Showing 9001 words to 12000 words out of 39627 words

Chapter 4 - FATTOMAH BOOK 1 by Nana Meera.txt

20 Dec 2024

2298

maid aiki dan idan batada abinyi kitchen take shiga, miƙewa Mommy tayi ganin an shigo da wani abu kamar mutum arufe kasa magana tayi dan duk tarasa abinda zata yi, Uncle Mansoor ne ya zauna gefen kujerar saboda wani irin sarawa da kansa ke masa Kalle-Kalle ta shiga yi ganin babu wanda yake komai cikinsu duk sunyi shuru, Imad ne ya shigo da sallama Jawaad na bayansa sai matarsa wacce suka tawo tare da niyyar gaisheda Mommy. Da mamaki Jawaad yake kallonsu sai kuma ya kalli gawar dake kwance nan ƙasa cikin rawar baki ya ce" Dad...Daddy..D.. Daddy waye wannan?" kallonsa sukayi duka atare sai kuma sukai shiru, ahankali kamar me tsoron taka ƙasa ya ƙarasa gaban gawar ya tsuguna tamkar an tilasta masa ya buɗe fuskarsa dan gani waye haka, wata irin ƙara da ta saka yasa duka suka juya suna kallonta kafin su ƙarasa ta waɗi ƙasa sumammiya.....






Allah Sarki rayuwa ayau akai sadaƙar bakwan mutuwar Abba wanda ya yi daidai da ranar juma'a, zaune take ta ɗora kanta kan cinyar Ammi banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa domin kukanma ya gagara kasawa take duk ta rame ta fice hayyacinta kamar ba Fattomah ƴar rigima ba tunda randa aka sallamota a asibiti bata kula kowa ba duk irin maganar da zaka yimata kuwa sai kuka dan ko abinci taƙi taci hatta Ammi ta gaji ta rabu da'ita domin duk irin yanda taso ta shawo kanta kasawa tayi, yanzuma tayi shuru tana tunanin Abbanta wanda shine abinda take kwana tana yi Mommy ce ta shigo ɗakin da sallama tana zuwa ta zauna gefen Ammi tana kallon Fattomah ta ce




"Dan Allah dan Annabi Faɗimatoh kiyi haƙuri ki yiwa Abbanki addu'a kinji wannan kukan bashi da amfani ki daina dan Allah" kamar wacce ta zugata haka ta sake fashewa da kuka kamar ranta zai fita rungumeta Mommy tayi tana shafa kanta ta ce" ya isa haka stop crying Baby kiyi masa addu'a" cikin kuka Fattum ta ce" Mommy Abbana ya tafi ya barni Mommy inason Abbana dan Allah Abbana ya dawo wajena kice masa karya tafi ya barni zanta yin kuka bazan daina ba ni inason Abbana Fattomah tanason Abbantaaa" hawaye suma sukeyi domin yanda take kukan sai ta baka tausayi tabbas Fattomah ta saba da mahaifinta kuma tana matuƙar ƙaunarsa kamar yanda shima yake nuna mata wannan soyayyar dan tafi jinsa azuciyarta fiye da Amminta gashi yanzu ta rasashi rasawa irinta har abada. Baccine ya ɗauketa tana cikin wannan kukan Mommy ta kwantar da'ita sannan ta kalli Ammi ta ce" dan Allah A'isha ki ƙara haƙuri karki dinga damun kanki addu'ar ku yafi buƙata yanzu fiye da kukan please" ajiyar zuciya Ammi tayi tana share hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata ta ce" Nagode Hajiya amma bazamu taɓa mantawa dashi ba domin shiɗin ba kamar sauran maza yake ba yanada halaye wanda ba kowane namiji yake dasu ba ya kula da rayuwarku cikin walwala dakuma tsanani, yana ɗaukan iyalansa tamkar duniyarsa bashi da damuwa indai yana tare damu kuma muma da haka muka tashi wlh har abada bazamu taɓa mancewa dashi ba Allah Ubangiji ya jiƙansa da Rahama" dafata Mommy tayi ta ce" nasani amma dole sai kun cire tunaninsa cikin ranku sannan zaku cigaba da gudanar da rayuwarku Allah ya gafartamasa" "Ameen ya rabbi".








Da murmushi a fuskarsa yake kallonta har ya ƙaraso inda take, zama ya yi kan kujerar dake facing wanda take kai ya ce" princess naji kinyi shiru lpy?" kallonsa tayi ta ce" yaya wai sai naga kowa yanada waya a school ɗinmu amma banda ni nima ka siyamin waya yau kuma" dariya ya yi yana kallonta ganin da gaske she's vert serious ya ce" toh Fattum zan siya maki idan kika yi graduation" wani irin kallo tayi masa sai kuma ta ɗauke kai tana kallon wani wajen daban, murmushi ya yi ya girgiza kai sannan ya ɗauko wata leda wacce take bayansa yana murmushi ya ce" kalli kiga" kin kallonsa tayi tana tura baki gaba, Jawaad ya ce" idan na mayar shikenan bazan baki ba shikenan kin rasa" satar kallon hannunsa tayi taga leda amma batace ga abinda yake cikin ledar ba, gyaɗa kansa ya yi sannan ya ɗauke ledar yana shirin mayarwa da sauri ta juyo ganin kamar waya ce cikin ledar tana washe baki ta tafi wajen tana zuwa ta karɓe ledar ta buɗe sakar baki Jawaad ya yi yana kallonta, tana gama ware wayar idanunta ya sauka kan iphone 11pro wata irin ihuuu ta saka tana ƙanƙameshi tana dariya ta ce" thank you so much Yaya nagode sosai Allah Ubangiji ya bikaya da gidan aljanna I'm so happy yayana" murmushi Jawaad ya yi yana kunshe idanunsa dan daman farin cikinta shine muradinsa ya ce" Ameen princess nima nagode" ledar kawai ta ɗauka ta fita daga garden ɗin da gudu da kallo ya bita sannan ya miƙe shima yabi bayanta






"Mommy kinga Yaya Jawaad ya siyamin" waro ido Mommy ta yi ta ce" enyeeee yarinya ƴar gidan yaya Jawaad to kince kin gode?" gyaɗa mata kai tayi tana washe baki daidai nan Jawaad ya yi sallama a parlon, gaisawa sukayi da Mommy ta ce" wato na fuskanci kaine kake shagwaɓata yasa take abinda taga dama ko Jawaad" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" A'a Mommy" murmushi Mommy tayi ta ce" kai da ita ni nan babu ruwana wlh" dariya ya yi ya ce"wai ina Footballer ne kwana biyu?" tsaki Mommy tayi ta ce" nima ina na ganshi sai ɗazu naji babansa ya ce wai ya tafi Spain shine amma ko ya sanar dani" murmushi Jawaad ya yi ya ce" kinsan halinsa sai shi watarana sai naji kamar dai yanada almutsutsai akansa" tuntsirewa tayi da dariya suka juya duka suna kallonta, saida tayi mai isarta sannan ta ce" yaya Jawaad ka bani dariya wai almutsutsai" sake tuntsirewa da dariya tayi Mommy ta ce" Allah Ubangiji ya shirya mana ke Fattum" tana dariyar ta ce" Ameen Mommy".










Haka Fattomah ta cigaba da gudanar da rayuwarta cikin gidan General Ibrahim Baira babu abinda ta rasa arayuwarta komai suna yi mata abu biyu ne kawai yake damunta na ɗaya rashin Abbanta wanda har sannan bai saketa ba sai kuma rashin Amminta kusada ita dan bayan arba'in ɗin Abba ta koma garinsu Katsina saidai suyi waya da'ita lokaci zuwa lokaci, banda waɗannan abubuwa batada wata damuwa rayuwarta tana tafiya yanda ya kamata hakana ɓangaren karatunta wanda yanzu taƙi kaɗan ya rage mata dan gab suke da fara jarrabar kammala karatu matakin secondary. Bangaren Jawaad ma yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kyautata mata duk da zuwa sannan Mommy ta gama fahimtar inda ya dosa saidai babu wanda ta sanarwa hakan ta bari har sanda suma zasu gano hakan da kansu, Ayrah kuwa da batasan wainar da ake soyawa ba ta ɗauki Fattomah tamkar ƙanwarta duk abinda ta samu tofa natane itada Fattum har kwana takeyi gidansa idan Daddy ya barta. Yauma suna cikin kitchen tare inda suke dafa jallof rice sai chips da zasuyi da kuma pineapple nd coconut drink, Banda ƙamshi babu abinda yake tashi dan indai girkine tofa Ayrah number ɗaya ce tanada kwarewa ta wannan fannin ba'a taɓa kada ita a girka haka itama Fattomah wacce yanzu take koyan duk wani abu wand da bata iya shiba. Sallama suka ji a parlon hakan yasa Fattomah ta miƙe daga kan stool ɗin tana kallon Ayrah dake ƙoƙarin wanke hannunta ta ce" aunty Ayrah bari na duba" ohk ta ce sannan ta cigaba da abinda take ita kuma ta fito dan ganin waye, da gudu ta tafi ta rungumeta tana dariya ta ce".








*Nanameera ce#*[5/13, 9:27 PM] Nanameera: *FATTOMAH*




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*






PAGE 13-14.




"Aunty Salma sannu da zuwa"




Murmushi Salma ta yi tana kallonta ta ce" Fattomah ya kike?" "Ina lpy muje ki zauna" okay Salma ta ce sannan tabi bayanta suka zauna kan kujera, Salma ta ce" Ayrah bata nan ne?" Tashi Fattum ta yi ta ce" muna aiki a kitchen ne bari na sanar da'ita" okay Salma ta ce sannan Fattomah ta juya ta shige kitchen ɗin, kallonta Ayrah ta yi ta ce" wace Fattum?" "Aunty Salma ce tazo" ok Ayrah ta ce sannan ta ce" ki ƙarasa haɗa drink ɗin please karki cika sugar Kinsan yayanki baya so" murmushi ta yi ta ce"toh in Sha Allah".








Murmushi ɗauke a fuskarta suka gaisa ta ce"sannu da zuwa sai yau?" Murmushin itama ta mayar mata sannan ta ce" wallahi kinsan halin mutumin ban samu saƙafar faɗa masa ba sai yau shiyasa ma kikaga ganni yanzu da yamma ya ce anjima zai zo mu tafi" Ayrah ta ce "wallahi yaya Imad halinsa sai shi rannar fa dakyar ya tsaya ya ci abinci wai tafiya zai yi bayan ya gama saka ni aiki" dariya Salma ta yi ta ce"Allah dai ya kyauta" Ameen Ayrah ta amsa sannan ta ce" let me get you something".








Harararsa Jawaad ya yi ya ce" bangane ba?"kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"wannan abinda kake shirin yi isn't proper matarka ta ɗauki yarinyar nan matsayin ƙanwarta bata nuna mata wani banbanci da ƴan uwanta shine zaka ɓata alaƙar tasu kuma sannan ma ka rasa wa zaka aura sai ƙaramar yarinya ubanme zata yi maka idan zakayi aure ka ɗauko babbar mace shine Malam ba wacce zaka zauna raino ba" tuntsirewa ya yi da dariya yana kallon ɗan uwan nasa ya ce" a naka tunanin kenan amma ni kam babu abinda zai hanani auran Fattum sai ikon Allah naji zanyi rainon nata kai bakasan sunfi daɗi ba yaran" taɓe baki Imad ya yi ya ce" bakada hankali ne shiyasa sai ka ƙara girma" wani shegen kallo Jawaad ya watsa masa ya ce" lailaima wato kaine ka girma ko Abba" haɗe rai Imad ya yi ya ce" E, kasan ai daman ni ba sa'anka bane" fitowar Fattum ya sanya sukayi shuru da maganar tana zuwa ta kalli Jawaad tana haɗe rai ta ce" yaya muje ka mayar dani gida" da mamaki ya ce" lafiya princess?" turo baki ta yi ta ce" kawai nidai ka mayar dani mana"




"Fattum!!! Fattum!!"




Ƙin juyawa tayi Ayrah tazo tana murmushi ta rungumeta ta baya ta ce" I'm so sorry dear ban ƙarawa" ƙin kallonta Fattomah tayi dan ita daman riƙo gareta, murmushi Jawaad ya yi ya ce"me kika yimata?" murmushin itama tayi ta ce" wai dear daga nace mata ta cika sugar cikin drink shine fa wai gida zata tafi" dariya ya yi ya ce" rigima dai Fattum?" zumɓura baki ta yi ta ce" ni bazan sake zuwa gidan nan ba" Jawaad ya ce" dan Allah kiyi haƙuri Fattomah Kinga yanzu dare ya fara yi ki bari gobe in Sha Allah da kai na zan mayar dake gida okay?" girgiza kanta tayi bata ce komai ba, babu yanda basu yi da'ita ba amma Fattomah taƙi haƙuta ita a lallai sai ta tafi gida. Ji tayi an fizgota ta juya kafin tayi aune har ya kaita compound ɗin gidan, cikeda ɓacin rai yake cewa


"Idan kika sake two minutes cikin gidan nan sai ranki ya ɓaci shashasha kawai"




Da sauri Jawaad ya ƙaraso wajen yana kallonsa ya ce" haba Imad mene ne haka yarinya ce fa?"


Afusace Imad ya juyo ya ɗaga masa hannu ya ce" enough!!, banason jin komai nd idan baki bar gidan nan ba I'll show you the other side of me" banda rawa babu abinda jikin Fattomah keyi Allah sarki duk tabi ta tsorata bata saba da irin wannan masifar ba domin kwata-kwata ba'a yi mata faɗa idan ka cire Ammi wanda shima a hankali take faɗa mata koda kuwa laifi tayi shiyasa duk tabi ta ɗimauce, ganin har sannan batada niyyar fita yasa yace da ƙarfi" ubanme kike jira ne?" jikinta na kyarma tayi hanyar fita daga cikin gidan veil ɗin nata ma ya waɗi saboda tashin hankali. Ganin ta kusa kai wai bakin gate yasa Jawaad ya bi bayanta ba tare da ya kalli Imad ba har zata fita dan gateman ɗin bai yi ƙoƙarin hanata ba ganin abinda ya faru, da sauri ya fice daga gidan yana bin bayanta ya ce




"Fattomah!!"


Ko juyowa bata yi ta cigaba da tafiya da sauri da sauri gudun kada ya cimma ta, kasancewar tafiyarta da tashi ba ɗaya ba yasa ya yi saurin shan gabanta yana kallon fuskarta wacce duk ta jiƙe da hawaye ya ce" Fattum!" kasa kallonsa tayi sai kawai ta rungumeshi tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ba ƙaramin tsorata tayi ba har jikinta ya fara ɗaukan zafi, tsam ya rungumeta a ƙirjinsa yana jin yanda take kuka a hankali shafa kanta kawai ya iya yi dan bashida zarafin ce mata tayi shuru tabbas akwai buƙatar tayi kukan ko ta samu sauƙi cikin ranta.








Saida tayi kukanta mai isarta sannan ahankali ta fara sauke ajiyar zuciya hakan yasa ya ɗago fuskarta akan hannayensa yana kallonta ya ce" I'm sorry kinji na baki haƙuri a madadin Imad" kwaɓe fuskarta ta yi cikin sanyin murya ta ce" yaya ka kai ni wajen Ammina please" sosai ta bashi tausayi jin wacce tskeson gani gashi yasan bashida wannan damar bazasu taɓa yarda ya kai ta ba, shurun da taji ya yi ne yasa ta ce" yayaaaa" lumshe idanunsa ya yi ya ce" na'am ƙanwar yayaaaa" murmushin da batayi niyya ba ta saki ta ce"Allah yaya ka daina banaso" okay ya ce sannan ya kama hannunta, sauri riƙe nasa hannun tayi tana kallonsa, kallonta shima ya yi ya ce" mene?" "bazan bika ba" haɗe ransa ya yi ya ce" bangane ba Fattomah ina ne bazaki bini ba?" sunkuyar da kanta tayi sai kuma ta share hawayen da yake ƙoƙarin fitowa kan idanunta ta ce"ka kaini wajen Mommy kaji Wlh bazan kwana anan ba" sosai ya yi mamakin jin furucin bakinta sanin kuma halin gaddamarta yasa ya ce"muje na ɗauko mota to" naɗe hannayenta tayi a ƙirji ta ce" kaje yaya ina jiran ka anan" girgiza kansa kawai ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan.








Zaune ya tarar da Imad yana danna wayarsa haka ma Salma wacce take zaune tana jiransa, sallama kawai Jawaad ya yi musu sannan ya haye sama ko kallonsa Imad bai yi ba saida ya haye saman sannan ya miƙe without looking at her ya ce"muje" babu musu ta miƙe dan daman sunyi sallama da Ayrah ɗaga mata hannu tayi itama ta mayar mata sannan sukai waje, fitowa ya yi jikin wata jallabiya ash colour wacce ta amshi farar fatarsa da mamaki ya kalli Imad wanda yake ƙoƙarin shiga mota bayan guards sun buɗe masa, ƙara sawa ya yi jikin mota ya yi nocking hakan yasa ya sauke glasses ɗin yana kallonsa ya ce" ina zaka je kuma yanzu fa zan dawo?" ba tare da ya kalleshi ba ya ce" gida" shuru Jawaad ya yi na wasu sakwanni sannan ya ce" okay saida safe" gyaɗa masa kai Imad ya yi sannan ya zuge glasses ɗin.








Komawa ya yi ya shige motarsa saida ya jira motocin Imad suka bar gidan sannan shima ya yiwa motar key ya fita, tsaye ya sameta daidai inda ya barta tana ganinsa ta tawo ta shiga motar sannan ya ci-gaba da tafiya, ganin yanda ta lumshe idanunta yasa ya ce" bacci ki keji?" buɗe idanunta waɗanda suka fara sauya kala ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce a hankali" zazzaɓi nake ji yaya" tsayar da motar ya yi yana taɓa jikinta ya ce"subhanallahi sannu bari na siya miki magani kinji" gyada masa kai tayi sannan ya ci-gaba da tafiyar. Wani pharmacy ya tsaya ya siya mata magunguna Sannan suka fito tafiyar 5mins ta kawosu wajen wani suya spot Banda ƙamshi mai daɗi babu abinda yake tashi a wajen fita ya yi ya karɓo kaza leda biyu sai chilli yoghurt daya siya sannan ya dawo, da idanu kawai Fattomah ta bishi har ya sake barin wajen.










Zaune suka tadda Mommy tana danna system da alama wani abun mai muhimmanci take gabatarwa, sallama sukayi ta ɗago idanunta tana kallonsu zare glass ɗin idonta, kwanciya Fattum tayi akan cinyarta tana lumshe idanunta sosai take jin Mommy tamkar Amminta kodan saboda yanda itama ta ɗauke ta matsayin ƴa ne????, Zama ya yi suka gaisa da Mommy sannan ya kalli Fattum wacce take shirin fara bacci ya ce"keee zo nan" a hankali ta miƙe tana tafiya kamar bata so ta ƙara so wajensa hannunta ya kama ya zaunar da'ita gefensa sannan ya buɗe ledar da ya shigo da'ita, kallonsa ta tsaya tana yi har ya kutsuro kazar yana kallonta ya ce"haaaa" babu musu ta buɗe bakinta ya dinga bata kazar har Saida ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya bata maganin ya miƙe ya ce" yanzu kije ki kwanta saida safe" tashi tayi ta shige apartment ɗinta shi kuma ya yiwa Mommy sallama, Mommy ta ce"wai lafiya naga ka dawo da'ita da daren nan?" murmushi ya yi ya ce"rigima ta sanya sai na dawo da'ita kuma zazzaɓi take" okay Mommy ta ce sannan ya juya ya fita, nima da naga dare ya yi kuma ga Meeyrah ta sanyani gaba da kallo yasa na tattara alƙamin na ajiye naje na kwanta.




*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*
[5/13, 9:28 PM] Nanameera: *FATTOMAH*


*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*




*PAGE 15-16*




Kusan 5days kenan basu haɗu da Imad ba dan daman Jawaad ne mai nemansa sosai kuma shima ransa ya ɓaci, kasancewar yau Friday yasa da wuri suka tashi daga makaranta, tsaye suke itada Aysha tana mata hira wacce ita kaɗai take abarta dan Fattomah ba saurarenta take ba, tsaki Aysha ta yi tana kallonta ta ce"wai ke wannan wane irin wulaƙanci ne ina yi miki magana kin yimin shuru" langwaɓar da kai ta yi ta ce"bana cikin yanayi na magana ne Aysha please ki rabu dani" murmushi Aysha ta yi ta ce"shikenan thank you" gaba ta yi Fattum ta bita da idanu dan ko ajikinta. Har wajen 12:30pm babu wanda ya zo tafiya da ita hakan yasa ranta ya ɓaci duba jakarta ta yi taga tanada kuɗi hakan yasa ta tsayar da keke napep ta sanar dashi inda zai kaita sannan ta shiga, shiga parlon ta yi bayan tayi sallama babu kowa cikinsa sai tv dake faman aiki ita kaɗai hakan yasa tayi shigewarta apartment ɗinta dan a matuƙar gajiye take, wanka kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login