Showing 33001 words to 36000 words out of 39627 words

Chapter 12 - FATTOMAH BOOK 1 by Nana Meera.txt

20 Dec 2024

2305

murmushi ta yi ta ce"lafiya klao Adda kawai Abbana na tuna shiyasa" cikeda tausayawa Adda ta ce"ayyah Allah ubangiji ya jiƙan Ahmad" cikin asanyaye ta ce"Ameen ya Allah".






Har wajen ƙarfe 12am ba suyi bacci ba suna hira idan wannan ta faɗa sai wannan ta ɗauke a haka har baccin ya ɗaukesu banda Fattum wacce take jinta cikin wata duniya tabbas rashin iyaye babu daɗi duk irin abinda zaka samu idan har babu iyayenka tofah bashida amfani haka ba kowane zai ƙaunaceka saboda Allah ba dukda ƙanƙantar shekarunta amma ta naɗe wannan cikin kwakwalwarta, ba ita tayi bacci ba sai wajen 2am a haka ma ɓarawone ya saceta. Da safe bayan sun idar da sallar asuba suka fito tsakar gida Abla ce ta shimfiɗa musu tabarma suka zauna suna cigaba daga inda suka tsaya jiya, Adda ce ta fito jin hayaniyarsu ta ce"tunda kun tashi sai ku nemi abun dafawa, Faɗeema me kike so?" sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ta ce"Adda kunu nakeso da ƙosai please" murmushi irinna manya Adda ta yi ta ce"tom shikenan Khaltum ki tashi ki kunna wuta bari nima na fito"toh ta ce mata sannan ta koma ɗakin. Suna gama karyawa suka haɗa kwanukan wanke-wanke suka fara yanda suke yi da nishaɗi yasa basu wani ji wahalar aikin ba har suka gama gyara gidan wajejen 10am sannan suka koma bacci, da rana Adda ta dafa musu dambun shinkafa wanda yaji zogale Masha Allah Khaltum ce ta daka musu yaji mai daɗi suka zauna yanda suke cin dambun shinkafar ni kaina saida yawuna ya tsinke musamman Fattomah dan ba ƙaramin ci tayi masa ba dan saida ya fice kanta tsabar irin cin da tayi masa ni kuwa na ce ko dan saboda harta sammin ne☹️babu komai Imad namu zai bani nasan 😂.






For a good three days data zauna gidan Adda taji daɗi sosai ta dawo asalin Fattomahnta kafin Abbanta ya rasu rayuwa mai daɗi cikin gidan Adda da taimakon su Khaltum wanda koda yaushe take sake jin ƙaunarsu aranta, kasancewar ranar Friday ƙarfe 7am suka gama aikin gidan, suna zaune tana kallo wayar Khaltum, shiru tayi sai kuma ta ce"yau yaushe ne wai?" Khaltum ta ce"Friday ko kin manta ma" afirgice ta miƙe ta ce"nashiga ukuna!" miƙewa itama tayi tana kallonta ta ce"lafiya Fattomah?" a rikice ta ce"gida zan tafi yau Uncle zai dawo" da mamaki ta ce"wane Uncle kuma?" "Bazaki ganeba kawai tafiya zanyi" waje Khaltum tayi dan kiran Adda dan ita bata gane abinda Fattomah ke nufi ba.






Ahankali yake sauke ajiyar zuciya lokacin da motocin nasa suka fara parking cikin gidan, fitowa ya yi yana sanye cikin wata suit black colour gashin kansa atufke da ribom, sosai ya kara kyau da fari abinsa Salma ce ta fito cikin wata abaya black colour tayi kyau har ta gaji kana ganinsu kasan ahuce suke abinsu, da sauri ya ƙaraso wajen ya rungumeshi yana murmushi ya ce"welcome back I.I Imadudden" dariya ya yi ya ce"thank you bro fatan kana lafiya?" murmushi Jawaad ya yi ya ce"Alhamdulillah, ina Fattum kuma?" sakinsa ya yi ya ce"ai daman ba tare da ita na tafi ba ko ka manta exam take" da mamaki Jawaad ya ce"wai ita kaɗai ka bari cikin gidan nan?" gyaɗa masa kai ya yi Jawaad ya ce"amma kayi ganganci fa" murmushi kawai ya yi sannan ya ɗauko wata ƴar teddy bear milk da ratsin ja kallonta Jawaad ya yi ya ce"wowwwww amma tayi kyau doll ɗin wace?" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce "*FATTOMAH*" da sauri Jawaad ya kalleshi dan tunda suke bai taɓa jin ya ambacin sunan ba sai yau, murmushi ya yi ya ce"tsaraba ka siya mata kenan?" ya ce"Eh naganta ne a wani mall dana shiga shine ta bani sha'awa shiyasa na ɗaukar mata"okay Jawaad ya ce sannan suka shiga cikin parlon.








Saida suka huta sosai sannan ya ce"Salma ki ramin ita"okay ta ce sannan ta bar wajen, kusan 5mins sannan ta dawo tana kallonsu ta ce"bafa ta nan" ya ce"kamar ya?, have you check?" gyaɗa masa kai ta yi ya ce"to ina ne inda zata je da safen nan?" tashi ya yi zuwa apartment ɗinta Jawaad yana biye dashi, babu inda basu duba ba amma babu Fattomah babu ma alamun mutum yana zaune cikin ɗakin, da sauri ya fito zuwa compound ɗin gidan wani socket ya danna nan da nan jiniya ta cika gidan cikin 2mins duka maids ɗin gidan suka hallara, kallonsu ya yi ya ce"ina Fattomah?" shiru duka suka yi domin sai daga baya gateman ɗin yake faɗa musu cewa ta bar gidan, cikin faɗa ya ce




"Ina magana kuna wani kallona nace ina yarinyar dana bari cikin gidan nan dazan fita?" shiru duka suka sake yi sai boss ɗinsu ne ya fito a hankali ya fara magana kamar haka




"Sir daman yarinyar ta tambayi zata asibiti kamar yanda muka sanar dakai a sannan toh kafin ya koma ya tarar ta gudu tabar gidan kuma tun ranar bata sake dawowa ba"




Wani irin kallo Imad ya ke binsu dashi kafin ya kalleshi ya ce cikin ɓacin rai"daman haka shine aikinka?, abinda na ɗaukeka kayi kenan?, yanzu ku tsaya ta ina kuke son nafara neman ƴar mutane daga ina zan fara?, Ko kuwa yawo zan shiga cikin gari ina nemanta?, saboda rainin hankali data ɓata aka samun wanda zai kirani ya sanar dani for almost 4days bata gida amma shine kuke zaune hankalinku kwance kuna cin abinci ku kwanta" kwafa ya yi ya ce"wallahi I'll teach you a......" maganar ce ta maƙale masa dalilin Fattomah da yaga ta shigo hannunta riƙe da jaka, banda faɗuwa babu abinda gabanta keyi tasan yau ubangiji ne kaɗai zai hanasa ya kasheta tsabar duka, yanda zuciyarta ke rawa haka ilahirin jikinta ma ke rawa tama kasa kallonsa, Jawaad ne ya zo zai je wajenta Imad ya jawo hannunsa ya dawo baya har sannan kuma bai ɗauke idanunsa daga kanta ba.






Yanda kasan wani zaki haka yake tafiya toward direction ɗin inda take tsaye sosai bugun zuciyarta ya ƙaru tsananin fargaba da tashin hankali sune cikin idanunta tabbas tayi nadamar zuwa gidan Adda tayi wannan kwanakin batareda ta sanar dashi ba, hucin mutum da taji ya sa ta tabbatar da yazo gabanta runtse idanunta tayi ta tsuguna kan ƙafafunta tana haɗe hannayenta biyu alamar roƙo ta ce"








*Ameenatou ce#*
*Nanameera ce#*








*Like nd share**💞 FATTOMAH 💞*


*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*






*Ameenatou I Ibrahim*
Nanameera.






PAGE 40.
*END OF BOOK 1*




*This page naku ne Nanameera's Library ina matuƙar jin daɗin sharhinku akan FATTOMAH 💞 kuna tashin kaina da yawa, Imadudden yace a gaisheku kyauta 😂team FATTOMAH idan za'a yi abu a dinga yi dan Allah Maganar gaskiya mun fasa halartar zaman Court ɗin tunda abun haka ne bamu son tashin hankali shiyasa bawai tsoro muka ji ba💪idan kunje ku sanarwa da judge I.I Imadudden baya ƙasar nan bazai samu damar halartar zaman ba🙏 FATTOMAH na godiya da nuna soyayya Nanameera's Library tana ganin saƙon abun arziƙi kuma ba zata baku kunya ba in sha Allah 😂much luv both Imadudden and Fattomah team❤️❤️*






*Special thanks to my dearest friend Khadeejerth Sabi'u Yahya The Nainarh Kd ✍️ Ina matuƙar jin daɗin zamanmu tare🥰📚Allah ya ƙara haɗa kanmu✍️*










Hannunta Imad ya kama bai ce komai ba ya koma cikin gidan da sauri Jawaad ya biyo bayansa, bai ganshi a parlon ba hakan yasa ya tsaya nan yana ɗan zagaye parlon shikuwa Imad master bedroom ɗinsa ya buɗe ya zurata sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, cikin sanyin murya Jawaad ya ce"dan Allah kayi haƙuri karka yi mata hukunci mai tsanani please"




"Lokaci na shigewa"




Gaba Imad ya yi Jawaad yabi bayansa dan daman yasan ba lallai ya ɗauki abinda zai faɗa masa ba, har suka je gidan mai martaba suka dawo Imad bai ce komai ba kuma bazaka taɓa gane halin da yake ciki ba dan kai tsaye ba zaka ce ransa a ɓace yake ba haka bazaka ce farin ciki yake ba, tsayawar da drivern ya yi yasa Jawaad ya ce"dan Allah Imad kayi haƙuri nasan bata kyauta ba amma kayi la'akari da yarintar ta kar kace zaka mata hukunci da abinda yafi ƙarfin shekarunta dan Allah ka sassauta mata" kallonsa kawai Imad ya yi dan idan ya ce zai iya rabuwa da Fattomah shima yasan ya yiwa kansa ƙarya tabbas sai ya hukuntata hukunci mai tsananin gaske yanda koda nan gaba bazata taɓa yunƙurin aikata makamancin abinda ta aikata yanzu ba, numfasawa Jawaad ya yi ya ce"ko kuma muje na ɗauketa please idan yaso nan two days sai na dawo da'ita" wani kallon ka zama mahaukaci Imad ya watsa masa sannan ya ce"inada abubuwan da zan gabatar a gida dayawa please ka sauka" murmushi ya yi ya ce"wato korata kake?" gyaɗa masa kai ya yi dan yasan bazai masa ƙarya ba, murmushi Jawaad ya yi ya ce"shikenan sai anjima amma ina sake baka haƙuri yallaɓai" ko kallonsa bai yiba ya cigaba da danna wayarsa har ya sauka sannan drivern yaja motar.








Shuru Fattomah tayi bayan ta idar da sallar la'asar ɗin ita kaɗai take tunani dan batasan irin hukuncin da Imad zai mata ba bata taɓa tunanin zai rigata dawowa ba da ko ƙarfe nawane zata iya tawo wa Saboda dai kar ya rigata gashi har yanzu bai shigo ba dukda taji sanda convey ɗinsa suka dawo, ko ruwa ta kasa sha saboda duk atsorace take, taɓa ƙofar da akayi yasa taji gabanta yayi wani irin faɗuwa lokaci ɗaya ta fara shivering dan tana tsananin tsoron abinda zai mata musamman yanzu da kwata-kwata bata jindaɗin jikinta, tamkar wani zaki haka Imad ya ƙaraso gabanta ji tayi kamar ta nutse a ƙasa ko hakan zai sa ya rabu da'ita, zama ya yi gefen kujera yana ƙare mata kallo from head to toe, hawaye ya fara sauka kan kuncin Fattum saboda two eyes da tayi da wata bulala saurin rufe bakinta tayi jin kuka na neman kwace mata, miƙewa ya yi yana zuwa inda take ya sanya hannunsa guda ɗaya ya ɗagota haɓarta ya tallafa akan hannunsa fuskar nan babu annuri ya ce




"Keeee!"




Sake runtse idanunta tayi saboda tsoro cikin faɗa ya ce"gidan ubanwa kika je?" rawa jikin Fattomah ya fara yi tama kasa furta masa koda kalma ɗaya sai kuka take kamar wacce ke gaban mala'ika, kwafa ya yi ya ce"wato bakida bakin magana saboda kin fita yawon gabanki yar ficiciya dake har kinsan fita wani wajen ki kwana har tsawon kwanaki wato duk abinda za'a yi miki ayi miki bakida asara toh bari kiji Wlh sai kin gane Allah ɗaya ne, daga rana mai irinta yau bazaki sake aikata abinda kika aikata ba ke koda kuɗi kuwa aka ce za'a baki I'll teach you a lesson" fashewa tayi da kuka ta fara zagaye ɗakin tana bashi haƙuri sosai abin ya ɓatawa Imad rai musamman yanda take kukan kamar ranta zai fita baisan sanda zuciya ta ɗebeshi ya fincikota ta waɗo gabansa ba, bulalar ya shiga sauke mata ta ko'ina dan baya ma duba inda zai daka jikinta, kusan 10mins yana aikin dukanta tuni jikinta yagama saki gabaɗaya dan babu alamun tana numfashi duk jikinta ya fashe gwanin ban tausayi, tsaki ya yi sannan ya taka cikinta ya yi ball da'ita ya shige yana fita ya mayar da ƙofar ɗakin ya rufe ya sanya lock sannan ya fice daga gidan gabaɗaya dan baya jin zai iya cigaba da kallon yarinyar musamman idan ya tuna abinda Yusuf ya faɗa masa akanta shine ma abinda ya ƙara sawa ya yi mata wannan mugun dukan da bai taɓa yi mata irinsa ba. Kai tsaye gidan gonarsa ya shige dan nan kaɗai ne yakejin zai samu farin ciki zuciyarsa tayi sanyi, sosai gidan gonar zai baka sha'awa saboda irin abubuwan dake cikinsa kai tsaye wajen da peacock ɗinsa suke nan ya nufa, gamayyar ɗawisu ne aƙalla sunkai guda 50 maza da mata yanda suke buɗe jelarsu kaɗai ya isa ya sanya mutum nishaɗi zama Imad ya yi kan wata farar kujera yana kallonsu. Har aka idar da sallar isha'i Fattomah bata iya tashi ba duk da zuwa sannan ta farfaɗo daga sumar da tayi yanda fuskarta ta koma sai ta baka tausayi dan bazaka taɓa cewa ita ce ba duk fuskarta ta kumbura saboda irin marunka da ya yi mata sannan ko'ina na fatar jikinta ya fashe sai jini ne ke ɗiga ko kuka ta kasa yi sai ajiyar zuciya da take saukewa duk irin yanda tayi attempting na tashi amma abin ya faskara, kifa kanta wanda yake barazanar tsage mata tayi kan cinyarta tana jin wani irin jiri na ɗibanta dukda azaunen da take. Har wajen 10pm tana nan zaune ahankali kuma akaro na babu adadi ta yunƙura da niyyar tashi wata irin ƙara ta saki saboda wani irin kullewa da cikinta ya yi tana jin kamar ana zarar ranta kasa komawa ta zauna tayi sai tsayawa da tayi tana riƙe da cikin nata, buɗe ƙofar ya yi bayan ya yi unlocking nata ya shigo kallo ɗaya ya yi mata sannan ya kama hannunta ba tareda ya ce komai ba suka fita a ɗakin, janta kawai yake domin ba tafiya take ba har sannan kuma hannunta na kan cikinta yana shiga bedroom ɗin ya hankaɗata har saida ta waɗi nan kasan carpet cikin kakkausar murya ya ce




"Daga yau nan ne wajen zamanki kuma ba zaki sake fita koda parlon cikin gidan nan ba saida kiyi rayuwarki anan tunda yar iska kike neman zama kuma koda school billahil Azeem ba zaki sake zuwa ba muddin kina cikin gidan nan saida bayan kin bar gidan nan" duk irin halinda Fattomah ke cike hakan bai hanata rike ƙafafunsa ba cikin dashasshiyar muryata ta ce"dan Allah Uncle kayi haƙuri ka barni naje makaranta wllh bazan sake zuwa ko'ina ba dan Allah Uncle karka hanani" janye ƙafarsa ya yi yana yi mata wani mugun kallo ya ce"idan kika sake riƙeni sai na gwaɗa miki mari" saurin ɗauke hannuta ta yi ya yi tsaki ya juya ya fita. Wani irin raunataccen kuka Fattomah ta fara yi kukane wanda yake tsuma zuciyar mai sauraro kukane wanda yake cikeda abubuwa daban-daban, kukane wanda yake tabbatar da maraicinta a wannan ranar tabbas da tanada iyaye toh haka bazata faru da'ita ƙaddara ce ta rabata da iyayen ta kawota rayuwa inda ake ɗaukarta tamkar dabba dan wani lokacin ma gwara dabba da abinda ake mata, gashi batada kowa wanda zai rarrasheta saida tayi kukanta ya ishe ta tayi shuru abinta haka ta zauna taci kukanta har Allah ya sanya mata dangana da haƙuri bacci ya ɗauketa a wajen.








Kallonsa Ayrah tayi sai kuma ta ce"wai saurin me kake ne?" hular hannunta ya karɓa ya ce"bazaki gane ba ke kam kawai sai nadawo" kwaɓe fuska tayi ta ce"wai kana nufin ba zaka ci abinci ba zaka fita dear?" murmushi ya yi yaja kumatunta ya ce"I'm sorry wlh idan na tsaya makara zanyi kuma kinsan halin Imad dai" haɗe rai ta yi ta ce"ni daman nasan tunda naga kana wannan saurin toh shine ya kira ka shi ya fiye nuna isa wlh ko kai da kake ɗan sarkin baka...." ganin kallon da yake mata ya sa ta yi shuru da bakinta saida ya ɗaura wrist watch ɗinsa sannan ya ce" banason sake jin irin wannan maganar a bakin ki okay?" gyaɗa masa kai tayi ta ce"I'm sorry dear" murmushi ya yi ya ce"ya wuce saina dawo" "bari na rakaka toh" okay ya ce sannan suka fita suna rike da hannu juna. Rai ɓace Aysha ta ce"banda rainin hankali tasan yau akwai paper amma tayi zamanta haka ranar Friday ma tayi ko ubanme take nufi da kanta bansani ba" murmushi Fa'eeza ta yi ta ce"ke kuma kin fiye saurin fusata maybe akwai wani abun kinsan haka kawai Fateemah ba zata ƙi zuwa exam ba" Zainab ce ta ce"wlh kuwa amma mu kirata awaya mana naga kwana biyu bata hau online kwata-kwata" tsaki Aysha ta yi ta ce"ai babu waya a hannunta bare a kirata kuma gashi bamusan gidan da take ba balle muje muga ko lafiya" da damuwa Fa'eeza ta ce"gaskiya kam Allah dai yasa lafiya" Ameen Zainab ta ce sannan suka miƙe dan sannan zasu shiga biology.










Dakyar ta idar da sallar asuba ɗin sannan ta zauna gefen gadon banda raɗaɗi babu abinda jikinta ke mata ko'ina babu daɗi ga bakinta wanda take jin yana yi mata wani irin ɗaci rabonta da abinci har ta manta dan bata iya cin komai ruwa ma dakyar take samu tasha kuma shima sai ƙishirwar ta ƙure kuma bata iya sha da yawa saidai kaɗan hakan yasa duk fatar jikinta ta fara yamushewa kana ganinta kasan babu wadataccen jini da ruwa ajikinta cikin sati ɗaya da tayi a haka koda sau ɗaya Imad bai leƙo da niyyar dubata ba saidai kullum taji alamun tashin motarsa idan zai fita idan har wanda yasan Fattomah watanni uku da suka shige zai ganta yanzu toh tabbas sai ya yi dagaske kafin ya iya gane itace duk tayi baƙi ga wata uwar rama da tayi idanuwanta duk sun faɗa ciki Fattomah wacce ta kasance mai yawan hira da wasa da dariya yau sai tayi kwanaki ba tace uffan ba idan har zata buɗi bakinta to saidai wajen karatun sallah amma ko kaɗan bata hira to dawa ma zata yi hiran???????? Ita ba uwa ba ita ba uba ba Allah sarki kaɗan daga cikin ƙalubalen maraici kenan. Cikin kwantar da murya da son faɗa masa gaskiya ya ce




"Wallahi dagaske nake maka babu amfanin wannan abinda kake aikatawa, yarinya ce ƙarama batasan komai ba ko wace irin tarbiyya kake so zaka iya ɗorata kuma tabi amma wlh duk ranar da Fattum ta fara gane kanta bazaka taɓa iya lankwasa taba, duka baya taɓa sakawa yaro ya daina abu saima tunzurashi da yake wasu lokutan bare kuma Fattomah da batada saka magana ko kaɗan yarinya ce wacce bata damu da rayuwar kowa ba beside kuma batada laifi dan ba itace ta kawo kanta gidanka ba bata cancanci irin wannan rayuwar ba kamata ya yi ka tausayawa maraicinta ka kula da rayuwarta naɗan wannan lokacin ka daina dukanta domin hakan tamkar zaluntarta ka ke, ka dinga ƙoƙarin sassauta fushinka akanta kuma wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login