Showing 6001 words to 9000 words out of 39627 words
sai nayiwa wannan yar taki duka tunda batajin magana" dariya tayi ta ce" aikuwa baka isa ka taɓa min ƴa ba sai dai can ku ƙarke amma ba duka ba" gyaɗa kansa ya yi ya miƙe yana gyara zaman t-shirt ɗin jikinsa ya ce" shikenan tunda kince haka ni zan tafi dan Daddy yana nemana" okay tace sannan ya juya ya fita.
Tsaye suke ƙofar makarantar tasu dan tashinsu kenan, Aysha ce ta kalleta ta ce" Nifa zanyi tafiyata wllh" marairaice fuska tayi ta ce" Ayyah bestie ki ɗan jira mana na tabbata suna hanya wlh banason abarni anan ni kaɗai nasan ke kaɗai zaki iya yimin haka please" ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta murmushi Aysha tayi ta ce" to kuka zakiyi ne?" tuntsirewa sukai da dariya atare kamar haɗin baki su kansu ba susan abinda suke wa dariyarba, wata ɓakar mota ce ta tsaya ƙirar Accord sport sai sheƙi take kana ganinta kasan bata ƙananun yara bace tsayawa kowa ya yi yana kallon motar ganin tunda tayi parking babu wanda ya fito kusan 2mins. Murmushi tayi ganin Jawaad ya fito daga motar yana nufo inda take, kallonsa tayi tana murmushi ta ce" yaya kai ne kazo ɗaukana?" gyaɗa mata kai ya yi yana rike hannunta bye bye tayiwa Aysha sannan tabi bayansa. Da sauri ta ja baya ganin kamar mutum daga ɗaya side ɗin mai zaman banza na motar
"Ki shiga baya Fattum"
Kallonsa tayi sai kuma ta buɗe back sit ɗin ta shiga, yana shiga ya tada motar suka bar harabar makarantar. Duk yanda Fattomah taso taga wanda yake gidan gaban kasawa tayi domin koda wasa bai yarda y juyo ba kuma bai ɗago fuskarsa ba har suka ƙarasa gida, yana gama parking ɗin ya ce" yawwa Fattum ki shiga gida za muje unguwa kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan a hankali ta sauka daga motar kamar me tsoron wani abu, shiga motar ya yi yay reverse yabar cikin gidan da kallo tabisu duka har suka ɓacewa ganinta ko wane wannan?????? abinda zuciyarta ta faɗa mata kenan ɗaga kafaɗarta tayi alamun ko'a jikinta sannan ta kama hanyar entrance ɗin shiga gidan..
*Manage this lover's abubuwan ne sun min yawa☹️☹️🥰*
*Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 08106571862*
*Kina sane da cewa free pages ya kusa ƙarewa ko kuwa A'a, kindly make ur payment sister 🤝🥰*
*Nanameera ce#*
[5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.
PAGE 9-10.
Kallonta Mommy ta yi ganin yanda take Kalle-Kalle ta ce" Fattum lpy?" Shafa kanta tayi ta ce"babu komai Mommy bari na cire kayana" daga haka ta haura sama, da kallo Mommy ta bita sannan ta girgiza kai, zama tayi gefen royal bed ɗinta tana sauke ajiyar zuciya hannayenta ta saka ta tallafi haɓarta tana tunane-tunane, ko waye wannan mutumin??, tsaki tayi tana cewa "ko ina ruwana ma oho" tashi tayi ta shige toilet dan gabatar da sabgar gabanta. Zaune yake kan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da parlon hankalinsa gabaɗaya yana kan system ɗin da yake dannawa yayinda Jawaad yake ta faman zuba da magana, kallonsa ya yi da lumsassun idanunsa ya ce" wai kai baka gajiya da magana?" murmushi Jawaad ya yi yana kallon abokin nasa kuma gudan jininsa ya ce" ina zan gaji da magana Imaad ma ya gaji da magana?" tsaki ya yi ya ce" Allah ya shiryeka kai kam" murmushi ya yi yana zama kusadashi ya ce" Footballer guda yana danna system" rufe system ɗin ya yi yana kallon Jawaad ɗin ya ce" mr talktive nifa na gaji da magana wlh ka tashi mu tafi gida" ok Jawaad ya ce sannan ya miƙe daidai lokacin wata mata ta fito daga cikin kitchen kallonsa ta yi ta ce" naga ka tashi?" Shafa kansa ya yi yana kallonta ya ce"wlh wai tafiya zai yi kinsan halin gogan" kwaɓe fuskarta tayi ta kalli Imaad ta ce" please yallaɓai ka zauna kaci abincin kaga na kammala" tashi Imaad ya yi yana murmushi ya ce" I'm sorry wani lokacin zanci kinji dear yanzu inason na tafi gida" shuru tayi na wasu sakwanni sai kuma ta ce" amma kasan ba haka mukayi dakai ba ko?" Dafe kansa ya yi ya ce" wayyo ni Imadudden na shiga uku da Ayrah shikenan naji zanci" murmushi tayi ta ce"yawwa ko kaifa bari na zubo muku" komawa tayi kitchen ɗin shi kuma ya zauna yana tallafar haɓarsa zama Jawaad ya yi gefensa ya tuntsirewa da dariya ya ce" yadai Footballer?" hmurmushi ya yi ya ce" wlh nifa babu macen da zata wahalar dani jifa yanda take shagwaɓa kana ƙoƙari" tuntsirewa ya yi da dariya harda riƙe ciki ya ce" shiyasa kenan matarka bata yi maka irin haka, dan baka samu wacce kake sobane wlh" tsaki Imad ya yi ya ce" kawai dan ina sonta saita dinga wahalar dani wlh bata isaba" girgiza kai ya yi ya ce" one day one time zakace na faɗa maka sai mace ta wahalar dakai fiye da tunaninka wuyarta ka samu wacce kake mutuwar so" numfasawa ya yi lokacin da Ayrah ke ajiye musu plates ɗin abincin kan Centre table ɗin dake tsakiyar parlon. Saida tagama jera musu tsaf sannan ta kallesu tana murmushi ta ce" yawwa yanzu ku sakko kuci abinci" ok suka ce sannan suka zauna dan cin abinci.
Kallonsa ya yi ya ce" bakaza shiga ba?" girgiza kai Jawaad ya yi ya ce"kasan nidai bana shiga harkar matarka coz batada kirki kawai kayi tafiyarka sai gobe yanzu zanje wajen Fattum ne saina wuce gida" wani irin kallo Imad ya yi masa ya ce" wace Fattum kuma?" harararsa ya yi ya ce" yarinyar da Daddy ya ɗauko fa munyi da ita zan rakata shopping mall"
"ƴar wace yarinyar?"
kallonsa y yi ya ce" nima bansani ba amma naje na duba baban nata Daddy ya ce ɗan uwanmu ne" okay Imad ya ce sannan ya ce" shine kai kuma kake shishshige mata?" dariya Jawad ya yi yana girgiza kai ya ce" bangane shishshige mata ba banason iskanci" shuru Imad ya yi ya ce" kai kasani, saida safe" ok ya ce sannan sukayi sallama.
Murmushi tayi tana rungumeshi ta ce"oyoyo dear sannu da zuwa" zameta ya yi daga jikinsa ya ce" thank you" shigewa ya yi ta bisa da kallo batasan mene ne matsalar Imad ba kwata-kwata bai iya soyayya ba ko kuma itace baya yiwa ohooo. Tsaye yake jikin dressing mirror ɗin dake kafe a bangon ɗakin sanye yake cikin wasu pyjamas blue colour sunyi matuƙar amsar farar fararta gashin kansa ya tufkeshi ya sakko har gadon bayansa sai a sannan na sake ƙare masa kallo Imad haɗaɗɗen matashin saurayine wanda yake ji da kuɗi da kuma kyau game da sarauta wacce take yawo cikin jinin jikinsu bashi da hayaniya ko kaɗan kuma bayason yawan magana ko cikin abokansa halinsa ya fita daban domin shi miskiline na gani kasheni kwata-kwata mata basa gabansa dan yarintar da yake aurema Daddy ne ya aura masa ita batareda saninsa ba, furzar da iska yayi daga bakinsa yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa sannan ya fito daga ɗakin.
Kallonta yake ganin yanda take ta nishaɗi, murmushi ya yi yana sake jin so da ƙaunar yarinyar cikin ransa da sauri ta tawo wajensa ta ce" yaya Jawaad kazo muce ka sha ice-cream ɗin akwai daɗi wlh" murmushi ya yi ya ce"nikam na yafe Fattomah dan Allah kiyi ki gama kinga dare ya kusa ya yi" kwaɓe fuska ta yi ta ce tana jan hannunsa " please Yaya kazo mujeeee" rasa abinda zai yi yasa ya bi bayanta tana murmushi, saida suka gama cin cake ɗin wanda Fattomah ta tilasta masa ya ci suka tafi, Kalle-Kalle ta shiga yi sai kuma ta ce" yayaaaa!" da sauri ya kalleta ya ce"lafiya Fattum?" langwaɓar da kanta tayi ta ce" ka siyamin kantu please" waro idanu ya yi ya ce" mene haka?" " gashi can waɗancen suna siyarwa" kallon inda take nuna masa ya yi ya ce" ok bari yazo nan" murmushi tayi ta ce" thank you yayana" murmushi ya yi ya ce" Allah ya shiryeki Fattum" dariya ta yi ta ce "Ameen yaya".
Wata irin shaƙuwa sukayi cikin yan lokuta ƙalilan ta saba da Jawaad fiye da tunani kulawa yake bata tamkar ƙanwarsa komai tace tanaso tofa sai ta samu duk inda yake saiya nemo mata haka ɓangaren Daddy da Mommy kulawa suke bata tamkar ƴar da suka haifa lokaci zuwa lokaci suke zuwa dubo Abbanta wanda ya samu sauƙi sosai amma asibitin basu sallameshi ba Saboda irin lalurarsa. Rayuwa take mai cikeda tsafta cikin Family ɗin sarki Baira mutum ɗaya ne wanda bazatace yana bata kulawa ba kuma daman bata damu dashi ba tunda batasan shiba, Imad baya shiga harkar kowa banda Daddy, Mommy, Jawaad sai uncles ɗinsa hatta matarsa ba wani shiga harkarta yake ba aƙalla yake shekaru 5 baya cikin ƙasar kasancewar professional footballer wanda ƙasar America ke ji dashi domin ya kasance asalin ɗan ƙasar dan ƙasar mahaifiyarsa ce da mutane kaɗan yake hira Kamar babu gobe ciki kuwa harda Jawaad wanda yake matsayin amininsa kuma ɗan uwansa domin Jawaad ɗan sarkin Kano ne. Shi kuwa Jawaad zuwa sannan babu wacce yake burin aure matsayin second wife ɗinsa sai Fattomah ya yarda zai jirata har tsawon sanda zata isa aure ya aureta domin yanada niyyar ƙara aure kuma daman su jininsu jinin auren mata ne.
Fitowa tayi tana dafe bango saboda wani ciwo da kanta yake mata, zaune ta tarar da Mommy tana kallo wani show da ake haskawa a Mbc max dan tana matuƙar ƙaunar dramar kallon Fattomah tayi wacce ta zauna daga ƙasanta tana runtse idanunta shafa kansa Mommy tayi taji zafi ta kalleta ta ce" subhanallahi Baby meya sameki?" kwaɓe fuskarta tayi ta ce" Mommy kaina ciwo yake min ki kiramin yaya Jawaad" langwaɓar da kai Mommy tayi ta ce" Ayyah sorry dear bari na kira doctor ya dubaki sai na kirawo yayan naki kinga maybe yanada ayyuka a office" fashewa tayi da kuka tana girgiza kai ta ce" A'a nidai yaya Jawaad nakeson ya dubani ki kirawon shi please" okay Mommy ta ce sannan ta ce" zauna anan toh bari na ɗauko wayata" gyaɗa mata kai tayi sannan ta kwanta kan three seater nan da nan bacci ya ɗauketa.
Kusan 5 missed call tayiwa doctor Amma bai ɗaga ba hakan yasa ta dawo parlon ta zauna dialing number Jawaad tayi amma itama bata shiga, tsaki tayi ta miƙe ta isa inda Fattum ta kwanta sake taba jikinta tayi taji har sannan zazzaɓin yana nan kamar ma ƙarashi akai, sallama ya yi yana shigowa parlon amsa masa Mommy tayi ya zauna kan kujerar yana kallonta ya ce" good afternoon Mommy" "katashi lpy?" "Alhamdulillah ina Daddy?" "baya nan" okay ya ce sannan ya kalleta ganin tana zaune gefen Fattomah shuru ya yi shikam baice komai ba ta ce" Imad please ka dubamin yarinyar nan batajin daɗi" kallonsu ya yi ya ce" what wrong with her?" "ciwon kai take" okay ya ce sannan ya miƙe ya isa gabansu, taɓa jikinta ya yi yaji yanda y ɗauki zafi hannunsa ya zame yaji ta riƙo hannunsa kallon fuskarta ya yi yaga arufe take cikin sambatun zazzaɓi ta ce" nikam ku rikeni zan mutu zafi yake mini wayyoo" kallonta kawai suke ya riƙe hannayenta ya shafa kanta ya ce" sannu" sake riƙe shi tayi ya kalli Mommy ya ce" zan tafi da'ita zuwa asibiti anjima in sha Allah zan dawo da'ita" okay Mommy ta ce sannan ya sunkuya ya ɗauketa tamkar Baby ya fice daga parlon.
Kai tsaye gidansa ya shige da ita lokacin Salma tana zaune kan kujera tana kallo dan shine kaɗai sana'arta sallama kawai ya yi sannan ya haye sama da kallo ta bishi dan ta taɓa ganin yarinyar time ɗin da taje gida gurin Mommy amma me ya kawo ta gidansu kuma harma ya yi mata irin wannan ɗaukar???, ƙawarda tunanin tayi daga ranta ta cigaba da kallonta. Wani ɗan ɗaki ya buɗe tamkar chemist haka yake komai na buƙatar asibiti akwai cikin ɗakin cikin gaggawa ya kwantar da'ita sannan ya sanya mata drip ya yi mata allura, ruwan sanyi ya ɗebo ya zauna gefenta ya dinga shafa mata nan da nan zazzaɓin ya sauka sakamakon Ac ɗin daya kunna da fan Saida yaga bacci ya ɗauketa sannan ya fito daga ɗakin, tsaye ya tarar da Salma tana ƙoƙarin shigowa ɗakin baya tayi tana kallonsa baice mata komai ba ya ratsa ta gefenta ya shige master bedroom ɗinsa. Tsayawa tayi wajen tana kallon hanyar da yabi amma ta kasa shiga ɗakin dan batasan me zata tarar ba, buɗe ƙofar tayi ta hangota kwance tana bacci numfasawa tayi Sannan ta juya ta sauka.
*Nanameera ce#*
[5/3, 4:22 PM] Nanameera: *FATTOMAH*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.
PAGE 11-12.
Buɗe dara-daran idanuwanta tayi tana kallon inda take kwance itadai tasan ba anan ta kwanta ba, buɗe ƙofar ɗakin akai yasa ta kalli ƙofar dan ganin wanda yake shigowa cikin sassarfa ya ƙaraso gare ta yana kama hannayenta duka biyun ya ce" ya jikin naki Fattum?" kwaɓe fuska tayi cikeda shagwaɓa ta ce" da sauƙi yaya, ina nake nan?" ajiyar zuciya ya sauke wacce shima bai san ya yi hakan ba ya ce" Allah ya ƙara lafiya ya kiyaye gaba Fattomah" shuru tayi tana kallonsa ganin kamar a dame yake ta ce" yaya ina Mommy?" murmushi ya yi ya ce" tana gida kema yanzu zamu tafi" "to ina muke nan?" dafe kansa ya yi ya ce" wayyo Fattum magana dai?, gidan Imad ne toh shine ya ɗauko ki" sosai taji gabanta ya faɗi dan harga Allah tsoro yake bata kwata-kwata batasan haɗa shirgi dashi lura da yanda ta tafi duniyar tunani yasa Jawaad ya ce" keeee!" a ɗan firgice ta ɗago tana kallonsa tana langwaɓar da kai ta ce" yaya kabani tsoro" yanda tayi maganar ne yasa shi tuntsirewa da dariyar da baiyi niyya ba murmushi itama tayi daidai nan Imad ya shigo ɗakin, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai yana zuwa ya zare mata drip ɗin hannunta batareda ya kalleta ba fashewa tayi da kuka dalilin zafin da taji shi kuwa gogan ko a jikinsa dan bama zaka ɗauka yana ɗakin ba
"Kayi mata a hankali mana"
Wani irin shegen kallo Imad ya watsa masa sannan ya cigaba da abinda yake, saida ya gama tass sannan ya juya yayi fitarsa bai sake bi takansu ba, riƙe mata hannu ya yi ya ce" sorry dear zo mutafi gida kinji zan siya miki abin daɗi" dakyar ya lallaɓata tayi shiru sannan suka fito daga ɗakin yana riƙe da hannunta. Babu kowa a parlon sai tv dake aiki hakan yasa kawai ya yi waje tana biye dashi, tsaye suka taddashi jikin mota yana magana da wani maid ɗinsa suna zuwa bai ce komai ba ya shige motar ya fuskanci abinda yake nufi yasa ya kalli Fattomah wacce har sannan bata wani jindaɗin jikinta ya ce" shiga baya kinji" gyaɗa masa kai tayi sannan ya buɗe mata backseat ɗin ta shiga shikuma ya shiga ɗaya side ɗin ya rufe motar, bakinsa ɗauke da Bismillah ya yiwa motar key suka bar gidan.
Saida sukayi nisa sosai sannan Jawaad ya ce" wai yaushe ne zaka koma America?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" randa Ubangiji ya hukunta" murmushi Jawaad ya yi ya ce" tom Allah ya yarda" lumshe idanunsa ya yi dalilin wani uban traffic da aka haɗa ahanyar, kusan 5mins kafin su samu su shige daga wajen yana shan kwanar round about ɗin ya ce" nikam halin ƙasar nan na ɓatamin rai komai babu tsari abunfa it's too much" dariya kawai Jawaad ya yi ya ce" dole kaga haka tunda ka daɗe rabonka da ƙasar amma da kasa ba zakaji ba komai ba" tsaki Imad ya yi ya ce" Allah ya kyauta" "Ameen".
Da sallama suka shiga ɗakin yana kallon yayan nasa, zama ya yi gefensa yana kallonsa ya ce" yaya ya jikin naka?" gyaɗa masa kai kawai Abba ya yi domin yanda jikinsa ya yi zafi ko magana ma ya gagara ya yi, tashi Daddy ya yi ya ƙarasa wajensa yana zuwa ya rike hannunsa cikin rauni da kuma dashewar murya yake cewa" kulamin da Faɗimatoh ka aurar min da'ita inda zata samu kwanciyar hankali ka riƙe mini ita amana karka bari wani abu mara kyau ya samu rayuwarta ina matuƙar ƙaunarta dan Allah ka cigaba da kulawa da rayuwarta daga inda na tsaya na tabbata Faɗima bazatayi maraiciba indai kana tare da'ita kuma...... Salƙafewa maganarsa tayi lokaci ɗaya ya hau wani irin tari kamar zai fasa ƙirjinsa, da sauri duka suka taso sukayo kansa Daddy Kabeer ne ya ce" sannu kaji yaya Allah ya baka lafiya" ƙam Abba ya rike hannunsa yana magana dakyar ya cigaba da faɗin"dan Allah ku riƙe min Fateema amana ku aurar min da'ita inda za'a kula da rayuwarta domin na sani yarinyar tanada rauni kuma bataji amma tanada tarbiyya daidai tata dan Allah ku tai....... tai. La'ilaha illallahu Muhammadu rasulullahi Sallallahu alaihi Wasalla.."
"Doctor!!! Doctor!!! Doctor!! Yaya!! Yaya!!"
abinda Daddy yake faɗa kenan yana jijjiga ɗan uwan nasu hankalinsa ya yi matuƙar tashi Ammi kuma mutuwar tsaye tayi dan tama kasa ƙarasawa inda yake, da sauri likitocin suka shigo suka rufa akansa hakan yasa su Daddy suka fito daga ɗakin jikin kowa asanyaye sai addu'a suke a zuciyarsu, kusan 35mins sannan likitocin suka fara fitowa, da sauri Daddy ya tafi yana zuwa ya riƙe wani doctor ya ce "ya jikin nasa?" kallonsa kawai doctorn ya yi sai kuma ya ce"I'm sorry sir mun rasashi Allah ya karɓi abinsa saidai haƙu..... bai tsaya sauraren abinda zai ƙarasa faɗa ba ya shige ɗakin da sauri turus ya yi ganin Abba kwance sun rufe masa fuskarsa jikinsa na wani irin kyarma ya ƙarasa gabansa yana zuwa ya riƙe hannunsa a hankali ya zame gyallen, kifa kansa ya yi akan jikin Abba ya na hawaye rabonda ya zubarwa hawayensa har ya manta sai yau dalilin mutuwar Abba tabbas Abba ya yi kyakkyawan ƙarshe sai fatan Allah Ubangiji ya jiƙanshi da Rahama 🤲🤲.
Convey ɗinsa ne suka fara shigowa sannan suma suka shigo lokacin Fattomah na kitchen tana taya