Showing 39001 words to 39627 words out of 39627 words

Chapter 14 - FATTOMAH BOOK 1 by Nana Meera.txt

20 Dec 2024

2306

ɗaukota daga asibiti ba kamata ya yi......" Wasu maruka da Daddy ya yi masa ya sanya ya riƙe kuncinsa kafin ya yi magana Daddy yara magana cikin tsananin baƙin ciki da ɓacin rai


"Kai har kanada bakin magana?, har kanajin zaka iya zuwa ka tsaya a gabana Saboda bakada kunya kenan?, na baka yarinya amana kawai ka zauna da'ita na wata uku shine abinda ka kasa, har ka iya saka hannun ka dinga dukanta, ka zageta kaci mutuncinta duka bai isheka har ka iya yi mata ciki bayan lalurar daka sanya mata kuma shine yanzu ka iya takowa kazo nan wajen ko?"




Shiru Imad ya yi bai ce komai ba Daddy ya cigaba faɗin"wallahi idan har sunana Ibraheem Baira babu kai babu Fateema har abada babu wata alaƙa da zata haɗaku sannan cikin dake jikinta sai an zubar dashi a yau ba sai gobe ba kai kayi kaɗan ka raina min hankali ba'a haifi ɗa ba, zan nuna maka true colour na yanzu" afusace Imad ya kalli Daddy da duk sauran mutanen dake parlon sai kuma ya ce


"Daddy I'm sorry abinda ya faru zan kuma karɓi laifina duk inda za'a je amma wlh bazan taɓa yarda a zubar da abinda ke cikin yarinyar ba saboda daga shi bazan taɓa samun wani ba kamar yanda ka sani a baya yanzu ma haka take saboda haka na shirya karbar kowane irin hukunci amma banda na cire cikin dake jikinta I'm sorry"




Murmushi Daddy ya yi sannan ya ce"Okay mu zuba mu gani tsakanin ni dakai zan ga mai gaskiya" Mai martaba ne ya mike yana kallonsu ya buɗe baki zai magana, ɗaga masa hannu Daddy ya yi ya ce"babu ruwanka Muhammad banason kowa ya shiga maganar nan kowa ya yi shiru" shuru mai martaba ya yi dan tunda yaga Daddy ya yi haka to ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci kuma abune ma wuyaci ya sakko. Kallon Imad ya yi ya ce"banason ganin cikin gidan nan ina the next 10mins kabar gidan nan" Imad ya ce"I'm sorry Daddy zan tafi amma ka fara kirawon Fattomah saboda tare zamu.........." Wasu tagwayen maruka Daddy ya ƙara sauke masa a fuskarsa zuwa lokacin fuskar tayi jajawur saboda kasan cewar sa fari cikin zallar ɓacin rai Daddy ya ce




"Wlh na rantse da Allah baka isa ka ɗauki yarinyar nan ba har ƙarshen rayuwarka kuwa sannan kuma abinda ke cikinta tamkar an zubar dashi ne ka rubuta takardar saki ka turon kamar yanda na tsara"




Cikin zallar ɓacin rai Imad ya shige cikin bedroom ɗin Mommy, da kallo suka bisa har ya fito hannunsa riƙe da Fattomah wacce take kallonsa sai rarraba idanu take, yana zuwa ya kalli Daddy ya ce"I'm sorry Daddy zan tafi da'ita saboda she's under medication kamar yanda na faɗa ba zai yiwu abarta haka ba" gaba ya zo zai yi Daddy ya sha gabansa yana yi masa wani irin mugun kallo mai cikeda ma'anoni daban-daban ya ce".






*End of book 1*




*Shin mene ne abinda Daddy zai ce?*
*Shin wane hukunci zai yanke akan Imad?*
*Shin dagaske za'a zubar da cikin dake jikin FATTOMAH ko A'a?*
*Shin FATTOMAH zata auri yaya Jawaad ko A'a?*
*Shin da gaske Kamal zai aureta ko A'a?*
*Shin IMADUDDEN zai cigaba da zama da FATTOMAH ko kuwa za'a raba auren kamar yanda Daddy ya yi Alkawari?*
*Shin Ammi zata dawo Kano ko A'a?*
*Shin Aslaam zai auri FATTOMAH kamar yanda ya ci alwashi ko A'a?*
*Shin FATTOMAH zata haife ƴaƴan IMADUDDEN ko kuwa.....?*






*DUKA ZAKU SAMU AMSOSHIN TAMBAYOYINKU CIKIN LITTAFIN FATTOMAH💞 NA BIYU (2)WANDA YAKE KAN KUƊI NAIRA ƊARI BIYAR 500#*




*Zakuyi making payment ta wannan account ɗin 9086030007 Hauwa lawan opay digital service evidence via 09086030007 or 07041901078 Whatsapp only*


*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁENI TA WANNAN NUMBER 09086030007 OR 07041901078*






MUHAƊU A BOOK 2 DOMIN JIN YANDA ZATA KASANCE, TEAM FATTOMAH AND TEAM IMADUDDEN 💞💞.




*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login