Showing 15001 words to 18000 words out of 39627 words

Chapter 6 - FATTOMAH BOOK 1 by Nana Meera.txt

20 Dec 2024

2300

da wani harafi zata yi masa bayani ya fahimceta ba sai faɗa yake mata akan abinda bata da laifi, cikeda masifa wacce batasan Jawaad ya iyata ba yake cigaba da faɗin




"Wlh Fattomah duk ranar dana sake ganin kamamancin wannan abun ya faru nayi miki alƙawarin ɓata miki rai irin wanda ba'a taɓa yi miki ba, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci daga ke har shi shegen wanda kike kulawar, har yaushe kika yi girman kula saurayi nawa kike?, You Are just 15yrs amma kina tunanin namiji kodan kin ganki da girman jiki?, toh ki sani ko nan da 2yrs baki isa barinki tsayawa da wani ƙato ba bare yanzu shashasha kawai get out of my side"






Da sauri ta tashi har tana ƙoƙarin bigewa ta shige bedroom ɗinta tana zuwa ta waɗa kan gadon ta fashe da wani matsananci kuka, kallonsa Ayrah ta yi bayan ta ajiye food flask ɗin hannunta ta ce"doctor lafiya?" tsaki ya yi ya ce"babu komai" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce"haba dan Allah ai tunda naga kana wannan faɗan dole akwai abinda ta aikata dan Allah ka sanar dani" numfasawa ya yi sannan ya bata labarin abinda ya faru briefly. Ajiyar zuciya Ayrah ta sauke ta ce"toh akan wannan kake ta faman faɗa doctor macace fa dole daman ai maza su biyota musamman Fattum" wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce"Eh tunda ita mace akuyace da ake barinta sakaka ke kina kamar shekarunta aka fara barinki tsayawa da samari?" Murmushi ta yi ta ce"Allah ya baka haƙuri yallaɓai ni da wasa nake, saida na kammala secondary school na shiga University sannan Daddy ya fara barinmu" harararta ya yi ya ce"okay shine ita kike son abarta tun yanzu ko?" girgiza kai tayi ta ce"tuba nake dear" murmushi ya yi sannan ta fara serving nasa.












Tashi tayi duk idanuwanta a kumbure dalilin kukan data kusan kwana tanayi, a hankali ta sakko daga saman without making any sound ta fice daga parlon, ko kallon masu gadin gidan bata yi taje ta buɗe ƙofa tayi fitarta, cikin Sa'a ta samu wani napep ya shiga ɗaukan ƴan makaranta ta faɗa masa inda zata ya ce to tahau suka tafi.








Murmushi ta yi ta ce"kayi kyau sosai doctor" jan kumatunta ya yi ya ce"kema haka dear" dariya ta yi ta ce"mu tafi?" girgiza kansa ya yi ya ce" kirawo Fattum" haɗe rai ta yi sai kuma ta juya ta shige bedroom ɗin da take, kalle-kallenta ta gama ta fito tana kallonsa ta ce"dear bafa ta cikin ɗakin" da mamaki Jawaad ya ce"kamar ya?" ɗaga masa kafaɗa tayi alamar bata sani ba, da kansa ya shiga ɗakin dan tabbatar da gaske Fattomah bata ciki ɗin, tsaki ya yi sannan ya fita wajen masu gadi zuwa sannan hankalinsa ya fara tashi yana zuwa ya kalli gateman ɗin ya ce"kai ina kaga Fattum?" cikeda ladabi yake cewa" yallaɓai naga sanda ta fita ina yi mata magana taƙi kallona wajen 3hrs kenan" da mamaki Jawaad yake furta kalmar ta fita ɗin toh ina ta tafi da safiyar nan da sauri ya shiga motarsa Ayrah ma ta shiga sannan suka bar gidan.










*Nanameera ce#*
*Ameenatou ce#*




*Like nd share*[5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH*


MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.






PAGE 19-20.






A hankali yake ƙarewa farfajiyar gidan kallo wacce ta kasance iya ganinka sosai ya yi mamakin ganin fadawa a wajen kenan mai martaba yazo???, kama hannun Ayrah ya yi wacce itama take kalle-kallenta suka shiga cikin gidan. Zama ya yi aƙasa bayan sunyi sallama cikeda ladabi ya gaida iyayen nasa kallona Uncle Kabeer ya yi ya ce"son meyasa ka makara Faɗeemah ta ce kuna bacci ta tawo?" Jawaad ya ce"Eh wlh Abba naɗan tsaya yin wasu abubuwa ne shiyasa"okay ya ce sannan ya kalli Imad wanda tunda ya shigo bai ce komai ba ya ce"kaifa goga?" ɗan murmushi Imad ya yi amma bai ce komai ba, mai martaba ne ya yi musu addu'a sannan ya fara cewa


"Kamar yanda kuka sani mun tara wannan taron ne saboda sanar daku abinda ku baku saniba da kuma irin hukuncin da muka yanke a tsakaninmu"




Shiru kowa na parlon ya yi dan jin abinda zasu faɗa Uncle Mukhtar ne ya cigaba da faɗin




"Kunsan yaya zai bar garinnan zuwa Friday sannan kuma Fattomah tana karatu cikin garin nan bazai yiwu ya tafi da ita ba saboda haka muka yanke shawarar zata zauna gurin ɗaya daga cikinku wanda kuma Imad kaine wanda zata zauna cikin gidanka"




Da wani irin expression Imad ya ɗago kai yana kallon Uncles ɗin nasa ba shi kaɗai ba harda su Adda da Fulani Jawaad kuwa mutuwar zaune ya yi, kasa magana Imad ya yi amma banda tafarfasa babu abinda zuciyarsa ke yi baya jin zai iya zama gida ɗaya da wannan mara hankalin yarinyar ba wacce batada nutsuwa ko kaɗan cikin lamuran rayuwarta tabbas saidai idan ta zauna gidan Jawaad amma ba nashi gidan ba, gyaran murya mai martaba ya yi sannan ya cigaba da faɗin




"Kasan kuma bazai yiwu ace anbar yarinya budurwa ta zauna cikin gidanka ba kuma ba muharramar kaba tabbas anyi ganganci bawai dan ba'a yarda da kai ba a'a saboda ita rayuwa abar tsoro ce za'a iya zuwa mas'asal da ake buƙatar muharraminta awajen kuma babu, saboda haka muka yanke shawarar aura maka ita yanda duk abinda zai je ya dawo babu tashin hankali ko fargaba aciki"






Wata irin zabura Imad ya yi ya miƙe tsaye yama kasa magana sai riƙe gefen zuciyarsa da yayi ba shi kaɗai ba hatta Jawaad Saida ya mike tsaye baisan yaushe ba kuma baisan meyasa ba kawai yaji wasu zafafan hawaye na gangarowa kan fuskarsa, kallonsu kawai iyayen sukayi da rashin fahimta, sosai parlon ya yi shiru kamar ba'a taɓa hallitar mutane cikinsa ba sai Imadudden da yake ta sauke ajiyar zuciya har sannan kuma bai zauna ba. Daddy ne ya kalli Jawaad ganin yanda yake kuka kamar ƙaramin yaro yasa ya kamo hannunsa zama Jawaad ya yi yana kallonsu kamar wani zararre Daddy ya ce"Jawaad meya faru?"kallon Daddy ya yi sai kuma ya fashe da kuka kamar ba shiba ya ɗora kansa kan cinyar Daddy yana kukan, da mamaki kowa yake kallonsa banda Mommy wacce daman tasan kwanan zance kwata-kwata basu yanke abinda ya kamata ba domin Jawaad shine wanda yafi dacewa da Fattomah ba Imad ba dukda tanason Fattomah ta kasance surika awajenta amma tasan bazata samu farin ciki ba indai tana tare da Imad dan ba tun yau ba ya nuna zallar ƙiyayyarsa ga yarinyar. Shafa kansa Daddy ya shiga yi dan yasan tunda har Jawaad ya zubar da hawayensa to tabbas abune mara daɗi ya sameshi, ita kuwa Ayrah da idanu ta bishi tama rasa murna zatayi ko baƙin ciki








Mai martaba ne ya ce"wai Jawaad mene haka wannan wane irin abune mene yake damunka?" a hankali Jawaad ya fara rage kukansa amma har sannan bai ɗago fuskarsa ba Daddy ne ya ce"kai kuma akanme kake tsaye kan mutane?" A fusace Imad ya ce






"Daddy wallahi bazai yiwu ba, ni bazan iya zama da wannan yarinyar matsayin wata matata ba banida wani interest nayin aure yanzu kuma koda zanyi auran to ni ban shirya auran ƙaramar yarinya ba bazan iya wahala ba banida wani feeling akan yarinyar kuma kunsan bazanyi abinda zan cutar da rayuwata ba banasonta kuma bazan taɓa sonta ba domin ita bata dace dani ba nima kuma ban dace da ita ni ba ajinta bane ni Imadudden Ibraheem Baira nafi ƙarfin auran wannan yarinyar shi dayake da buƙata kuma ya nuna yanaso kuna iya bashi aurenta amma ni.......har abada!!"










Yanda yake huci yana maganar yasa duka suka zuba masa idanu suna kallonsa duk sunyi mamaki banda Daddy wanda daman yasan hakan zata iya kasancewa domin ya daɗe da lurada yanda yake mu'amala da yarinyar cikin gidan kuma yasan halin Imad da mugun taurin kai ga kafiya kamar mutanen farko koda yake barewa batayi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba dan shima Daddy number 1 ne wajen kafiya da gaddama. Uncle Kabeer ne ya ce rai a haɗe"ba shawararka muke nema ba Imad umarni ne kuma dolenka kayi biyayya ko kanaso ko baka so"






Bai ce komai ba kuma har sannan bai zauna ba sai wani irin numfashi yake saukewa kamar wani zakin da yake a yunwace danma sun raina masa hankali shine sai shi zasu bawa auren yarinyar da ko a hanya baya fatan haɗuwa da'ita bare kuma ya zauna da'ita gida ɗaya matsayin matarsa never!!!








Mai martaba ne ya ce anutse"Imadudden!" kallonsa Imad ya yi cikeda girmamawa ya ce"na'am Dad" da hannu ya yi masa alama da yazo ya karaso gabansa ya tsuguna kallonsa ya yi cikeda tausayawa ya ce"mene matsalar?" ajiyar zuciya ya sauke ya ce




"Dad wallahi bana so bamu dace da juna ba amma shi Jawaad yana matuƙar ƙaunarta dan Allah Dad ku mayar da auran kansa please ban shirya ba wlh" shafa kansa Mai martaba ya yi ya ce"ƴar uwarka ce Imad kuma munyi la'akari da cewa kaine kafi buƙatar mace ba Jawaad ba kaine kake da buƙatar second wife dan kamar wanda bashida mata haka kake kuma Fateema yarinyar kirki ce marainiya idan ka kula da rayuwarta Allah zai kula dakai kaima" girgiza kai Imad ya yi ya ce"Dad wallahi banajin zan iya domin zuciyata zafi yake min idan ina tuna cewa wannan yarinyar matsayin matata take ko a mafarki bantaɓa tunanin haka ba ko Jawaad daya nuna yana so banyi supporting nasa ba why yanzu kuma abun zai ƙare akaina Da?, wlh banason auren yarinya" murmushi mai martaba ya yi ya ce"itama yarinyar watarana girma zatayi sannan duk abinda ka ɗorata shine wanda zata aikata maka yarinya tafi daɗi wajen sha'anin aure kayi tunani Imad" shuru Imad ya yi badan ya gamsu da abinda mai martaba ya faɗa masa ba saidan bayason yawan jayyaya da iyayensa, Fulani ce ta ce"nikam dan Allah yaya idan abun zai zama faɗa kawai a haƙura" wani kallo uncle Kabeer ya yi mata ya ce"ku daman mata ai ƙaramin tunani ne daku karki sake cewa komai amaganar nan" shiru ta yi batace komai ba.








Daddy ya ce"shikenan Imad kanason yarinyar nan ko baka sonta?" kallonsa Imad ya yi da idanunsa wanda suka canza launi ya ce"wlh Daddy bana sonta" jinjina kai Daddy ya yi ya ce"good, yanda kace haka za'ayi an rigada an ɗaura muku aure saboda haka dole sai ka saketa"




Shiru duka suka yi suna sauraren maganar yayan nasu tunda suka ji ya magantu tofah tabbas akwai abinda hakan zai haifar kuma daman bada son ransa suka ɗaura musu auren ba




"Zan raba auren dake tsakaninka da'ita amma bisa sharaɗi guda ɗaya" da sauri Imad ya ce"na amince koma mene ne Daddy zanyi"girgiza kai ya yi ya ce"ka fara tsayawa kaji abinda zance, zan bar garin nan ita kuma yarinya anan take karatunta kuma ta kusa ƙarasawa babu buƙatar a tsayar mata da karatu saboda haka Faɗeematoh zata zauna wajenka cikin gidanka a matsayin yarinyar da kake riƙo daga nan har zuwa sanda zata kammala karatunta wanda yanzu ya kasance watanni uku nan gaba har sanda wannan lokacin zai cika bazaka saketa ba daga ranar da suka gama jarrabawa zan aiko a ɗaukar min ita shikenan daga nan sai ka saketa" gorar ruwan da take gefensa ya ɗauka ya buɗe saida ya kusa shanyewa sannan ya ajiye ya cigaba da faɗin




"Har zuwa sanda zan karɓeta zata zauna matsayin ƴar riƙo wacce zaka kula da rayuwarta matsayin ƴar uwarka banason jin wani tashin hankali ko wata magana tsakaninku Fattum batasan da wannan maganar ba kuma ba zata sani ba" kallon Jawaad ya yi wanda har sannan yake kwance kan cinyar Daddy ya ce"karka damu Jawaad nayi maka alƙawarin auren Fateema indai ina raye kuma kaima kana raye da zarar ta kammala secondary school zan ɗaura maka aure da'ita karka damu kanka kaji" sanin indai Daddy ya faɗi magana sai ya cikata yasa Jawaad goge hawayensa ya ce"thank you Daddy"shafa kansa Daddy ya yi ya ce"Allah ya yi maka albarka" Ameen kowa na parlon ya amsa.






Mai martaba ya ce"Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi"Ameen suka amsa sannan ya kalli Imad ya ce"ka yarda da wannan hukuncin?" gyaɗa masa kai y yi y ace"magana zakayi Babana" a hankali cikin sanyin murya ya ce"na yarda Dad zan barta cikin gidana har zuwa sanda zata kammala karatunta amma zan dawo da'ita kuma kome za'a ce bazan zauna da'ita na tsayin rayuwa ba domin ni bana sonta" murmushi Daddy ya yi ya ce"ba Saika cigaba da faɗa ba mu muna sonta muna ƙaunarta kuma bamu kyamatarta Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya"




Miƙewa Imad ya yi ya ce"zan tafi inada ayyuka" gaba ya yi kafin ya kai waje ya tsinkayi Daddy yana cewa




"Amma ka sani koda wasa naji wani abu bayan zamanta matsayin ƴar riƙo ranar zaka gane bakada wayo kuma bakasan kanka ba, ranar zan nuna maka the other side of me saboda haka take note" wani irin murmushi Imad ya yi sannan ya fice daga parlon. Daddy ne ya kalli Jawaad ya ce"tashi ku tafi kaji karka damu kamar yanda na faɗa maka Fattomah matarka ce in sha Allah"murmushi ya yi ya ce"tom Daddy nagode sosai Allah ya ƙara girma" Ameen ya ce sannan ya miƙe yana kallon Ayrah wacce ta cika ta batse ya ce"tashi muje" miƙewa tayi ko sallama bata yi musu ba ta fice daga parlon saida ya yiwa su Mommy Sallama sannan ya fita shima. Murmushi Uncle Mukhtar ya yi ya ce"Allah ya nuna mana wannan ranar" murmushi shima Uncle Kabeer ya yi ya ce"aikam ranar akwai kallo dukda nasan babu lallai ma su rabu" miƙewa Daddy ya yi ya ce"kamar sun rabu sun gama saidai idan bana raye amma sai Imad ya saki yarinyar" shuru sukayi jin ya yi magana mai martaba ya mike ya ce"zan koma Allah ya tsare hanya" okay Daddy ya ce sannan duka suka tashi kowa ya tafi Daddy ya kalli Mommy wacce ta dawo daga raka su Fulani ya ce"jeki kiramin Fattum"toh ta ce sannan ta juya ta fita










*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*






*Like nd share*
[5/13, 9:29 PM] Nanameera: *FATTOMAH*


MIKIYA WRITERS ASSOCIATION.






PAGE 21-22.




*Ameenatou I Ibraheem*


*Nanameera ce#*








Cikin yanayin na mutuwa Daddy ya fara cewa"Fateema zan bar garin nan ranar Friday kuma naso ace tare zamu tafi saida ke kinada makaranta kuma banason karatunki ya tsaya tunda har kinzo gangara, saboda haka zaki zauna gidan Imad har zuwa sanda zaki kammala karatunki daga nan zaki dawo wajena mu cigaba da rayuwa"




Hankali tashe Fattomah ta ɗago idanunta ta kalli Daddy lokaci ɗaya hawaye ya game kyakkyawar fuskanta bakinta na rawa ta ce"Da..Dad.Daddy dan Allah ka barni anan gidan zan zauna ni kaɗai ko gidan yaya Jawaad kaji Daddy" yanda tayi maganar dole ta baka tausayi hakan yasa Daddy ya taso ya zauna gefenta ya kamo hannayenta cikin nasa ya ce"Fattum kiyi haƙuri kinji ki ɗauki Imad matsayin yayanki na tabbata zai kula dake koda kuwa bakuyin shiri sosai bazai yiwu ki zauna gidan Jawaad bane da can zaki zauna sannan bana son zamanki a fada shiyasa bance Muhammad ya tafi dake ba kiyi haƙuri zaman wata uku kawai zakiyi daga nan zaki dawo kuma Imad bazai cutar dake ba muddin baki saɓa masa ba kinji" cikin kuka ta riƙe hannun Daddy ta ce"Daddy wlh tsoronsa nake ji dan Allah karka barni wajensa wayyoo Allahna Daddy" rungumeta Daddy ya yi ahankali yake faɗa mata kalamai masu kwantar da hankali wanda duk suka saka jikinta ya yi sanyi, saida yaga tayi shiru gabaɗaya sannan ya ɗago fuskarta ya goge mata hawayen ya ce"karki damu kinji zan dinga kiranki mu gaisa kuma Imad zai dinga kawo ki one's in a tym saboda haka you don't need to worry dear"jinjina masa kai tayi ya shafa kanta ya ce"good gurl Allah ya yi miki albarka" a hankali ta ce"Ameen Daddy" miƙewa ta yi Mommy ta ce"ki je ki shirya zuwa anjima zamuje super market sai a siyamiki abubuwan buƙata"toh kawai Fattomah ta ce sannan ta shige ciki. Zama Mommy ta yi tana kallon mijin nata ta ce"wlh ina tausayinta" kallonta Daddy ya yi ya ce"akanme kuma?" numfasawa ta yi ta ce"bata saba da Imad ba kuma kasan Imad ko mutum ya saba dashi toh fa yanada wahalar sabo sannan gashi ita kanta matar tasa bawani alaƙa ce mai kyau tsakaninsu ba kaga kuwa kullum zata kasance lonely" tashi Daddy ya yi ya ce"babu wata mafitar ne sai wannan dole hakan za'a yi" "Allah ya rufa asiri" Ameen ya ce sannan ya yi waje.








Tunda ta shiga ɗakin take kuka bata taɓa jin kewar iyayenta irin wannan ranar ba tabbas da suna kusada ita to makamancin wannan abun bazai faru da'ita ba, da yanzu tana wajen iyayenta suna rayuwa cikeda farin ciki kamar yanda suka saba kowane lokaci Allah sarki rayuwa batada tabbas ko kaɗan bata taɓa tunanin rayuwarta zata juye zuwa haka ba sai gashi cikin ƴan watanni komai ya koma upside down, tasan zamanta gidan Imad tamkar ƙarewar farin cikinta ne domin ko kaɗan baya ƙaunarta wanda take sa ran farin ciki daga gareshi yaya Jawaad ne kuma gashi ya juya mata baya haka tayi ta saƙe-sakenta har akayi sallar azahar sannan ta tashi ta shige toilet dan shiryawa. Kamar yanda Mommy ta ce haka ya kasance karfe biyar suka isa super market ɗin, siyayya sosai sukayi Fattomah tana tsaye wajen ɗaukan chocolate saboda ƙaunarta da'ita kamar daga Sama ta ji ya ce




"Nima ki siya mini man"




Aɗan firgice ta juyo idanunta suka sauka kan Kamal wanda yake kallonta da murmushi afuskarsa, sunkuyar da kanta tayi ya ce"sannu ya kike kwana biyu?" kallonsa ta yi amma bata ce komai ba ya sake cewa"I'm sorry rannar na saka anyi miki faɗa nasan kiyi haƙuri kinji" sai a sannan ta ce"babu komai" murmushi ya yi ya ce"me zaki siya?" kamar bazata yi magana ba sai kuma ta ce"chocolate zan ɗauka" "can i help you?"shiru tayi batace komai ba ya fara zaɓar mata chocolates ɗin masu matuƙar tsada ita kuwa Fattum tsayawa ta yi tana kallon ikon Allah juyowa ya yi suka haɗa ido ta tuntsire da dariya tsayawa ya yi yana kallonta ganin yanda dariya tayi matuƙar yi mata kyau tabbas

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login