Showing 1 words to 3000 words out of 131263 words

Chapter 1 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Ayshatuu   

20 Dec 2024

5189

MACE A YAU
Written by Shatuuu
The story of Sulaim and Khulthum, the two besties and bussoms.
Completed
Shatuuu095@wattpad
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
[6/16, 10:31 PM] Anty Fauzar: 💄💅💖
👜👠💖
*MACE A YAU!*
💄💅💖
👜👠💖


01


✍️Shatuuu ♥️


Shatuuu095@wattpad


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION






This page completely, wholly goes to Anty Sumayya...... I hail you


"Abu daya zan fada miki shi ne yanzu kin girma kin mallaki hankalin kanki, Kinsan daidai da wanda ba daidai ba, Kinsan idan akace *budurci* ko virginity Kinsan me hakan yake nufi, nasan Kinsan shi ne Abinda ya zaunar damu gidan mazajenmu har yanzu, idan kika Bari ya kubce miki I'm so sorry to say bana tunanin zakiyi darajar da wadda ta kaishi gidanta zatayi, inason Kiyi tattalin shi don kuwa shi zai fadi tarbiyya da kika samu. Kada wani ya baki abu ki karba Kici, Kada wani ya kaiki alley ko wani isolated area, Kawaye kisan wacece kawarki da kuma wa kike mu'ammula dasu .... Abu na karshe ki kula da addininki sannna kiyi hakuri shi ne rayuwa! "


Se lokacin Mami tayi shiru yayinda Baki daya Sulaim tayi shirun tana sauraren mahaifiyar ta, dago kanta tayi muryar ta Cikeda rauni tace


Inshaaa Allah Mami, bazan Baki kunya ba, zan zame miki abin alfahari!


Kai Mami ta gyada tace


"Allah yayi miki albarka, idan kikayi haka kin gama mana komai"


"Amin" Sulaim ta furta kafin Mami tace


Kije ki shirya da munyi La'asar Zamu fita, make sure kin saka dan kunne da sarka.


Murmushi Sulaim tayi wanda ya fito da dimple dinta hakan yasa tayi kyau sosae dukda maganganun Mami taba ta suke ga kuma kewar gida da ta Fara ji Tun kafin lokacin tafiyar. Mikewa tayi jiki a sanyaye 1 Don komawa dakinta, dakin yana facing wanda ta fito Daga ciki, tura kofar tayi nan take komai na ciki ya bayyana, oil paint ne jikin bangon dakin purple colour wanda yasa dakin yayi dan duhu kadan, gadonta Irin silver poster bed dark purple, se wata resting chair a gefe, Daga Dayan barin akwai study table da kujerar shi sannan walk in closet da kuma toilet, akwai stickers a mammane jikin bangon dakin hakan yasa dakin ya zama very girly.


Tana ta jan kafa ta fada gadon tayi rub da ciki, hakan ya kasance aladar ta duk lokacin da take son tayi tunani ko kuma ta zama emotional haka nan. Ta jima a Wannan yanayin kafin kiran sallar laasar ya tashe ta, mikewa tayi ta shiga toilet wanda komai na ciki yake light blue ta daura Alwala, wani lungu ta isa a dakin ta shimfida sallaya ta Bada farali, Tana idarwa taji ana knocking hakan yasa tace


Yes... Come in please


Yarinya ce wadda shekarunta bazasu wuce sha uku ba ta shigo tace


Anty Mami tace ki shirya.


Kai kawai ta gyada hakan yasa yarinyar ficewa ita kuma ta isa gaban dressing mirror dinta ta Fara assessing kanta, atamfa ce jikinta turquoise green se circle pattern pink, dinkin skirt da Riga ne, kasancewar batada kiba yasa kayan sukai mata cas a jikinta, powder ta shafa ta gyara daurin dankwali ta feshe jikinta da turare sannan ta yafa pink veil ta dauki jaka tayi hanyar fita, kafin ta kai ga bude kofar ta dawo da sauri ta janyo drawer ta dakko dankunne da bracelet sanin matsawar ta fita haka se Mami ta dawo da ita, saboda Mami mutum ce da ta dauki abubuwan mata da muhimmanci.


Tare suka fito Daga dakunan su, seda Mami ta gama assessing Sulaim kafin ta gyada Kai Tace


"ko ke fa gashi kinyi kyau abinki kin fito a mace"


Murmushi kawai tayi saboda ita din ba Mai yawan magana bace, batada surutu ko kadan wanda hakan yake fito da gentility dinta. Jakar Mami ta karba ta rufo dakunan kafin suka sakko downstairs, gidan ya hadu karshe duk yadda zuciya zata kai ga hasashe to abin ya wuce haka. Suna isowa tsakiyar falon sega wani matashin saurayi ya turo main kofar parlour Sanye da kananan kaya wanda sukai masa kyau suka fito da tsantsar yarintar shi, da murmushi saman fuskarsa ya karaso har inda suka ja tunga,


Mami ina zaku je da yammar nan?


Ya tambaya Yana maida dubansa kan Sulaim wadda Ke kallonshi fuska dauke da murmushi,


Inda Jawad ubana ya aikeni.


Baki daya suka saki dariya Don karan Mami da Jawad babu wasa, fuska ya bata yace


Haba mana Mami daga tambaya,


Kallon Sulaim tayi tace


Leka kice dasu Iya Abu mun tafi.


To Mami" ta amsa mata kafin ta rabe Jawad ta nufi wata kofa, Baifi 5 minutes ta dawo suka fita duka su ukun banda tsokana babu Abinda Jawad kewa Mami ka rantse da Allah Kace Mami din kakar shi ce, a haka suka isa bakin wata bakar Prado se kyalli take, suna isa wani daga cikin sojojin dake bakin gate ya iso tareda saluting Mami, kanta ta gyada alamun ta karba tace


Babu damuwa, da jawad zamu fita.


Kanshi ya gyada yace


OK Ma'am


Jawad ya amsa key din ya shiga Mami ta kame a baya yayinda Sulaim ke gefen Jawad, suna tafe suna hirarraki gwanin shaawa.


A gaban wani katon mall yayi parking suka fito, cikin nitsuwa suka taka ciki inda babu bata Lokaci suka Fara shopping yawanci cosmetics ne, toiletries se suka fada boutique din inda Mami ta dinga dibar kaya yawancinsu Abayas ne se kuma suit suit na mata. Sun kusa 2hours a ciki kafin akai musu packaging aka kai har mota Jawad se cin magani yake Don babu Abinda Mami ta siya mishi, daya isheta da mita se cewa tayi


Jawad kudinka ne ko nawa?


Itakam Sulaim murmushi kawai take a haka har suka je gida.


Bayan kwanaki biyar aka gama dukkan shirin tafiyar Sulaim BUK inda anan ta samu admission into Law, kullum zancen Mami daya ne Sulaim ta kula da wayanda take mu'ammula dasu da kuma addininta, sanin son da Sulaim ke yiwa Law batada matsala hakan yasa Bata taba ce mata tayi karatu ba don tasan zatayi.


Mami is very caring kuma Bata wasa da yayanta especially akan Sulaim wadda gani take amana ce Allah ya bata kuma duk idanun duniya na kansu, da zarar wata baraka ta auku zasui dariya tareda Allah ya kara..... This is the world we live in! Da kanta ta hada mata kaya duk Abinda tasan zata bukata seda ta saka mata tareda sake jadadda mata kula da kanta da addininta.


Kasancewar early February ne garin na Kano yayi lum shi babu Rana kuma haka babu zafi se guntun sanyi da bai gama wucewa ba. Cikin bakar Benz Ja'afar ke driving Wanda shi ne male version na Mami saboda yadda kamannin Mami suke prominent akan Fuskarshi, babu yabo babu fallasa haka yake murza steeree Cikeda kwarewa yayinda a gefenshi Sulaim Ke Zaune tana cikin abaya wadda stones suka kawata ta, fuskarta tayi fayau se idanunta da ta boye su cikin dark shade hakan ya bayyanar da pointed nose dinta. Itama fuskarta tayi kyau sede she looks pale. A baya kuma Mami ce Tana rikeda newspaper itama tayi kwalliyarta da yake ita mutum ce me kwalliya. Gefenta Dan gidanta ne Jawad Hannunsa rike da waya Yana ta danne danne ga uban headphone ya saka hakan yasa gaba daya hankalinsa baya cikin motar. Wayarta dake hannun Sulaim ce ta Fara ringing, ba tareda ta duba ba ta mika mata se ji sukai tana fadin


Soja marmari daga nesa, I salute you


Baki daya dariya suka saki Don sunsan Jabir ne his father's inherent the thug of war..... A tsanake yace


Mami barka da warhaka


Barka dae, ya aiki dasu Imratu?


Gaba daya suna lapiya? Kun tafi Kano din.


Kai Mami ta gyada kamar yana gabanta tace


Gamu a BUK road, mun kusa gidan.


Dan tsaki yayi yace


Mami place me on speaker


Haka kuwa akai Sega muryarshi ta cika motar Baki daya, duka suka gaisheahi yana fadin


Sulaim Duk Abinda Subay'a tayi miki just call me kinji?


Murmushin nan dai shi tayi tace


Angama Yaya JB


Se kuma ya koma kan Ja'afar yace


Mutumin make sure you strictly warn Subay'a cewar autar Mami ce Sulaim Kada tayi wani Gigi....


Kafin ya bashi amsa Mami tace


Bakuda kirki matar yayan naku kuke yiwa haka, kanada digit dinsa call him but not through my phone.


Daga haka kit ta kashe wayar aikuwa suka saki dariya kafin suka koma yadda suke.


A unguwar rijiyar zaki dake gefe daga tsakiyar birnin na Kano anan gidan babban yaya Junaid yake inda a tsarin Baba da Mami nan ne gidan da Sulaim zata zauna Zuwa lokacin da Allah yayi. Horn yayi take aka wangale gate din inda farfajiyar gidan ta bayyana, Cikeda kwarewa ya danna motar ciki ya samu gefe yayi parking motar wanda hakan ya janyo hankulan mutane dake cikin gidan. Yara biyu ne suka fito a guje baki daya bazasu wuce shekaru shida da uku ba, gurin Mami suka Fara isa suka dane ta saboda lokacin kowa ya fito, itama hannunsu ta rike baki daya suka nufi kofar parlour, seda sukai sallama aka amsa kafin suka shiga baki dayansu, babu kowa se Nanny din yaran da take tattare toys din da Ahmad yayi wasa dasu, suna zama Sega wata farar mata ta fito wadda shekarunta bazasu wuce 25 ba, kyakyawa ce Irin shouting beauty hakanan take irinsu masu manyan kyau kuma as kana Zaune dasu time zaka gane cewar ba wani mashahurin kyau bane ba haka Subay'a take mace daya tak wajen Junaid uwa ga Muhammad da Ahmad. Kujera daya ta samu ta xauna fuskar ta babu annuri ko daya tace


Mami sannu da zuwa


Inda sabo kowa ya saba da halin subay'a, babu Wanda taki jinin gani sama da 'yan uwan Junaid hakan yake tsoratar Dani Irin zaman da xa'ayi tsakaninta da innocent Sulaim.


Lapiya lau Subay'a ya yaran.


Lapiya.


Daga haka babu Wanda ta kara yiwa magana se Sulaim da Jawad suka gaisheta suma tana ta cika da batsewa ta amsa, dama Ja'afar tasan karya take tayi tunanin zaiyi mata magana Don ya fita zafin kai. Ko ruwa bata basu ba suma babu Wanda ya nema cikinsu se su Muhammad ne Ke ta faman basu labarai yawanci na school da islamiyya.


Har wajen Mintina sha biyar suka shude Bata ce musu Kala ba haka suma, se Mami tace


Subay'a Junaid baya nan ne?


Dago idonta tayi daga Kan wayarta data Ke dannawa tace


Ahmad go call your Papa.


Baki daya tsananin mamaki ya mamaye su kada ma Sulaim taji labari don tasan yadda Matar Yaya Jabir take musu yadda kukasan ta hadiye su Don Imratu is one among millions, unlike Subay'a wadda ita dole yaki ke tsakaninta da dangin miji. Ja'afar ne ya bude Baki yace


Amma ke anyi.......


Sabr! Sabr!! Ja'afar


Mami ta katse shi kanta ta sake girgizawa tace


Don't do that, allow her.


Shiru parlour ya ratsa, Sulaim na kara girmama hakurin Mami cikin ranta, is not like tunda tazo duniya take tareda Mami amma shekaru hudu da tayi tareda su Bata tunanin akwai rana daya da taga wata baraka daga gurin Mamin ko alamun rashin hakuri ko fada she's the best woman she have ever seen a rayuwarta, Shiyasa Mami is her role model.


A hankali Cikeda nutsuwa da tsantsenin inda kyakyawar kafarshi zata taka ya fito Daga wata karamar kofa, dogo ne Yana da tsayi, jikinshi a murmure yake babu alamar rama ko daya, shi ba fari bane haka zalika baya cikin layin bakake, yana Sanye da jallabiya brown me short sleeve, kanshi babu komai banda suma wadda batada yawa kasancewar shi ma'abocin aski, ko cikin mata aka samu mutum me tsaftar Junaid lallai se ayi barka.


Bakinshi dauke da sallama ya iso parlon sede ganin Mami da ahalimta yasa yaja ya tsaya kafin ya maida dubansa kan Subay'a wadda gaba daya hankalinta yana kan wayarta,


Mami kada kice min tun dazu kukazo? Subay'a me yasa baki kirani ba se yanzu? Sulaim ya banga an kawo muku komai ba?


Duka cikin seconds yayi maganar ko nace tambayar, baki daya kallonshi suke da tausayi Don Yana son yan uwanshi musamman Mami da Sulaim. Murmushi Mami tayi tace


Relax Junaid, yanxun nan muka zo, zauna a gaisa ko.


Kasa ya tsugunna yana sauke ajiyar zuciya ya gaida Mami sannan ya samu cushion ya zauna, nan sauran suka gaishesu se kuma hira ta balle, can Sega Subay'a da abinci da drinks itada masu aikinta. Babu Wanda ya kalli abincin bare suci se Jawad ne dake food monger ne baya wasa da abinci.


Subay'a.


Mami ta kira sunanta lokacinda suka Mike don tafiya, dagowa tayi batareda ta amsa ba itama Mamin she wasn't expecting such don haka ta cigaba da fadin


Ga Sulaim na kawo gidanku zata zauna, ban taba rokarki abu ba amma yau na roke ki da Allah ki kulamin da amanata kamar yadda kike kula da Ahmad da Muhammad. Kinsan wacece ita idan kika cuce ta Keda Allah!


Tana gama fadar haka ta nufi kofar fita, duka suka mara mata baya Harda Sulaim wadda ta Fara sharar kwalla.


Shatuuu ♥️
[6/17, 7:38 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU!*


02


✍️Shatuuu ♥️


Shatuuu095@wattpad


🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION


Fitowarta kenan daga daki, fuskarta dau tayi wani Irin haske kamar fitila Sede babu digon kwalliya a fuskar hakan yasa fuskar ta kumbura saboda rashin kwalliyar Don ba sabon Khulthum bane zama babu make up, Duk bala'i Duk masifa Bata taba fita se tayi kwalliya hakan yasa matsawar ta fita batai kwaliyya ba to se ta koma tamkar Marar lapiya.


Gidan karami ne Wanda dakuna kwatakwata biyu ne a ciki kanana wanda Bana tunanin zai cinye gado da wardrobe amma hakan bai hana mazauna gidan alfahari dashi ba. Se Bandaki a gefe da ko kofa babu se buhu, Daga gefe akwai langa langa (zinc) da aka gewaye Dan karamin guri da ya bada kitchen wanda duk ranar da ruwa ya taso bansan a ina matar gidan zatayi girki ba.


Tunda ta fito baki daya babu annuri ko digo saman fuskarta, tana sanye da bakar riga wadda tayi dabbare dabbare, tabarma ta shimfida sannan ta dubi yan matan dake tsaye kikam tace


Bismillah.


Babu musu suka zauna ita kuma ta koma ciki, dakin wata yan kwananniyar katifa ce a shimfide a mata shimfidawa bedsheet, Daga gefe na hangi akwatuna wajen biyar a jibge ga kuma katuwar Ghana must go a Cike taf da kaya, daga gefe kwanuka ne cikin kwando, daidai Bayan kofa ta tsaya inda buhun Lalle yake a jingine ta diba sannan ta tsugunna ta kwaba da sinadaranta, seda ta gama tsaf sannan ta fito inda yan mata biyun ke jiranta, seda suka gaisa kafin ta Fara da wadda nake tunanin Itace babba, Tunda suka Fara bata ce dasu uffan ba se waya da take abinta.


A hankali yara suka Fara dawowa daga islamiyya, biyu Maza se uku mata, ko sallama basui ba suka shigo hakan yasa Khulthum tace


Dan ubanku ku fita a gidannan kuyi sallama.


Babu Wanda ya kalleta cikinsu sema dakin dake gefen nata da suka shige, tsaki tayi ta cigaba da kunshin sega Amira ta fito ta zo inda ake kunshin ta tsaya Don babu Abinda take so irin yadda Khulthum ke designing kafafun mutane Amma Khulthum taki barinta ta koya.


Uban me kike Yiwa mutane Akansu? Dallah bar gurinnan.


Sumsum ta wuce, ta samu dan nesa da gurin ta zauna don Tana hangowa, amma ganin haka yasa Khulthum daukar mafici ta wulla mata tareda fadin


Ke mayyar Inace ne, dallah tashi kafin na karya ki.


Mamaki sosae ya kama yan matan har daya a ciki tace


'Yar President dan Allah ki Bari ta gani mana.


Dake duk wanda yasan Khulthum da 'Yar President ya Santa saboda idan kuka hadu a waje karya kake Kace daga wannan gidan take, sede kayi tunanin Irin yar wani shegen ce baka taba tunanin Wannan kufan ne gidansu ba.


Rabu da ita, wanke wanke zatayi tasan aikinta ai.


Turo Baki Amirar tayi tace


Ki bayar a siyo OMO Kinsan babu.


Batace komai ba ta cigaba da kunshin har ta gama Sega sallamar wata dattijuwar mace ta shigo da kuma alamun Matar gidan ce saboda yadda suke kiranta da Mama. Bakin kofa ta zauna, yanmatan suka gaisheta Khulthum tayi mata sannu da zuwa sannan ta koma gefe tana waya.


Amira maghariba ta kawo Kai ace har yanxu ba ayi wankewanke ba.


Mama to babu OMO a gidan ya kare.


Tsaki Mama ta danyi ta dubi inda Khulthum ke Zaune tace


Ummu bayar a siyo OMO Kada dare yayi.


Kafin Khulthum ta bada ansa A'isha ta fito tace


A hada da kudin ashana da gishiri saboda suma sun Kare.


Wai gidan ubanwa ake kai kayan gidannan ne? saboda ba ubanku ke bada kudin ba yasa kuke almubazarranci. Ni na gaji Wallahi.


Gaba daya babu Wanda ya tanka hatta Maman se ta kunce bakin zaninta ta ciro hamsin tace


Gata nan canjin da na dawo dashi Maza kiyi sauri ki sayo a tsallake.


Karbar kudin tayi ta fice, yayinda Khulthum ta Fara kiran Amir, amsawa yayi tace


Je ka karbo min kayan guga kasan gobe zan fita.


To


Ya fada ya cigaba da tsayuwa, tasan Abinda yake so amma se ta share shi ta cigaba da Abinda take, ganin da gaske bazai je ba ta ciro 200 ta mika masa, murmushi yayi yace


Yanzu kika Yi magana hajiyata.


Daga haka ya fice.


Ana Idar da sallar isha'i yayi daidai da gama shirin Khulthum, tayi wani Irin fittinnan kyau, babu kuma abinda Ke tashi Daga jikinta banda wani kamshi me dadi. Gyara zaman mayafinta tayi ta fito Daga daki, tabarma ce a shimfide inda duka yaran Ke Zaune se A'isha da take bakin murhu tana karasa abincin dare, babu Wanda tace wa Kala tayi hanyar zaure se Mama ce tace


Kulthum ina zakije.


Tsayawa tayi batare da ta juyo ba tace


Ashir ne a waje Yana jirana.


Daga haka tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login