Showing 27001 words to 30000 words out of 45438 words
yafuto, Mota yakoma yabude gidan Gaba ta onas kwana.
Ido suka Hada DA Radiya,
Ganin Radiya Zaune tana Danna waya yasa yatuno DA ita Domin Shap shikan yamanta yanada abokiyar tfy, sbd Tunanin macen DA zaayiwa aikin ma'aifa acire Mata sbd kansa daya kama maaifar,Daren jiya aka kawota Asibitin Shi sosai jikinta yayi tsanani dole ayimata Thiater Na gaggawa Dan ceto Ranta.
Duk DA matar talakane hasalima Basu DA kudin aikin nantake dr Obinna Yace ayishiri gobe zaayi Mata aiki sadaka fisabillahi.
Dr Obinna Yace"
Ohh God afili,Yana kallon Radiyar dake sanye DA Karin hijabi,Takardan yaajiye aKujeran Direba tsakiyar kusa DA ita, shikanshi ya Yaba DA shigarta Na kamala dominshi yatsani Duk wata mace musulma or Kristan masu Shigar banza, awani bangare kuwa sosai yayi mamakin ganinta DA hijab Dan yafi zaton itadin kiristan ne Duba DA Yanda yaga kowa agidan Hakan suke time DA yaje gaisheta tana Cikin ciwo.
Ganin Zai damu Kanshi Kan abunda bayida hurumi Kuma Zai Bata lokacin Shi yasa ya share mgnr zucinshi.
Saidai ganinta Cikin mutumci hakan yasa yadan saki fuskar Shi kadan,Yau Radiya taci albarkacin dress Na mutumci,Cikin tabe baki Kamar bazaiyi mgnba yace"Am sorry Gv me some minutes I have emargency Operation abeg.
Radiya batasan lokacin DA tayi murmushiba Cikin Jin dadi tace"No problem Dr do Ur work.
Itakan gAreta dr bayi laifi,Hakan daya Mata Ko kadan baibata rantaba illama Kara Mata soyyrshi sbd sosai Aji DA Izzar dr Ke burgeta.
Karan Murfin motar DA yarufe Mata shine yasata dariya afili Harda tsalle Akan Kujeran motar aranta tana fadin Yau itace dr yacewa sorry wow very fantastic.
Thiater room dr Obinna yashige tare da Nurse dazasu Shiga aiki, Shigar Shi Dakin keda wuya doctors din suka Fara Mika mishi gaisuwa Hannu kawai yadaga musu,Dr mu'azune yace she's ready dr yace"Am coming.
Wani karamin Daki dake Cikin Thiater room din yashige,Cikin Sauri yafara canza Kaya wayar Shi yaajiye tare dacire agogonshi harya juya zaifuta adakin yadawo DA Baya wayar yadauka yayi Dan Short rubutu send yayiwa Wanda yakeso Akon yaje Cikin Sauri yafuto Daga dakin Kan patient din yayi Dasauri Suma Sauran doctors din suka rufa mishi Baya inda suka Fara aiki Cikin kwarewa DA sanin madafan aiki.
'kwan'kwan Radiya Taji ana buga glass din motar,Hakan yasa tayi saurin lekawa Tacikin Glas din azatonta dr NE saidai sabanin Hakan tagani,wata macece matashiyar Budurwa sanye DA fararen Kaya Na aiki DA alaman nurse CE itama acikin asibitin,Radiya ta Saka Hannu ta zuge glass din,Cikin faraa Sannu yarinyar taiwa Radiya,Itama Radiyar sannun tace,Cikin harshen turanci tace "Dr yace kiboyoni.
Jin abunda yarinyar tace yasa Radiya tace "To motar tabude tafuto wayar ta kadai tasauka harta karamin Jakarta taajiye, nurse din tace" mujeko.
Office Na dr Obinna tabude Tace "DA Radiya Shiga kiga kizauna dr Obinna Yace abaki masauki kafin yafuto a Thiater batajira amsar Radiyaba tajuya waje,Radiya taja ajiyan zuciya Bayan tagama karewa office Na dr kallo Mai dauke DA Babban Falo DA bandaki Sai Wani room guda daya Mai dauke DA gAdon hutawa.
Falon kuwa tarkacen kayan aikine Na Duba marasa lfy,Sai Wani karamin gado Na Duba patients Tv ne babba Manne ajikin Bango Sai karamin Furji dake gefen Kujeran dr din.
Tsab tsab office din yake Sai Kanshi dake tashi Na turaren dr da alaman baajima DA Gyara office din ba masu aiki.
Bangon office din Manne yake DA manyan photon dr Shikadai Har guda 3 Sai family pictures nasu Wani Kala ba irin Wanda tagani afalon gidanshiba.
RADIYA Tamike Jikin photon taje ahankali tasanya Hannu tashafo fuskan dr Obinna,sosai takejin shauki aranta da tsananin 'kaunar Shi,harta saita Wayarta Camara Zata dauki photon fuskan dr Obinna meta tuno oho tafasa wayae ta kawar Jikin photon.
Tare da komawa wajen zamanta, saiyanxu cikinta Yafara Kuka alaman yunwa Yafara damunta,Haushine yakamata data tuno tana DA break fast amota Cikin jakar Hannunta saidai fidis tamanta Bata daukoba sbd rudewa Kan dr.
Dole ta maida yunwarta Tacigaba DA Zaman jiran dr, jikinta ta jingina ajikin Kujeran Zaman banxa datake Zaune a office din, ahankali tafarajin bacci Yafara daukanta Abunka DA Wanda Daman bacci Bai ishetaba Tuni ta bingire Tacigaba DA kwasan baccinta.
Dr Obinna Saida yayi awa uku cur kafin suka Gama aiki,Cikin Sauri yashige Dakin change dress baijimaba yafuto,Hannu suka Fara sha DA abokan aikinshi tare da murnawa juna Kan Saar aikn DA sukayi wato sunyi aiki Cikin nasara Domin Allah yayarda ansamu hanyar warakan matar.
Office nashi yawuce Bayan yabar komai Na matar ahannun abokan aikinshi, Saida yayi nokin Kamar ba office nashiba.
kafin yashiga Dan gudun Karya Ganta Cikin Wani Hali Dan yasan Mata bakowa keda hankalin kintsiba, Aiko Yana Shiga yahangota Kwance Kan kujera tana baccinta hankali Kwance,ta dukunkune DA hijab DA alaman sanyin AC Yana damunta, akanta yatsaya Yana Kare mata Kallo.
Ko kadan Babu hayaniya acikin baccinta Kamar ba maceba, Ahankali numfashinta Ke Shiga dafuta,fuskanta fayau Babu ado Sai Jan janbaki DA tasanya akaramin labbanta,gashin Idonta yabazu sbd tarufe Idonta Hakan yakara Mata kyau,dr yatabe baki aranshi Yana fa'din Balaifi tana DA.....shiru yayi sakamakon Bude Ido DA Radiyar tayi sbd Jin alaman kamar ana tsaye akanta.
Dr yahade Giran Sama Dana 'kasa Cikin Hararanta yace" Karki batamun lokaci kisameni amota,harya juya zaifuta yatsaya Daga nesa yace"While ki tabbatar kina DA kudin biyana ladan Mun bacci a office without my permission.
Baijira amsarta ba yafuta a office din,Itakan Radiya mgnr dariya yabata Hakan yasa Yana futa ta fashe DA dariya,Dasauri tabude Wani kofa Wanda take zaton bandakine Aiko Cikin saa tasamu hakane,fuskanta ta dauraye sbd baccin datayi agaban Mirrow Na toilet din ta tsaya tasake Gyara fuskan ta Duk dababu kayan makeup fuskar tayi kyau .
Jin hon Na motar dr Obinna Daga waje yasa DA gudu tafuto Daga bandaki,Cikin Sauri tayi wajen motar nashi Domin Har yayi Ribas Murfin Gaba tabude tashige, yayinda patients dake bin layi dr Hassan Yana Dubasu Wanda ya wakilci dr Obinna ayau suka bita DA kallo aransu Suna mamakin wacece ita Dan sunga Ko kadan basuyi kama DA dr ba bare suce Ko 'yar uwanshine.
Cikin Haki sbd gudun DA tayi tace"Am sorry dr,Dr ya kauda kai Yana tukinshi maigadi shine yabude masa get tare damishi adawo lfy,Saida suka Hau Kan titi kafin dr Yajuyo gAreta Azatonta mgn zaiyi Mata Amman saitaga sabanin Hakan Takardan daya ajiye dazu shine yadauka yabude hannun Shi daya Yana tuki Dayan Yana rike DA Takardan time to time Yana Kalla Yana gyada Kai DA alaman Wani abun yake dubawa.
Itakan Radiya Hannu tasa abayan motar ta dauko Jakarta I rish nata DA lemun Coca cola ta'dauko Cikin Jin yunwa tabude Atsakiyan su tasaka itada dr Tace "Dr Bismillah.
Dr ya girgiza Kai alaman ah ah,saidai itama Bataci DA yawaba sbd kunyar dr din datakeji Duk DA yinwar DA take tsananin Ji karshe lemun kawai ta iyashan Rabi ta mayar Cikin Jakarta taajiye.
Tfy sosai suka farayi Wanda bakajin komai Sai iskan mota,Daga ita harshi Babu Wanda tace DA kowa komai.
RAdiyAr nema Cikin karfin Hali tare da sonjin Muryan Dr din DA Bata gajiya dajinshi, tace"Nawa zanbiya kudin baccin? Gara kasanar Dani intanadi kudin biya sbd nasan dole lallausan Kujeran nan yayi da'din tsadan biya.
Sarkin surutu dr yafa'da aranshi Bayan yagama Jin mgnrta,saidai abun mamaki kanzil baice mataba sabanin hakanma wayar Shi dake Saman mota yadauka yafara dannawa Kida ya yasa Wayarshi tare dayin connection Cikin Bluetooth dake kunnan Shi Yafara saurara motar ya karawa gudu tare da sake tamke Belt Na Mota dake jikinshi,Ido ya maysr Kan Radiya Cikin kallon uku taro Sisi yace"Daura belt.
Ikon Allah Radiya tafa'da aranta Wai Yau itace tazamo Sarkin surutu Wanda Har ana kosawa DA ita,atarihin rayuwarta tasan itaba Mai shishshigi Ko yawan mgn bane Abu daya tasani itadin Sarkin fadane uwar Rigimah Amman Yau Sanadin makauniyar soyy Tazamo Aku kuturu.
Ido ta rufe ta budesu Akan dr dake sharara gudu Cikin Jin haushi tayi kwafa tace zanramane.
Plz my Frnds share ND comments.
08100044786.
*AUREN CHOCHI.*
*Book one.*
*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*
*Page 43&44*
Wow Aljannar Duniya Radiya tafa'da aranta,sakamakon Shigar DA Mota DA dr Obinna yayi Cikin Wani ha'de'd'an gida Mai tsananin kyau infact tunda tazo Garin lagos Har Yau izuwanta Cikin Ibadan Bata taba ganin gidan DA yamata kyau tundaga bakin get irin wannanba, Ranta tace Allah kadai yasan iyakar Tsaruwan Cikin gidan.
Motocine jere reras acikin gidan kamada motocin Daddy motocin Momcy danasu Rahap harma DA Na dr Obinna DA suke fake acikin tangamemen get din Cikin runfar maadana motocin,Wanda akallai motocin sunkai 14 Afake wasu arufe DA tanfol wasu abude.
Dr Obinna kusa DA wata katuwar Jep yatsaida motar nashi Cikin nutsuwa yayi parking, Murfin gaban Motar yabude baice komai DA Radiyaba ganin yafuto yasa itama Dasauri tabude mazaunin ta tafuto,Bayan motar tabude taciro madaidaicin jakar kayanta tarataya akafadarta tare da daukan jakar Hannunta.
Baba Mai gadine DA masu baiwa fulawa ruwa DA Sauran Maaikatan gidan dasuke Zaune Kan fararan kujera Suna Hira suka taso DA Sauri Dan kwasan gaisuwa awajen dr, Cikin ladabi suka ringa gaisheshi,yayinda dr Ke amsa musu Cikin faraa tare da Tambayar su aiki.
Da'alama.
Itama radiyA gaisuwa suka Fara Mika Mata tare da kokarin karban Jakarta RAdiya ta Amsa Cikin sakin fuska,saidai fur tahanasu Jakarta ganinta jakarBabu nauyinda harsai antaimaketa dashi.
Dr Obinna Kai tsaye Yafara takawa izuwa Cikin gidan nasu, DA fari Radiya Ido tabishi dashi Bata bishi ba Dan son ganin iyakar gudun ruwanshi saidai ganin Ko ajikinshi Bai sake in ta kantaba yasa DA Dan Sauri Itama Radiya tabi bayanshi, tana turo baki sbd Ganinta aiko Babu komai zaice Mata muje tunda ita bakuwace agidan, Amman dake shidin Dan rAinin wayone jishi yayiwani tfyrshi,Ido taware tana karewa kyakkyawan gidan kallo inda yaji kyau saikace gidan shugaban kasa,aranta tace shiyasa Suda 'yan uwanshi sukeda girman Kai Ashe sudin attajirai ne.
DA Dan gudu gudu Radiya harta cimmashi, Cikin haki sbd tayi gudu,gefen dr din tabi suka jera zuwa Cikin gidan,DA wutsiyar Ido take kallonshi kozai Mata mgn Amman Ina wayar shima yaciro Yafara amsa call,Jin yace alhmdullh Mun iso lfyne yasa tagane DA dr David yake mgn,Aiko kashe wayar dr din keda wuya saiga Kiran dr David yashigo wayar Radiya, daidai lokacin DA suke Shiga Cikin haraban DA zaikawo su Shiga Babban falon gidan.
Wayar ta Kara akunnanta Cikin ladabi tafara gayda dr David,Shima Cikin Faraa yace"Tnz God kun Isa lfy ai yanzu mutumina yace kun iso Anyway kishiga inkin huta zamu Kira anjima GA auntynki tana Miki sannu DA hanya,Radiya tayi dariya Tana fa'din"Ngd broda Dr Bari Inna hutan zankira ace Ina gayda Aunty big.....Ihun DA Rahap tayine Na murnan ganinsu yasa Radiya takashe wayar Bata shiryaba,Rahap ta chakumo Radiya Cikin farinciki tana Mata oyoyo sanye take DA Dan karamin mini skt Sai Yar best DA ya'dameta Duk Rabin nonuwanta awaje Kanta yasha gashin attachment.
Itakan Radiya sarin gashin Kan rAhap Tuni yadameta shiyasa Cikin dabara tazame ajikin Rahap din tana faraa tare da rungume Momcy dake Miko Mata hannu,shikan dr Obinna Wajen Daddynshi yayi Cikin faraa suka Yi musabaha Daga bisani suka rungume juna.
Tare suka wuce Cikin falon Na Momcy,Masha Allah gida yatsaru fiye DA zaton Mai karatu Duk DA gidan daddy akwai kayan Duniya DA arziki Ko kadan bazaka hadashi DA gidansu Dr Obinna ba Dan Babu Karya yakere Na Daddyn akomai.
Cikin farin ciki Momcy tariko Radiya zuwa Dinning table,abinci tafara Kokarin zuba Mata Radiya tace"Barshi Momcy kar inbaki wahala barin zuba DA kaina tafa'da Cikin ladabi,Aiko Hakan ya Burge Momcy Hakan yasa tace"God bless you my Dota okey.
Hakikanin gaskia,Radiya taga gata,wajen
.'yan gidan su dr Obinna, DA alaman sun Sanda zuwan Radiya sbd tarba sosai suka Mata Kama Daga Na abinci abunsha harma DA shinfidan fuska Wanda hausawa suke cewa tafi shinfidan Tabarma.
Shikanshi Daddy bazakace yaune farkon ganinshi DA Radiyarba Duba DA Yanda take amsa gaisuwar ta Cikin faraa,tare da Tambayar ta mutanan gida DA gAjiyan hanya,RAdiyatace"Lfy Lau since agaishe ku.
Haka Momcy Rahab Abraham Harma DA Shi kanshi Daddy din Sai nan DA nan sukeyi DA Radiyar Kamar wata Yar uwansu.
Sosai Radiyatasamu nutsuwa,sabanin inda take DA adarare ganin zatazo inda Bata sababa.
haka Farin Cikin DA tagani awajen Family Na dr saboda zuwan shi dr din sosai yabAta mamaki Duk DA tasan Dr din Dan gatane Duba DA Yanda 'dan dajinshi da family nashi tagani saidai Yau tsantsar kulawa DA inaka Saka inaka dauka DA akeyi DA dr din yakara tabbtr Mata dr Obinna Na musamman ne awajen iyayenshi harma DA 'yan uwanshi.
Abun mamaki dr Kamar bashine Mai cin 'daciba,sosai yasake acikin family nashi Suna Jin da'din ganin juna,Saima shagwaba DA Sakalci dayake tayiwa Momcy Kan cewan shibazaici Sakwaraba DA miyan ogun Wanda yasha Naman kaxa DA busheshshen kifi yace shifa saidai ahada mishi Chekas custard.
Aiko DA Sauri Momcy Tamike DA Kanta tashiga Kicin Dan aiwatar DA Abunda ran Dr Obinna keso.
Itakan Radiya Yar kallo tazama agidan,Duk saitaji dr din yakara burgeta Yayinda Tsananin begenshi gami DA 'kaunar life style nashi yakara burgeta.
Tfyr momcy bAta jimaba tadawo falon Hannunta rike DA Dan tea cup dake Kan karamin tire Na tangaram Sai karamin Glas DA aka Saka sugA aciki Wanda zaiyi amfani DA Shi son ranshi.
Cikin kulawa tace" my swtheart tashi Kasha kasan Bana son zamanka DA yunwa, Dr yamike Zaune Daga Kwance ajikin Daddynshi Cikin Shagwaba yace tnz my swthrt much love you.
ITAKAN Radiya Yar kallo tazamo afalon Duk DA tagama cin nata abincin tun dazu saidai framam dr Obinna DA iyayenshi yahanata tashi tashiga Daga ciki Kamar yadda tun dazu Rahap kebinta suje tarage kayan jikinta Tai wanka kodata huta Gajiyan hanya.
Wayar Radiyar CE tayi Kara,alaman ana Kira, ahankAli tadaga wayar dake Kan cinyarta saidai ganin sunan Halil Akan wayar yasa tadanja karamin tsaki Cikin dabara tacire ringtone Na wayar izuwa silent, Ko kadan Bata 'kaunar abunda Zai Tabata DA kallon fuskan dr Cikin wannan Hali Na shagwaba Wanda yake tsananin tfy DA imanin Duk wata mace Mai Rai DA lfy.
Radiya Kanta Takuma mayarwa Kan dr dake Shan kunun custard Cikin nutsuwa inda yake Dibanshi DA tea spun Kamar yaro karami,Momcy Sai lallashinshi takeyi Cikin kauna shikoyana Kan Zuba Tabata.
Daddy Kan dariya yakemusu sbd yasaba DA ganin wannan kauna,Cikin tsokana Daddy yace"Kai swthrt Wato yanzu Ahmed yakwace soyyta Ko? Yaushe Rabon kibani abinci abaki?
Momcy tarike baki tana murmushi,tace"Kai Daddyn Yara Rufamin asiri Har yau Har gaban abada bazan bar bakA kulawaba,bt amun Afuwan sbd Obinna bakone I know tsananinta 2 days Zai wuce.
Momcy tajuyo Kai,tace DA "Rahap Kai Radiya daki ta huta,ki kaita Dakin kusa danaki hop angyara Babu datti?Rahap tace"Yes Mommy aitun DA safe dabroda yakira waya yasanar Tuni Blessing ta Gyara,Momcy tace"Yawwa to kuje.
DA alaman agajiye take, taje ta Dan watsa ruwa Inta huta saita sauko tayi Hira anjima,dafatan Radiya kin koshi DA abinci?Radiya datake mikewa tace "Yes Mommy ngd sosai Allah yakara zumanci Momcy tace Amin kuje.
Radiya ta Kalli Daddy Cikin ladabi tace" Daddy barinje Sai anjima,Daddy yace "Tnz Radiya jeki ki huta Nima barin tashi naji anfara Kiran sallar laasar son Sauri kagama muje,Radiya batasan lokacin DA murmushi ya kufce Akan fuskantaba Jin Daddy yace zaije Sallah Hakan ya tabbatar Mata shidin musulmi ne.
Wani sanyine Dadine Yafara sauka ajikinta,yayinda Taji Kamar ansata Cikin ni'imar aljanna Itakan harga Allah Ranta Yana 'kaunar dukkan Wani musulmi sannan Ranta Yana tausayin taga mutum Har mutum Amman Babu addinin Allah.
Rahap ne takarbi jakar kayanta itako radiyA tariko jakar Hannunta,harta juya tafara bin Rahap din tatsaya sakamakon tuno DA Laidan sakon aunty Saada datayi,Hakan yasa Tace"Ayya dr nayi mantuwa amotarka PLC Ko xakabani key indauko tafa'da Cikin langwabe Mai.
Dr yatabe baki Yana Shan kamun shi,Kamar baxaiyi mgn ba Har tacire Rai Zata bi Rahap,Muryan Shi ta tsinta Yana cewa zanshigo Miki dashi anjima Hakan yasa Momcy dake kusadShi. Tasauke ajiyan zuciya sbd kunya DA Yafara kamata Na Shirin DA dr din yayi.
Radiya tace"Tnz somuch,Bayan Rahap tabi Cikin takunta Mai tattare DA nutsuwa.
Bayan sallar isha'i dukansu suka hadu afalo Kan dining table dancin abincin dare,blssn Mai aiki tare day Jon sune sugama Hada dinning table din,Tuwone ruwan shinkafa miyan Kalkashi Wanda yaji Naman Rago DA Ganda, Sai soyyan agada DA Farar taliyan laida DA yaji miyan jajjage.
Dr Obinna Kujeran Shi kusa Dana Daddynshi Hira sukeyi Cikin aminci DA 'kaunar juna,Sai Mommy dake gefensu Sai Abraham Dana Rahap sAi radiyA akusa DA Rahap din sukansu kowa takiyar DA miyan jajjage yasa,dr kadai DA Daddynshi Momcy Tazuba musu tuwo kowa DA fulet nashi.
Cikin nutsuwa dr yasanya fararan hannunshi sol Cikin roban wanke Hannu Bayan yawanke fulet din tuwan yajawo yayi Bismillah afili kafin Yafara yankan tuwan Yana kaiwa bakinshi Ko Rabi baiciba yamatsa DA fulet din gefe,hannunshi ya wanke Daddy yace"Ahmed badai ka koshiva? Dr yace"Alhmdullh daddy Mommy tace"Ahmed mekaci DA kakoshi sbd dakaifa akayi tuwan nan Dan nasan kanaso.
Dr Obinna yaturo karamin bakinshi,Yana cewa"Mommy kinmanta dazu nasha custard yafa'da Yana shafa cikinshi alaman yakoshi,Mommy tace"Shkn swthrt I know Koda Na takura baci zakayiba plx Dan Allah kadinga cin abinci sbd Kai likitane kafini sanin muhinmanci abinci ajikin Dan Adam,Daddy yace"Gaskiane fa'da mishi Dan Naga wannan Yaron nakiBayi kiyaye dokokin nasu DA suke fadakar DA mutane koyaushe,Dr yayi murmushi Bai Kuma cewa komaiba yamike DA Goran ruwa ahannu Cikin sassarfa Yafara hayewa Kan benen DA Zai sadashi DA dakinsa gabaki dayansu suka bishi DA ido Cikin soyy,Itakan Radiya Jitayi taliyan yafuta aranta sbd rashin dr awajen Cikin yatsina fuska Kamar maicin mgni Tacigaba dacin abincin batawani chi dayawaba Tamike Akan Kujeran dinning table din Takoma Kujeran Falo inda Rahap take tafara kallon Tv.
Plz my friends share ND comments.
Taku Har akullum matar Faisal Zakhari.
08100044786.
*AUREN CHOCHI.*
*Book one.*
*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*
*Littafina Na kudine sbd masoyana masu kaunar book dina Na mayar DA complete 1 kyauta bt 2 kadai Zaku biya kudinshi Cikin farashi Mai sauki only 300NaiRa, gamai bukatar Shiga group Na Auren CHOCHI just call me,08100044786.*
*PAge 45&46*
Hira suka cigaba dayi afalon Suna dariya,Rahap tace Momcy Gaskia banji dadiba DA broda baizo mana DA Anitha ba DA hiran tafi armashi, Abraham yace"Ainima banji dadiba DA munsha dariyar tsokanar sis,Momcy tace"Aikunsan swt Son, Dan ganin damane Yau Baiyi niyar zuwada itabane.
kawai Duk muyi hakuri konima ainaso ganin Yar 'diyata agefena bt no problem tunda GA Auta aita Maye gurbin Anitha Daman Auta DA Autane Momcy tafa'da tana kallon Radiya.
Hakan yasa Radiyar tayi murmushi tare day Jin da'din mgnr Momcy, baki tabude zatayi mgn saidai Jin alaman