Showing 3001 words to 6000 words out of 39627 words

Chapter 2 - FATTOMAH BOOK 1 by Nana Meera.txt

20 Dec 2024

2294

gefen Ammi tana kallon Abbanta wanda idanunsa suke a lumshe juyawa tayi kuma tana kallon manyan mutanen da suke zaune kan tabarmar suma kana ganinsu kasan masu arziƙine kuma jinin sarauta kowanne sun yana ji da kansa kuma ba yara bane domin Zasu iya girman Abbanta dukda kasancewarsa mai yawan shekaru, sunkuyar da kanta ƙasa tayi dan ita bata gane mene ne abinda yake faruwa ba kuma batasan wnada zai mata bayani game da hakan ba, tsinkaya tayi yana cewa






"Wannan ita ce yarinyar taka?"




Gyaɗa masa kai Abba ya yi har sannan kuma idanunsa a rufe suke ita kuwa Fattomah kallo kawai take binsu dashi ya ce" ya sunanki?" "Fattomah" ta bashi amsa a taƙaice"Masha Allah nice name dear" shuru tayi ta juya ta kalli Abbanta sai a sannan ta ce


"Abbana mene ne ya sameka?"


Riƙe hannunta ya yi cikin nasa yana magana da kyar ya ce" Faɗimatoh ki kula da kanki kinji ki riƙe tarbiyarki ki zama mai jin magana ga kowa ki daina rashin jin magana dan Allah Faɗimatoh" bakinta na rawa ta ce" Abbana bazan sake ba kaji kayi haƙuri wlh Adda ce tace saina kwana amma ban ƙarawa" tallafo fuskarta ya yi ya ce ahankali kuma cikin rauni" bakiyimin laifin komai ba Fattomah Abbanki yana matuƙar ƙaunarki kuma yana son ki kula da rayuwarki kinji" gyaɗa masa kai kawai ta iya dan duk ta rikice ganin haka yasa ɗaya daga cikin mutanen wanda ba shine ya yi mata magana ba ya ce"inaga zamu tafi da ita sai ta zauna a gidana" da sauri ta kalleshi amma ta kasa magana dukda tanajin babu inda zata iya tafiya tabar Abbanta a wannan halin duk inda yake toh itama nan zata zauna.








Kiran sallar la'asar da akayi yasa ya ce" yanzu idan mun idar da sallah za'a koma asibitin in sha Allah" gyaɗa masa kai Abba ya yi sannan ya yi waje suka bishi abaya, wajejen ƙarfe 6:45pm aka fito dashi daga ward ɗin bayan an bashi ɗaki Fattomah na zaune gefensa sai Ammi wacce duk ta fice hayyacinta cikin lokaci kaɗan, cikeda damuwa Fattomah ta ce




"Ammi wai mene ne ya samu Abbana?" Kallonta Ammi tayi ta ce"nima bansani ba Fattum kawai gani nayi anshigo dashi wai awajen aikinsu ya akaga ya waɗi shine fa yasa na kirawo masa Hakeem sai kuma naga waɗannan mutanen sunzo ashe sune yayyensa wanda suka banzatar da rayuwarsa Saboda bashi da kuɗi amma a zahiri suma ba su suka aikata ba iyayensu ne shine suka zo suka kaishi asibiti hankalina ya tashi sosai Fattomah" ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Allah ya bawa Abbana lafiya" Ameen Ammi ta amsa mata. Tana idar da sallar magrib ta sauko daga benen kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Abba ta nufa babu ruwan kowa da kowa a cikin asibitin kasancewarsa asibiti mai tsada duk wani abu da kake buƙata tun daga mai jinya har wannan yake kulawa dashi zasu baka dan yafi wasu gidajen, tana shiga ta tarar da mutanen ɗazu su uku juyawa tayi zata fita ya ce"zo nan" batare musu ba ta komo da baya tana zuwa gabansa ta tsuguna tana kallon ƙasa, murmushi ya yi ya ce"meyasa baki shigo ba Fateema?" sunkuyar da kanta ƙasa tayi ya cigaba da faɗin" daga yau ki ɗauke mu matsayin iyayenki domin mahaifinki ɗan uwanmu ne I'm General Ibrahim Baira shikuma wannan Dr. Mansur Baira sai kuma Dr. Kabeer Baira muɗin mun kasance yaya ga sarkin Kano His highness Mukhtar Baira wanda yanzu Allah ya yi masa rasuwa yanzu haka ƙanina shine wanda yake matsayin sarkin Kano na wannan lokaci kuma mun kasance Cousins ne da Abbanki saboda haka muma ki ɗauke mu tamkar Abbanki kinji" jinjina masa kai tayi ta ce"toh Abba" shafa kanta ya yi ya ce"Allah ya yi miki albarka dear" Ameen ta amsa sannan ta tashi a hankali ta fita.






*Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 09121033575 or 08106571862 WhatsApp only*




*Fattomah*


*Nanameera ce#*


*Idan har kin karanta to kiyi sharing ɗinsa sister*
[5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH*




MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.








*Nanameera*


PAGE 5-6.




Wajen ƙarfe 9pm suka shigo ɗakin saida likita ya sake duba shi sannan ya fita kallonta Daddy ya yi ya ce" Fateema taso mu tafi" da sauri ta ɗago tana kallonsa amma ta kasa cewa komai murmushi ya yi ya ce" gidana zan tafi dake kinji" sunkuyar da kanta ƙasa tayi Ammi ta ce"tashi kuje" tashi tayi tana sake juyowa tana kallon iyayennata haɗa ido sukai da Abba ya gyaɗa mata kai hakan yasa taji ɗan sanyi cikin ranta, sallama suka yiwa su Abba sannan suka fito suma, tsaya suka tadda ita gefen wani ɗaki tayi shiru da alama wani abun take tunani kallonta Daddy ya yi ya ce" Fateema me kike tunani haka?" girgiza masa kai tayi ya ce"tom muje" gaba ya yi tana biye dashi abaya har suka ƙaraso wajen da aka jere motocin nasu saida sukai sallama da ƴan uwansa sannan ya ce tashiga motar shima ya shiga.






Cikin unguwar tudun yola ɓangaren satellite town gidan yake gidane iya ganin ka wajen girma da kuma haɗuwa kana ganinsa kasan da kuɗi aka gina gidan ko'ina na gidan zagaye yake da securites wanda zai tabbatar maka da babban mutum ne mammalakin gidan, a parking lot ɗin gidan sukayi parking sannan suka fito banda kallo babu abinda Fattomah takeyi domin tunda uwarta ta haifeta bata taɓa ganin gida ma girma da kyau irin wannan gidan ba idan ba sani kayi ba to tabbas za'a iya ce maka a ƙasar waje ne kuma ka yardar domin ginin gidan ba irin na ƙasar nan bane, sosai ta shagalta da kallon gidan dan batasan sanda Daddy ya ce mata ta shiga ba lura da ba saurarensa take ba yasa ya ce"Fattomah me kike kalla?" saurin ƙasa tayi da kanta dan saida taji kunya murmushi ya yi ya ce" kibari idan Allah ya kaimu da safe sai kiga ko'ina na gidan kinji" gyaɗa masa kai ta yi ya kama hannunta suka shiga ƙofar entrance ɗin parlon wacce itama kaɗai abar kallo ce, babu kowa a parlon sai sanyin AC dake tashi tare da wani daddaɗin kanshi ko'ina tsaf kamar a zubar da abinci a ƙasa ka ci ganin ta tsaya a tsaye yasa ya ce"zauna mana" a hankali kamar me tsoron wani abu ta zauna gefen royal cusion ɗin dake zagaye da parlon zama shima ya yi not to long ta fara jin ƙara saukowa daga kan stairs da sauri ta juya tana kallon matar da take sakkowa farace tass kuma doguwa kana ganinta kasan ba bahaushiya bace domin tafi kamada ƴan yankin saudia arabia murmushi ɗauke a fuskarta take kallon Fattomah har ta ƙaraso tana zama kan kujerar dake gefenta mijin nata ta ce" wannan ce yarinyar?" gyaɗa mata kai Daddy ya yi tace "Masha Allah she's beautiful" murmushi ya yi ya ce" sosaima naga kamar kunyarmu takeji" kwaɓe fuska ta yi tana kallon Fattomah ta ce mata" haba daughter ki ɗauka nan gidanku ne kuma mune iyayenki kinji karki wani ji kunyarmu koda yake nasan ma zaki saba nan bada jimawa ba" shuru Fattomah tayi tana wasada fingers ɗinta, tasowa Mommy tayi tana zuwa gabanta ta tallafo fuskarta tana sakar mata murmushi ta ce" taso muje ciki ko" murmushin itama ta mayar mata sannan ta miƙe tana kama hannunta suka haura stairs ɗin gidan.






Kallon ɗakin Fattomah take Saboda yanda ya haɗu ya yi kyau har ya gaji komai na ɗakin purple and white ne sai tashin ƙamshi yake kallonta ta yi ta ce" yawwa sai kiyi wanka ki shirya akwai wasu kaya da aka kawo ɗazu ki sanya sannan sai ki fito kici abinci" gyaɗa mata kai tayi sannan ta ce"tom" shafa kanta ta yi ta ce"gud gurl" sannan ta juya ta fita. Kayanta ta cire sannan gas shige toilet ɗin dan yin wankan kamar yanda Mommy tace mata, kusan 3omins sannan ta fito daga toilet ɗin tana zuwa ta tsaya jikin dressing mirror ɗin dake maƙale a ɗakin tana kallon fuskarta murmushi ta yi sannan ta hau shafa mayukan data gani ajiye a wajen, tana gamawa ta buɗe wardrobe ɗin data gani a hankali ta dinga kallon duka kayan ciki kana ganinsu kasan they're expensive yawancinsu duk abayas ne sai riga da wando saida tagama dube-dubenta sannan ta ɗauko wata Turkish abaya black colour ta sanya komawa tayi gaban madubin ta kalli fuskanta sosai abayar ta haskata farinta ya fito sosai duk da ita ba fara can bace veil ɗin abayar ta saka ta ɗaure kanta sannan ta fito daga cikin ɗakin tana ƴan kalle-kallenta, murmushi Mommy tayi ganinta tana sakkowa daga benen tabbas Fattomah kyakkyawa ce dukda kasancewarta yarinya zaka fahimci hakan kuma tanada dirin halitta irin wadda wata ƴar shekara 20 ɗinma bazata fada mata ba komai nata cikin nutsuwa take gabatar dashi sannan kuma ga kunya wacce daman ita gadonta ce, lumshe ido Mommy tayi haka kawai taji wani tunani ya kawo zuciyarta ko hakan zai yiwu??????








Sallama Fattomah tayi ganin kamar hankalinta baya wajen, kallon Fattum tayi sai kuma tayi murmushi ta ce" sorry kinji" girgiza kanta tayi ta ce" babu komai Mommy" tashi tayi ta ce" bari nasa akawo miki abinci kici kinji" jinjina kanta tayi sannan ta zauna kan kujerar tana kallon wani movie da ake haskawa a Bollywood.






Mamaki ne ya ishe ta ganin yanda ake kawo abinci kala-kala tana tunanin itadawa zasu waɗannan abincin wnada ya isa mutane biyar su ci su ƙoshi, saida aka gama jerasu kan Centre table sannan Mommy ta fito kallonta ta yi ta ce" A'a Fattomah me kike jira naga baki fara cin abincin ba?" Murmushi ta yi ta ce" babu komai Mommy" girgiza tayi ta ce" ki saki jikin ki please I'm ur Mom ok?" gyaɗa mata kai tayi ta ce" yanzu kigama cin abincin sai muyi magana" daga haka ta shige sama, da kallo Fattomah ta bita sannan ta juyo ta kalli abincin gabanta.








Juyi kawai take kan makeken royal bed ɗin amma bacci ya gagari idanunta tunanin Abbanta kawai take ko wane irin hali yake ciki??? wannan tunanin yasa ta kasa Bacci domin da tana kusadashi dole zataga yanda yake da jikin amma yanzu babu wannan damar wannan tunanin ne yasa ta fashe da kuka ita kaɗai, saida tayi mai isarta sannan ta miƙe ta shiga banɗaki ta wanko fuskarta sannan ta ɗauro alwala prayer mat ta shimfiɗa ta sanya wani hijab ta tada sallah dan neman sauƙi wajen Ubangiji.






Da sassafe Mommy tazo ta tasheta dan Daddy ya ce zata makaranta shiryawa tayi cikin sabon uniform ɗinta wanda batasan sanda aka ɗinka mata ba tana fitowa ta zauna breakfast not too long kuma driver da guard suka tafi rakata makaranta, da mamaki kowa yake kallon Fattomah bayan ta fito daga cikin motar domin kowa yasan a keke napep take zuwa makaranta yau kuma a mota harda masu tsaronta bayan sun shiga aji Aysha ta ce" wai Fattum wane ya kawoki yau?" tsaki tayi ta ce"nikam kinsan banason munafurci ko?, sai shegen gulma kuka ajiye to yayan Abbana ne shikenan" murmushi Aysha ta yi ta ce" toh hajiyar bala'i daga tambaya" "Eh kema kinsan banason irin haka ay" shiru sukai duka dalilin malaminsu daya shigo.






Ganin yanda tayi shuru yasa Mommy ta ce" Fattomah lafiya?" kwaɓe fuskarta ta yi kamar zatayi kuka ta ce" Mommy wajen Abbana nakeson naje" murmushi Mommy ta yi ta ce" keee Fattum ki bari sai zuwa gobe nima zani dubashi sai muje tare kinji ai Daddy ya ce min zai shiga wajen nasu" badan ranta yaso ba ta ce" Tom shikenan Allah ya kaimu Mommy" murmushi ta yi ta ce" Ameen ya rabbi".








Dariya Khaltum tayi tana kallon yayan nata ta ce" tab ɗijan yanzu yaya ka rasa wacce zakace kana so sai Fattomah tab wlh kuwa kana tare da wahala dan ka rigada kasan halinta kuma yanzu ma bata gida ɗazu Mama tace Ammi ta faɗa mata a asibiti" zaro ido ya yi ya ce" dan Allah ina ta tafi kuma?" "Wai yayan Abbanta ne ya ɗauketa tana gidansa a tudun yola" numfasawa ya yi ya ce" nikam babu ruwana dole sai naje inda Fattomah take domin har cikin raina ita ce wacce nakejin zan iya rayuwar aure da na daɗe inason yarinyar cikin raina bazan bari na rasata ba in sha Allah" kallonsa kawai Khaltum take dan ita batasan sanda ya koma haka ba shida magana ma bata damesa ba amma duk yabi ya rikice akan Fattomah, saida yagama fadar duk abinda yakeso sannan ta ce" yaya wlh ka cire ranka da Fattomah kaga yanzu ta koma gidan yan gayu kuma daman ita tafi kala da masu kuɗi idan kace zaka zira jiki ranka zai zo yana ɓaci abanza kawai kayi haƙuri ka rungumi Hafsarka itace take daidai dakai nidai a tawa shawarar" girgiza kansa ya yi ya ce "wlh bana daina son Fattomah ba har ƙarshen rayuwata kuma in Sha Allah sai na aureta ta zama mata agareni" rasa abinda zata ce masa tayi dan taga abin nasa ya fara sauka daga kan layi kuma duk irin shawarar da zata bashi ba ɗauka zai ba yasa ta ce" Allah ya taimaka yaya" miƙewa ya yi ya ce" Ameen Ameen shine abinda yafi dacewa ki faɗa" gaba ya yi ta bisa da kallo tana tausayin halin da yake ƙoƙarin sanya kansa.




Har wajen ƙarfe 10pm Daddy bai shigoba ita kuma taƙi kwanciya tana zaman jiransa babu yanda Mommy batayi da itaba tace ba bacci take jiba dukdan yadawo taji halinda Abbanta yake ciki, kallonta ya yi ganin yanda take bacci akan kujera kana gani kasan baccinne ya ɗauketa ƙarasawa ya yi gabanta yana kallonta sosai yaga tana bacci hakan yasa baiyi tunanin tashinta ba ya ɗauketa tamkar Baby ya shige da'ita saman.




Yana shiga ya kwantar da'ita sannan ya jamata duvet ya lulluɓeta addu'ar bacci ya yi mata sannan ya ƙaro gudun AC ya juya ya fita kai tsaye kuma ɗakinsa ya nufa.








*Fattomah isn't free it's 500# via 9086030007 Hauwa lawan opay evidence via 09121033575 or 08106571862 WhatsApp*




*FATTOMAH*




*Nanameera ce#*


IDAN HAR KIN KARANTA TO KIYI SHARING ƊINSA SISTER.[5/3, 4:21 PM] Nanameera: *FATTOMAH*


MIKIYA WRITER'S ASS.


BOOK ONE


PAGE 7-8.






Kallonsa Mommy tayi ta ce" babu yanda banyi da'ita ba amma taƙi yarda taje ta kwanta wai batajin bacci dukda nasan daman ta gaji" murmushi ya yi ya ce" Allah sarki kawai ta damune akan halinda mahaifinta yake ciki in sha Allah gobe zakije ki dubashi sai ki tafi da'ita" okay tace masa sannan ya shige toilet dan watsa ruwa. Kalle-Kallen inda ta kwanta ta hauyi dan ita dai tasan ba anan wajen tayi bacci ba hasalima batasan sanda ya yi bacci shuru tayi na wasu mintuna sai kuma ta sakkoda ƙafarta a hankali ta miƙe ta shige toilet ɗin, shiryawa tayi cikin uniform ɗinta ta fesa turare wanda har Saida ya fara yawa murmushi tayi ita kaɗai sai kuma ta ce" I'm Fine gurl" tuntsirewa tayi da dariya Ni kuwa nace Fattum anajida yarinta. Kallon wanda yake zaune a parlon takeyi har ta ƙara so ɗaga kansa ya yi aikuwa cikin sa'a idanunsa ya shige cikin nata saurin ɗauke nata idanun tayi tana sunkuyar da kanta murmushi ya sakar mata ya ce" Hello!" sunkuyawa tayi ta ce" ina kwana?" "Lpyklao ya kike?" tana zama kan ɗaya daga cikin royal cusion ɗin parlon ta ce" ina lafiya" shiru sukayi duka na rashin abin faɗe dan ita bata taɓa ganinsa ba kuma shima haka tsinkayar muryar Mommy sukai tana faɗin




" Jawaad yaushe ka shigo?"




Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce"kina can ciki Mommy daman banason na tashe kine that's why nayi zamana anan sai kuma naga wata baƙuwa" ya ƙarashe maganar yana kallon Fattomah, murmushi Mommy tayi ta ce" kai kam bakada dama toh ba baƙuwa bace cousin ɗinku ce" sake kallon Fattomah ya yi sai kuma ya kalli Mommy yana dafe kansa ya ce" sai yanzu na lura Mommy wllh tana kamada Family" zama Mommy tayi tana murmushi ta ce"kadai ji dashi, Fattomah kin ci abinci?" girgiza mata kai tayi Mommy ta ce" ok bari na saka akawo miki amma ki dinga shiryawa da wuri saboda lokaci kinga yanzu ma kusan 7:25am ne" Tom tacewa Mommy sannan ta cigaba da wasada fingers ɗinta.












Murmushi ɗauke a fuskarta ta ce" Abbana sannu kaji ya jikin naka?" Shafa fuskanta ya yi ya ce" nasami sauƙi Faɗimatoh ki daina damuwa kinji" goge mata hawayen fuskanta ya yi da hannunsa ta sakar masa murmushi, murmushin shima ya mayar mata ya ce a nutse "Allah ya yi miki albarka Faɗimah" "Ameen ya Allah Abbana".






Saida aka idar da sallar isha'i sannan suka baro asibitin wanda azahirin gaskiya bada son ran Fattomah suka baro ba dan tafi ƙauna zama wajen Abbanta da Amminta, murmushi Mommy tayi ganin yanda take ta cin magani a hanya suna zuwa wajen wani mall tacewa drivern ya tsaya, parking ya yi sannan ta kalli Fattomah ta ce" Baby zo muje ki rakani ciki" gyaɗa kanta tayi sannan Mommy ta kama hannunta suka fito Da motar dan shiga cikin mall ɗin, duk irin yanda take moody saida ta saki jikinta tana zaɓar duk abinda taga ya burgeta awajen domin Fattomah batada rufi indai abu ya yi mata tofa sai ta ɗauke shi har suka gama siyan duk abinda suke buƙata aka kai musu mota sannan suka shige gida.










Murmushi tayi ganinsa zaune a parlon da alama kallo yake yi zama tafi kan kujerar cikeda gajiyawa ta ce" washhhh!!" Kallonta ya yi ya ce" keee Fattomah yaushe kika gajin?" dariya tayi tana kallonsa ta ce" ayyah yaya Jawaad wllh nagaji sosaima" harararta ya yi ta gefen ido ya ce" babu wani nan"tuntsirewa tayi da dariya ta ce"kaga yanda kayi kyau kuwa yaya?" waro idanunsa ya yi yana kallonta dan yagama fuskantar raina masa hankali take ƙoƙarin yi ya ce" zan kamaki ne yarinya zaki gane ne" gwalo tayi masa lokacin tana hawa kan stairs ɗin benen ya kalli Mommy wacce take tsaye tana dariya ya ce" Mommy watarana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login