Showing 27001 words to 30000 words out of 131263 words

Chapter 10 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt

Ayshatuu   

20 Dec 2024

5194

Yaya Suhaila ita take aurenki ko Papa ke aurenki. Kin ganni da ne nayi sokanci nake bin duk Abinda suka gindaya min amma ki sani tun ranar da na fahimci cewar ina dauke da cikin nan naji tabbas bazan iya sake yiwa Umman D iskanci ba haka darajar D ta sake karuwa a idona. Yanzu akan D babu Abinda bazan iya ba kuma na yadda na Bata da kowa Don duk ranar da aurena ya mutu babu Wanda zai jajanta min cikinsu kin tuna yadda Yaya Safina tayi. Tunda na haihu nasan darajar da kuma naji idan ace Dana yayi aure matarshi take neman rabani dashi Se inda karfina ya kare, Umma tayi hakuri don haka I'll make it up Kema ki yadda komai ki fuskanci aurenki Sister.


Share hawayenta tayi tace


Ki bani shawara ya zanyi


Ki jira ayi suna Seki koma kafinnan kiyi mishi text ki bashi hakuri sannan kiyi addu'a ki kuma gyara kurakuranki is never late.


Haka Sulma ta dinga bata shawarwari kafin kuma suka fada wasu hirar abinsu na yan uwantaka hakan yasa ta ware abinta.




Mami yau dinner amaryar Ridwan inason Sulaim ta rakani.


Junaid ya fada suna zaune lokacin shida Mami, Sulaim dake gefe tayi saurin dagowaa Sede suna hada ido da Mami tayi saurin dauke kanta. Murmushi Mami tayi tace


Babban Yaya ni na amince ita zaka fadawa.


Wani fari tas yaji ranshi yayi mishi hakan yasa ya dubeta yace


Auta ki shirya 8pm Zamu je.


Se taji bazata iya missing opportunity din ba hakan yasa tace


Tom.


Tunda ta Idar da sallar isha'i ta bude wardrobe dinta tana assessing kayanta, tunani take tayi me zata saka a jikinta, haka kurum take son fitar dashi kunya, so take tayi kyau. Tana tsaye taji ringing din wayarta da sauri ta isa gurin amma maikmakon ganin kiran Junaid as expected se kiran Ja'afar, karamin tsaki tayi ta aje wayar can ta hango wani lace har ta kai hannu zata ciro se ga Mami ta shigo, da murmushi saman fuskarta tace


Troubled?


Kanta ta gyada hakan yasa Mami tazo ta tsaya tana scrutinizing kayan har takai kan wani kyakyawan code net wanda ta dinka mata a wani biki kuma aka fasa Baki daya, gold ne material din me dinkin skirt da Riga se ta dakko wani black scarf ta daura mata bayan tayi touching mata fuska da light make up, take sulaim ta fito tayi kyau kamar ka saceta. Seda ta gama komai sannan suka fito tare har kasa, Junaid ta Fara hangowa cikin milk tuxedo suit se tie Baki da leather covered baki da matching wrist watch. Yayi kyau sosae shima tamkar ka sace su. Baba yana zaune ganin sun fito yace


Is like an wareni fa, se ina haka?


Dariya duka sukayi Mami tace


Ridwan ke kara aure shi ne zasuje dinner.


Kallonsu yayi sosae bai kara cewa komai ba Mami tace


Allah ya kiyaye, Junaid Kada kui dare.


Inshaaa Allah Mami, Baba se min dawo.


Kamshi ya gyada musu yayinda Sulaim tayi waving dinsu suka fita, zama Mami tayi ta fuskanci Baba Don taga akwai magana bakinshi, aikuwa tana zama yace


Kin kusa hada wani auren ne?


Me ka gani?


Ta bashi amsa da tambaya ,


Yaranki is like they're in love amma ko nayi mistake ne?


Kanta ta girgixa tace


I'm not sure, so Kaga bazan ce maka komai ba amma from yadda suke exhibiting wasu signs ina tunanin kamar .......


Is not kamar they're deeply in love with each other, kawai dai ina tunanin basu fahimta bane.


Kai Mami ta rike tace


Amma Ja'afar fa?


Dariya Baba yayi yace


Keda yaranki ni nawa ido kawai.


Shiru Mami tana nazarin maganganun Baba.


A cikin mota babu me magana baki dayansu sunyi shiru se karar ababben Hawa dake yawo kan titin. Junior ne ya fara breaking silence din yace


Yaushe zaki koma Kano?


Saturday


Ta bashi amsa, ita ta rasa dalilin da idan suna tare se tana jin bugun zuciyata yana karuwa sosae, ga wani uneasiness da take ji ko kuma da yayi mata magana se taji dukkan ilahirin jikinta ya amsa, ko kuma ta zama short of words gwara ma idan waya suke.


Basu kuma magana ba har suka isa event center din, cike gurin yake da motoci Nawa Kece raini, guri ya samu yayi parking sannan ya dubeta yace


Shall we?


Murmushin nan nata me kyau tayi masa sannan ta bude kofar suka fito a tare, seda ya rufe kofar da kyau sannan suka shiga shoulder to shoulder. Dake gurin yan Boko ne masu kudi kuma komai a tsare hakan yasa kowa Yana zaune dake Baifi Mintina biyar da Fara event din, suna shigowa idanun MC ya sauka kansu kawai se ya fara fadin


Kaga wasu couples wanda Bayan Amarya da ango Bana tunanin akwai wasu perfect match kamarsu, kallesu fa


Gaba daya wani nishadi ya mamaye Junaid ya dago idanunshi lucky enough ya hade cikin na Sulaim take wani covolent bonding yayi taking place dukkansu seda zuciyoyinsu ta tsaya cak kafin kuma sauke idanunsu hakan yasa hanaklin kowa ya koma kansu Sega Amarya da Ango sun sakko daga inda suke Zaune dan karrama su, hakan yasa duk inda suka gifta kallonsu ake a haka suka zauna, se taga yawancin abokansu in one way or the other tasansu a Faculty yawanci lecturers dinsu ne. Suna ta zuwa suna gaisawa har wani da bakinshi baya shiru yace


Ashe mun kusa zuwa wani bikin, da farko nayi tunanin uwargida ce ai.


Dan murmushi Junaid yayi yace


Bakaga muna kama ba autarmu ce banaso zuwa ni daya.


Autarmu ta maimaita cikin ranta, shikenan matsayinta no any other special matsayi only a sister. Baki daya se taji ta gundura da zaman garin duk yadda ake abubuwa na ban dariya saboda MC akwai barkwanci Amma se taji gaba daya haushin gurin takeji. Duk Abinda take yana Lura da ita amma bazaice ga takaimaiman abinda ya bata ranta ba ganin haka yasa yace


Kin gaji mu tafi ne?


Da sauri ta gyada kanta, se ya Mike itama tabi bayanshi sukayiwa Ridwan sallama wanda se tsokanarshi yake ba tareda ya Bari Sulaim din taji ba.




Shatuuu ♥️
[6/30, 7:28 PM] Shatuuu😍:
*MACE A YAU*
10


✍️Shatuuu♥️


🌈Kainuwa writers Association


#⃣shatuuu095@wattpad


Let's call it a day! We meet in our next class and hopefully there will be test then.


Malamin ya fada bayan ya kammalla darasin shi na wannan ranar, haka ya shiga tattare kayansa cikin briefcase yayinda sauran students din dake cikin ajin kowa Ke hade nashi dukda bawai sun gama classes din ranar bane Amma akwai interval na zuwa aje ayi sallar axahar, Wanda zasu ci abinci suje suci. Seda yazo fita kafin yace class rep dinsu ya bishi.


Sulaim na zaune inda kusan kullum nan take zaune har tana neman maida gurin permanent seat dinta, hada book din datayi taking note a ciki Ta zura cikin wata off white back pack, dake ranar talata ce hakan yasa kowa Yana sanye da black and white, haka tsarin Law school yake a BUK every Tuesdays and Thursdays black and white ne sede wasu ranakun ko Za'a fita ko kuma zaayi mood trial to dole ne a saka wannan uniform din, hakan yakan sa su zama elegant and attractive.


Yan mata uku suka taho inda take Zaune tana niyyar mikewa, Khulthum ce ta Fara cewa


Sulaim tashi mu tafi.


Mikewa tayi ta sabi back pack din a shoulder dinta daya wrist watch din hannunta wanda yake Baki kuma yayi kyau kan shiny caramel skin dinta ta duba. Tare suka fito su hudun Ummu_Sulaim, Ummu_Khulthum, Ummu_Aimana da Ummul_khairi.....the 4 Ummu's. Khairi tace


Kuzo mu fara yin sallah kafin muje neman abinci.


Khulthum ta bata rai tace


Gaskiya ni yunwa nakeji, mu fara cin abincin kawai.


Ke kullum yunwa kikeji baki cin abinci daga gidan ku ne?


Harara ta watsa mata Wanda yasa Khairi yin dariya itakuma Aimana tace


To meye abin hararar tawa, ba gaskiya na fada ba, malama sallah zamu Fara yi.


Itakam Sulaim jinsu kawai take don bawai tayi wani sabo bane ita dasu last week suka dawo Daga mid semester break, ranar da ta dawo ta nemi Khulthum saboda zaman ita daya baya mata dadi to ita kuma Khulthum already tanada su Aimana hakan yasa sukai jamming baki dayansu. Amma har yanxu bata fiya sakewa ba sosae. Massalacin suka Fara zuwa suka bada farali Khulthum tana ta bacin rai wai ba'a girmama opinion dinta ba. Sulaim kam murmushi kawai take musu. Wani joint sukaje nanma kafin aje seda aka bata Lokaci kan ayi deciding gurin da Za'a ci abinci Se sulaim taji tarayyar batada amfani don lokacin tana ita kadai yanxun ta kammalla komai ta koma class amma ya zatayi Tunda ta Riga ta biyosu. A joint din sukai order fried rice da salad se Beef akai da drink. Dama se an gama ake biya kuma kana shiga gurin kasan na manyan yara ne ya'yan masu kudi don hardly kaje baka hadu da wani lecturer ba a gurin, sunsan takan iya girki. Suna fara cin abincin wayar Khulthum ta Fara ringing gaba daya suka kalleta itakam tana kokarin picking tana sakin wani lallausan murmushi


Kina ina ne?


Shi ne tambayar da Hu ya Fara mata, cikin daidaita muryarta ta fada masa joint din da suke. Tana aje wayar Aimana tace


Wa zaki rakito mana?


Khairi wadda wasu abubuwan nata na shige Dana Khulthum tace


Batta yazo dama yau purse dita babu nauyi, Dan kun nace Keda Sulaim ne amman yau banyi niyyar Zuwa gurinnan ba.


Dariya Sulaim tayi ta cigaba da cin abincinta saboda itama yau yunwar takeji Don Junaid Nada class din safe yau hakan yasa ya figo ta bata wani Yi breakfast din kirki ba. Suna tsaka da cin abinci Hu ya shigo shida abokansa kusan zan ce muku babu Wanda a gurin bai san lucky Hu ba, har wani kirari ake mishi Kaga yaro me kudi kana gudu luck na binka, yaro me tashe. Kusan bawai a faculty dinsu yayi suna ba entire new site ansan Lucky Hu saboda yadda yake da yanmata idan baiyi dating dinki ba to yayi flirting kawarki haka abin yake Shiyasa ko award night ake shi ke daukan most popular a cikin faculty. Abokansa uku suna bayanshi, Tunda ya shigo Khulthum baki daya ta rasa nutsuwarta, ta gyara nan ta matsa can har Aimana tace


Dallah ki nutsu se kace tsutsa kin kasa zama guri daya Bari naga waye wannan saurayin.


Me zasuyi banda dariya Don Aimana ita ke maganin rawar kan Khairi da Khulthum. Gefenta ya tsaya tareda dubansu Sulaim yace musu


Sannunku!


Suma sannu sukai mishi daidai lokacin gama cin abincinsu Aimana wadda tana kallon Hu ta ganeshi kasancewar faculty dinsu daya da yayanta kuma yana yawan bata labarinsa, mamaki sosae tayi haka yake kamar me charm indai yace yana so to dole ne mutum ya amince dukuwa da sanin halinshi da sukai, mikewa sukai Don biyan bill ya dakatar dasu yace


Paid! Kuna kawayen Her Majesty ta yaya zaku biya kudin abinci.


A'a Khulthum se aka Fara blushing Irin taji kunyar nan, itakam Sulaim shiru tayi tana jiran jin Abinda sauran zasu fada. Aimana ce tace


No Dan Allah Karka Kara biya mana , zamu biya namu ita se ka dinga biya mata. For today thank you!


Tana fadin haka taja hannun Sulaim suka fito ita kuma Khairi ta zauna godiya, yayinda Huzaifa ya bisu da kallo saboda bai taba katari da irinsu ba, kawayen yan matanshi shishige masa suke amma wannan har akan Fuskarshi take fada masa bata bukatar payment dinsa.


A class Khulthum ta shigo lokacin already Ridwan was in class, dayake period dinsa ce yana taking dinsu wani course shima banashi bane mutumin bazai samu Zuwa bane Shiyasa ya turoshi, so ranar ne ranar farko da ya Fara shiga class dinsu. Tana ta yauki ta shigo class din itada Khairi, bai ce musu komai ba seda t
Suka zo tsakiyar aji yace


Hey! Get out of my class, irresponsible ones.


Simsim kamar an dakesu haka suka fito Khulthum tana ta Balai yaci musu mutunci, se bayan La'asar ya fita kowa ya tashi ya fito, tunanin Aimana da Sulaim Khulthum tuni ta tafi dake Khairi a hostel take su uku suna day. Tana hangosu ta nufo su, Sulaim ce ta Fara fadin


Me yasa kuka zo late gashi yayi yabbing dinku.


Tsaki Khairi tayi tace


Rabu da shege, ya dauki tsayi kamar Daren bakin ciki.


Dukda maganar batayiwa Sulaim dadi ba ganin laifinsu ne for coming late, banging into the class without permission seda tayi dariya wai tsayi kamar Daren bakin ciki. Khulthum ce ta Fara magana ranta a bace tace


Aimana ni banji dadin Abinda kikayiwa Huzaifa ba, har zakice wai ya rike kudinshi, don kin samu ya kalleki ma.


Baki sake Aimana take kallon Khulthum kafin tace


Ya kalleni? Na rokeshi ne? Ke nifa Bana son wani kato ya biya min abu har idan zan wuce yana tunanin favor yayimin, kuma Inace cewa nayi ya biya muku nida Sulaim Bama bukata.... Ke bana son nonsense stuffs kinji.


Ganin ta dauki zafi yasa Sulaim tace


Kai friends basa fada, Dan Allah kui hakuri meye a ciki.


Khulthum dai batace komai ba se juyawa tayi ta nufi inda yake jiranta kullum ta bi bayanshi ta fada mota suka tafi, Khairi ma sallama tayi musu ta tafi hostel itada wani gaye dan class dinsu. Se ya rage Aimana da Sulaim wadda har lokancin mitar abin take, suna tsaye Sega kiran Oga Junaid ya shigo gabanta ya fadi don ta rasa me ya hanata kiranshi tace ta gama kamar yadda suka Saba bare yau tasan har ta gama lectures bai tashi ba Balle tace ko Yana gida. A hankali kamar me tsoro ta Kara a kunne tace


Yaya na gama.


Ki samu napep ya kawoki na wuce Tun dazu, zamuje shopping da Subay'a


Zaro idanta tayi don bai taba barinta ba ko ya tafi se ya dawo ya dauketa hakan ya kular da ita ba tareda ta amsa ba ta kashe wayar, kallon Aimana tayi tace


Bari na tafi me daukan nawa baya kusa.


Kai ta girgixa mata tace


Yanzu Yaya Nu'uman zai zo se mu Baki lift.


Itama kanta ta girgixa tace


A'a gaskiya ki......


Bata karasa ba Se gashi yayi parking a gefen su hakan yasa taja hannunta suka isa bakin motar, baya ta budewa Sulaim ta shiga ita kuma tayiwa kanta masauki a gaba, waya yake Don haka ko gaisuwarsu bai amsa ba in fact baisan Sulaim na ciki ba a haka suka fito Daga BUK, kafin su karaso AA Marmaro inda nan ne kwanan gidan Junaid Aimana tace


Sulaim kiyi mishi kwatance.


Aje wayar yayi yace


Keda waye.


Kafin ta bashi amsa ya hango Sulaim ta jikin mirror, bai kalla fuskarta da kyau ba se side view dinta dake gefen window take kalla, gabanshi yaji ya fadi take zuciya ta kwadaitu, muryata yaji a hankali tace


Kwana ta gaba zan sauka.


Kasa furta komai yayi saboda yadda ilahirin jikinshi ya amsa Daga Wannan furucin da tayi, seda Aimana tace


Yaya Nu'uman magana ake maka


Naji


Ya fada suna zuwa Kwanar Tace zata sauka se ta karasa tunda babu Nisa, godiya tayi musu a lokacin ya samu damar kare mata kallo, itama kuma haka, fari ne sosae kamar yadda Aimana take babu laifi yanada kyau. Suna amsa mata godiyar ta nufi layinsu, tafiya kadan ta isa gidan, tura karamar kofar tayi ta shiga ta gaida maigadin sannan ta nufi parlourn, kafin ta kai ga budewa aka bude, Junaid ne shida Subay'a wadda ta dawo tun Kwana hudu da haihuwar Sulma ta bashi hakuri sosae tareda nuna nadamar ta, shi bashida matsala hakan yasa ya manta da abin suka cigaba da rayuwarsu. Bayansu Ahmad da Muhammad ne da dukkan alamu fita zasuyi, seda ta Fara gaida Subay'a sannan ta tsaya Seda suka fito sannna Junaid ya dubeta yace


Ya akai se yanzu kika dawo.


Kanta ta dan dauke Daga kanshi tana jin yadda yake ke beating wanda ta rasa dalilinshi kuma abin is only idan tana tareda Junaid ne tace


Babu komai.


Tana fadin haka ta Kara da fadin


Allah ya kiyaye


Tayi ciki abinta, shiru yayi a gurin ya bita da kallo se yaji kamar bataji dadi ba, se zuciyarshi take tuhumar shi akan ya bata mata rai ne? Kallon Subay'a yayi wadda tuni ta isa gefen motarshi ya Dan Daga murya yace


Nayi mantuwa Bari yanxu zan fito


Kanta ta gyada mishi, shikuma ya koma cikin parlour, straight dakinta ya nufa ya kwankwasa kofar. Itakam Tunda ta shiga kujera ta fada ta zauna tayi shiru haka kurum taji ranta a tsananin bace kuma babu abinda take bukata tayi irin kuka, kafin ta gama tunanin aka Fara knocking tasan su Atika ne a ranta tana mitar Daga dawowar mutum Za'a isheshi, kofar ta bude se taga Junaid a tsaye Yana kallonta, kanta ta dauke tareda pouting face dinta, se yaga tayi mishi wani kyau yaji if to say it's okay he'll hug definitely hug her dan fuskarta ta nuna ranta a bace yake amma babu dama hakan yasa yace


Shopping zamuje kiyi min text din abinda kike so kinji?


Unconsciously ta buga mishi Harara wadda tayi cikin sa'a ya gani hakan yasa ya zaro ido da mamaki amma se ta dauke kanta tamkar ba ita tayi ba tace


Tohm.


Tana fadar haka ta tura kofar ta shige, kanshi ya shafa saboda ba haka zuciyarshi ta aiko shi yayi ba, ta aiko shi yaji damuwar abinda take so sannan ya fada mata abu me dadi, who knows he will mess up but he couldn't! Bazai iya ba he lacks wannan courage din.


Fita yayi suka tafi Yana ta mamakin shi Sulaim ta harara, yayinda take kwance har aka kusa kiran maghrib sannan tayi wanka ta bada farali, Tana idarwa wayarta ta Fara ringing, Bro ta gani hakan ya tabbatar mata Junaid ne se ta samu kanta da kin picking, sau biyu yana kira Tana kin dauka shima se ya hakura. Can Sega kiran Ja'afar ya shigo, Kwana biu nan se taji yau tana daukin jin muryarshi, cikin silvery voice dinsa yace


Ina gate gidanku fito mu gaisa.


Da gaske!


Ta tambaya Tana jin wani nishadi from no where


Come and see

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login