Showing 33001 words to 36000 words out of 131263 words
Chapter 12 - MACE A YAU Document By Shatuu from kanopost.ng.txt
khairi tayi cikin jin dadi tace
Haba! Shiyasa Naga Bakin ya kasa rufuwa. Kinga lecturer wai se karfe biyu zaiyi holding class din shima ba Zuwa zaiyi ba idanshi zaizo wani Dr waye? Oho!
Ta fada Tana son taunawa, itadai Aimana na tsaye batace uffan ba seda suka gama tace
Muje Nan cikin quarters akwai gidan yayata mu zauna kafin time din.
Seda sukai nisa sannan Khulthum tace
Banga Sulaim ba ko bata zo ba?
Aimana ta girgixa Kai tace
Tazo Tana class
Class? Kuka baro ta? Ita kadai?
Tsaki Aimana tayi tace
Meye zai kamata, kamar tana da damuwa ne munyi munyi taki biyo mu Shiyasa muka barta.
Kai Khulthum ta kada amma se taji babu dadi cikin ranta har zuciyarta take son Sulaim, there's something unique about her. Aimana dake tsakiyarsu ta kalla Khulthum in a polite manner yadda tasan words dinta bazasu Bata ran Khulthum ba tace
Nikam Khulthum me yasa kike wearing makeup zuwa school ne? Kwatakwata bai dace ba se kace ba professional course kike taking ba.
Kafin Khulthum ta bada ansa, khairi tayi caraf tace
Ke Aimana ina ruwanki? Bakya gani kiyi shiru ne?
Hararar ta sakar mata Tace
Nasa bakinki, I taught ba da ke nake ba, Khulthum as I was saying ki rage kwalliyar nan batada amfani a matsayinki na student. Kinada kyau basai kin hada da artificial fixations dinnan ba shi ne banbancin ki da gidan biki.
Khulthum batace komai ba don ta rasa abin fada se can tace
Kwaliyya ai Itace mace, in the first place Meye ruwanki da kwaliyyata so bakyayi shikenan ni bazan yi ba? Rayuwarki daban tawa daban.
Very calm ta fadi hakan kamar ba Khulthum ba, Aimana taja bakinta ta tsuke tana nadamar dalilin da yasa tayi magana.
Kwanaki hudu kenan da faruwar incidents din Sulaim, Ja'afar da Junaid... Love triangle kenan.... Ta rame tayi xuruxuru saboda yadda ta kwarzabi Rayuwarta she's going through a hard phase, ita kanta idan kace Meye damuwar ba lalle ta sani ba Sede mu hadashi da Marin Junaid don har lokancin ba sui communicating da Ja'afar ba ita tayi parking dinsa a side. Junaid kam ba'a magana ta hukunta shi ko kuma nace tana hukunta shi kamar yadda take hukunta kanta ba tareda sanin ta ba. Shiyasa gabaki daya ta zama moody ta rasa me yake mata dadi gaba daya kanon ma ta fita a kanta sede babu damar tafiya Don kuwa 2 weeks ya rage a fara exams. Tana nan Zaune a class itada daidaikun mutane yawanci karatu haka itama ta daure ta samu tayi karatun hakan yasa ta danji dadi a ranta. Mikewa tayi saboda yadda cikinta yake gugi, jin hakan yasa ta tuna yau Batayi breakfast ba kuma jiya ba taci dinner ba kuma ga mamakinta Junaid ko takanta bai bi ba hakan shi yake sakawa take kara zama very mad at him, yaya zaiyi laifi kuma ya fita fushi wannan ai son kai ne, da hanzari ta Mike ta dauka handbag dinta ta fita a class din don taci abinci wayarta dake rike a hannunta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, a mamakance ta sake duba wayar Dan tabbatar da cewar Junaid ne me kiran, shi dinne kuwa haka kurum se taji tamkar ana cire mata damuwar dake dankare a cikin ranta da ziciyarta.
Ni dai nace magulmata...... Halo wattpaddians double, triple, quad appreciation goes to you for the comments and votes. Thank you very much..... I'm proud of you and as such d page is completely yours.
Shatuuu♥️
[7/5, 11:46 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU*
13
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
*Hello pipu of whatsapp...... Here's your page habibties I'm very grateful..... Have the page*
Se kawai ta samu kanta da kin picking call din a ranta tana fadin ko iya haka aka tsaya babu damuwa tasan Rabin damuwarta ta tafi, ita kanta tana mamakin halin da ta jefa kanta a ciki, yadda ta dauki Junaid ta bashi wani mugun mukami a zuciyarta..... Wayarta ta sake ringing a Karo na biyu hakan yasa batada wani zabi face tayi picking, kafin tayi magana cikin muryarshi me Amon dadi yace
Ina jiranki a office yanzu.
Ta bude Baki dan protesting taji ya kashe wayar babu yadda zatayi haka ta juya ta nufi offices din dake cikin faculty. Kafin ta isa kiran Yaya Jb ya shigo, soja kenan marmari Daga nesa. Dan tsayawa tayi ta amsa call din suka gaisa yana tambayarsa ko akwai matsala ta nuna mishi babu komai sannan yace mata
Ayi mana addu'a zamuje Riyadh ganin wani gynae ni da yayarki.
Kanta ta gyada kamar yana kallonta, Tana jin tausayin Yaya Imratu da Ya Jb komai is abundant cikin rayuwarsu haihuwa ce kawai Allah bai kawo ba, to dama mutum Tara yake ba goma ba amma tasan ba kowanne so bane yake zama samu.
Allah ya kiyaye Yaya yasa a dace mu samu baby.
Da sauri yace
Amin Lil, wannan adduar taki ina fata ubangiji ya amsa ta. Yayarki na toilet me zance mata?
Kace ina gaisheta, safest trip and Allah's khair.
Murmushi yayi sannan sukai sallama kafin ta ja kafarta Zuwa office din Junaid, haka kurum se zuciyarta ta Fara increasing bugun da takeyi wanda kullum idan hakan ta kasance se ta rasa gane ko dai she's psychologically sick ne ko kuma me? Itakanta tayi iyakar tunani akan me yasa take jin ireiren stuffs dinnan idan ta doshi inda Junaid yake, Sede ta rasa amsar ta kuma rasa me Bata.
Seda tayi knocking yayi mata izinin shiga kafin ta murda kofar ta shiga, yana zaune kan kujerar shi, table din yana cike da takaddu daban daban, ya cire coat din saman se white long sleeve shirt a jikinshi, tie dinma yayi loosing dinshi kadan, idanunsa cikin farin medical glasses wanda yasa yayi kyau sosae dukda Fuskarshi na nuna gajiya amma hakan bai hana kyanshi, cikar haiba da kuma zati fita ba. Tunda ta rufe kofar ta tsaya a gurin ba tareda tace dashi komai ba, se lumshe idonta da tayi saboda yadda Acn office din ke aiki babu hutawa, se taji inama tayi bacci. An kusa Mintina biyar kafin ya aje pen din hannunshi tareda mikewa yayi baya da kujerar ya iso tsakiyar office din tareda zura hannayenshi cikin aljuhun wandonshi yace
Zo ki zauna.
Babu musu ta taho kamar wata chameleon ta zauna kan soft sofas din da suke aje daga extreme din office din. Seda ta zauna kafin ya iso shima ya zauna Yana dubanta Irin kallon da bai taba yi mata Irinshi ba, kallo ne Wanda ta ko ina ta kasa fassara shi se ya zamana idanun nashi sun takura mata ainun, taji tamkar ta Mike ta fice, ga zuciyarta is adding more issues to her yadda take bugawa tamkar zata balla chest wall dinta ta fito. Bakinta ta turo mishi hakan yasa yayi murmushi sannan yace
Sulaim
Tamkar magnet haka muryar ta fito wadda ta tilasta mata dole seda ta dago ta zube idanunta cikin nashi. Yadda taga idanun nashi yana wani maiko tamkar an disa mai ciki ga wasu molecules dake fita daga nashi idanun suna piercing Sclera and cornea dinta yasa babu Abinda ta iya yi face ta maida kanta kasa. Murmushi me taushi ya kuma saki yace
Me yasa kika daina min magana? Me yasa kika daina cin abinci?
Bata dago kanta ba bare ya saka ran zata bashi amsa se ma yatsunta ta dinga wasa dasu. Ganin haka yasa ya sauke ajiyar zuciya me nauyin gaske tareda sake tattara hankalinsa kanta yace
Saboda na mareki ko? I'm sorry.... I'm very sorry I shouldn't have been mad na yanke hukunci cikin fushi I'm sorry kinji.
Maimakon magana kawai se ta Fara kuka kamar wadda aka tuna mata wani abu, tayi cupping fuskarta a tafukan hannayenta tana kuka Wanda ita kanta bata san dalilinshi ba,
Oh God! Sulaim please ki daina kukan nan bakisan yadda kukanki ke damuna ba.... I said I'm sorry ko na juya fuskata ki rama.
Dago idonta tayi ta kalleshi tareda tunzura bakinta tana share hawayen fuskarta, to meye abin kukan ta tambayi kanta, dadi kuma ta dinga ji tareda jin komai ya wuce tunda har yasan yayi laifi kuma ya bada hakuri
Zaki rama din na juyo?
Ya fada cikin wani Irin sauti Wanda seda yasa taji ilahirin Tsikar jikinta ta zuba tareda lumshe idonta se kuma ta turo Baki tace
Ni bance ba
Nima ban ce ba Sede idan baki hakura ba feel free ki rama indai zaki daina fushi Dani kinga we're even.
Tissue box din dake aje Kan glass center table din ta dauka ta goge fuskarta kafin kuma ta kalleshi ta sakar murmushi, shima murmushin yayi mata yana jin wata nutsuwa ta baibaiye shi sede wata zuciyar na ganin me yasa zai zauna Yana apologizing ma karamar Yarinya wannan ai ya siyarwa kanshi raini ne, Baibi takanta ba don idan ya biyewa thoughts dinnan haka zasuyi ta zama da Sulaim bai gyara barakar da ta wanzu tsakanin su ba har Ja'afar yayi nasarar dauketa. I mikewa yayi ya koma mazauninsa tareda daukar wayarshi yayi kira dake hankalinta kwatakwata baya kanshi tana nan tana lissafi farin cikin da Lokaci daya ya zama ta bata ji abinda yace ba se gani tayi an shigo an hada lunch a inda take Zaune Kan table. Dagowa tayi ta dubi abincin sannan ta dubi Junaid wanda ke sallamar dan aiken kafin ya dawo da hankalinshi kanta, suna hada ido ta dauke kanta tareda yin wani side murmushi shikam kanshi ya girgixa yace
Fara ci gani nan sakkowa .
Babu musu saboda bata kasance me yin musun ba ta bubbbude wrapped plates din dake gabanta, jollof rice ce da hadadden salad se pepper soup na kayan ciki. Nata ta zuba cikin separate plate ta Fara ci, saboda yunwar da take ji gani take Bata taba cin abinci Irin wannan ba, Seda ta kusa gamawa kafin ya sakko yayi joining dinta. Massalaci ya fita ya barta tayi a office din, yana Dawowa daya da Rabi tayi gashi ta dan kintsa mishi kan table din nashi da shelf dinsa. Yaji dadi har yace
Tukwicin abinci na aka min gyara.
Dariya tayi siririya kafin ta Mike tace
Yaya na tafi class, munada class by 2pm.
Kanshi ya gyada yace
Better go, we meet after.
Ficewa tayi shikuma ya tsaya Yana kallon ficewar tata seda ta rufe mishi kofar kafin ya saki murmushi tareda shafa kanshi a ranshi yace
Junaid what's all this?
Shima baisan amsan ba haka ya Fara shirin abinda zai aiwatar. Sulaim na fita taji tamkar irin born again dinnan zuciyarta tayi wasai kamar anyi mata albishir. Tana zama a sit dinta mutanen ta suka shigo baki daya inda take suka zo.
Kinci abinci?
Aimana ta tambayeta, murmushi tayi tace
Naci, kun dawo?
Khulthum ta gyada Kai kafin suka Fara hira ko nace yawanci suna brainstorming ideas ne akan karatun da sukai babu laifi Baki dayansu kwari ne kansu na ja. 2pm daidai ajin yayi tsit saboda shigowar lecturers guda uku na gaba kana kallonshi kasan ya manyanta na bayanshi is a well known personnel amma a gurin Sulaim kadai hannunsu na rike da Apple System dinshi wannan gajiyar dake tattare dashi lokacinda ta sameshi a office yanzun babu se kamar farin ciki da yake tattare dashi though babu wani fara'a a tattaredashi amma kuma Sulaim ta fahimci hakan. A bayanshi level coordinator dinsu ne . Gaba daya ajin yayi tsit level coordinator yazo ya gabatar da Prof shu'aibu as Deen din faculty, cikin nitsuwa ya basu welcoming address wanda bai samu yayi ba Don lokacin matriculation Dinsu baya gari so bai samu yaje ba. Ya basu fatherly advice sannan ya dan tabo musu Irin gwagwarmayar da yasha wajen karatu, don haka yake basu shawarar they should never give up no matter what. Yana gamawa ya fice saboda meeting da zasui da VC a haka ya fice sannan level coordinator ya bawa Dr Junaid damar yin magana.
Yana tsaye gaban podium din, ya gyara zaman glasses dinsa, ya kunna system dinshi kafin ya dago idanunshi masu haske ya dubi students din dake Zazzaune.
Khulthum Tunda ya dago ta bude Baki tare da fadin
Khairi kinga wata halitta?
Da sauri Sulaim ta kalleta, se taji Khairi tace
Oooooo dama akwai Irin wannan charming guys din a Faculty nan, gaskiya ya hadu.
Sulaim Baki daya se taji haushi baki daya ya rufeta, ga tana ta kallon yadda Mata ke kallonshi da admiration fal idanunsu wani Irin nauyi taji kirjinta yayi mata kawai se ta janyo wayarta ta kunna data ta shiga instagram, lokaci Zua Lokaci tana jiyo muryar da take ratsa mata ilahirin jikinta sede ta kasa dago idonta ta kalleshi saboda batasan kallon da mutane Ke yi mishi Amma baki daya hankalinta yana kanshi. Duk yawancin Maganganunshi suna kan exams din da zasui da rules da suke guiding exams. Yana gamawa ya bada room for question kawai wata budurwa very courageous tace
Sir we need to know your name
Dama kanshi Yana kan wayarshi hakan yasa seda ta maimaita kafin ya tuna cewar bai yi introducing kanshi ba, a nutse yace
I'm Dr. Junaid Lukman Birnin kudu, I'm a lecturer here amma Bana daukar class dinku se kunzo level 3, I'm the exam officer of the Faculty.
Daga haka aka ta mashi tambayoyi yana bada amsa amma ko sau daya Sulaim bata bari sun hada idanu ba Duk yadda yake son hakan saboda tun zuwanshi class din ya marking inda take. Seda ya gama komai kafin ya basu best wishes sannan ya fice. Daga haka class coordinator ya sallamesu, suna fitowa taga message din Junaid akan ta jirashi yanzu zasu wuce gida. Tare suka fito duka su hudun kuma Monday Za'a Fara exams don haka sukaiyi akan zasui karatu su hadu Washegari.
Sulaim tace
Gaskiya I'm not sure idan zanzo amma dai zan fada ma yaya idan ya yadda.
Aimana tayi dariya tace
Kanwar Yaya, kullum yaya zanso naga wannan Yayan.
Dayake Sulaim Abinda tafi ambata kenan Yaya, tayi dariya a ranta tace ai yau kowa yaga Yaya. Sunanan tsaye Sega Motar Hu ta iso kafin ta Daga kafarta kamar Da hadin baki Sega Ashir akan Lifan dinshi sannan da azababben guy cikin azabbabiyar mota shima ya iso, idanu a waje ta dubi Sulaim wadda ita tasan Ashir saboda sun taba fita tare suka hadu dashi anan yasan Sulaim itama ta sanshi, Hu kuwa Duk sun sanshi se Yusuf Wanda dazu ta hadu dashi. Kallon Aimana tayi tace
Ya zanyi dan Allah?
Aimana ta dauke kanta don batasan me zatace da ita ba Balle Sulaim wadda Baki daya mamakin abin take amma ga mamakinsu se kawai ta nufi inda Hu yake da murmushi da komai tace
Yau duka bamu hadu ba Inata missing dinka.
Murmushi yayi yace
I missed you more, Munje ko?
Kanta ta girgixa tace
Ga uncle dina can yazo daukata muje ku gaisa.
Tana fadar haka ta nufi inda Yusuf ke tsaye ko kallon inda Ashir yake Batayi ba se kallon ta yake mamaki kamar ya kasheshi, Tana zuwa suka gaisa kafin Hu ya iso tace
Ga brother na ku gaisa yazo daukata.
Yana zuwa suka gaisa tabi Yusuf suka tafi Hu yaja motarshi yayinda Ashir ya iso inda su sulaim suke seda suka gaisa, Sulaim tayi introducing dinsa ma su Aimana shima haka,
Su waye wanda Khulthum taje gurinsu suka fita a mota?
Yayi directing tambayar ga Sulaim, kallon Aimana tayi tace
Answer him please.
Hakan yasa ya kalla Aimana yace
Aimana Ku Fada min Kada Ku damu ba zance mata ku kuka fada ba, sannan na dade da sanin tunda Khulthum ta samu admission halayenta sun canza, gaba daya ta dauki wata rayuwa da bata taba kuma bata dace da ita ba.
Kafin Sulaim tayi magana kiran Junaid ya shigo ta musu sallama akan ko meye Ashir yayiwa Aimana bayani.
Shatuuu ♥️
[7/6, 7:09 PM] Shatuuu😍:
*MACE A YAU*
14
✍️Shatuuu♥️
🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION
#⃣Shatuuu095@wattpad
Disposable cup din dake Cikeda da sassanyan ruwa ta kafa bakinta akai Seda ta shanye tas kafin ta wulla cikin bin dake gefen table dinta. already ta kamalla tattara kayanta lokaci kawai take jira yayi ta samu ta koma gida don Baki daya yau a gajiye take tubus kamar wadda Tasha wani aikin. wayarta da tuntuni take cikin hand bag taji vibration dinta hakan yasa ta ciro ta ganin sunan Beloved Hajiya yasa tayi murmushi yau Baki daya bata kirata ba, seda ta Bari ta katse kafin ta kirata
Hajiya barka da yamma
Barka ka dai Subay'a
Hajiya ta fada Daga Dayan bangaren,
Ya aiki ko har kun tashi?
Kai subay'a ta girgixa tace
Muna kokarin tashin dai.
Allah ubangiji ya taimaka ya muku albarka Baki daya.
Cikeda jin dadi Subay'a tace
Amin Amin Hajiyata.
Itama Hajiyar taji dadi Don tanason yadda Subay'a ke yi mata.
Dama nace idan kin samu dama zuwa anjima ko zaki shigo akwai muhimmin abu da Zamu tattauna.
Dan zaro ido Subay'a tayi tace
Ba dai wani abunne ya faru ba ko hajiya?
Murmushi hajiya tayi don haka sauran ma sukai
Babu komai, kawai dai bazan iya jira bane har Zuwa Sunday.
To shikenan Bari yanxu zanzo.
Tana kashe wayar ta Mike da kayanta tayiwa colleagues dinta sallama Don suma shirin tafiya suke , seda ta shiga mota sannna ta nemi number Junaid ita Baki daya ta manta warning din da yayi mata akan se ta zartar da abu kafin ta sanar mishi. Lokacin Sulaim da Junaid sun manta sun fita saboda dadewar da sukai da komawa gida, yana parlonshi Yana reviewing questions da aka