Showing 30001 words to 33000 words out of 39627 words
kwana.
Dakyar take buɗe idanunta wanda sukayi mata nauyi sosai hasken data gani ya sanya ta runtse idanunta dan rabonda taga haske yau kwana 4 kenan, kallonta ya yi ya ce"tashi ki fita ko ranki ya ɓaci" kasa koda motsi Fattomah ta yi, kukanma na zuci take domin hawaye ya daɗe da ƙafewa daga idanunta, kama gefen gadon ta yi ta miƙe wani jiri taji yana ɗibanta komawa ta yi ta zauna kan gadon ta fashe da kuka ta ma rasa abinda zatayi ga ciwon da jikinta ke mata, ga yunwa, ga ciwon da cikinta ke mata goge hawayen idanunta ta yi sannan ta sake attempting na miƙewa akaro na biyu baya tayi zata faɗi taji an riƙe ta, kwantar da'ita Jawaad ya yi akan gadon sannan ya kalli Imad wanda ya shigo sannan rai a ɓace ya ce
"Wannan abunda kake zalunci ne Imad, wane Irin rashin imani ne wannan har ka kulleta a ɗaki for almost 4days babu abinci baka damu wane hali zata shiga ba wannan ba adalci bane Imad kuma wlh sai Allah ya tambayeka, idan kana ganin bazaka iya zama da'ita ba ta kusa ƙarasa makarantarta ka bani ita na tafi da'ita gida idan ta ƙarasa sai na mayar da'ita wajen Daddy"
Murmushi Imad ya yi ya ce"abinda nakeson naji ka faɗa kenan, wato na baka ita ka tafi da'ita gidanka to bazan bayar ba, kuma wlh ko yanzu zata sake gwada aikata sheɗanci wlh saina hukuntata daidai da laifin data aikata idan kuma tana ja dan Allah yau ma ta sake haɗa kayanta zata bar gidan nan taga" kallonsa kawai Jawaad ya yi dan shi arayuwarsa bai iya tashin hankali ba idan kaga yayi faɗa toh tabbas abinda akai ya kai abu, tsaki Imad ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Ƙara sawa gabanta ya yi yana kallonta ganin duk yanda ta rame ga jikinta duk tabon duka tayi duhu ba kamar da ba, runtse idanunsa ya yi sannan ya ce"sannu kinji bari na kai ki asibiti" juyawa ya yi zai fita ta riƙe masa hannu kallonta ya yi yana sanya hannayensa cikin nata ya ce"mene ne?" Murya can ƙasa ta ce"yaya karka tafi ka barni ka tafi dani" yanda take maganar zaka gane har cikin ranta haka take nufi, shafa kanta ya yi ya ce"kiyi haƙuri babu inda zani Fattomah asibiti zan kai ki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya sake ya fita.
Wani banzan kallo Imad ya watsa masa sannan ya ce"babu wani asibiti da za'a kai ta ko mene za'a yi mata ai mata a gida wlh babu inda zata je, kai bari kaji ma babu inda zata sake fita indai tana cikin gidan nan" murmushin takaici Jawaad ya yi ya ce"shikenan duk abinda kake dai ka dinga tuna akwai ranar sakamako akwai ranar da zakayi regreting abinda ka dinga aikata mata alokacin kuma ba zai amfane kaba, dan kana ganinta yarinya ko kuma marainiya wacce batada wani gata to ka sani Allah yana nan a madakata kuma wlh bazai barka ba Imad ya kamata ka daina wannan abunda kake I'm not force you kawai shawara nake baka a matsayina na ɗan uwanka" cikeda rainin hankali Imad ya ce"aikuwa nagode" gaba ya yi bai sake bi takansa ba.
Sosai ta sami sauƙi saboda yanda yaya Jawaad ya kula da rayuwarta har yaga ya ta samu sauƙi sosai sannan dukda Imad ya hana akaita asibiti haka ya dinga jigilar zuwa gidan safe da yamma, zaune take kan kujera tana kallon dramar da ake a arewa 24 sosai ta bawa kallon muhimmanci dan batasan sanda ya shigo ba tsaki ya yi sannan ya kashe tv hakan yasa ta ɗago idanunta tana kallonsa, harararta ya yi sannan ya zauna kan kujera yana kallonta ya ce
"Duk randa na sake ganin kina wannan kallon na asara sai ranki ya ɓaci wlh" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba ya ce"zan tafi Spain yanzu and bansan tsawon lokacin dazan ɗauka ba maybe one week maybe kuma yafi haka ina sanar dake ne saboda idan har na dawo na samu kina aikata wani abu daban wlh Fateemah sai ranki ya ɓaci ki kama kanki ki zauna idan safiya tayi ki tafi makaranta idan kin dawo babu ke babu yawo" raurau tayi da idanu tana kallonsa ta ce"Uncle ka kaini gidan yaya Jawaad tsoro inaji" harararta yayi ya ce"ki mutu" miƙewa ya yi ya fice daga parlon without looking at her, hawayene suka shiga sakko mata kan kuncinta tana sharesu wasu na sake zubowa.
Convey ɗin da taji ya sanya ta mike taje jikin window tana kallonsu har suka shiga mota shima Salma sannan guards suka shiga suka rakashi, sauke idanunta tayi tana rufe bakinta saboda wani kuka daya tawo mata tayi saurin komawa parlon ta faɗa kan kujera ta rushe da kuka.
*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*
*Like nd share*
[5/18, 9:52 PM] Nanameera: *💞 FATTOMAH 💞*
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.
*Ameenatou I Ibrahim*
Nanameera
PAGE 36-39.
Da sauri ta gama shiryawa dan ta kusa makara ko kallon abincin da maid ta ajiye mata batayi ba tayi waje, bayan ta zauna a motar tana ɗan Kalle-kallenta drivern ya ce"Hajiya ƙarfe nawa zaku tashi dan sir ya ce azo a ɗauke ki da wuri" kallonsa ta yi ta mudubi sai kuma ta ce"sai 4pm sannan"okay ya ce sannan suka ci-gaba da tafiya ba tareda ta sake furta wata kalma ba. Fa'eeza ta ce"wai yanzu babu kowa a gidan sai ke kaɗai?" gyaɗa mata kai Fattum ta yi ta ce"kuma kika zauna tab ni ce ke wallahi bazan zauna ba ko tsoro baki ji" murmushi kawai Fattomah ta yi batace komai ba Aysha ta ce"kawai ki zo mu tafi gidanmu idan aka tashi sai ki dinga kwana acan" da sauri Fattum ta kalleta ta ce"ke bakida kai ne?, so kike Uncle ya kusa kasheni idan ya dawo?" tsaki ta yi ta ce"to ai bai saniba kuma baya nan yanzu ke kinfiye tsoro wllh" dariya kawai ta yi ta ce"ni babu inda zani kinji" harararta ta yi"to kar kije mara mutunci".
Kallon noodles ɗin tayi wacce taji kayan haɗi kana gani kasan ba ƙaramin daɗi zata yiba, Aysha ta ce"kee Fattum nasan halinki wlh karki yi cin mugunta kinga mu ukune" harararta ta yi ta ce"saboda kin maidani kwaɗayayyiya?" ta ce"nasan halinki da indomie shiyasa" "to ni bama ci zanyi ba" kallonta Aysha tayi ta ce"dan Allah kiyi haƙuri da wasa fa nake" ta ce"nima wlh nasani kawai bana cine rabonda naci indomie har na manta ni mango ma zan siya" haɗe rai Aysha ta yi ta ce"shikenan Nagode babu matsala amma wallahi nima bazan sake cin abin hannunki ba har muyi graduation" dafata Fattomah tayi ta ce"I'm sorry dear wlh na ƙoshi shiyasa kema kinsan bama haka dake" doke hannunta ta yi ta ce"dallah rabu dani" dariya ta yi ta ce"bari naje na siyo Mango kafin sannan kun kammala cinyewa" ko kallonta Aysha ba tayi ba bare ta bata amsa ta cewa Fa'eeza"please muci na rabu da wannan yar iskar" dariya Fa'eeza ta yi sannan suka fara cin abincin.
Ganin yanda take haɗe rai yasa Fa'eeza ta ce"wai Fateema lafiya?" ya mutse fuska Fattum ta yi ta ce"wlh Mangon babu daɗi kamar gwanda" tuntsirewa sukayi da dariya Aysha ta ce"A'a kin manta kamar abarba" harararta ta yi ta ce"na saka ki a maganata?" Aysha ta ce"ban sani ba" miƙewa tayi ta ce"nidai na tafi gida sai kuma Friday please ku shigo da wuri" Aysha ta ce"wai bazaki gidan namu ba?" girgiza mata kai Fattum tayi sannan tayi gaba dan ba wani son yawan magana take ba. Tsaye taga drivern da alama bai koma gida ba saida suka fara tafiya sannan ta ce masa"wai anan ka zauna tunda safe?" murmushi ya yi ya ce"Eh haka sir ya ce idan mun kai ki azauna a jiraki har ki gama sannan"taɓe baki Fattum ta yi aranta tana cewa"wato ashe har ma'aikatan nasa ma muguntar yake musu?????".
Sosai tasha baccinta sai wajen ƙarfe 8pm sannan ta shirya cikin wasu riga da wando ash colour wandon iya gwuiwa yazo mata kasancewar ita kaɗai ce gidan yasa bata damu ba, murmushi tayi ganin yanda abincin ke turiri saboda tsabar dawuwar da ya yi zama tayi ƙasan carpet ta tankwashe ƙafafunta ta ajiye plate ɗin jallof rice ɗin gabanta wani ɗan bowl ta ɗauko wanda Aysha ta kawo mata yajin daddawa ta buɗe ta zuba akai har saida abincin ya fara yin wannan kalar sannan ta rufe ta fara ci, haka ta dinga cin abincin kamar mayya saboda yaji sai shuuuuuu take da baki amma hakan bai sa ta haƙura ba, saida ta jinye tasss sannan ta ɗauki wani ruwa mai mugun sanyi ta sha gyatsa tayi sannan ta ce"Alhamdulillah" tashi tayi ta kwashe plate ɗin ta kwanta kan kujera nan da nan wani sabon baccin ya ɗauketa
Da gudu ta ƙarasa toilet ɗin tana zuwa ta zube nan ƙasa ta shiga gwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta saida duk abincin ya fita sannan ta jingina da bango hannunta bisa cikinta tana sauke numfashi, dakyar ta samu ta mike ta ɗauraye bakinta da wajen Sannan ta fito tana bin bango sake kwanciya tayi amma kwata-kwata ta kasa baccin banda ciwo babu abinda cikinta ke mata gashi babu wani magani cikin gidan bare ta ɗauka tasha kuma batada waya bare ta kira yaya Jawaad tunanin hakan yasa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita. Haka ta gaji da kukan tayi shiru dan kanta tunda babu wani mai rarrashinta, sai wajen ƙarfe 12am sannan ta fito parlon tana riƙe cikinta wanda take jin kamar zai bar jikinta dakyar ta sauka daga benen tana dafe bango ta fita daga cikin gidan tana kallon compound ɗin gidan wanda ya wadatu da kayan ƙyale-ƙyale haske ta ko'ina wani guard ne wanda yake aikin night ya kalleta ganin yanda take tafiya, tashi ya yi ya ƙara sa gabanta ya ce"ina zakije ƴan mata?" kallonsa ta yi ta ce "dan Allah kabani magani cikina ciwo yake min zan mutu please" ya ce"ohh sorry zo muje na baki drug kisha sannu kinji" toh ta ce masa sannan ya yi gaba tana biye dashi abaya.
Sosai Fattum ta gaji da tafiyar ganin kamar ma ba tafiyar suke ba, saida suka je daga bayan gidan inda babu haske sosai ya ce"yawwa zauna anan bari na ɗauko miki acan"toh kawai ta ce sannan ya juya ya bar wajen gajiya tayi da tsaiwar ganin kusan 5mins bai dawo ba, zama tayi awajen saboda ba zata iya cigaba da kasancewa a tsaye ba
"Keeeee!!"
Aɗan firgice Fattomah ta ɗago kanta tana kallonsa ya ƙaraso yace"me kike yi anan?" ta ce"dama..daman wannan ne ya ce zai ɗauko mini magani anan na jira shi shine na zauna cikina yana min ciwo" tsaki ya yi ya ce"ke wace irin shashasha ce?, bakida hankali ko ko ya ya?, mene ne ma abinda kika fito yi a wannan daren?" hawayene ya kawo idanunta ta ce"cikina ne yake ciwo kuma na kasa Bacci shine nake neman magani" girgiza kai ya yi aransa yana cin babu daɗi tabbas abinda Imad ya aikata ba daidai bane bai dace barin yarinya budurwa cikin gida ita kaɗai ba tareda wani wanda zai kula da'ita ba, ganin tana neman faɗuwa yasa ya ce"shige ki koma gida da safe sai kije asibiti a dubaki" gyaɗa masa kai tayi sannan ya ce"yi gaba" gaba tayi yana binta abaya daga yanda take tafiyar zaka gane tana matuƙar jin jiki dan dakyar take ɗaga ƙafarta a haka har suka fito compound na gidan, saida yaga ta shiga ciki sannan ya girgiza kansa ya koma wajen gate ɗin aransa yana tausayawa rayuwarta.Fattomah kuwa na shiga ta zauna a parlon nan tana kuka saboda wani irin zafi da cikinta ke mata ita kaɗai tasan masifar da take ji da wannan ciwon ciki, haka ta ƙarasa wannan daren ba tareda tayi bacci ba sai wajejen asuba sannan ta samu ya ɗauketa
ABUJA
Rai ɓace Daddy ya ce"when zaka dawo malam?" ya ce"in sha Allah ranar Thursday Daddy zanfara biyowa nan maybe" Daddy ya ce"Imad karka ce zaka rainami hankali"murmushi ya yi ya ce"Daddyyyy calm down wlh zan zo ko ban biyo ba ina komawa gida zan tawo" yace"nadai faɗa maka" kashe wayarsa ya yi yana kallon Mommy ya ce"ya kusa dawowa ai" Mommy ta ce"toh Allah ya dawo dashi lafiya amma dan Allah idan zai tawo ya tawo mini da Fattomah naganta" Daddy ya ce"why?, bai fi ba sauran 5weeks ta dawo nan duka ba please ki bar wannan maganar kawai"murmushi kawai tayi dan tasan saboda ransa aɓace yake ne ta ce"toh na bari yallaɓai" tashi ya yi bai sake cewa komai ba ya shige bedroom.
KANO
Tashi tayi wajen karfe 10am kalle-kallen inda ta kwanta ta shiga yi dafa cikinta tayi wanda har sannan yana mata ciwon amma ba kamar ɗazu ba, freezer ta buɗe da ɗauki ruwa ta sha sannan ta haye sama dan kintsawa. Kallonta gateman ɗin ya yi ya ce"yanzu ke dawa zaki je asibitin?" ta ce"nida ƴar uwarmu ka kaini gidanta please" girgiza kansa ya yi ya ce"bari akira yallaɓai dan ya ce kar a kuskura a barki ki fita wani waje idan ba makaranta ba" turo baki Fattum tayi bata ce komai ba ya ce"bari naje wajen oga" tafiya ya yi ta bisa da kallo. Saida taga ya shige sannan ta yi sauri ta kalli ƙofar, ahankali kamar wata mara gaskiya haka ta buɗe gate ɗin ta fice da gudu.
Cikin wayar Imad ya ce"A'a kar wanda ya barta ta fita indai ba school ba kuma koda school ne idan an kaita kar a tawo abarta tare da'ita zaku dawo" toh kawai sukace sannan ya katse wayar, da mamaki gateman ɗin yake kallon wajen da yabar Fattomah tsaye dan yanzu bai ganta wajen ba, sosai ya duba bai ganta ba kuma babu alamun ta koma cikin gidan buɗe ƙofar ya yi yay waje ya fara tafiya cikin unguwar kwata-kwata babu mutane a titin kowane gida kuma arufe yake wani ƙofar gida ya gani da gateman zaune kan kujera da sauri ya ƙarasa bayan sun gaisa ya ce"dan Allah kaga wata yarinya ta shige tanan?" gateman ɗin ya ce"ai kuwa wata ta sanya abaya blue ko?" da sauri ya ce"Eh ita ce" ya ce"wallahi naganta ɗazu ta shige tana tafiya da sauri kamar tayi gudu ma, amma lafiya" cikin tashin hankali ya ce"inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun meyasa yarinyar nan zatayi haka?' magana gateman ɗin yake masa amma ko juyowa bai yiba shi kaɗai yasan tashin hankalin da zasu fuskanta wajen Imad idan har ya dawo ya tarar bata nan fatan shi ɗaya Allah ya bata ikon dawowa da wuri duk inda taje,koda ya shiga gidan babu wanda ya sanarwa cewa bata nan ya koma ya yi zamansa dukda zuciyarsa fal take da tunani kala-kala.
Da gudu Khaltum ta zo ta rugumeta tana sake kallonta cikeda murna ta ce"Fattomah ke ce dagaske?" murmushi ta yi ta ce"to dafa?" dariya suka yi tare ta ce"ina Adda?" "yanzu ta fita taje wajen biki yanzu zasu dawo" okay ta ce Sannan ta zauna kan katifar
"Washhhh wlh nagaji sosai"
Kallonta Khaltum ta yi ta ce"wai daga ina kike?" "daga gida mana, ina yaya Aslam?" ta ce"wallahi ya tafi Katsina mukaje gidan da kika koma muka tarar arufe shine ma ya tafi" miƙewa daga kwanciyar da tayi ta ce"dan Allah fa meyasa baku bugamin waya ba nag ...." shiru ta yi tunawa da tayi babu waya a hannunta Khaltum ta ce"wallahi mun kira ki amma wayar akashe shiyasa kawai muka haƙura muka dawo gida, kina waya da Ammi?" hawayene ya kawo idanunta amma ta ɓoye ta ce"rannan na kirata please kina credit wayarki kimin kiranta?" okay ta ce sannan ta ɗauko wayarta, ringing ɗaya Ammi ta ɗaga wayar tana yin sallama Fattomah ta ce
"Ammina!!Ammina!!Amminaaa".
Kukane yaci ƙarfinta tama kasa magana ita kanta Ammi kuka take domin tana matukar kewar ɗiyarta saida ta daidaita muryarta sannan ta ce"mene ne haka Faɗeematoh?" sake rushewa tayi da wani kukan saboda tunawa da tayi da Abbanta da yake yawan ce mata Faɗeematoh, cikin sheshsheƙar kuka ta ce"Amma.Amm...Ammina dan Allah ki dawo Kano kinji banason zama gidan uncle ki dawo mu zauna agidanmu kinji yafi daɗi Ammi" cikin raunin zuciya Ammi ta ce"kiyi haƙuri Fattum ina nan zan zo wajen ki in sha Allah karki damu ki daina kuka kinji ki daina rigima" Fattomah ta ce"Ammina inason naganki dan Allah" murmushi tayi wanda yake zuba da hawaye ta ce"Nima haka Fattum inason naganki amma in sha Allah zan zo nan kusa" "Ammi amma bazaki koma ba?" ta ce"ai nadawo gida Fattum nida rayuwa cikin Kano saidai hukuncin Ubangiji" sake fashewa ta yi da kuka Ammi ta ce"ya isa kiyi shiru banason kukan zan zo shikenan?" gyaɗa mata kai ta yi ta ce"to sai kin zo Ammi kuma so nake ki dafamin dambun shinkafa da zogale da gyaɗa Ammina" dariyar da bata shirya ba ta yi tanajin zallar rigimar ɗiyar tata ta ce"in sha Allah randa nazo Kano duk zan dafa miki wannan abubuwan Fattum" murmushi ta yi ta ce"toh Ammina sai kin zo" ta ce"toh Faɗeema" murmushi ta sake yi ta ce"ina sonki Ammina" dariya ta yi ta ce"nima inasonki Fatyy na", sallama sukayi sannan ta miƙawa Khaltum wayarta.
Dariya ta yi ta ce"naga randa zaki daina shagwaɓa arayuwarki" harararta ta yi ta ce"babu rana kuwa wollah" dariya Khaltum ta yi ta ce"ai shikenan" kwanciya Fattomah tayi gefen katifar nan da nan bacci wanda baya mata wahala ya sake ɗauketa. Murmushi Adda ta yi ta ce"aikuwa kin kyauta Faɗeematoh amma dai kwana zaki yi?" gyaɗa mata kai Fattum tayi tana murmushi dan daman haka ta shirya, Abla ta ce"kinyi kyau abunki amma duk kin rame Fattu"harararta Adda ta yi ta ce"ke kam da gulma Allah ya shirya" dariya suka yi duka sannan suka cigaba hira gwanin ban sha'awa, tun bayan rasuwar Abba sai yau ta sake samun farin ciki irin wanda ake kira farin ciki domin ji take kamar zata koma gidansu ta tarar da Abbanta da Amminta zaune suna jiranta
"Fattomah kuka?"
Da sauri ta taɓa fuskarta taji hawayene yake zuba, Adda ta ce"faɗa min lafiya kuwa?"