa!bai fah komi nima kawai zuwan zance ne ai yanzu ya warke,kin san kuwa kishiyar ki ce ta fara kirana da *MATAR MAHAUKACI* ?"
"Dagaske wai?"Halima ta tambaya
Maryam tace "wlh kuwa lokacin an kawota ta na amarya sai ciwonsa ya motsa shine fah ta jefe ni da kalmar"cikin sanyi Halima tace "ayya dama su mutane haka suke babu lafazi mai daɗi,ni fah har yanzu ban ida yarda da Abban Yusu yayi rashin lafiya ba"
Maryam tace "ki shirya ki zo gidana sai na kunna maki videos bikin "
Halima tace "wai yaushe ne za ku koma sabon gidan?"Maryam ta bata amsa da "wai sai na haihu,kin sa kuwa babu abinda ba a saka ba kawai komawa ce za mu yi Abban Yusu yace ina haihuwa daga likita za'a yi tsinke da ni can"
Halima tace "Allah sauke ki lafiya,wlh in dai kika haifi mace sunana za'a saka mata"Maryam tayi dariya tace "ai kuwa ko dan ta samo jarumta da ƙawa zucin ki zan yi haka"nan dai suka cigaba da hira kafin Maryam ta koma ɓangaren su.










Sai da aka ɗauki lokaci sannan Farida ta farka, Abbasi ta ga zaune gefenta da sauri ta haɗe rai shi kuwa cikin murya rarrashi yace "please ki bar fushin nan kar ya taɓa lafiyar babyn mu"yayi maganar ya na kai hannu bisa mararta.


Kallon ban gane ba ta yi masa yasa shi gwada mata result,tsabar murna yasa taji duk wata damuwarta ta kau.
Taimaka mata yayi ta sauko daga gadon ya ja ta suka fita,ko inda Halima ta ke ba ta kalla ba sai wani shishige ma Abbasi da ta ke yi.
"Zan tafi na kai Madam gida duk wanda ya zo nema na in urgence ne ya tardo ni gida,uwanda ni ke da haɗuwa da su kuma a yau na soke zan tafi gida"cewar Abbasi ya na kallon Dr Halima ido cikin ido "to in shaa Allah DG prompte rétablissement à Madam"da sauri Farida ta buɗe ido jin wai Halima na cewa Allah ya bata lafiya harara ta watsa mata tace "ina ruwan ki da cikina?"
Abbasi yayi gaba da ita yace "yaushe kika ji ta ambaci cikin jikin ki sabida Allah?" Farida ta turo baki.
Key ɗin motar ta ya karɓa suka shiga yayi driving na su zuwa gida,a shagwaɓe tace "Allah bb na tsani waccan baƙar sakatariyar kawai ka sallame ta"Abbasi ya girgiza kai yace "da tayi maki mi?" "Hum!ai dama na san haka za kace tunda yanzu ma har da wani tankata kayi ka na gaya mata inda za ka je"
"To bbna ai saboda ita ke kula da lamurran office ɗina ne sannan please ki kwantar da hankalin ki ni na ki ke ɗaya ban son ki na damun kan ki bari na kira Hajiya na sanar da ita"rufe ido tayi da tafukan hannu wai a doli ta ji kunya ne.








Wata irin buɗa Atine ta saki ta fara taka rawa ta na cewa "komi da lokaci amarya zo taso ki bi bayan mijin ki,wacce ba ta da gata in ta rasa yanzu za ka ji shewar maƙwabta to ku cewa ƴan gulma su zo suji abun murna ya same ni ɗan Ɗan guda-guda shi ma zai zamo Abba nan da ɗan lokaci"
Inna wacce ke zaune ta na shan kunun da Ammi ta dama mata tace "to sakara sai aka ce maki in Allah ya baka wata ni'ima waƙa ake yi da habaici?mtsw ai sai kiyi sujudar shukur ba wai wani banzar habaicin ki ba maras kai"
Cak Atine ta tsaya "to Inna abun murna ya same ni sai na fasa rawa?ina ce a gaban ki Alhaji ke nuna banbanci kullum cikin sayo ma Yusu kayan wasa ya ke alhalin ba wani adana su ake yi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login